Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Ta Ciro Nono Ta Shayar Da Ɗanta A Gaban Yan Uwanta Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mace tana shayarwa se kuma ɗanta yana bukatar ta bashi nono amma tana cikin mutane sedai duka matane danginta shin zata iya ciro nononta agabansu tabashi????

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh idan duka matane a wajan kuma duk matan musulmaine sannan babu wata fitinarda ake tsoron faruwarta dan ta ciro agabansu tabashi nonon toh wannan babu lefi in sha Allahu ya halasta.

Amma wasu daga cikin malamai suna ganin cewa idan acikin matan akwai wacce ba musulmaba toh nanma suna ganin be halastaba a ra'ayin masu sashen malamai domin ance kada mata su bayyana adonsu se acikin mata musulmai.

Amma wasu malaman kuma sukace koda ace cikin mata kafirai take ya halasta tabashi nonon agabansu domin waccan ayarda wasu Malamai suka yi hujja da ita toh tana maganane akan cewa mace zata iya bayyana adonta agaban mata danginta a halitta koda kuwa ba musulmai bane. Kuma wannan ra'ayin na biyu shi ne abunda muke akansa in sha Allahu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments