𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum Don Allah malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikum Salaam; Toh ɗan'uwa Allah Maɗaukakin sarki ya
halatta maka jin daɗi daga dukkkan ɓangarorin jikin Matar ka, in ban da dubura ko kuma saduwa
da ita lokacin da take cikin haila, don haka ya halatta ka tsotsi nonon ta
mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, toh malamai sun yi saɓani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu:
1. Ya Halatta; Saboda kasancewar nonon da yake
haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda faɗin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam
"Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa",
Bukhari lamba ta; 5102, ma'ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono,
saboda shi ne abincin sa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don
haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan
malamai.
2. Bai Halatta ya sha ba; Saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace tom ta haramta a gare shi, domin Annabi Muhammad
Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim,
don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta:
2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa
idan babba ya sha nono toh zai yi tasiri wajan haramcin aure. Gaskiyar magana
shi ne maganin abun kawai kada Sha.
Amma a Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta
miji ya sha nonon matar sa, sai dai fa kamar yadda na aka Faɗi a Sama rashin shan Nonon Matar ka shi ne ya fi dacewa
kawai, saboda fita daga saɓanin malamai, mu
Dena ɗaukar Fatawa don an samu wannan yace ayi amma Kuma wancan
yace kada ayi, toh abun da yafi dacewa ga Bawa mai imani da tsoron Allah shi ne
kawai kada Sha Nonon Matar ka a kiyaye dokokin Allah kawai.
Amma duk abun da kake son kayi mata na jin daɗi a lokacin Jima'i da matar ka kana iya yin sa ya halatta
yin hakan in ma Tsotsan Nonon zakayi ba tare da ka Sha ruwan Nonon ta ba,
wannan yayi, amma ka zauna kana shan Nonon ta wai don an ce ma ya halatta toh
akwai matsala fa, a kullum idan an ce ma ga Fatawa me Sauki da mai Zafi, toh ka
ɗauki mai zafin kawai ko Zuciyar ku tana son Wannan abun,
toh kawai ku hakura da aikata wannan abun kawai shi ne yafi dacewa ga mutanen
Kirki, akan ka rufe Ido ka biyewa son zuciya ka ce ai an ce ya halatta kayi,
shikenan kayi ta Shan Nonon Matar ka oga Kuskure ne wannan, Allah ya shirya
Allah ya sa a gane, yana da kyau a kiyaye dokokin Allah.
Don neman Karin bayani duba :
Bidayatul-mujtahid 2\67.
Allah ne mafi sani
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.