Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta In Yi Masa Asiri Domin Mutane Su Tsane Shi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam akwai wani bawan Allah ɗan iska da yake ɓata min suna a wurin jama'a cikin unguwa. Wallahi yanzu duk yawancin mutane ya haɗa Ni dasu. Kuma wallahi tallahi babu laifin dana yi masa. Shine na yanke shawara yadda ya yi min wannan abin wallahi sai na yi duk yadda zanyi nasa mutane sun tsane shi. Nidai yanzu bani da wani makiyi sama da shi a duk duniya. Malam wai don Allah mi yake damun mutane da zarar an faɗa musu magana basa bincike kawai sai su hau su zauna. Wallahi tallahi har na yanke shawarar yiwa matsiyaci asiri na bakin-jini gun al'umma.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wannan laifin da kake zargin wancan mutumin ya aikata maka, idan har ya aikata ɗin to tabbas ya chutar dakai kuma ya chutar da kansa. Domin sunan wannan laifin 'Annamimanci' kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "MAI ANNNAMIMI BAZAI SHIGA ALJANNAH BA". (Bakhariy hadisi na 5,056. Muslim hadisi na 106. Abu Dawud hadisi na 4,871. Tirmidhy 2,026).

Acikin wani hadisin kuma wanda Imamu Ahmad ya riwaito ta hanyar Sayyidah Asma'u bnt Yazeed bn Sakan (radhiyal-Lahu anha), ta ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce : "(Kuna so) in baku labari game da mafiya alkhairin cikinku?' Sune waɗanda idan an gansu akan tuna Allah".

Sannan sai ya sake cewa : "Shin in baku labari su waye mafiya sharrin cikinku?" Sune masu yawo da Annamimanci, masu ɓata tsakanin masoya, masu ɗora laifi ga ku'butattun mutane". Aduba : Musnadu Ahmad juzu'i na 6 shafi na 459 da Sunanu ibn Maajah hadisi na 4119).

Don haka kada ka tada hankalinka bisa miyagun kalamai da Ƙaskanci ko mummunar mu'amalar da kake riska daga mutane. Kayi hakuri ka jure, ka gyara mu'amalarka da Mahaliccinka. In sha Allahu Ubangiji shi zai wankeka tsaf daga kowanne irin mummunan zaton da mutane ke yi maka, mutukar ka gyara tsakaninka dashi (SUBHANAHU WA TA'ALA).

Amma dangane da maganar da kakeyi cewar wai zakaje kayi masa asirin bakin-jini (wato karfa) idan kayi haka za ka kai karshe wajen zubar da kimarka awajen Allah. Domin kuwa shi sihiri yinsa kafirci ne. Kuma duk wanda ya yishi, to bashi da sauran rabo awajen Allah. Kuma yana daga cikin zunuban nan guda bakwai mafiya girman laifi kuma masu saurin hallakarwa.

Imamu Ahmad bn Hanbal da wasu daga cikin maluman magabata suna ganin cewa duk wanda ya yiwa wani mutum asiri, to ya kafirta. Ma'ana ya bar musulunci.

Al Hafiz Ibnu Katheer acikin tafsirinsa kan ayah ta 102 ta suratul baƙarah ya kawo cewar "Sarkin Muminai Umar ɗan khattabi ya rubuta (zuwa ga gwamnoninsa) cewa "KU KASHE DUK WANI MATSAFI DA MATSAFIYA".

Wanda ya ruwaito hadisin ya ce "Sai muka kashe wasu matsafa guda uku".

Ya ce Imamul Bukhariy ma ya riwaito acikin sahihinsa, hakanan ya inganta cewa Nana Hafsatu Uwar muminai (radhiyal-Lahu anha) wata baiwarta tayi mata asiri sai ta sanya aka kasheta.

Kuma Imamu Ahmad ya ce hadisai sun inganta daga Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa haddin matsafi shine a kasheshi da takobi".

Kaji tsoron Allah kada ka rama mugunta da mugunta. Kuma kada ka rasa imaninka wajen yin ramukon gayya. Kayi masa afwa ka barwa Allah zai maka sakayya aduniya da lahira.

WALLAHU A'ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments