Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ittikafi A Kowane Masallaci: Cikakken Bayani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum. Game da maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): Babu I’tikaaf sai a Masallatan nan guda uku (Harami, da Madinah, da Qudus). To, a ina aka samo hukuncin yin I’tikaafin a masallatan sauran ƙasashe? Ma’ana: Yanzu yin I’tikafin a masallacin garinmu ya halastta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Mas’alolin Fiqhu suna da mabambantan fuskoki a wurin malamai mujtahidai . Yadda wani yake duban mas’ala ba haka wani yake dubanta ba. Don haka ake samun saɓani a tsakanin maganganunsu da fatawoyinsu. Ba su da wani laifi a kan haka. Abin ƙyama dai kawai shi ne bin son-zuciya da sha’awar-rai a wurin mabiya, da ƙyale gaskiya. Kuma dole mu san cewa duk lokacin da mujtahidai suka samu saɓani a kan wata mas’ala daga cikin mas’aloli, to guda ɗaya ce kawai daidai sauran kuma kuskure ne, kodayake kuma wanda ya faɗi abin da ya saɓa wa daidai ɗin ba za a zarge shi ba, tun da ma har lada guda za a ba shi, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya nuna a cikin hadisinsa sahihi:

»إِذَا حَكَمَ الْحَاكِمُ فَاجْتَهَدَ ثُمَّ أَصَابَ فَلَهُ أَجْرَانِ ، وَإِذَا حَكَمَ فَاجْتَهَدَ ثُمَّ أَخْطَأَ فَلَهُ أَجْرٌ «

Idan mai hukunci ya yi ijtihadi a wurin hukunci sai kuma ya dace, to yana da lada biyu; idan kuma ya yi ijtihadi a hukuncin sai kuma ya yi kuskure, to yana da lada ɗaya. (Al-Bukhaariy: 7352, Muslim: 1716)

Shiyasa idan malami muttabi’i ya zo irin wannan wurin dole shi ma hanya guda ɗaya yake bi da gwargwadon abin da ya bayyana masa na ƙarfin hujjojin mujtahidan da suka saɓa a gabaninsa. Kamar matafiyin da ya zo mararrabar hanya, dole hanya ɗaya kaɗai zai bi. Ba zai iya bin dukkan hanyoyin a lokaci guda ba.

Daga cikin irin waɗannan mas’alolin na saɓani ne, wannan mas’alar ta nau’in masallacin da ake yin i’tikafi a cikinsa:

Malamai sun saɓa wa juna a kan haka ne saboda kalmar ‘Masallatai’ da ta zo a cikin maganar Allaah Ta’aala:

وَلَا تُبَـٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمۡ عَـٰكِفُونَ فِی ٱلۡمَسَـٰجِدِۗ

Kuma kar ku shafi juna da su (matanku) alhali kuma yin i’tikaafi a cikin masallatai.

(Surah Al-Baqarah: 187)

(i) Al (Alif da Laam) na cikin ‘ Al-Masaajid’ (Masallatai), wasu malaman sun ɗauke shi na istigraaq ne, watau wanda ya haɗe kowane irin masallaci. Don haka, suka halatta yin i’tikafi a cikin kowane irin masallaci a duniya: Babba ko ƙarami, kuma na-Jumma’a ko ba na-Jumma’a ba!

Sai dai yawancin malaman Fiqhu ba su yarda da wannan ra’ayin ba, domin da farko dai ba a ƙaramin masallacin da ba na-Jumma’a ne Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi nasa i’tikafin ba. Sannan kuma in aka yarda da wannan fassarar, to yaya za a yi idan ranar Jumma’a ta zo alhali mutum yana cikin i’tikafin? Fita zai yi zuwa masallacin Jumma’a don sallar Jumma’a ya bar i’tikafin, ko kuwa i’tikafin zai cigaba da yi ya manta da sallar Jumma’ar?!

(ii) Wasu malamai kuma sun zaɓi cewa Al a cikin Al-Masaajid ɗin na Al-’Ahd ne, watau wanda ya tattaru a kan abin da zuciya ta riga ta san shi, watau: Waɗannan Masallatan da aka sani ɗin nan, waɗanda a cikinsu ne ake iya yin i’tikafi ! Suka ce: Don haka, ana iya yin i’tikafi a duk wani babban masallacin Jumma’a a ko’ina a cikin duniya, tun da shi ne ya yi kama da masallacin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi nasa i’tikaafin a cikinsa. Kuma dayake mai i’tikafi a cikinsu ba zai buƙatu ga fita zuwa Jumma’a a wani wurin daban ba. Wannan shi ne ra’ayin da yawancin malamai suka ɗauka.

(iii) Wasu malaman kuwa cewa suka yi: Sauran masallatan Jumma’a na duniya ba su yi daidai da irin Masallacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi i’tikafi a cikinsa ba, saboda dalilai kamar haka:

1. Darajarsu ta fi ta sauran masallatan duniya, kamar yadda ya nuna a cikin hadisai: Yin sallah a masallacina ya fi sallah dubu (1,000) a cikin wanda ba shi ba, sai dai masallacin Harami. Yin sallah a masallacin Harami kuma ya fi sallah dubu ɗari (100,000) a cikin wanda ba shi ba. (Ahmad, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin Al-Irwaa’u: 1129).

Game da Masallacin Qudus kuwa, an riwaito cewa: Yin sallah a cikinsa ya fi na sauran masallatai da daraja dubu hamsin (50,000) ne. Sai dai bai inganta ba. (Al-Irwaa’u: 1130).

2. Masallatan uku su kaɗai ne aka yarda a ɗaura sirdi domin a tafi yin ibada a cikinsu. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ba a ɗaura sirdi sai dai zuwa ga Masallatan nan guda uku: Masallacin Harami da Masallacina wannan, da Masallacin Qudus.

3. Sannan kuma ga shi su kaɗai ne Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ware su da cewa: A cikinsu ne kaɗai ake yin i’tikaafi .

Don haka, waɗannan malaman ba su yarda a yi ƙiyasin sauran masallatai a kan waɗannan masallatai uku ba, saboda bambancin reshe da asali. Sun kafe a kan lafazin maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: Babu i’tikafi sai dai a cikin masallatan guda uku.

Waɗancan malaman kuma suka ce: Da farko dai akwai tababa game da ingancin wannan hadisin. Sannan kuma ko da ya inganta, fassararsa ita ce: Babu i’tikafi kammalalle ko cikakke sai a cikin masallatan guda uku . Amma ba kore yiwuwar yinsa a cikin sauran ba ne!

Sai su kuma suka amsa da cewa: A wurinmu wannan hadisi ingantacce ne, babu wata tababa a kansa. (Dubi yadda As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaniy (Rahimahul Laah) ya tattauna a kan haka, kuma da irin martanin da ya bayar ga mai musun hakan a cikin mashahurin littafinsa: Silsilah Al-Ahaadeeth As-Saheehah: 2786)

Amma kuma fassarar da kuka bai wa hadisin ba daidai ba ne, domin a asali harafin istisnaa’i (illaa) a irin wannan wurin korewa ta matuƙa ya ke yi sai dai abin da ya togace kawai, amma ba wai kore kamala ko cika kawai yake yi ba.

Da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

لَا تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلَّا إِلَى الْمَسَاجِدِ الثَّلَاثَةِ

Babu ɗaura sirdi sai dai zuwa ga Masallatan nan uku

Zai yiwu ku iya yi masa irin wancan fassarar: Babu ɗaura sirdi kammalalle ko cikakke…?!

Ko kuwa a inda ya ce:

(Laa Ilaaha Illal Laah)

(Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah)

zai yiwu shi ma a fassara ma’anarsa da cewa: Babu abin bautawa kammalalle ko cikakke…?!!

A taƙaice dai akwai maganganu masu yawa da faɗi a irin waɗannan mas’alolin da malamai suka saɓa wa junansu a cikinsu, waɗanda kowannensu za ka ga yana da dalilinsa a kan abin da ya tafi a kansa, kuma yana da dalilai ko martani ga dalilan da wasu malaman suka ɗauka. Don haka dai, su malaman da suka ga dacewar yin i’tikafi a kowane babban masallaci, har da na garinmu suna da na su dalilai, kamar yadda ka ji.

Sai dai mu a Markazu Ahlil-Hadeeth a cikin rubuce-rubucenmu kamar na: Goron Azumin Ramadan da makamantansa muna ƙoƙarin tafiya a kan doron hadisai sahihai ne, kamar yadda manyan malamai masana hadisin suka bayyana. Kuma muna fatar hakan ya zama kyakkyawar mafita gare mu da sauran al’umma a duniya da barzahu da lahira, in shaa’al Laah. Domin malamai muhaqqiqai sun tabbatar da cewa: Hanyar malaman hadisi ita ce hanya sahihiya ingantacciya wacce a cikinta babu irin matsalolin da sauran hanyoyin suke fama da su. (Dubi littafina: Darajar Malaman Hadisi).

Amma ba mu cewa sauran malamai waɗanda suka saɓa a cikin mas’alolin fiqhu daga wannan matafiyar da ijtihadinsu , ko don bin malamansu mujtahidai , ɓatattu ne ko hallakakku ne! Musulmi ne Ahlus-Sunnah ’yan uwanmu matuƙar dai sun nufaci dacewa da gaskiya ne, ba sun bi sha’awar-rai ko son-zuciya ba ne.

Allaah ya haɗa mu gaba-ɗaya a Ranar Lahira tare da waɗanda Allaah ya yi musu Rahama: Daga cikin Annabawa da Siddiƙai da Shuhada’u da Salihai.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments