Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Sabon Musulunta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yaya matsayin auren Wanda ya musulunta? Shawara nake nema , mene ne mahangar malam akan Hakan? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ai a musulunci babu wani fifikon daraja tsakanin wanda ya tuba ya shigo musulunci da kuma wanda aka haifa acikin addinin. Kamar yadda kuma babu fifikon da wasu ke dashi akan wasu saboda garinsu ko Ƙabilar da suka fito. Kamar dai yadda kika sani, ana samun girma ne ta dalilin fifikon tsoron Allah.

Don haka halayensa za ki duba, da kuma irin rikon da yake yiwa addinin musuluncin. Idan kin gamsu da halayensa da rikon addininsa shikenan ki bashi dama ya turo mutanensa. Amma idan baki gamsu da halinsa ko rikon addininsa ba, kada ki yaudareshi ta hanyar cin kuɗinsa. Gwanda ki sallameshi da wuri ki fito ki gaya masa gaskiya.

Wannan ita ce shawarata kuma ina tayaki addu'ar Allah ya zaba miki miji nagari.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments