Ticker

6/recent/ticker-posts

Wani Matsafi Ya Mutu A Nan Niger - Shin Za Mu Yi Masa Sallah

TAMBAYA (253)

Assalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu

Wani mushriki ne ya mutu jiya a nan kasar NIGER, ya shahara da tsibbace - tsibbace, gashinan an kawo shi cikin masallachi, shin ya halatta mu yi masa Sallar Gawa sannan mu yi masa addu'a?

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Baya halatta a yiwa mushriki Sallah

Idan kun yi masa Sallah a rashin sani ba laifi amman idan mutum ya sani to yana da laifi

Domin kuwa munada nassi:

( مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَن يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَىٰ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ )

التوبة (113) At-Tawba

Bã ya kasancwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.

To in dai baya kasancewa a nemi yafiya ga Kafirai to Ina Kuma ga ayi Masa Sallah idan ya mutu

Don haka in dai ya mutu ne yana wannan harkar ta duba a matsayin sa na "ar-Raf" kamar yanda Annabi ya fada a cikin Sahihul Muslim to makomar sa Jahannama ce kamar yanda Allaah Azzawajallah ya fada a cikin waccan ayar

Muna zaune da irinsu a anguwanmu

Sannan kuma zan yi amfani da wannan damar don jan hankalin mutane su guji bibiyar wani qasurgumin boka da ake Kira da Malam Zaki, yananan a media platforms yana ta dulmiyar da mutane. Sannan a jawa mutane irinsu Musa Mai Sana'a kunne da su dinga fadakar da mutane illar bibiyar bokaye

Ya Allaah ka rabamu da Yan Duba da Yan Tsibbu da Yan bugun Kasa da Yan Gobe da Nisa da Astrologers da sauransu

Ya Allaah ka tsare imaninmu ka dauki ranmu Muna Muminai la'akarida kowanne mumini musulmi ne sai dai ba kowanne musulmi bane mumini

Allaah ka zabemu cikin Muminai masu gadon birnin Aljannah kamar yanda ya faɗa:

( الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )

المؤمنون (11) Al-Muminoon

Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.

Wallaahu taala aalam

Masu bukatar shiga Telegram Class na littafin "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU", ku shiga Telegram kuyi searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments