Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Yawan Fitan Ruwa Mai Kaikayi Daga Farji

MAGANIN YAWAN FITAN RUWA MAI ƘAIƘAYI DAGA FARJI

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam ina yawan samun fitar ruwa a farji kuma yana ƙaiƙayi dan ALLAH mene ne, kuma mene ne maganin ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumussalam........ Lalai wannan shine infection dan haka kibi wayannan hanyoyin dan maganceshi. Ki gwada ɗaya daga cikin wadannan:-

1. Ki samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya ɗan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau ɗaya. Yana maganin budewa da kaikayi.

2. Ki samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

3. Ki samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection.

4. Ki samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a haɗa waje ɗaya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya ɗan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.

5. Ki samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.

6. Ki dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a ta ce, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.

7. Ki samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.

8. Ki samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su tayi Yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni'ima da magance duk

matasalolin sanyi.

9. Ki samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma'ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau ɗaya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.

19. Ki samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje ɗaya. Mace ta dinga shan cokali ɗaya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni'ima.

11. Ki samu Ciyawar Kashe-Zaƙi da Farin Magani sai ta haɗa waje ɗaya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali ɗaya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.

12. Ki samu garin saiwar Zogale se a debi cokali ɗaya adafashi da 'yar jan kanwa se adinga sha. Yana maganin fitar Ruwa ta gaba in sha Allahu.

Allah Yasa Adace.

Jamila Dahiru Muhammad

(Muhsinat Datti)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments