HUKUNCIN ƘARYAR DA IYAYE SUKE YI WA YARANSU
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalama alaikum malam, Ina da tambaya. Malam mene ne hukuncin ƙaryar da iyaye suke yiwa yaransu, don su aikata wani abun koh kar su aikata. Malam mene hukuncin rantsuwa akan se ka daki yaro akan wani laifi da ya aikata, misali ya yi barna se kayi saurin cewa wallahi in na tashi se na dake ka, saboda ya bata maka rai kafin zuwa anjima se ka huce.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:-
Su Yara ne Babu wani Hukunci a Kansu a yanzu. Amma
Kuma ku Iyayen su wajibi ne gare ku, ku Rika Hana su yin irin wannan Rantsuwar
Ko yin Karyar Nan, domin idan sun girma da shi a Haka, toh fah za su Zama
mutanen banza waɗanda ba su cika
Alkawari da Yawan yin Karya, Kuma duk Mai yin Karya Makomar sa ba ta yin kyau.
Don Haka Idan kina Son Tarbiyyar Yaran ki ya yi Kyau toh Wajibi ne ki Ja Masa
Layi da irin Waɗannan Maganganun
Na Karya Ko Yawan yin Rantsuwa irin wannan.
Za ki yi Azumi 3, wato Azumin Kaffara domin yin
Rantsuwa da Kika Yi na Za kiyi Abu Kaza Amma kuma ba ki zo kika Yi sa ba. idan
kin San Za ki zo ki huce ba za ki buge shi ba, Shin Me zai Kai ki har kiyi
Rantsuwar Cewa sai kin buge shi? Kin ga kenan kun mayar da rantsuwar abun Wasa.
don Haka akwai Azumi 3, za ki yi su, idan ba kiyi su ba, toh shi Allah ya San
wani Hukunci zai miki akai.
Kin ga ita wancan maganar yaran da Kika ce Suna
yiwa Junan su Rantsuwa Kuma Karya ce, idan kin Saba yin Haka yaran Suna jin ki,
Suma sai su Rika ɗaukar Cewa
Mahaifiyar su, Makaryaciya ce domin ko ta ce za ta buge mu ba za ta Yi ba Kuma
ga shi ta Rantse. Sabida Haka ko ranki ya ɓaci ai Bai kamata ki Rantse ki wallahi sai buge ka,
Alhalin za ki zo ki huce Kuma ba za kiyi Dukan ba.
Abun da ya dace kawai sai kiyiwa Yaron ki
barazana, ya ji tsoron abun da kika Gaya masa ba tare da kin Yi Rantsuwar komai
ba. Amma kin Yi Rantsuwar kin zo ba ki Buge shi ba Wai kin huce, Shin da can ke
ba ki San Za ki huce ba ne za ki Rantse? Wannan ai ba Abun kirki ba ne ga Uwa
Mai son Tarbiyyar Yaran ta ya yi Kyau ta Rika yin haka, Kuma yin irin wannan
furucin Shima Hanyar Koyar da Karya Ce ga Yaran Ku.
Kin ga Ma Kenan ai Yaran ku a Gurin ku ne suke jin
Rantsuwar ku har Su ma suke koya, ga shi yanzu Suna yiwa yan Uwan su Yara, kin
ga kenan nan gaba Suma Yaran Za su Dawo Yan Karya da Rashin Cika Alkawari da
Yaudara, Su dawo Suma Suna muku Karya a Cikin Maganar su, Kin ga Tarbiyya ta
Lalace kenan. Allah ya Shirya Wajibi ne Iyaye ku kiyaye Harsen ku Iyaye.
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.