Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Siyasar Jam’iyyu a Nijeriya: Takaitaccen Sharhi Kan Jigo da Salo

Citation: Adamu, Y.I. (2024 Waƙoƙin Siyasar Jam’iyyu a Nijeriya: Taƙaitaccen Sharhi Kan Jigo da Salo. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 478-486. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.059.

WAƘOƘIN SIYASAR JAM’IYYU A NIJERIYA: TAƘAITACCEN SHARHI KAN JIGO DA SALO

Yunusa Ibrahim Adamu

Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Tsakure: 

Manufar wannan bincike ita ce, fayyace irin gudummuwar da marubuta waƙoƙin siyasa suka bayar wajen bunƙasar siyasar jam’iyyu a Nijeriya. An yi amfani da sharhantaccen bincike (Qualitative Method) wajen gina wannan aiki. Haka kuma, an ɗora wannan bincike a kan ra’in muhimmancin Rubutacciyar Waƙa, (Theory of Appreciation on Hausa Written Poetry) wanda Farfesa Ɗangambo (2007) ya assasa, musamman ɓangaren da ya yi magana a kan jigo da hanyoyin binciko manya da ƙananan jigogi a Rubutacciyar waƙa.Da kuma salo da sarrafa harshe.A wajen tattaro bayanan wannan bincike, an yi amfani da hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da; ziyartar marubuta waƙoƙin siyasa. Da tattaunawa da su domin jin bayanin yadda suka ɗauki waƙoƙin siyasar jam’iyyu. An yi bitar matanin waƙoƙin a rubuce domin a samu damar ƙalailaice jigon siyasa a cikinsu. Binciken ya gano cewa da yawan marubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu na ƙasar Hausa, sun fi shahara a kan abin da ya shafi siyasar aƙida, a wasu lokutan sukan yi amfani da dabarun jawo hankalin masu sauraron waƙoƙinsu wajen yin karin magana da zambo da habaici domin kushe abokan adawar siyasa, da kushe jam’iyyarsu duk domin masu zaɓe su ƙaurace mata, da kuma cusa musu ra’ayin riƙau na kishin jam’iyya da rashin tsaro a kan duk abin da ya taso. A ƙarshe binciken ya gano cewa, marubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu sukan yi amfani da salon kamantawa da kwatantawa da siffantawa da jinsintarwa da mutuntarwa da dabbantarwa dakambamawa da alamtarwa duk a cikin waƙoƙinsuna siyasa.  Haka kuma, binciken ya lura da wasu Jigogi da su keamfani da su. Irin waɗannan jigogi sun haɗa da na yabo da zuga ta hanyar bayyana manufofin jam’iyyu da na tallata ayyukan raya ƙasa na gwamnati..

Fitilun Kalmomi: Waƙoƙin siyasa, Jam’iyyu, Jigo, Salo, Nijeriya

Gabatarwa

A cikin wannan takarda an yi nazari ne a kan waƙoƙin siyasa da yadda suke da kuma yadda suke bayar da gudummuwa ta fuskar kafa gwamnati da takara da lashe zaɓe da adawa da farfaganda da yarfe na ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban tun daga lokacin da aka samu ‘yancin kai daga Turawan Ingilishi, da irin gudummuwar da waƙoƙin siyasa suke bayarwa tun daga jamhuriya ta farko har zuwa yau ɗin nan. An ɗauki wasu daga cikin irin waɗannan waƙoƙi na siyasa daga jam’iyyu daban-daban an yi nazarinsu daki-daki, domin samar da muhimman bayanai game da waƙar, da jigo da salon da mawaƙin ya yi amfani da shi wajen isar da saƙonsa ga ‘yan jam’iyyarsa. Kafin nan, an duba ma’anar waƙa daga masana daban-daban domin fito da irin gudummuwar da marubuta waƙoƙin siyasa kan bayar.

1.1 Ma’anar Waƙa

Yahaya (1997:1) ya ce“Ita kanta kalmar waƙa a wuirn waɗansu musamman mawaƙa ta rabu zuwa sassa biyu (2) da aka kira waƙa da waƙe, kuma kowacce kalma daga cikinsu ma’anarta daban da ta ‘yar’uwarta. Waƙe a ganin wasu shi ne rukunonin waƙe da suka danganci addini, wanda muhimman abubuwan da waƙe suka ƙunsa su ne, wa’azi da madahu (yabo) da furu’a (fiƙhu) da makamantansu. Daga ɓangaren da wasu ke kira waƙa ya shafi jigogi baduniya kamar yabon wani mutum domin abin duniya, wataƙila mulki ko dukiya ko shahara a ɓangaren siyasa ko jaruntaka da makamantansu.

To amma, a wurin mawaƙa wato waɗanda suke mayar da kiɗa sana’a, an sami rarrabuwar ra’ayi har kashi 2. A cikinsu akwai masu tunanin waƙa a matsayin tarin kalmomi da aka ƙuƙƙulla cikin azanci, kuma masu amfani da kiɗa.

Wasu kuma sun ce waƙa magana ce da ke zuwa cikin wani tsari kuma a rera, sannan ga saurin jan hankalin mai sauraro. Haka kuma masana ta fannin ilimi da dama sun bayyana ma’anar waƙa kowa da yadda ya bayar da ma’anarta. Daga cikin su akwai:

Ɗangambo (1984:3) ya ce “Waƙa rera ta ake yi kuma tana da tsari da sigogi har ma da ƙa’idoji na musamman”.

Ya ƙara da cewa, “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi a kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne haka suke ba a maganr baka ba”.

Gusau (1993:59) ya bayyana waƙar baka da cewa “Daɗaɗɗiya ya ce wadda aka faro ta tun lokaci daɗaɗɗe mai nisan gaske”.

Yahaya (1984:2-3) ya ce“Waƙa maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu tsararru, kuma zaunannu”.

A ra’ayina ina ganin cewa: “Waƙa wata dunƙulalliyar magana ko furuci ne mai ma’ana cikin hikima da basira, wanda ake tsara shi cikin azanci tare da rerawa,domin jan hankalin mai sauraro cikin wasu ƙa’idojin da babu su a maganganun yau da kullum”. Na kafa hujja da waƙar da Malam Tijjani Tukur Yola ya kawo game da ma’anar waƙa, inda yake cewa:

“Waƙa da zance dole ne a raba su,

  Zance da ban waƙa ko ana tsarawa.

In za ka yo zance kana yin lura,

Waƙa kana yin lura ka zo ka kwatanta.

Sannan a zance babu tsari ɗas-ɗas,

Tamfar a waƙa yadda za ka tsananta.

Zance a dokokinsa dai ganewa,

Waƙa kwa sai kogi yake kutsata.

Sannan akwai wasu ƙa’idoji sosai,

Sauti da sauran ƙafiya a kula ta.

Tijjani ne ya tsaya yake rabewa,

Domin a san waƙa a ko gane ta.

Zance ko rarara a zan gane shi,

Sam babu sauti kun ji na nanata.

  Tijjani Tukur Yola, 1976.

2.0 Ma’anar Siyasa

Kalmar siyasa ta samo asali daga “al-siyasat” ta cikin harshen Larabci, kuma kalmar tana nufin shugabanci ko jagoranci. Ɗiso (1997:1-2).

Ga alama wannaan na iya zama ma’anar kalmar ta kai tsaye ko kuma ta zahiri. Abin fahimta a nan, an bayyana siyasa tamkar salo ko tafarki ko kumadabarun aiwatar da shugabancin jama’a, ba hanyar hawa kan karagar mulki ba.

Bugu da ƙari akwai bayanai da masana da masu bincike a kan ma’anar wannan kalma suka bayar daga cikinsu har da Mashi (1986:41) wanda yake cewa waɗansu mutane sun ɗauki siyasa da cewa cin amana ce da butulci, wanda wannan ne ma ya sanya da zarar an ambaci siyasa cikin mu’amala sai dattawa su zare jikinsu domin kuwa kalmar kishiyar dattako ce. A nan kalmomin cin amana da butulci su ne suka nuna bambancin wannanma’ana da wadda aka kawo a farko.

Haka nan, idan muka ƙara yin nazarin wannan ma’ana tare da la’akari da yadda ake gudanar da siyasa a yanzu, ba laifi ba ne, don an bayyana siyasa a matsayin jayayya ko yin gumurzu da fafatuka da kuma tsayuwar mai daka kan meman wani abu da yadda za a kasafta shi a lokacin da aka samu, kuma a ba wanda aka so.

 Ɗiso (1997:1-2) yana cewa, “Siyasa tana iya ɗaukar ma’anar dabara da yaudara da sauƙi da sulhu da wayo da kuma ƙwarewa wajen iya hulɗa da jama’a”.

Masana daga ɓangaren koyar da siyasa ma ba a bar su a baya ba, kuma ga ra’ayin wasu dangane da ma’anar siyasa.

Dahl (1950:1-5) cewa yayi, “Siyasa hanya ce da akan bi don kafa hukuma kuma a gudanar da tsare-tsarenta wannan na nuna siyasa tsari ce na shugabanci da tababtar da an kiyaye manufofin wannan hukuma”.

Jega, (2005:223-224) yana mai ra’ayin siyasa ta shafi jagorancin mutane da sarrafa albarkatun ƙasa don ci gaban wannana al’umma.

Sa’id (2002:172) Yana ganin cewa “Siyasa wata hanya ce ta gudanar da zaɓaɓɓiyar gwamnati ta hanyar dimokraɗiyya a ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa, inda za a zaɓi shugabanni masu tafiyar da ita a ƙarƙashin ƙafafun wasu jam’iyyu”.

Ƙamusun Hausa (2006:397) ya bayyana ma’anar siyasa da cewa “Tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwarinsu”.

A nawa ra’ayin na kalli siyasa da cewa “Wani tsari ne na shugabantar al’umma a madafun iko daban-daban, ta hanyar zaɓe, ko naɗi, sai dai zaɓen yakan kasance ɗayan biyu, ko dai ya zama an kwatanta gaskiya ko kuma a yi ka ci baka ci ba, ko kuma baka ci ba ka ci”.

2.1 Ma’anar Waƙar Siyasa

Yayin da ake ƙoƙarin fito da ma’anar waƙa, galibi akan yi la’akari da wasu muhimman abubuwa da suka ƙunshi tsararriyar ƙa’ida ta baiti da ɗango da kari da amsa-amo, wani lokacin da zaƙin murya da kuma kiyaye saurna ƙa’idojin da suka saɓa da maganar baka, kuma ana gabatar da waƙoƙin domin yaɗa manufofi iri daban-daban, ciki kuwa har da siyasa. Dan haka da wannan wuri, za a iya bayyana waƙar siyasa a matsayin wani furuci kan wata manufa da aka gina ta hanyar amfani da keɓaɓɓun kalmomi a kan tsari da ya bambanta da hanyoyin rubuta sauran nau’o’in adabi. Alal misali, a waƙar “NEPU Sawaba” ta Gambo Hawaja Jos cikin Dokaji (1990) yana cewa:

 “Jam’iyyan nan da an ka ce,

 Wai ta NPC ta mace,

 ‘Yan halak duk tarkace,

 Yanzu saurna sun fice,

  Masu son danne gaskiya.

Muhimman kalmomin da ke nuna wannan baiti cikin waƙar siyasa yake akwai ‘jam’iyya’ wadda ke bayyana taron wasu mutane bisa aƙida ɗaya ta yin mulki, sai NPC, wannan kuma suna jam’iyya ce da aka yi a jamhuriya ta ɗaya. Akwai ‘yar halak wadda ke bayyana rukunin mutane na cikin jam’iyya da suka riƙe manufarta da gaskiya.

Ni kuma a ra’ayina na mai nazari zan iya cewa waƙar siyasa, wani tsararren zance ne da ake tsara shi da niyyar yabo ko kambamawa ko zuga ga waɗanda zuciya ke so, da kuma yin zambo da habaici da gugar zana da hannunka mai sanda ga abokan adawa.

2.2 Halayen Waƙoƙin SiyasanaHausa

Waƙoƙin Hausa na siyasa suna da wasu keɓaɓɓun siffofi da suka bambanta su da suaran waƙoƙin Hausa. Muhimman cikin waɗannan halaye sune:

Bayanin manufofi da alamomin jam’iyyu

Yabon shugabanni da fitattun ‘ya’yan jam’iyya

Yadda ake gudanar da siyasa.

Tallata jam’iyya don a zaɓeta

2.3 Ma’anar Jam’iyya

Jam’iyya na nufin wata ƙungiya mai wakiltar wani ra’ayi na neman mulkin al’umma (Mashi 1986)

Haka kuma Ƙamusun Hausa (2006:212) ya bayyana cewa “Jam’iyya na nufin wata ƙungiyar jama’a ta siyasa ko ta sana’a, mai manufa iri ɗaya da tsarin ƙa’idoji da zaɓaɓɓun shugabanni”.

A ra’ayina, Jam’iyya na nufin haɗuwar wani rukuni na jama’a da suka amince su tafi a kan ra’ayi ko manufa iri ɗaya, domin cimma wani buri nasu na neman mulki”.

Waƙoƙin Siyasa a Nijeriya:  Daga shekarar 1946 bayan ƙarewar yaƙin duniya nabiyu ne waƙoƙin siyasa suka fara kankama a Najeriya, inda ‘yan ƙasa suka riƙa yin aikace-aikace na siyasa” Gusau (1984:64) Waƙoƙin siyasa waƙoƙi ne da ake rubutawa, domin bayyana abin da ake nufi da siyasar zamani da kuma ƙa’idojin siyasar jam’iyyu. Haka kuma waƙoƙi ne da ake shiryawa da nufin yabon shugabanni ko jam’iyyun siyasa daban-daban, da kuma yin suka ga abokan hamayya na wasu jam’iyyun. Akan shirya waƙoƙin siyasa ne ta yadda za su isar da saƙon da ake son su isar ga jama’a. Yahaya (1997:21)

Marubuta Waƙoƙin Siyasa a Jamhuriyya ta farko 1960-1966

Mulkin Turawa ya zo ƙarshe ranar 1 ga watan 10, 1960.Inda aka kafa jam’iyyun siyasa da suka samo asali daga ƙungiyoyi.An  samu jam’iyyun NEPU daga Arewa, sai NCNC daga yankin Ibo daUNCP daga tsakiyar Nijeriya, sai kuma A.G daga yankin Yarabawa.

Mawaƙa irin su Gambo Hawaja da malam Aƙilu Aliyu da Mudi Sipikin duk sun gabatar da waƙoƙi da nufin kare jam’iyyunsu.Misali Alhaji Mudi Sipikin ya yi wata waƙa mai suna ‘Murnar Karɓar Mulki Kan Jihar Arewa ta Nijeriya. Inda yake cewa:

 Bauta da zafi da ciwo da ɗaci,  Ballantana har a ce ba mutunci,  Kayanka an ƙwace duk shugabanci,

Yaya idan kana ka samu ‘yanci,   Kayanka an ba su mulki nasa.

 Abin da ya shekara sittin rabonmu,

 Da shi yanzu yau ya zo gare mu,

 Gidan nan Arewa ƙasar kakannimu,

 Da can ƙaddara  ta taho ta rabab u,

  Allahu yau ya yi iko nasa.

 Mun samu kanmu yau ba wata illa,

 Babu jinaya faɗa ko su zilla,

 Sai lafiya da aminci kamala,

 Cikin haƙuri gaskiya da adala,

  Kowa ya zauna da hujja tasa.

 Idan har mutum ya zamo babu ‘yanci,

 Ƙalata da yunwa da zafi da ƙunci,

 Rashin lafiya kuma sanyi da kirci,

 Yawan zazzaɓi kuma sannan talauci,

  Ga duk wanda ya rasa ‘yanci nasa.

 A yau ga shim mun zama ‘ya’ya kamar da,

 Mutunci da ‘yancinmu yau ba makida,

Aminci na sosai cikin fa’ida,

Yau ga shi mun soma samun sa’ida,

  Mai hassada kuma kaito nasa.

Mudi Sipikin 1966.

3.1 Jamhuriya ta Biyu (1979 -1983)

Ranar 18 ga watan Janairun 1966 ne aka kawo ƙarshen mulkin jamhuriyya ta farko,wanda sojoji suka yi a ƙarƙashin Manjo General Johnson Thomas Aguyi Ironsi. A lokacin ne aka kawo ƙarshen mulkin siyasa a ƙarƙashin dokar soja ta Deccree 33 of 1966, aka kuma haramta duk wata jam’iyyar siyasa, sai dai daga baya, Sojoji sun yarda su bayar da mulki ga farar hula. A nan ne jam’iyyun siyasa kusan 50 suka bayyana. Waɗanda suka haɗa da Unity Party of Nigeria (UPN) ta Chief Obafemi Awolowo, sai Nigerian People Party (NPP) ta Waziri Ibrahim wanda daga baya ta koma GNPP, sai kuma People’s Redemption Party (PRP) ta Malam Aminu Kano. Duk da yawan jam’iyyun siyasar da suka fito a wancan lokacin, jam’iyyu biyar ne kacal suka samu damar tsallake sharuɗɗan da gwamnati ta kafa.Waɗannan jam’iyyu sun haɗa da UPN da NPP da GNPP da NPN da PRP. Daga baya kuma aka samu ƙarin su NCNC wato National Congress of Nigerian’s and Cameroon, ta Dr. Nnamdi Azikiwe, da NPN sai kuma PRP wadda ta zama NEPU ta fuskar aƙida. Awannan jamhuriya an samu manya da ƙananan mawaƙan siyasa da suka waƙe jam’iyyunsu, waɗanda suka haɗa da Malam Bello Giɗaɗawa wanda ya yi waƙar siyasa lokacin salama, da Shekara Sa’ad wanda ya yi waƙar yabon Sardauna. Da Malam Aƙilu Aliyu da ya yi waƙar Tauraron zamani, sai Malam Gambo Hawaja Jos, wanda ya yi waƙar ‘Yan sawaba, da sauransu da dama. (Ɗangambo1984: 14)

3.2 Jadawalin Sunayen wasu Fitattun Mawaƙan Siyasar jam’iyyun da suka yi waƙa a jamhuriya ta biyu

S/N

MAWAƘI

WAƘA

JAM’IYA

1.

Shekara Sa’ad

Yabon Ahmadu Bello

NPC

2.

Bello Giɗaɗawa

Siyasar Zamani

NPC

3.

Abdullahi mai Gwandu

Yabon Sardauna

NPC

4.

Mohd Giɗaɗo

Yabon Sardauna

NPC

5.

Aƙilu Alyu

Tauraron zamani

NEPU

6.

Aƙilu Aliyu

Jiya da Yau

NEPU

7.

Yusuf Kantu

Ya Allah K aba mu Sawaba

NEPU

8.

Gambo Hawaja

Waƙar ‘Yan Sawaba

NEPU

9.

Malami A. Yabo

A zaɓi ‘yan Fi ‘yan

NPN

10.

M.S. Ɗunɗaye

‘Yan santsi kun zama ƙaya

NPN

11.

Yakubu Labaran

‘Yan santsi sun ji kunya

NPN

12.

Musa Madugu

Ya Allah K aba mu Aminci

NPN

13.

Isah I. Bunguɗu

Fi Ar Fi maganin zamba

PRP

14.

Isah I. Bunguɗu

Ɓarawon Akwatu

PRP

15.

Magaji Sudawa

Jam’iyyarmu ce PRP

PRP

16.

Garba Gashuwa

Ɗan hakin da ka raina

PRP

 

Kamar yadda kowa ya sani ne, ɗaya daga cikin irin gudummuwar da waƙoƙin siyasa suke bayarwa sun haɗa da tallata jam’iyyu da ‘yan takara da jawo hankalin masu zaɓe da kuma yin kushe ko zambo ko habaici ko gugar zana ga abokan hamayya. Don haka, wanna takarda ta duba wasu waƙoƙin siyasa da aka yi a wannan jamhuriyya, da nufin yin tsokaci game da zambo da habaici.

A waƙar ‘Yan Sawaba ta Gambo Hawaja yana cewa:

Kai tunturmi jaki daƙiƙin duniya,

Ƙaton cikin wofi na cinye haramiya,

Gemunka har sajenka ba su da martaba,

In dai ya zam aikinka babu na gaskiya.

(Gambo Hawaja a waƙar Sawaba).

A baitukan da suka gabata, Gambo Hawaja mawaƙin NEPU ya yi zambo ga wani da ake zato Sardauna ne, inda yake siffanta shi da wasu halaye na rashin adalci. Da yin wannan waƙar Gambo Hawaja bai ci ɓagas ba, domin kuwa Malami A. Yabo na jam'’yyar NPN, ya yi masa raddi a cikin waƙar a zaɓi NPN, inda ya ce:

 Na ji wanda ya tsara waƙar Nepuka,

 Asalinsa Arne ne a Jos Sardauna.

 Sunan Ubansa Aɓom tsirara ma yake,

 Goyon tsiraici jakunan Sardauna.

(Malami A. Yabo a waƙar ‘Mu Zaɓi NPN)

Wannan ya nuna irin ɗauki ba daɗin da ake yi a tsakanin mawaƙan siyasa na wancan zamani, duk da nufin kare muradunsu na siyasa a jam’iyyunsu. A wani misalin inda Malam Lawal Maiturare a cikin waƙar murna inda yake yi wa ‘yan jam’iyyar NPC, inda yake cewa:

 Wasu sun je sun zo tuntuni,

 Sun kasa bayani gaskiya.

 Ba wakilai ne bana gaskiya,

 Burinsu kashe Nijeriya.

A wannan baitin, Malam Lawan Maiturare ya nuna irin yadda ‘yan jam’iyyar adawa da rashin gaskiya da kuma son kasha ƙasar ma baki ɗaya.

Shi ma Malam Aƙilu Aliyu ya yi irin wannan zambon inda yake cewa:

Aikinsu kamar rawaninsu yake,

 Ɗaure-ɗauren banza ba nazari.

Akwai waƙoƙin siysa da dama masu jigon zambo ko habaici,waɗanda ake yi domin a aibata abokan adawar siyasa. Auwal Isah Bunguɗu a waƙar Ɓarawon Akwatu, ya yi irin wannan zambon.Haka ma Muhammad S. Ɗunɗaye a waƙar ‘Yan Santsi Kun Zama Kaya, da Yakubu Labaran a waƙar ‘Yan Santsi Sun Ji Kunya, da sauransu da dama. Don haka yanzu wannan nazari zai ɗauki waƙoƙi biyu daga kowanne ɓangare da nufin yin nazarinsu ta fuskar jigo da Salo da sarrafa harshe.

Nazarin waƙar Ya Allah Ka ba mu Aminci ta Musa Madugu

An haifi Malam Musa Madugu a garin Keffi a lokacin tana cikin jihar Platoe, yanzu kuma tana jihar Nasarawa, a shekarar 1948. Ya halarci makarantar Allo tun yana ƙarami, a garin na Keffi. Bayan ya sauke Alƙur’ani mai tsarki ne ya karanci litattafai manya da ƙanana waɗanda suka shafi addini. Bai halarci makarantar Boko ba, sai da yako yi yadda ake yin rubutun boko na Hausa, da karantawa har ma da Ingilishi daga abokai da ‘yan uwa. Tun yana ƙarami ya fara koyon sana’ar tela, wacce sana’ar mahaifinsa ce, har ya ƙware sosai, sai kuma noma da kiwo a matsayin sana’a kamar kowane Bahaushe.

Mutum ne mai sha’awar waƙe-waƙe tun yana ƙarami sosai, har ya iya karanta wasu waƙoƙi guda biyu, ɗaya ta Hausa ɗaya kuwa ta Larabci. Ta Larabcin itace ‘Al-wasa’il Al-mutaƙabbala wadda aka fi sani da Ishiriniya ta Alfazazi, sai kuma ya iya karanta waƙar Infiraji ta marigayi malam Aliyu na Mangi. Bai taɓa rubuta waƙa ba, har sai shekarar 1978, inda ya rubuta waƙar ‘Rabbana Nuna Mana Gaskiya Mu Bi NPN Baki Ɗaya, sai kuma ya rubuta waƙar ‘Ya Allah KaBa Mu Aminci Ya Riƙa Mana Ba Da Ya Gaza Ba, ya rubuta wata mai suna ‘Haɗa Kai a Wajenmu a Zauna ba Bambanci Tsakaninmu, da sauran waƙoƙi da dama.

Sharhin waƙar Ya Allah kaba mu Aminci.

Amshi: Ya Allah ka ba mu aminci NPN ba za ta gaza ba.

To Bismillah ni zan fara,

Sunan Rabbana naf fara,

Nai nufin waƙa in tsara,

Ya Allah kaba ni basira,

 In waƙar ba ban fasa ba.

Tun a amshin wannan waƙa Malam Musa ya nuna cewa waƙar siyasa zai yi, kuma ta jam’iyyar NPN. Don haka sai ya yi roƙo ga Sarki Allah kan yaba su aminci, ya zamo jam’iyyarsu ta NPN ba ta gaza ba wajen lashe zaɓuka da kafa gwamnati.

A baiti na farko mawaƙin ya fara buɗe waƙarsa da sunan Allah, domin Allah ya lamunce masa, yadda zai fara waƙar NPN. Wannan wani salo ne daga cikin mawaƙan ƙarni na19 waɗanda tasirin addini ya shige su sosai.A baiti na biyu ya ci gaba da cewa:

Idan aka ce da ku wane ne,

 Mai waƙar ga ? Ni Musah ne,

 Nai nufin waƙar haɗa kai ne,

 Yau waƙar na NPN ne,

  Za mu yi ba da mun fasa ba.

A baiti na biyu mawaƙin ya sa hannu ya kuma buga hatiminsa, ya sanar da mai sauraro sunansa ta fuskar jawo hankalinsa ya san cewa, ga wanda ya yi waƙar. sai kuma ya fara fito da manufar waƙar, wato ya bayyana jigon waƙar da cewa haɗinkai ne ga ‘yan jam’iyyar NPN.

Da farko nai kira ga samari,

‘Yanmata mu tashi da sauri,

Mui yaƙi mu kakkaɓe ƙwari,

Don ‘yanci ya tabbata sauri,

  Ba su wane mai ha’inci ba.

A baitoci na 3 da 4 da 5 Malam Musah Madugu ya ƙara fito da jigon wannan waƙar ne, domin ya nuna cewa matasa maza da mata su tashi tsaye wajen ganin sun haɗa kai.

Na yi kira wajen haɗa kanmu,

Samari har da ‘yanmatanmu,

Mui haƙuri mu riƙe junanmu,

Mui ladabi wajen manyanmu,

  In mun haka to ba ma taɓe ba.

Kar mu riƙe juna a zukata,

Samari har zuwa ‘yanmata,

Yau mu riƙe a shirya zumunta,

Kar mu wa junanmu mugunta,

  Mu dage ba da ha’inci ba.

Duk jam’iyyu huɗu ba ma son su,

Don mun gane irin manufarsu,

Su burinsu dai gina kan su,

Kana har zuwa ‘ya’yansu,

  Mun gane ba ma faɗa ba.

Kalli ji NPP mun manta ta,

UPN kuma tamfar ba ta,

NPP mun gane ta,

PRP kuma mun ɗaure ta,

  Ba za ta ɗaga ta je yawo ba.

To yanzu sai mu kame kanmu,

Don mu tsare mutuncin kanmu,

Mui haƙuri mu riƙe junanmu,

Ba gaba a tsakaninmu,

  Mu ɗaure ba da mun watse ba.

Idan an duba baitocin da suka gabata za a ga cewa marubucin wannan waƙayana ƙoƙarin warware zaren waƙarsa ne, ta hanyar koɗa jam’iyyarsa da tallatata da kuma dakushe hasken jam’iyyun adawa. Ya ci gaba da yi wa ‘yan jam’iyyarsa nasiha a kan kowa ya tsaya a matsayinsa kar manya ko ƙananan ‘yan jam’iyya wani ya je yana aikata wasu abubuwan da ba su dace ba.Haka wannan mawaƙi ya yi amfani da abubuwan da suka shafi warwarar jigo a cikin wannan waƙar, har zuwa ƙarshe.

4.1 Sharhin Waƙar Nagari na Kowa ta Alhaji Garba Gashuwa wadda ya yi wa tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau

An haifi Alhaji Garba Gashuwa a shekarar 1957 a cikin garin Bade da ke ciki tsohuwar jihar Borno, wanda yanzu garin Bade ya ke a jihar Yobe.Ya yi karatun Alƙur’ani mai tsarki, sai ya shiga harkokin kasuwanci. Ya fara waƙa a shekarar 1978 wato yana shekara 21 kacal a duniya. A lokacin da Malam Aminu Kano na jam’iyyar PRP, ya je garin Gashuwa yaƙin neman zaɓe ne ya ga Garba Gashuwa, ya kuma lura yana da basira sosai. Sai ya nemi ya dawo Kano da zama, domin ya riƙa waƙe jam’iyyarsu. Garba Gashuwa ya rubuta waƙoƙi sama da 600, sai dai sabo da daɗewar lamura da rashin taskace waɗannan waƙoƙi ya sa, waƙoƙin da aka samu ba su fi 400 kacal ba. Malam Garba yana rubuta waɗannan waƙoƙi ne da Hausar Ajami.

4.1.1 Jigo

Jigo na nufin muhimmin saƙon da mawaƙi yake son isarwa ga al’umma, wato abin da waƙar ta ƙunsa dangane da manufa. Auta(2008:203)

Jigon waƙar ‘Na gari na kowa’: Idan an yi la’akari da babban jigon wannan waƙar za a iya cewa yabo ne na Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau. Za a iya ganin haka tun a sunan waƙar, sai kuma mawaƙin ya ƙara tabbatar da haka a cikin baiti na 7, inda yake cewa:

 Ibrahim Allah sa kana gida,

 Gaisuwa ta ishe wa maigida,

 Sardauna riƙonka yana da fa’ida,

 Ku jama’a ku gujewa mahassada,

  Gara ku san Allah shi ne ɗaya.

Jigo a taƙaice: Baiti na 3-4 kira ya ke yi ga jama’ar birni da na karkara a kan su zo su tsaya kan gaskiya, su zaɓi mutum na gari wanda ya zo da gaskiya.

A baiti na 5-7 kuwa mawaƙin yana bayani ne a kan kyawawan halayen malam Ibrahim Shekarau.

A baiti na 8-10, mawaƙi ya ɗan yi shaguɓe ne a kan wasu abokan adawar Malam Shekarau.

A baiti na 11-12 ya bayyana irin samun nasarar da Malam ya yi sakamakon halayensa na kirki.

4.1.2 Warwarar Jigo

Wannan waƙa tana da babban jigo na yabo ne. Ya ƙara fito da hakan tun a baiti na 4, inda ya ce :

 Kai ku san malam ya zo da gaskiya,

 Yai horo a tafi da gaskiya,

 Ya kori du mai son hayaniya,

 Mai haƙuri shi zai ci moriya.

  Jalla ka ba mu riƙo na gaskiya.

A baiti na gaba ya ci gaba da zayyana kyawawan halayen Shekarau, inda yake cewa:

 Tunda shi Gwamna ne mai kishin ƙasa,

 Ga taimakon jama’a mutan ƙasa,

 Hadda na nesa zuwa na nan kusa,

 Ku daina zuwa neman bugun ƙasa,

  Yarda da Allah kuma gaskiya.

A nan mawaƙin ya yi ƙoƙarin dai-daita ma’auninsa a cikin baitocin inda ya ɗora baitocin a kan Karin ‘Madid’ wato 7+5+7(+5) na faa’ilatun + faa’ilun.

4.1.3 Salo

Salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo ga mai karatu ko sauraro (Ɗangambo 2007:35-37). Dangane da salo a wannan waƙar ana iya cewa mawaƙin ya yi amfani da miƙaƙƙen salo ne, sabo da ya isar da saƙonsa kai tsaye, ba tare da ya yi wani ƙaƙale-ƙaƙale ba.Wannan ba ya rasa nasaba da jigon waƙar. Akwai iren-iren salo da mawaƙin ya yi amfani da su, wanda suka haɗa da:

4.1.5 Mutuntarwa

Mutuntarwa ita ce a mayar da abin da ba mutun ba, ya zama mutum. Ɗangambo(2007:45-46) Malam Garba Gashuwa a cikin wanna waƙar yakan ɗauki wasu halaye ko siffofi da darajoji da mutane ke da su, ya laƙaba wa wani maras rai ko dabba ko tsuntsu ko ƙwari. Kamar yadda za a ga misali a baiti na 8, inda ya ce:

 Ke kurciya ki guje wa hassada,

 Ke hasbiya ki rage gada-gada,

 Ke ba ki dawa kuma ba ku nan gida,

  Ku yi fassara ku fahimci gaskiya.

(Garba Gashuwa a waƙar Na gari na kowa).

4.1.6 Alamtarwa

Dabara ce ta bayyana wani abu ta hanyar ba shi wata alama, wadda za ta tsaya a maimakonsa. Ɗangambo(2007:423) A cikin wannan waƙar ta ‘Na gari na kowa wadda malam Garba Gashuwa ya yi wa Sardaunan Kano malam Ibrahim Shekarau, ya yi irin wannan alamtarwar a baiti na 12. Ga abin da ya ce:

 To a she malam ya samu garkuwa,

 A gun Allah ya samu karɓuwa,

 Ai ruwan tasah na ta ɗuruwa,

 Mik kai mai shanu shige ruwa,

  Tai ka fake kar in yi dariya.

(Garba Gashuwa a waƙar ‘Na gari na kowa’ baiti na 12)

 A ƙarshen wannan nazari an kawo abuwan da suka shafi wannan waƙar muhimmai.

4.2 Sharhin waƙar CPC mai Alƙalami ta Malam IbrahimSaleh (Iyala)

An haifi Ibrahim Saleh a unguwar Kawo a cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, ranar 1-1-1973.Ya yi karatu a KTC Kaduna, da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna (KAD-POLY) inda ya karanci fannin aikin jarida a shekarar 2002. Tun Ibrahim yana ƙarami ya ke da sha’awar waƙoƙi har ya girma. Shi ne ya wallafa waƙar ‘Yan Najeriya riƙo sai mai gaskiya, Baba Buhari kai muke so Najeriya’ wacce ta yi fice sosai.Daga baya kuma ya wallafa wannan waƙar ta CPC Mai Alƙalami.

Dalilin yin wannan waƙar:  Babban dalilin yin wannan waƙar ba ya rasa nasaba da sauya sheƙar da tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja Janaral Muhammadu Buhari mai ritaya, ya yi ba daga jam’iyyar APP, zuwa CPC Mai Alƙalami.

Kai tsaye jigon wannan waƙar ya fara ne tun daga baiti na 7 da 8 a cikin waƙar, Inda ya ce:

Na ɗau Alƙalamin rubutu,

Zan fara baituka da dama.

 

Kaifinsa ya wuce takobi,

Da Bindiga Allah ba ni himma.

Mai sha’awar ya bi tafiyarmu,

Yo maza kar mu baro ka baya.

(Ibrahim Saleh, waƙar CPC mai Alƙalami 6-10)

Tsarin waƙar: Waƙar ta fara da Basmala, ta kuma ƙara jaddada manufar waƙar. Sannan ‘yanƙwar biyu ce, tana ɗauke mabambantan amsa amon da yake sauyawa daga baiti zuwa baiti. Sannan tana da yawan baituka 205. Ta fuskar aron kalmomi, an yi amfani da kalmomin harshin larabci da ingilishi. Misalan kalmomin larabci sun haɗa da: Alƙawiyyu da Allamal insan bil ƙalam da khaliƙi da Alƙur’ani da Alƙalami da Ahli Ashabu. Da sauransu.

4.2.1 Salo da Sarrafa Harshe

Mawaƙi ya yi amfani da sassauƙan Salo wajen isar da saƙonsa. Sai dai akwai adon harshe kamar su ba’a da zambo da kirari da habaici da baƙar Magana. Haka kuma akwai alamtarwa da dabbantarwa da kamantawa da sauransu. Misalin inda ya yi zambo a waƙar ya haɗa da baiti na 32 da 33 da 34 da da 41 da 46 da 47 da 52 da 56 da 57 da 66 da 88 da 92 da 158 da 175 da kuma 176. Misali a baiti na 32 ya ce :

32. Ashe malami tsiya ne,

Kun ji Babur mai kaya da kowa.

33. Sai na ce kun gad an baƙin nan,

In ya yahe za mu dinga fama.

57. Akwai wani ma mai kama da Malam,

Gulma kwai shi yai yo iyawa.

5.0 Naɗewa

A wannan takarda an bayar da ma’anar siyasa da ma’anar jam’iyya da yadda mawaƙan siyasa suka sha gwagwarmayar neman ‘yanci da yadda suka riƙa faɗi-tashin tallata ‘yan takara daga matakai mabambanta da yadda suke tallata jam’iyya. Wannan aikin ya duba yadda irin waɗannan mawaƙa suka riƙa aiwatar da waƙoƙinsu na siyasa masu jigogi mabambanta, tun daga jamhuriya ta farko da jamhuriya ta biyu da ta uku da kuma wacce ake ciki a yanzu wato jamhuriya ta huɗu. Haƙiƙa wannan aiki ne da zai bayar da haske musamman ga manazarta Adabin Hausa da kuma ma su sha’awar waƙoƙin siyasa. Don haka an samar da sharhin wasu daga cikin waɗannan waƙoƙi na siysa, an kuma kawo salonsu da jigoginsu da yadda aka yi afani da dabaru iri-iri wajen isar da wannan saƙo.

Manazarta

Auta, A.L. (2008). Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a Ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Birniwa, H.A. (2010). “Matsayin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Wajen Yaƙin neman zaɓe: Misali daga Jamhuriya ta Ɗaya da ta Biyu”. Takardar da aka Gabatar a Taron  Ƙara wa Juna Sani, Katsina: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.

CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Ahamadu Bello University Press Limited.

Ɗangulbi, A.R. (2003). “Siyasa a Nijeriya: Gudunmuwar Marubuta Waƙoƙin Siyasa naHausa ga Kafa Dimokraɗiyya.” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɗan’illela, A. (2010). Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Nazari a kan Jihohin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara.” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar gadon feɗe waƙa. Zaria: Amana Publishers Ltd.

Ɗangambo, A. (1986). “Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano  Triumph.

Ɗiso, A.H (1997). Zambo da Yabo a Matsayin Dabarun Jawo Hankali a Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Hausa. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen HarsunanNijeriya. Jami’ar Bayero.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose And Popular Culture in Hausa. London EPU Press.

Gusau, S. M (1984).(2) Nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙin baka na Hausa. Cyclostyled Edition. Kano: Sashen koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.

Jumare, B. (2008). Tarken Waƙoƙi Uku na Mudi Spikin. Kundin Digiri na Farko. Zaria: Sashen Harsunan Nijeriya da Al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello.

Mashi, M.B. (1986). Waƙoƙin Baka na Siyasa: Dalilansu da Tasirinsu ga Rayuwar Hausawa.  Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Mukhtar, I. (2006). Gudunmawar Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Wajen Adana Tarihin Siyasar Nijeriya. Algaita: Journal Of Current Research In Hausa Studies, (14).

Sa’id, B. (2002). Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin a Sakkwato, Kabi da  Zamfara. Kundin Digiri na Uku. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya. Kano: BayeroUniversity, Nigeria.

Yahaya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Yahaya, A.B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Yahaya, I.Y. & Ɗangambo, A. (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: NNPC.

Yakawada, M.T. (1987). Tarkakken Matanin Waƙar ‘Kanzil Azim’ ta Aliyu Namangi. M.A Arts. Department of Nigeria and African Languages. Zaria: AhmaduBello University,  Nigeria.

Siyasa

Post a Comment

0 Comments