Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Musulmi Zai Kunyata Yahudu Da Nasara Da 'Yan Shi'a

Wata Tattaunawa ta gudana tsakanin wani Musulmi da wani Bayahude a Birnin Basra ta Kasar Iraki. Bayahuden ne ya fara tambayar Musulmin.

Bayahude ya ce:

Annabi Musa (as) Annabi ne cikin Annabawan Allah, kuma Annabtarsa gaskiya ce, ta tabbata da dalilai da hujjoji, to shin ka yarda da wannan, ko kuma a'a ba ka yarda ba?

Musulmi ya ce:

Amsar tambayarka za ta kasance ne ta fiska biyu kamar haka:

1- Annabi Musan (as) da ya ba da tabbacin Annabtar Annabi Muhammad (saw), kuma har ya yi umurni da yin Imani da shi da binsa, har ya yi bushara da shi da Annabtarsa, wannan Annabi Musan (as) na yi Imani da Annabtar.

Don haka idan wannan Annabi Musan (as) kake nufi, to ko shakka babu na yarda da shi, kuma na yi Imani da shi.

2- Amma idan kuma kana tambayana ne a kan Musan da bai yarda da Annabtar Annabi Muhammad (saw) ba, kuma bai yi umurni da binsa ba, bai yi bushara da shi ba, to ni ban san wannan Musan ba, kuma ban yarda da Annabtarsa ba. Kai, ni a wajena wannan Shaidani ne.

Nan da nan sai Bayahude ya rude, ya rasa me zai ce.

Sai ya sake yi masa tambaya.

Bayahude ya ce:

To me za ka ce a game Littafin Attaura?

Musulmi ya ce:

Amsar tambayarka ta fiska biyu ce kamar haka:

1- Idan Littafin Attaura da aka saukar wa Annabi Musa (as), wacce a cikinta take tabbatar da Annabtar Annabi (saw) to Attaurar gaskiya ce, na yi Imani da ita.

2- Amma idan kuma Attauran da kake magana a kanta, ba ta yi Bushara da Annabi Muhammad (saw) ba, to ba gaskiya ba ce, kuma ban yi imani da ita ba.

Karshe Bayahude ya rasa abin fada, sai ya ce: Ina son ganinka, sai da suka kebe gefe, ya dauka abin kirki zai fada masa, sai ya zo kusa da kunnensa, sai ya ce: Uwarka kaza da kaza... Ya dura masa ashar...

To haka dai Bayahude ya yi girman kai, ya rufe da zagi da cin mutunci.

To haka ake yin Mujadala, ta hanyar tambaya da Istifsari.

Saboda haka idan ka fahimci wannan, to haka za ka yi wa Banasare idan tattaunawa ta hada ka da shi.

Haka Dan Shi'a ma a game da Sayyidina Aliyu (ra).

Idan Dan Shi'a ya ce maka:

Imam Aliy (as) shi ne dan uwan Annabi (saw), kuma mijin Fatima (ra), wacce tsoka ce daga Annabi (saw), kuma wanda yake a wajen Annabi (saw) a matsayin Annabi Haruna (as) a wajen Annabi Musa (as), ka yarda da shi a matsayin Imami da Khalifa bayan Annabi (saw) kai tsaye, ko kuma ba ka yarda ba?

Kai kuma Ahlus Sunna sai ka ce masa:

Amsar tambayarka ta fiska biyu ce kamar haka:

1- Wannan Aliyun da kake magana a kansa, idan shi ne Sayyidina Aliyu (ra) wanda ya yarda da Khalifancin Abubakar (ra) da Umar (ra) da Usman (ra), yake daukarsu a matsayin 'yan uwansa a Addini da Imani, kuma shugabanninsa, har ya yi Mubaya'a ma kowannensu, kuma yake a matsayin Wazirinsu, kuma shi ne Khalifa na hudu a bayansu, har yake cewa: Duk wanda ya gabatar da ni a kan Abubakar da Umar sai na yi masa haddin Kazafi, to na yarda da wannan Aliyun (ra), kuma ina sonsa.

2- Amma idan kuma kana nufin shi ne Aliyun da bai yarda da Khalifancin Abubakar da Umar da Usman ba, har yake cewa shi ne Khalifa Imami a bayan Annabi (saw) kai tsaye ba tare da maraba ba, kuma yake daukarsu a matsayin azzalumai 'yan fashin Khalifanci fasikai, ko kafirai to ban san wannan Aliyun ba, kuma ban yarda da khalifancinsa ba, kuma ba ruwana da shi, kuma fitinanne ne kawai.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments