Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Samu Damar Karatu A Saudiyya Sai Dai Kuma Yanzu Haka Ina Karatu A Nigeria: A Ba Ni Shawara

TAMBAYA (252)

Assalamu alaekum Ina wuni malam ya ibada Allah yakarba mana

Mallam don Allah Ina Neman shawara ne nasamu scholarship domin yin karatun degree a saudiya kuma tafiyan baxae wuce cikin shekarar nan ba insha Allah amma Matsalar shi ne Ina karatu a nan Nigeria har na Kai 300 level shekara daya ya rageman nagama shi ne nake Neman shawara malam miye yakamata na yi gashi kuma Idan nace nabari nagama karatu na a nan xan yi missing wancan opportunity din don Allah abani shawara malam nagode asha ruwa lafiya.

AMSA

Waalaikumus salam

Masha Allaah

Da farko dai na tayaka murna domin kuwa wannan dama ce babba wadda ba kowa bane yake samunta

Idan mutum ya tsinci kansa a wannan yanayin ba abin da yafi cancanta ya yi sama da bawa Allaah zabi ta hanyar yin Istikhara

Sannan kuma abu na biyu shi ne

Ka duba ka ga tunda al'amuran sun shigo cikin shekara guda ne to sai ka duba yaushe zamu tafi Saudiyya din ?

Shin zamu tafine a lokacin da muka yi graduation a level 400 ?

Shawarar da zan baka anan ita ce

Ka yi Istikhara din sannan kuma idan ya rage sauran kwanaki kadan ku kammala karatun alhalin tafiyar za ta tabbata ne kafin ku kammala to sai ka je ka samu Department naku ka nemi alfarmar su akan ba ka son wannan damar ta subuce maka

Idan suka ce ba za su iya ba

Sai ka garzaya Faculty

Suma idan suka ce ka hakura sai ka tafi Admin na Jami'ar ka ce a baka appointment da VC akan wani emergency issue

Idan nan ma ka ga an ki baka damar haduwa da shugaban jami'ar sai ka dinga ware lokacin da yake zuwa office

Kana ganinsa sai kayi sauri ka sameshi ka ce masa ga issue din da ya taso kuma Allaah ne kadai zai kawo maka mafita kuma ta dalilin sa

Ka girmama shi

In sha Allaah zai baka lokacin da za ku tattauna

Daganan tunda an samu shugaban Jami'ar to in sha Allaahu za a samu mafita

Mu kaddara ya rage maka lokacin da zaka kammala level 400 din cikin alfarmarsa, to Alhamdulillah haka ake so

Amman idan shima yace sai dai ka zabi guda daya

To shawara ta anan shi ne ka zabi zuwa Saudiyya din

Hujja:

Ina maka kwadayin falalar dake cikin sahihin hadisin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Yin sallah a Masallachin Ka'aba ya fi falala sau 100,000 akan kowanne masallachi sai dai Al-Masjid An-Nabawi wanda shi kuma za ka samu ladan sallah 1,000 akan kowanne masallachi wanda ba shi ba"

Ko da ace inda zakaje karatun ba Jami'atul Islam dake Madinah bane amman dukda haka kusancinka da can yafi nan (Nigeria) kuma akwai yiwuwar za ka samu damar sauke farali na aikin Hajji ga kuma bonus na Umrah

Wallaahu taala aalam

Masu bukatar shiga Telegram Class na littafin "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU", ku shiga Telegram kuyi searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments