Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Malamai Da 'Yan Siyasa

Ni a fahimtata ba ka iya raba Malamai da siyasa, saboda tun asali siyasar ta Malamai ce, daga baya ne wasu wadanda ba Malamai ba suka kwace musu kayansu.

Kuma Malamai su ne shugabannin al'umma na asali. Saboda su ne masu jagorantar al'umma a Addininsu da rayuwarsu. Su suke gyara wa mutane duniyarsu da ruhinsu da tarbiyyarsu. Su suke gyara wa al'umma duniyarsu da lahirarsu.

Malamai masu Nasiha ne wa al'umma, wato su suke nuna wa al'umma maslahohinsu na Addini da na rayuwa, da abin da zai gyara musu duniyarsu da Lahirarsu.

Ita kuma siyasa da shugabanci na mulki ta shafi Maslahar al'umma, maslaharsu ta Duniya da Addini da Lahirarsu. Don haka duk lokacin da aka zo zaben shugabannin siyasa, to al'umma tana bukatar Malamai su yi musu nasiha, su fadakar da su, su nuna musu wadanda zabarsu shi ne Maslaha wa al'umma a rayuwarta da Addininta.

Saboda haka lallai Malamai suna da alaka da siyasa. Ba za a ce sun kwace ma 'yan siyasa kayansu ba, har ma 'yan siyasar suna cewa; bai kamata Malamai su hada biyu ba; jagorancin Addini da na siyasa.

wannar magana ba dadai ba ce. Ba a raba siyasa da Addini. Kuma asali siyasar ta Malamai ce, daga baya ne aka fi karfinsu a kan kayansu.

Daga karshe wani abu da na fahimta shi ne; idan ka lura, za ka ga cewa; dan siyasa, dan jam'iyyar PDP shi ne yake sukar Malamai da cewa; sun shiga siyasa. Saboda yana jin takaicin Malamai sun fadakar da al'umma, sun ce a zabi Buhari. A bayansa kuma suka ce a zabi Muslim-Muslim ticket, alhali duka 'yan APC ne. To wannan ya sa dan PDP a kullum yana ganin Malamai sun ba ta masa siyasa, sun kwace musu harka. Har ya zargin Malamai da saka manyan riguna, alhali kwalliya abu ne mai kyau a Shari'a.

Amma kuma fa, duk da haka zargin da ake yi shi ne; asali wasu Malaman ba su cancanci zama Malamai ba. Kawai sun daura rawanin malumtar ne don su nemi abinci.

Ko kuma, ko da Malaman ne, amma maslahar aljifansu ne a gabansu, da neman duniya, ba Maslahar al'umma ba. Irin wadannan kuwa su ne tun a zamanin Magabata ake zarginsu, ake kiransu da sunan "Malaman fada", kamar yadda a yanzu ake cewa; "Malaman Gomnati", yaran 'yan siyasa. Masu zayyana musu barna, da daure ma karya gindi.

Saboda haka wajibi ne kowa ya ji tsoron Allah a duk matakin da yake.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments