Citation: Sani Magaji Abubakar, S.M., Adamu, U. and Gawuna, G.A. (2024). Sharhin Waƙar Gogarman Tudu ta Ibrahim Narambaɗa Tubali. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 295-298. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.036.
SHARHIN WAƘAR
GOGARMAN TUDU TA IBRAHIM NARAMBAƊA
TUBALI
Sani Magaji
Abubakar
Usman Adamu
Garba Adu Gawuna
Sashen Hausa,
Jami’ar iIimi ta Saʼadatu
Rimi Kumbotso, Kano
Abstract
This paper employs the research of oral formulae of one of
the oral songs of a renowned singer in Hausa land by name Ibrahim Narambaɗa tubali. the song titled Gogarman
Tudu. Hausa oral songs have arose the attention of the researchers due to the
logical themes established in them compared with other disciplines of Hausa literature
for this reason this paper intends to find a little contribution to fill some
of the gaps in this field. this study is built on the theoretical frame work of
waƙar baka Bahaushiya (wbb) to
make the analysis clear and befitted the context. the finding has shown that Makaɗa Ibrahim Narambaɗa has the power to
competently filter his messages to the audience as he adopt wbb theoretical
stanza pattern of + lead + chorus + cocoding + increase + corollary.
Gabatarwa
Wakar baka
tana buƙatar aiwatar da wasu abubuwa
daban-daban daga shi mawaƙin kafin ta
kai ga madakin isar da ita ga masu sauraro. ana shirya ta ne ta hanyar tsarawa
da samar da gangar jikinta cikin azanci da hazaƙa tare da naƙaltar
harshe ta wajen jagora da kuma masu amshi ko karɓi
ko rakiya.(gusau:1993:04).
harshen da
makaɗa da mawaƙa suke
amfani da shi cikakke ne kuma yana tafiya ne tare da kama irin tasa wadda ta
sha bambam da tsarin zance na yau da kullum haka kuma a waƙoƙin baka ana
amfani da hanyoyi daban-daban wajen shiryawa da salon jan hankali mai burgewa idan
an samu fasihi kuma gwani wajen aiwatar da waƙar. wannan takarda ta yi duba ne ga ɗaya
daga cikin waƙoƙin ibrahim narambaɗa tubali
mai suna ‚gogarman tudu‛ wadda ya rera wa sarki isa da ke gobir.wannan nazari
ya kalli batu guda ɗaya ne daga cikin batutuwan da a ke kalla a fagen nazarin
waƙar baka wannan batu kuwa shi ne ‚awon
baka‛
gusau
(1993:04) ya bayyana cewa akwai wasu matakan da za a iya amfani da su wajen
fito da ma’anar waƙar baka,
wasu daga cikin matakan sun haɗar da rerawa da rauji da hawa da saukar murya da ƙari da amsa – amon da dai sauransu.shi wannan fagen
nazari na awon baka ya shafi yadda makaɗi yake
shirya waka a cikin zubin ɗiya da kuma dabarun karin murya da zubin layukan ɗiyan
waƙa da tsarin rerawa da karin murya da
dai sauran abubuwan da suka shafi nazarin awon baka.
1.1
Taƙaittacen Tarihin
Rayuwar Ibrahim Narambaɗa Tubali
masana waƙoƙin hausa irin su gusau (1987) da shinkafi (1998) dan bunza
(2009) sun tabbatar da cewar babu takamaimai lokaci da shekarar da za a ce an
haifi ibrahim naramba ɗa. amma za a iya kirdado ko
hasashe da wasu abubuwa da suka faru a wancan lokaci bisa wannan dalili ne ake
hasashen cewar an haife shi a shekarar (1894 ko 1874) a garin tubali a shiyyar
da ake kira dembo. wannan gari na tubali yana a gundumar da aka kira jangeru a ƙaramar hukumar shinkafi. haka
kuma ya rayu na tsawon shekaru saba’in da ‘yan kai kafin ya koma ga allah.
kamar yadda ya bayyana a wata waƙarsa
inda ya ce,
Jagora: na wuce ƙaryako ina kiɗi
Na bar ƙarya ko ina kiɗi
Nai sittin saba’in naka hwaɗi.
Y/ amshi: Mai
saba’in yai ƙarya
Ana ta zunɗe nai
Ko yaran da ag
garai
Warwatse mashi
sukai
Shina yawo shi ɗai baran-baran.
Y/amshi: Ya ci
maza ya kwan yana shiri
Gamda’are sarkan tudu bala.
1.2
Ma”anar Awon Baka
awon baka kamar yadda gusau
(2003:23) ya bayyana, yana nufin nazarin yadda makaɗi yake shirya waƙa
da zubin layuka da yawan ɗiyan waƙwa da tsarin rerawa da karin
mura da amsa-amon kari da dai sauran abubuwan da suka shafi awon baka. a yanzu
za mu koma wajen ɗora waɗannan abubuwa da muka ambata na nazarin awon baka a waƙar gogarman tudu.
1.2
:1 Yawan Layukan a Ɗiyoyin
Waƙar
awannan fanni ana duba yadda
makaɗi ya shirya layuka ne na ɗiyan waƙoƙin sa ne nan take, a inda wasu
kuwa tun daga gida suke shirya ɗiyan waƙarsu. ita wannan waƙa ta ‚gogarma tudu wadda ibrahim
narambaɗa tubali ya yi, duka-duka ta ƙunshi ɗiya ashirin da ɗaya ne (21). a cikin waɗannan ɗiyoyi za mu ga cewa ɗa na 1 da na 2 da na 4 da na 6 da na 9 da na 11 da na 15 da
na 20. dukkansu suna ɗauke da layuka biyu biyu ne, da
na 3 da na 16 kuma suna ɗauke ne da layuka ukuuku na 7
kuwa ya na ɗauke da layukla huɗu ne, na 18 kuwa yana ɗauke da layuka biyar ne, shi ma
na 19 layuka biyar yake ɗauke da su shi kuwa layi na 17
yana ɗauke da layuka tara ne da dai
sauransu. ga misalin wasu daga ciki:
Jagora: shiri gama aiki na Dodo.
Y/amshi: ki fasawa
Amadu wan alƙali
(ɗa
na ɗaya mai layuka biyu ).
Jagora: maradun
raba Dogon daji
Samarafa, da gusau da kadassaka,
Y/amshi: du dai
Amadu ab babban ɗa
Ba ɗan tashi ka rama ne ba
Giyan tudu ka yi
wa yaro nisa.
(ɗa
na 19 mai layuka biyar).
Jagora: ai ba a
gama ni da yaro,
Na san yaro bai yi
muƙamina ba
Kak ku gama ni da
yaro
Na san yaro bai yi
zalaƙata ba
Kak ku gama ni da
yaro
Na san yaro bai yi fusahata ba.
Y/amshi: ƙaryar banza yaro bai ka in da
narambaɗa.
Mai tabarukin
sarki
Kak ku gama ni da
yaro
(ɗa
na 17 mai layuka tara)
1.2.2
Zubin Ɗiya a Waƙar.
a wannan waƙar makaɗa ibrahim narambaɗa ya shirya waƙar ne ta hanyar bayeyeniya a
tsakaninsa da masu yi masa amshi ta idan ya ƙulla zaren layi ɗaya ko biyu su kuma ‘yan amshi
sai su karɓa su ƙarasa. shi maimaita gindin waƙar yakan zo ne jefi-jefi bayan
rero ɗayoyi masu yawa . ga musali:
Jagora: ruwa da kada baban
mandede
Y/amshi: baban
shamaki manyan daga .
(maimaitawa).
Gogarman tudu
jikan Sanda
Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa
1.2.3
Tsarin Ɗan
Waƙar .
gusau (2003:33) ya bayyana cewar
shi ɗiyan waƙa tamkar rassa ne na bishiya
wadda ake fara hawa daga tushenta kuma a sauko ta tushen dai kuma . abun nufi a
nan shi ne akwai hawa da sauka . a wasu lokutan akan samun jagora ya hau ta
fuskar ma’ana da shirya ɗan waka sai kuma ‘yan amshi su
sauko da shi ko kuma a yi akasin hakan .duk wadannan ana yi su ne ta fuskar
kananan sakonnin da ake shiryawa a cikin wakar. gusau (1992) ya bayyana cewar
hawa shi ne inda ma’anar saƙon
da yake cikin ɗan waƙa ya fara shi kuma sauka yana
nufin inda .
ma’ana ta sauko ɗan waƙa
ya ƙare. ga misali:
Tsari ma’ana .
a1: Ai sarauta ban da nufin
allah ce
b1: Da ɗiban ta akan yi da ƙarfi
.
b2: Waɗanda nag gaza ganewa .
b3: Da sun ga .
ɓ1: Gogarman tudu jikan Sanda .
ɓ2: Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa .
a wannan ɗiyan waƙa
na sama akwai:
a shi ne hawa wato farko sakon ɗan waƙa
bisa ma’na. shi kuma harafin .
b1 yana a matsayin sauka watau ƙarshen saƙon ɗan waƙa
waɗanda ‘yan amshi suka karɓa. ɗ shi she gindin waƙa .
Ga wani misalin:
a1: Ai ba a gamani da yaro ,
a2: Na san yaro bai yi mukamina
ba .
a3: Kak ku gama ni da yaro .
a4: Na san yaro bai yi zalakata
ba .
a5: Kak ku gama ni da yaro .
b1: Ƙaryar banza yaro bai kai inda
Narambada .
b2: Mai tabarukin Sarki .
ɗ1: Gogarman tudu jikan Sanda .
ɗ2: Maza su ji tsoron dan mai Hausa .
1.2.4.
Tsarin Rera Waƙar
tsarin rerawa wani yanayi ne
wanda makaɗi yake rera waƙar cikin rauji dalhatu (2001) da
gusau (2003) .a wannan fage ana duba yadda makaɗi
yake haɗuwa da masu amshi wajen isar da
saƙonnin da suke cikin ɗiyoyin waƙa.
suna yin haka ne ta hanyar bin
matakai kamar haka:
kaɗaita: furucin jagora
karɓi: furucin yan amshi
ƙulli: kari ne daga jagora
Tarbe: karasa isar da sako daga ‘yan amshi wato jagora ya killa.
Karɓeɓeniya: dabara ta maimaita ɗiyan waƙa
a tsakanin jagorada .yan amshi
Bayeyeniya: karɓa karɓa-karɓar furuci tsakanin jagora da ‘yan amshi
Ga jadawalin a takaice:
i-
+ ƙungiya
+ ƙulli + ƙari (+ gindin waƙa)
–
i + karbebeniya ko
ii-
ƙulli + i – ƙari
+ i – bayeyeniya + l – karɓeɓeniya.
ga misali daga waƙar
Ƙulli: Dubu ta kamala ga Gwadabawa kable da fadar Gwandu
Ta kuma Tangaza nan ga Yabo
Ƙari: dange da Wurno da fadar
Sakkwato
Dud dai Amadu ab babban ɗa
Gindin waƙa: Gogarman tudu jikan sand
Maza su ji tsoron ɗan mai hausa
1.2:5
Karin Murya a Waƙar
makaɗan baka na hausa suna amfani da hawa da saukar murya da faɗuwarta ko saɗaru na waƙa (gusau: 2003) wannan fage yana
da matukar tasiri a tsarin waƙoƙin baka.
2.9
Kammalawa
wannan takarda ta yi duba ne ga
abubuwa daban daban a fagen nazarin awon baka a waƙar ibrahim narambaɗa mai suna gogarman tudu. daga cikin abun da ta duba sun haɗar da yawan ɗiyan waƙar da karɓi da yadda akaƙulla
zaren jerangiya na bayeyeniya a tsakanin jagora da kuma masu amshi haka kuma an
ɗora wannan sharhi ne bisa ra’in
waƙar baka bahaushiya wbb. haƙiƙi bisa ɗan wannan tsokaci da aka yi na
wannan waƙar an ƙara gano yadda makaɗa ibrahim narambaɗa yake gwarzo wajen samar da
sinadaran janhakalin masu sauraron waƙarsa,
shi ya saka har yanzu waƙoƙinsa suke zama tamkar sababbi ga
masu sauraro.
Manazarta
Ɗangambo, A. (1985). Ɗaurayar gadon fede waka’ makala
wadda ba a bug aba. kano sashen harshen
Gambo, D. (1990). Maidaji sabon
birni da waƙoƙinsa’. kundin digiri na farko
kano: jami’ar beyero.
Gusau S. M (2003) Jagoran nazrin
waƙar baka kano: benchmark
publishers.
Gusau, S. M (2001). Waƙar gogarma tudu ta ibrahim
narambaɗa a mazubin nazari’ a cikin
algaita: journal of current research in hausa studies, vol. 1. kano: sashen
harsunan nijeriya, jami’ar bayero
Ibrahim M. S (1978), Kowa ya sha
kiɗa ibadan: longman nigeria
limited.
King, A. Ɓ. (1980). Statement, restatement
and eɗtension: stanzaic structure in
hausa court songs’. zariya: department of nigerian and african languages,
ahmadu bello university.
King, A. Ɓ. (1981). Form and funtions in
hausa professional songs’ a cikin nigerian magazine.
King, A. Ɓ. (1986). An introduction to the
life, and works of abubakar akwara (1876 - 1962). zariya: department of
nigerian and african languages, ahmadu bello university.
Muhammad D. (edita), 1990 Hausa
metalanguage (kamus na kebabbun kalmomi). ibada: university press limited.
Muhammad, Ɗ. (1973). Waƙa bahaushiya’ a cikin studies in
hausa language, literature and culture no. 1. kano: cibiyar nazarin harsunan
nijeriya, jami’ar bayero
Mukhtar,
(i2000). Jagoran nazarin kagaggun labarai. kano: adamu joji publishers.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.