Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sakin Mace Ta Waya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Fatan alkairi Malam ya matsayin sakin mace amusulnci ta waya yake? ni atunanina saki yana afkuwane ta wajan furtashi ko shedar ta takarda Dan Allah adinga tunatar da maza wajan saki ta waya ni aganina sakin wulakanci ne tunda ba ta waya ake ɗaura musu aure da mata ba yakamata malamai sudunga Jan hankalin maza akan haka inda ba hakan yananufin daidai bane nice ban fahimta ba Allah ya sa mu dace

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam: Kin Saku, Kuma Saki ya tabbata, Sa'annan ai bawai Malamai su dinga yiwa maza Nasiha ko tunatarwa bane akan wannan, Bari na Gaya Miki duk wannan Laifin ku ne Mata domin ku ne kuke kawo Mazan ku ce Kun ji Kun gani duk duniya babu wadda kike so sai shi.

Dalilin shi ne ai duk Namijin da ya San Darajar Mace, ya San Kimar ki, ya San Mutuncin ki, ya Martabatan ki, ya San Addinin sa, ya sa tsoron Allah a ran sa, yana ganin Girman Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ya San Darajar Iyayen sa da na Matar sa, ya San Mene ne Aure, toh wallahi Bari na Gayaiki ba zai taɓa Sakin Mace a irin Haka ba, ba tare da Shedun Waliyyin ki da Shedun Waliyyin Sa, ko Kuma Wani Sheidar wani mutum Mai Mutunci da kima ba. Dole Sai ya nemi Waliyyin ki ko Waliyyin Sa, ko shaidar wani Mai Mutunci ya ce zai sake Matar sa, ya rubuta Takarda a gaban sa a tura Miki shedar, Kuma wata kila a dalilin Kawo maganar a gurin Waliyyin ki ko Waliyyin sa ko wani sheda akan cewa zai Sake ki, toh idan shedar ya yi Masa Nasiha ya tunatar da shi, sai ki ga ya Fasa Sake ki ya yi amfani da abun da aka tunatar da shi. Amma Samarin yanzu Auren kawai ake yi amma ba a san mene ne Dokokin Aure da Hukunce-Hukuncen saki ba, sa'annan ba su San Darajar ki ba, dole ne a yi sakin da ake yi a Shirin Films domin an ɗauka wasa ne an mayar da Auren kamar dai yadda ake yi a Fina-Finan Hausa.

Sa'annan bayan ya Sake ki Yana dakyau a Ka'idar Shari'ar Musulunci ya Miki wani Isani, wato ya ɗauki Kuɗi ya ba ki kyauta, ya Siya Miki Suturar Sakawa ya ba ki, abun da Za ki Rika Ci kina Sha har iya Wadda zai ɗauke ki na Wasu Watanni zuwa gama iddar ki, ba tare da kin daga Hankalin ki ko kin Fara bin maza ba, in dai mutum yana da hali abun da Shari'ar Musulunci ya ce kenan amma idan babu shikenan ya sake ki a cikin Mutuncin kamar yadda na yi bayani a sama. Shin Samarin Yanzu suna yin Haka Idan sun saki Matar su? Amma kuma idan an taɓo ku sai ku Ce Suna son ku Suna Kaunar Ku kamar za su Mutu, Kuma duk Wadda yake son Abu yake Kaunar Abu ba zai Yi irin yadda Kika ce ba.

Kai idan ma Mijin Yana da Hali wato Mai Arziki ne shi, zai ba ki harda Kyautar Gida da Motar shiga, idan ba Mai Arziki bane toh zai Miki Isani irin yadda nace a sama bawai Dole bane sai an Miki, Amma Yana dakyau idan Miji ya sake Matar sa ya bi irin wannan Tsarin na Shari'a.

Toh Amma ke kin je kin Auri Namijin da Bai San Komai ba a rayuwar da sai kawai ya yi Jima'i da ke ya ji daɗin ki Bukatar sa ta biya, don Haka ne ma ya Auro ki, Bai San Darajar Mace ba, Bai San Kimar Mace ba, Bai San Mutuncin Mace ba, Bai San Martabatan Mace ba, Uwa Uba Bai San Girman Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Bai San Mutuncin Waliyyin Sa ba, Bai San naki ba, Bai san Darajar Iyayen ki ba, Bai San Naki ba, Bai San Dokakin Sakin Mace ba, Bai San hukunce-hukuncen Aure ba, Shin Yaya ba zai Sake ki ta yadda yake so ba a Ransa ba??

Wallahi duk Namijin da ya San waɗannan abubuwan ba zai Sake Mace irin yadda Kika ce ba, Amma Wadda bai san su ba, ai Dole ne ya yi irin wannan Sakin fiye da hakan ma, ai kema kin San me Kika Aura, inda a Lokacin Za a ba ki Shawara ace ki bar shi kada ki Aure shi, zai Zo ya Miki irin wannan Sakin, da Wadda ya ba ki Shawarar shi ne abokin Gaban ki, toh yanzu ga shi ta faru.

Don Haka Ni a ganina laifin ku ne Mata domin Kun San me kuke Aurowa su Zama Mazajen ku, yanzu Haka inda ace Za a tara Samari masu yin Aure, ace idan ka sake Matar Ka, sai kayi mata Isani zaka ba ta kuɗi da siya mata Suturar Sakawa da Sauran su, da za su yi ta mamaki Sabon Hadisi ya zo, domin ba su san ma ana Yi ba Kuma ba su yin Haka.

Kina Gaya musu za su ce an kawo Sabon Addini Amma a gurin Wadda ya San me yake Yi, shi ya San ba Sabon Addinin bane.

Samarin kawai sai dai suyi Aure amma ba su San Darajar Waliyyan su ba, kuma Allah ya sanya Waliyyin ki da Waliyyin sa domin su zama garkuwa ne gare ku duk wani abun da zai faru a tsakanin ki da shi, toh dole ne Waliyyin sa ko naki su ji sa'annan su zo suyi muku Silhu da Nasiha, idan abun ya gagara su Waliyyan da kansu za su bayar da shawarar a rabu, amma kuma duk wadda ya san Darajar Waliyyin sa da naki wallahi ba zai taɓa Kunya ta su ba duk abun da suka gaya masa dole ne ya gyara, kema duk abun da suka gaya miki dolen ki ne ki gyara, toh amma da yake ke da Mijin gaba ɗayan ba a Darajar Waliyyin Aure ba shiyasa komai zai iya faruwa.

Wata ma wallahi a yanzu haka tafi shekara 10 ko 5 da yin Auren amma idan kin tambaye ta waye Waliyyin ta da Waliyyin Mijin ta? za ta ce ba ta San su ba, haka shima Namiji da za ki tambaye shi waye Waliyyin sa da Waliyyin Matar sa zai ce bai sani ba, don Allah an San Darajar Aure kenan? Ai dole ne in dai Miji me tsoron Allah ne dole ne ya San Waliyyin ki da Waliyyin sa, kema haka dole ne ki san su sa'annan a rika girmama su, domin haqqin Auren ku yana kansu dolen su Allah zai tambaye su akan zamantakewar Auren ku, amma wani zai Sake Matar sa babu wadda zai sani, wani zai yi ta kuntatawa Matar sa Waliyyan ba su sani ba ko sun sani amma Mijin ya fi Karfin su, sabida haka a ji tsoron Allah a san wanne irin Miji za a Aura a rayuwa. Allah ya shirya dafatan kin gane Koh???

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments