TAHAMISIN WAƘAR "MUNAFUNCI DA ANNAMIMANCI"
RUBATAWAR ASALI: MALAM SALIHU KWANTAGORA
TAHAMISI: MALAM USMAN NAGADO (II)
Bismil Ilahi Gwani taimakeni nai furuci,
Allah ruɓanya salati gun mafifici,
Mun sallama a gareka Ilahu kaimu gaci,
Ya Rabbana Jalla mai ƙudura da adalci,
Kamun ƙafa naka yi da Rasulu Manzona,
Da mutunta alaye da sahabu du zumuna,
Allahu ya Allahu ka karɓi roƙona,
Ka tsare mu sharrin ɓatattu masu sa fitina,
A gari akan aikin da sukai munafinci.
Ya ƴan'uwa ku riƙe jaki ku bar taiki,
Ku taya ni mui nazari kan masu ɗan aiki,
Ni kam abin ga yana daɗa sa na bar ɗoki,
Lallai abin ga da ban tsoro da mamaki,
Duk galibinmu mutanen yanzu mun ɓaci.
Duba ka tarda samari na ta kai-kawo,
Sai dai su tsoma biyar ba cefane da awo,
Kullum ubansu kwaraf tamkar yana kiwo,
Ka ga saurayi majiyin ƙarfi yana yawo,
Ya kasa samun sana'a ban da shashanci.
Sai dai zaman banza kullum akan hanya,
Shi babu cas ba as sai dai baƙar aniya,
Sai dai ya watsa biyar sannan ya kora giya,
Sai bin gari da rawan ƙwambe abin kunya,
To mai ka je yi a ofis ce munafinci.
Ko tsegumi da haɗin gulma ka ɗau zunubi,
Duk mai irin wannan kau ba shi kyan ladabi,
To wane halinka tabban dai akwai wabi,
In banda ka je munafinci da kinibibi,
Zauna gidanka ka zam yaƙi da lalaci.
In ka zamo magidanci amana sai ka riƙa,
Ka tsare ɗiyanka ƙiyama ba ka cin sarƙa,
Fa ina ta ƙara nasiha ta gareka riƙa,
Zauna ka nemi sana'a wadda zaka riƙa,
Ka bar yawan tsegumi da yawan munafunci.
Babban abinda yake daɗa bani mamaki,
Ka ga jahili da talauci wai yana mulki,
Haka na abinda ka san kuka na mamaki,
Ka ga maigida da iyali ga shi ba aiki,
Sai bin gidajen mutane dan munafinci.
Haka nan idan da mutum kuka ƙulla sa-in-sa,
To ba ka san a gari ka ji an yabo gunsa,
Burinka koyaushe fa ka yaɗa sirrinsa,
Ka je ga alƙali ka ji duk asirinsa,
Ka kai ga sarkin gari dan annnamimanci.
Ai wane yau sarki saura kaɗan ya mace,
Bashi ya je ya ciyo yau ba shi ko na ice,
Burinka kai ƙazafi ga mutum ka samu fuce,
In an gane ka ace ku tsaya tukun ya wuce,
Kwaɗayin kwabonka shi jawo ma wulakanci.
Ya ƴan'uwa ga kashedina ku bar hasadu,
Mai ujbu an yi hani nai har da mai bugudu,
Kaicon namimin mutum kullum shina liddu,
Shi annamimi abin a guje shi ne da gudu,
Cutarsa ɗai da maciji babu bambanci.
Kai yana gaban fa maciji tunda bai magana,
Domin ko zai iya jawowa ƙasa fitina,
Duk inda yag ga zumu da zumu fa zai zauna,
Sai ya ji ƴar magana a wajen waƴancena,
Shi ƙudundune ta shi kai gaba don munafunci.
In ya ishe wasu zai haɗa gaskiya ƙarya,
Ya iyar garesu da harshe nai kama da ƙaya,
Ya haɗo zumu da zumu dan ai tsiya da tsiya,
Gaba ta tashi tsakanin masu soyayya,
Duk babu mai yinsa sai sarkin munafinci.
An gargaɗe ku ku zam tashi ɗiyan malam,
Ku riƙe zama na aminci duniya bi salam,
Mai tambayar a ina zamu samu hakan malam,
Tafi ofishin gaskiya ka ga kyan zama malam,
Don babu ƙwanji da jin zafi da makirci.
Duka aiyukansu fafes kullum ka ji shi tatar,
Komai bisa tsari da shirinsu za su fitar,
To sai ka ganshi sarai fa garai-garai tar tar,
Mataimakin Editar kai har da shi Editar,
Sun kyauta halin zamansu da ba munafinci.
Domin tsakankaninsu fa hairi ke yawo,
Ko da batun shawara kowansu zai kawo,
Kowansu na fara'a yana ta kai-kawo,
Babba da yaro abinsu zamansu zak kyawo,
Duk wanda kag ganshi can ya yaƙi jahilci.
Jama'a ku zan faɗaka yau dai muna huɗuba,
Tubu ilalLahi ya jama'a mu nem tuba,
Duka mai namimanci fa wutarsa ta fi guba,
Kai annamimin mutum kam bai ji daɗi ba,
Allah wadan wanda yat tsare yin munafunci.
Duka mai munafinci ya tsunduma halaka,
Kai ko ga Ƙur'ani tuni an kwaɓe shi haka,
Kullum ga al'uma cutarsa na haɓaka,
Cutarsa ta fi gaban a ƙididdige ta duka,
Ɓarnar wuta ma tana bayan munafunci.
Fa a yanzu ba ƙarami ba babba gun kauɗi,
A batun munafunci wai har da masu kuɗi,
Ya sulmiya da gudu i zuwa ga masu naɗi,
Babban abin tsoro ɗaya wanda za ni faɗi,
Ka ga malamai masana su tsaya munafunci.
A makin su gargaɗi al'uma su zam kuɓuta,
Wai sai su ruɗu da jahilci su ja su ɓata,
Allah wadai da sanin da ba zai hana ka ɓata,
Kuma malami ya ƙi yin aikinsa malanta,
Ya kutsa kansa ga son muli da zalunci.
Usman Nagado na hammasa ta ga mu,
Na kammale TAHAMISIN dan fahimtarmu,
Fi HAMTASHUN ramzin Hijirar Nabiyyunmu,
Allah ka sa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,
Ka sa mu wanye cikin sutura cikin ƴanci.
Mai tambayar asalin waƙar fa ga amsa,
Malam fa Salihu ne Kwantagora yai ta bisa,
Halin munafukai ku ji ko dalilinsa,
Allah Ta'ala da iko nai da iko da girmansa,
Yaɓ ɓaci jimlar waɗanda ka yin munafunci.
TAMAT
TAHAMISI: 10/RAMALAN/1445 (H)
20/MARIS/2024.(H)
20/MARIS/2024.(H)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.