𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam alaikum malam dan Allah ina neman fatawa Akan wani aure. Wani bawan Allah ne ya auri bazawara bayan aure da kwana shida sai take laulayi ana dubawa aka ga cikin sati bakwai 7 inda ta yi rantsuwa batasan da cikin ba tasan dai tsohon mijinta ya yaudare ta da cewa zai maida ita ya yi lalata da ita. A yanzu haka ta saka iyayenta da dangi cikin Hali domin kunyar abin da ta iya bayyana sannan shima mijin haka. Malam tambaya ta ta farko shin za su iya zubarda wannan cikin kasancewar sati bakwai ne? Sannan za su iya ci gaba da auren domin rufin asirin iyayen da dangin idan mijin ya amince? Allah yasaka da alkairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Tabbas
wannan abun akwai rikici mai girma cikinsa. Sai dai in sha Allahu akwai hanyoyi
kamar guda biyu da za a iya binsu domin warware sarkakiyar dake cikin lamarin.
Kafin mu
shiga cikin maganar warware sarkakiyar, dole ne mu kalli shi wannan sabon auren
amatsayin cewa "BAI ƊAURU BA". Wato ka'idar ita ce Duk
auren da aka ɗaura alokacin da mace take cikin iddah ko take ɗauke da juna biyu,
to ba aure bane.
Don haka
wannan mutumin ba mijinta bane. Sai dai ayi kokarin bin hanyar da komawarta
gidan farko za ta tabbata.
Hanya ta
farko ita ce, mu yi aiki da fatawar Mazhabin Imam Abu Hanifah wanda ya ce
"Namiji yana iya mayar da matarsa ta hanyoyi ne guda biyu. Kodai ya gaya
mata da bakinsa ko arubuce, ko kuma ya mayar da ita a aikace (wato yaje ya yi kwanciyar
aure da ita).
To idan dai
wannan saduwar da ya yi da ita, alokacin ba ta Qare iddah ba, to za a ɗauki wannan
amatsayin kome ne (wato kai tsaye ya mayar da aurenta tunda har ya sadu da
ita). Don haka sai ta kwaso kayanta daga gidan wannan mutumin na biyu, to mayar
dasu gidan mijinta na farko.
Idan kuma ta
riga ta yi iddah alokacin da ya sadu da ita, to duk da haka dai za a iya
jingina abin da ta haifa izuwa gareshi idan har ya yarda kuma ya amince, amma
abisa wata fatawa daga magabata na kwarai irin su Imam Hasanul Basariy da kuma
wasu daga cikin Maluman Musulunci kamar Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (Sun ce
idan har mazinaci ya amince cewar shi ne ya yi mata ciki kuma ya yarda cewa duk
abin da ta haifa nashi ne, shikenan za a jingina yaron izuwa gareshi).
Su kuwa
iyaye, dole ne su ajiye son rai su dawo subi abin da addini ya fada, koda kuwa
bai zo daidai da son ransu ba. Bai halatta a zubar da wannan cikin ba, domin
zubar da ciki haramun ne sai dai idan akwai wata larura wacce shari'ah ta yarda
da ita. Wannan kuwa ba larura bane.
WALLAHU
A'ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.