Ticker

6/recent/ticker-posts

Kididdigar Wakilin Suna a Wakar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya Ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa

Citation: Hassan, S. and Nalado, N. (2024). Ƙididdigar Wakilin Suna a Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 468-477. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.058.

ƘIDIDDIGAR WAKILIN SUNA A WAƘAR TA’AZIYYA GA ALHAZAN NIJERIYA TA NASIRU JIKAN SARKI AGADASAWA

Sani Hassan

Nuhu Nalado

Sashen Nazarin Harshen Hausa, Tsangayar Nazarin Ilimin Sakandare Ɓangaren Harsuna, Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita

Tsakure: 

Wakilin suna yana ɗaya daga cikin muhimman rukunnan nahawu, don kusan duk zancen da za a yi a rubuce ko a baka, sai an samu ɗaya daga cikin nau’o’insa. Don haka, manufar wannan takarda ita ce ta ƙididdige nau’o’i da kuma yawa ko adadin wakilan sunayen da suke cikin waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa. An gudanar da wannan nazari ta hanyar karanta waƙar domin fito da yawan nau’o’i da kuma ƙididdige adadin wakilan sunayen da suke cikinta. Sannan kuma, an gabatar da sakamakon wannan takarda ta hanyar amfani da taswirar kara-tsaye (bar chart) wajen ƙididdige wakilan sunayen da ke cikin waƙar. Takardar ta gano yadda marubucin waƙar ya yi amfani da wakilan sunaye guda casa’in da huɗu wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Binciken ya nuna cewa marubucin waƙar ya ambaci nau’in wakilin suna rakaɓau sau 23 a waƙar tasa. Sannan ya ambaci wakilin suna zagin aikatau sau (45). Ya kuma ambaci wakilin suna mallakau sau 15. Har wa yau, marubucin ya ambaci wakilin suna dogarau sau 4, haka shi ma wakilin suna gama-gari ya ambae shi sau 4a cikin waƙarsa. Har ila yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna nunau sau 2. Daga ƙarshe kuma, marubucin ya yi amfani da wakilin suna kaikaitau sau 1 rak a cikin waƙar tasa..

Fitilun Kalmomi: Ƙididdiga, Wakilin Suna, Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya, Nasiru Jikan Sarki Agadasawa

Gabatarwa

Wakilin suna yana ɗaya daga cikin rukunnai ko azuzuwan nahawu a kowane harshen da ake samun kalmomin da suke wakilcin suna a zantuka na yau da kullum. Harshen Hausa yana ɗaya daga cikin harsunan da suke amfani da wasu mabambantan kalmomin da suke taka rawar wakilcin suna a tsarin nahawunsu. Shi ya sa sanin sa yake da matuƙar muhimmanci a fagen ilimin nahawun Hausa, kuma shi ne abu na biyu da ake farawa kawowa baya ga suna a tsarin rukunnai ko azuzuwan nahawun Hausa. Kasancewarsa ɗaya daga cikin muhimman rukunnan nahawu ya sa ake samun shi a kowane zance na baka ko rubutacce. Kuma shi wannan rukuni na nahawu yana bayyana a mabambantan muhallai a zantuka na yau da kullum ko a rubuttun bayanai irin su rubutattun wasannin kwaikwayo ko rubutattun waƙoƙi ko tatsunniyoyi ko labarai, da dai sauransu. Wannan ne ya sa wannan takarda ta yi nazarin da ya ƙididdige ire-iren  wakilin suna a waƙar da Nasiru Jikan Sarki Agadasawa ya rubuta mai suna Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya. Ita wannan waƙa, waƙa ce wadda aka isar da saƙonta a cikin baitoci talatin da huɗu (34), kuma kowane baiti ƙwar biyu ne. Ma’ana, kowane baiti yana ɗauke da ɗango biyu (2). Wannan nazari ne da ya ƙididdige adadi ko yawan wakilan sunayen da marubucin ya yi amfani da su wajen kulla zaren tunanin waƙarsa ko saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Kuma ya yi bayanin nau’o’in wakilan sunayen da aka samu a cikin wannan waƙa.

2.0 Taƙaitaccen Tarihin Marubucin Waƙar (Nasiru Jikan Sarki Agadasawa)

Shi marubucin wannan shi ne Alhaji Nasiru Jikan Sarki Agadasawa. An haife shi a Agadasawa a gida mai lamba ɗari da shida (106) a cikin birnin Kano a shekarar alif ɗari tara da arba’in da shida (1946).Ya yi makarantar allo a hannun Alhaji Amadu Ceɗiyar Kudu daga alif ɗari tara da hamzi (1950) zuwa alif ɗari tara da sittin da biyu (1962). Sannan ya yi karatun ilimin fiƙihu da kuma na tauhidi. Bayan nan kuma, ya yi yaƙi da jahilci a shekarar alif ɗari tara da sittin da takwas (1968) zuwa alif ɗari tara da saba’in (1970) a makarantar Ɗantata. A yanzu kuma, ya rubuta waƙoƙi kusan tamanin da biyar (85) a kan abubuwan da suka shafi addini da gargaɗi da yabo da sauransu. Ya zama mamba na Hikima Kulob a cikin shekara ta alif ɗari tara da sittin da bakwai (1967). Alhaji Nasiru marubuci ne, kuma jikan sarkin Pawan Agadasawa ne. (Hikima Kulob, 1979, sh. 93).

3.0 Ma’anar Wakilin Suna

Zarruk da Kafin Hausa da kuma Al-Hassan (2005, sh.36), sun ce “Wakilin suna su ne kalmomin da ake iya amfani da su a maimakon sunaye. Wato maimakon a ambaci sunan abu kai tsaye, sai a yi amfani da wata kalma a maadadin abin.” Shi kuma Sani (2005, sh. 62) cewa ya yi “Kamar yadda sunan yake nuni, wakilin suna nau’i ne na kalma da ke wakiltar suna a magana.” Haka kuma, Zaria (1981, sh. 8) ya nuna cewa, “Wakilan sunaye sukan fito idan sunaye ba su samu damar fitowa ba. Ko dai da yake lokaci da dama wakilan sunaye na iya fitowa tare da sunaye a jimlolin Hausa.” Shi kuma Garba (2021, sh. 101), cewa ya yi, “Wakilan sunaye su ne kalmomin da suke maye gurbin suna ko sunaye.” Nkopuruk da Odusina (2018, sh. 2), sun cewa “Wakilin suna ɓangare ne na nahawu wanda yake zuwa a madadin suna ko rukunin suna.” Haka kuma, Andersen (2014, para. 1), ya ce “Ana amfani da wakilin suna wajen wakilcin sunan da aka rika aka ambata a baya.”

Shi kuma Caulfield (2022, para. 1), ya nuna cewa “Wakilin suna kalma ce da take zuwa a muhallin suna domin kauce wa maimaicin sunan da aka ambata a baya.” Har ila yau, Gelderen (2011, para. 2), ya ce “Kalmar wakilin suna tana nufin abubuwan da suke nuna cewa wannan yana a matsayin suna ko kuma yana wakilcin suna.” Sannan Wren (1983, sh. 141), ya nuna cewa “Kalmar da ake amfani da ita a madadin suna wadda take taƙaita tsawon jimla, kuma ta ƙara mata inganci ita ce wakilin suna.” Daga nan, sai Wiharjokusumo (2015, sh. 96) ya ce “Kalmomin da ake amfani da su a muhallin suna su ne ake kira wakilan sunaye.”Ta la’akari da waɗannan ma’anoni na wakilin suna, za a iya cewa wakilin suna wasu mabambantan kalmomi ne da ake amfani da su wajen wakilcin sunan da ake magana a kan sa. Kuma waɗannan kalmomi sukan zama wakilan sunaye a cikin zance idan har ba su zo tare da sunan da suke wakilta ba, idan kuma suka zo tare da shi, to sun zama mafayyata.

4.0 Yanaye-Yanayen Wakilin Suna a Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki

A wannan waƙa, an gano cewa marubucin ya yi amfani da nau’in wakilin suna rakaɓau da wakilin suna zagin aikatau da wakilin suna mallakau. Hakazalika, ya yi amfani da wakilin suna gama-gari da wakilin suna nunau da wakilin suna dogarau da kuma wakilin suna kaikaitau a wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi ga al’umma. Don haka, a wannan takarda an ƙididdige yawan kowane nau’i na wakilin suna tare da bayanin muhallin da aka yi amfani da shi a wannan waƙa kamar yadda ya bayyana a bayanan da suke biye.

4.1 Wakilin Suna Rakaɓau

Shi wannan nau’i na wakilin suna a rakaɓe yake, kuma yana cin gashin kansa. Wato yana iya zama shi kaɗai ba tare da ya haɗu da wani abu daban ba. (Sani, 2005, sh. 63). Shi wannan nau’i na wakilin suna shi ne wasu suke kira da wakilin suna raɓewa. Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wannan nau’i na wakilin suna wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi ga jama’a. Gaba ɗaya ya yi amfani da wakilin suna rakaɓau guda ashirin da uku (23), kuma za a iya kallon su kamar haka.

4.1.1 Wakilin Suna Rakaɓau Ajin Mutum na Ɗaya

 Bincike ya tabbatar da cewa, marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wakilin suna rakaɓau ajin mutum na ɗaya sau goma sha ɗaya (11).  Don marubucin ya yi amfani da wakilin suna mai nuna jinsin mace da namiji ‘ni’ a baiti na4, ɗango na 2 “Kowa ya saurare ni babu hayaniya” da baiti na 19, ɗango na 1 “Kar wai ka ce ni ai ɗariƙata daban”da kuma baiti na 23, ɗnago na 1“Ni ne fa Nasiru naku Jikan Sarki”. Haka kuma, ya yi amfani da ɗayan nau’in wakilin suna ajin mutum na ɗaya mai nuna jinsin mace da namiji ‘na’ a baiti na 1, ɗango na 1 “Bismil Ilahi Jalla na biɗi taimako” da baiti na 19, ɗango na 2 “Ba na ɗariƙar wane ko ƙwaya ɗaya”da kuma baiti na 29, ɗango na 2 “Na nan kiyayewa gare ka lahiya”. Har wa yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna ajin mutum na ɗaya mai nuna jam’in mace da namiji a baiti na 3, ɗango na 2 “Ka yi mu ne don shugabanmu abin biya” da kuma baiti na 13, ɗango na 2 “Ita ce isharar wanda yai mu baki ɗaya.”A baiti na 15, ɗango na 2 ya fito sau 2 “Mu tsaya ga Allah wanda yai mu gaba ɗaya.”Daga nan, sai a baiti na 17, ɗango na 2 “Yai gafara a gare mu du baki ɗaya” da kuma baiti na 22, ɗango na 2 “Sun kai mu hanya wadda ba mai shan wuya.”  Ga bayanin adadin fitowar kowane ɗaya daga cikinsu a wnnan hoto da yake a ƙasa. 001

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli bayanan da suke a cikin wannan hoto na taswirar kara-tsaye (bar chart)da yake nuna yawa ko adadin fitowar kowane ɗaya daga cikin wakilan sunayen da aka yi bayani a sama. Hoton ya nuna cewa, marubucin waƙar ya fi amfani da wakilin suna mai nuna jam’i ‘mu’ daga cikin sauran wakilan sunayen da suke a ajin mutum na ɗaya. Don marubucin ya yi amfani da kalmar ‘mu’ sau biyar a matsayin wakilin suna rakaɓau. Haka kuma, ya yi amfani da kalmar ‘ni’ da kuma ‘na’ kowace sau uku kamar yadda hoton da ke sama ya nuna.

4.1.2 Wakilin Suna Rakaɓau Ajin Mutum na Biyu

Wakilan sunayen da suke a wannan aji, su ne wakilan sunayen da suke maye gurbin sunan wanda ake magana da shi, wato kai ko ke ko kuma ku. Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da nau’in wakilin suna ‘kai’ sau ɗaya rak a cikin waƙarsa. Don wannan nau’i na wakilin suna na ‘kai’ ya bayyana ne a baiti na 29, ɗango na 1 “Ya Rabbana kai ne Hafizu da ba i kai”. Sannan kuma ya yi amfani da wanda yake nuna jinsin namiji a ajin mutum na biyu, wato ‘ka’ sau 3 a cikin waƙarsa. Inda ya bayyana a baiti na 1, ɗango na 2 “A gare ka ya Allahu Sarki kai ɗaya” da baiti na 29, ɗango na 1“Na nan kiyayewa gare ka lahiya” da kuma baiti na 30, ɗango na 1 “Ya Rabbana Allah ka amsa du’a’iya.” Sai dai marubucin bai yi amfani da wakilin sunan da yake nuni da jinsin mace a ajin mutum na biyu ba. Za a iya ganin adadin yawan wakilin sunan da aka yi amfani da shi a wannan hoto da yake biye. 002

Kididdigar Wakilin Suna

A bayanan da suka bayyana a wannan hoto na taswirar kara-tsaye (bar chart)da yake a sama sun nuna cewa, a ɓangaren wakilin suna rakaɓau mai nuni da ajin mutum na biyu, marubucin ya fi amfani da kalmar wakilin suna mai nuna jam’i ‘ka’ daga cikin sauran wakilan sunayen. Don a nan kalmar ta fita sau uku a cikin waƙar. Daga nan, sai kalmar ‘kai’ mai wakiltar jinsin namiji ta fito sau 1 rak a cikin  waƙar. Sai dai marubucin bai yi amfani da wakilin suna mai nuni da jinsin mace ‘ke’ a cikin waƙarsa wanda ya zo a matsayin rakaɓau ajin mutum na biyu.

4.1.3 Wakilin Suna Rakaɓau Ajin Mutum na Uku

Shi kuma wannan nau’i na wakilin suna, shi ne wanda yake maye gurbin sunan wanda ko waɗanda ake magana a kan su, wato ‘shi’ ko ‘ita’ ko ‘su’. Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wannan nau’i na wakilin suna rakaɓau ajin mutum na uku wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Don ya yi amfani da wakilin suna rakaɓau ajin mutum na uku mai nuni da jinsin namij ‘shi’ sau 3. Inda ya bayyana a baiti na 5, ɗango na 2 “Amma fa yanzu ba za ku ji shi ba ko ɗaya”da baiti 16, ɗango na 1“Istingifari du mu dinga kula da shi” da kuma baiti na 27, ɗango na 2 “Ya Rabbana sawaƙe shi du baki ɗaya.” Sannan kuma, ya yi amfani da wakilin suna mai nuna jinsin mace ‘ita’ sau ɗaya a waƙarsa, wanda ya bayyana a baiti na 13, ɗango na 2 “Ita ce isharar wanda yai mu baki ɗaya.”

Har ila yau, ya yi amfani da wakilin suna rakaɓau ‘su’ mai nuna jam’in a ajin mutum na uku. Don wannan nau’i na wakilin suna ya bayyana sau 4 a cikin waƙarsa. Wannan wakilin suna ya fito a baiti na 12, ɗango na 1 “Ya Rabbana kai gafara a gare su du” da kuma baiti na 21, ɗango na 1 “Sun ce idan muka bi su tsira za mu yi.”Har wa yau, ya fito a baiti na 21, ɗango na 2“A gidan ƙiyama to mu bi su da gaskiya” da kuma bait na 32, ɗango na 1 “Ya Rabbana ka nufa su dawo lafiya.” Za a iya ganin adadin bayyanar kowane a wannan hoto da yake biye. 003

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli bayanan da suka bayyana a wannan hotona taswirar kara-tsaye (bar chart) da yake a sama, sun nuna cewa, a ɓangaren wakilin suna rakaɓau mai nuni da ajin mutum na uku, marubucin ya fi amfani da kalmar wakilin suna mai nuna jinsin namiji ‘shi’ a waƙar tasa. Don a nan kalmar ta fita sau uku a cikin waƙar. Daga nan, sai kalmar ‘ita’ mai wakiltar jinsin mace ta fito sau 1 rak a cikin  waƙar. Haka kuma, marubucin ya yi amfani da wakilin suna mai nuna jam’i a jinsin mace da namiji ‘su’ a cikin waƙarsa wanda ya zo a matsayin rakaɓau ajin mutum na uku.

4.2 Wakilin Suna Zagin Aikatau

Shi kuma wannan nau’i na wakilin suna, kamar yadda sunan yake nuni, koyaushe zuwa yake yi kafin kalmar aikatau ko kuma a ce gaban aikatau. Wato da ka gan shi za ka ga aikatau biye da shi. (Sani, 2005, sh. 64). Dangane da abin da ya shafi wannan aji na wakilin suna, marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wasu mabambantan kalmomin zagin aikatau wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Misali, a baiti na 2, ɗango na 1 “Kuma nai salati ga Annabinmu Muhammadu” da baiti na 5, ɗango na 1 “Da na yi niyya zan taho da yabon Kano” ya yi amfani da ‘na’ a matsayin wakilin suna zagin aikatau, kuma ya fito sau biyu rak a waƙar tasa. Haka nan, ya yi amfani da kalmar ‘ka’ sau 9 a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Inda ya fito a baiti na 3 ɗango na 2“Ka yi mu ne don shugabanmu abin biya” da baiti na 10, ɗango na 2 “Ya Rabbana ka ji ƙansu ya Sarki Ɗaya” da kuma baiti na 12, ɗango na 1 “Ya Rabbana kai gafara a gare su du.”Haka kuma, ya fito a baiti na 19, ɗango na 1“Kar wai ka ce ni ai ɗariƙata daban” da kuma baiti na 24, ɗango na 1 “Wannan mutane Rabbana ka ji ƙansu du.” Bayan wannan kuma, wannan wakilin suna na ‘ka’ ya fito a baiti na 26, ɗango na 2“Ya Rabbana ka jiƙanmu ya Sarki ɗaya” da baiti na 30, ɗango na 2 “Ya Rabbana Allah ka amsa du’a’iya.” Haka nan, ya fito a baiti na 32, ɗango na 1“Ka ba su sauƙi Rabbana ya Rabbana” da kuma baiti na 33, ɗango na 2 “Ya Rabbana ka nufa su dawo lafiya.”

Sannan marubucin ya yi amfani da ‘ku’ sau 5 a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Don ya bayyana sau 2 a baiti na 4, ɗango na 1 “To ‘yanuwana sai ku saurarar ku ji”, kuma ya fito a baiti na 5, ɗango na 2 “Amma fa yanzu ba za ku ji shi ba ko ɗaya” da baiti na 20, ɗango na 1 “Dukkan ɗariƙun Shehunanmu ku tabbata” da kuma baiti na 22, ɗango na 1 “Ku matso mu ƙanƙame Shehunanmu da kyau mu san.” Haka kuma, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘zan’ sau 2 a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Inda ya bayyana a baiti na 5, ɗango na 1 “Da na yi niyya zan taho da yabon Kano” da kuma baiti na 31, ɗango na 1 “Waɗanda du suka tsira zan masu addu’a”. Har wa yau, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘ta’ sau 4 a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Don kalmar ta bayyana a baiti na 6, ɗango na 1 “Domin akwai wata ƙaddara da ta afku ne” da kuma baiti na 6, ɗango na 2 “Ƙudurar Ta’ala ta wuce haka kun jiya.”Hakazalika, kalmar ta bayyana a baiti da baiti na 8, ɗango na 1 “Da faɗuwarsa wuta ta kama ciki nasa” da kuma baiti na 11, ɗango na 2 “Ni’ima ta tabbata gunsu yamma da safiya”. A baiti na 6, ɗango na 2 ne kawai marubucin ya yi amfani da kalmar ‘kun’ a matsayin wakilin suna zagin aikatau “Ƙudurar Ta’ala ta wuce haka kun jiya”, kuma kalmar ta fito sau ɗaya rak a cikin waƙar.

Sannan a baiti na 8, ɗango na 2 “Amma mutane arba’in sun sha wuya” da baiti na 9, ɗango na 2 “Ɗari da sittin sun mace baki ɗaya” da kuma baiti na 14, ɗango na 1 “Sun ƙare yin bautarsu tun a ƙasar Maka” marubucin ya yi amfani da ‘sun’ a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Hakazalika, a baiti na 21, ɗango na 1 “Sun ce idan muka bi su tsira za mu yi”da kuma baiti na 22, ɗango na 2 “Sun kai mu hanya wadda ba mai shan wuya” nan marubucin ya yi amfani da ‘sun’ a matsayin wakilin suna zagin aikatau, kuma ya fita sau 5 a waƙar tasa. Haka nan, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘suka’ sau 2 a matsayin wakilin suna zagin aikatau. Inda ya fito a baiti na 14, ɗango na 2 “Suka zo Kano aka karɓi ransu gaba ɗaya” da kuma baiti na 31, ɗango na 1 “Waɗanda du suka tsira zan masu addu’a.” Hakazalika, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘muka’ sau 1 rak a matsayin wakilin suna zagin aikatau a baiti na 21, ɗango na 1 “Sun ce idan muka bi su tsira za mu yi.” Haka nan, ya yi amfani da kalmar ‘muna’ ita ma sau 1 rak a matsayin wakilin suna zagin aikatau a baiti na 18, ɗango na 2 “In dai muna ƙaunar Rasulu da auliya.”

 Daga ƙarshe kuma, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘mu’ sau 7 a matsayin wakilin zagin aikatau. Don ya bayyana sau 2 a baiti na 15, ɗango na 2 “Mu tsaya ga Allah wanda yai mu gaba ɗaya” da baiti na 16, ɗango na 1 “Istingifari du mu dinga kula da shi” da kuma baiti na 17, ɗango na 1 “Safe da rana dare mu roƙi Ubangiji.” Hakazalika, ya fito a baiti na 21, ɗango na 1 “Sun ce idan muka bi su tsira za mu yi” da baiti na 21, ɗango na 2 “A gidan ƙiyama to mu bi su da gaskiya”, a amma baiti na 22, ɗango na 2 ya bayyana sau 2 “Ku matso mu ƙanƙame Shehunanmu da kyau mu san.” Za a iya ganin waɗannan bayanai a hoton da yake a ƙasa. 004

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli bayanan da suka bayyana a cikin wannan hotona taswirar kara-tsaye (bar chart), za a ga cewa marubucin ya yi amfani da mabambantan wakilin suna zagin aikatau guda 11 wajen isar da saƙonsa ga al’umma. Sannan za a ga cewa wakilin suna zagin aikatau ‘ka’ shi ne wanda marubucin ya fi amfani da shi, don ya ambace shi sau 9 a waƙar. Daga nan, sai ‘ya’ da ya ambata sau 8. Wanda yake bin wannan kuma shi ne ‘mu’ wanda aka ambata sau 7 a waƙar. Bayan wannan kuma, hoton ya nuna cewa, marubucin ya ambaci wakilin suna zagin aikatau ‘ku’ sau 5 a waƙarsa. Har wa yau, hoton ya nuna cewa, marubucin ya ambaci wakilin suna zagin aikatau ‘ta’ sau 4 a cikin waƙar tasa. Hakazalika, hoton ya nuna cewa marubucin ya ambaci wakilin suna zagin aikatau ‘na’ da kuma ‘zan’ kowane sau 2 a waƙar tasa. Har ila yau, marubucin ya yi amfani da kalmar ‘kun’ da ta ‘suka’ da kuma ta ‘muna’ a matsayin wakilin suna zagin aikatau sau ɗai-ɗai a cikin waƙarsa.

4.3 Wakilin Suna Mallakau

Shi kuma wannan nau’i na wakilin suna, shi ne wanda yake nuni da wanda ya mallaki wani abu. Kuma ana samun dogon wakilin suna mallakau da kuma gajeren wakilin suna mallakau. Dogon wakilin suna mallakau shi ne inda ake samun kalmomin suna cin gashin kansu, gajeren kuma, shi  koyaushe kalmomin ba su cin gashin kansu, suna jingine da sunan abin da aka mallaka.

Dangane da wannan nau’i na wakilin suna, marubucin ya yi amfani da shi wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Don marubucin ya kawo wasu kalmomin da suke ɗauke da nasabar gajerar mallaka har sau 12. Haka kuma, ya yi amfani da kalmomin doguwar mallaka guda biyu a cikin waƙarsa. Misali, a baiti na 2, ɗango na 1 “Kuma nai salati ga Annabinmu Muhammadu” da baiti na 2, ɗango na 2 “Manzonka ne kuma shugaban duka anbiya” da kuma baiti na 3, ɗango na 2 “Ka yi mu ne don shugabanmu abin biya.”Hakazalika, a baiti na 4, ɗango na 1 “To ‘yanuwana sai ku saurarar ku ji” da kuma baiti na 8 ɗango na 1 “Da faɗuwarsa wuta ta kama ciki nasa” marubucin ya yi amfani da gajeren wakilin suna mallakau. Har wa yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna mallakau a baiti na 9, ɗango na 1 “Mutum ɗari biyu cikinsa haƙiƙatan” da baiti na 11, ɗango na 2 “Ni’ima ta tabbata gunsu yamma da safiya” da kuma baiti na 14, ɗango na 1 “Sun ƙare yin bautarsu tun a ƙasar Maka.”Saikuma a baiti na 14, ɗango na 2 “Suka zo Kano aka karɓi ransu gaba ɗaya” da baiti na 16, ɗango na 2 “Har ma salati ga Annabinmu abin biya” da baiti na 19, ɗango na 1 “Kar wai ka ce ni ai ɗariƙata daban”da kuma baiti na 20, ɗango na 1 “Dukkan ɗariƙun Shehunanmu ku tabbata.” Bugu da ƙari, marubucin a baiti na 11, ɗango na 1 “Ya Rabbi sa rahama cikin ƙabari nasu” da kuma baiti na 23, ɗango na 1 “Ni ne fa Nasiru naku Jikan Sarki” ya yi amfani da dogon wakilin suna mallakau a waƙar tasa. 005

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli bayanan da suke a cikin wannan hotona taswirar kara-tsaye (bar chart)da yake sama, za a ga cewa bayanan suna nuna cewa marubucin wannan waƙa ta ‘Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya’ ya fi amfani da kalmomin da suke ɗauke da gajeren wakilin suna mallakau. Ma’ana, kalmomin da ya yi amfani da su na wakilin suna mallakau, sun fi karkata ga gajerar mallaka, don kalmomi biyu kacal ya yi amfani daa su na doguwar mallaka.

4.4 Wakilin Suna Dogarau

Wakilin suna dogarau, wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen bayani ko isar da saƙon da wani yanki na jimla da ba ya iya zama da kansa yake ɗauke da shi. (Traffis, 2022 para. 1). Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wasu daga cikin kalmomin wakilin suna dogarau. Don a baiti na 13, ɗango na 2 “Ita ce isharar wanda yai mu baki ɗaya” da kuma baiti na 15, ɗango na 2 “Mu tsaya ga Allah wanda yai mu gaba ɗaya” ya yi amfani da kalmar ‘wanda’ a matsayin wakilin suna dogarau. A baiti na 22, ɗango na 2 “Sun kai mu hanya wadda ba mai shan wuya”, ya yi amfani da kalmar ‘wadda’ a matsayin wakilin suna dogarau mai nuni da jinsin mace. Sai kuma a baiti na 31, ɗango na 1 “Waɗanda du suka tsira zan masu addu’a” ya yi amfani da kalmar waɗanda a matsayin wakilin suna dogarau mai nuni da jam’i. Za a iya ganin waɗannan bayanai a wannan hoto da ya zo a ƙasa. 006

Kididdigar Wakilin Suna

Bayanan da suke ƙunshe a cikin hoton da yake samana taswirar kara-tsaye (bar chart) suna bayyana cewa marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wakilin suna dogarau jinsin namiji sau 2 a wajen isar da waƙarsa. Sannan ya yi amfani da mai nuni da jinsin mace sau 1, sai wanda yake nuna jam’i shi ma sau 1.

4.5 Wakilin Suna Gama-Gari

Shi kuma wannan nau’i na wakilin suna, wasu kalmomi ne ake amfani da su a muhallin suna, domin su wakilci kowane irin abu ko al’amari. Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da irin wannan wakilin suna wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Saboda a baiti na 3, ɗango na 1 “Kai ne da komai duniya har lahira” da kuma baiti na 30, ɗango na 1 “Kai ne Ƙadiru bisa ga komai ka isa” ya kawo ɗaya daga cikin wannan nau’i na wakilin suna gama-gamri ‘komai’, Hakazalika, a baiti na 4, ɗango na 2 “Kowa ya saurare ni babu hayaniya” da kuma baiti na 15, ɗango na 1 “Kowa ya gane wagga aya ‘yan’uwa” ya kawo wani nau’in wakilin suna gama-gari ‘kowa’ wanda yake wakiltar abu mai rai namiji. Za a iya ganin waɗannan bayanai a wannan hoto da yake biye. 007

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli wannan hoto da yake a sama na taswirar kara-tsaye (bar chart), za a ga cewa yana bayanin adadin wakilin suna gama-gari da wannan marubucin waƙar ya yi amfani da su wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa. Ma’ana’ bayanan hoton sun nuna cewa marubucin waƙar ya yi amfani da kalmar ‘komai’ da kuma ‘kowa’, sannan kowace kalma ya ambace ta sau 2 a cikin waƙar tasa.

4.6 Wakilin Suna Nunau

Shi kuma irin wannan nau’i na wakilin suna, nuni yake yi da nisa ko kusancin abin da ake magana a kan sa da shi mai maganar. Wato kalmomi ne da ake amfani da su domin nuna yadda abu ya kasance kusa ko nesa da maimaga. Wannan nau’i na wakilin suna ya kasance cikin nau’ikan wakilan sunayen da wannan marubuci ya yi amfani da su wajen shirya ko ƙulla zaren tunaninsa. Domin a baiti na 13, ɗango na 1 “To ‘yan’uwa wannan fa aya ce haka,”ya kawo irin wannan nau’i na wakilin suna mai nuni da kusancin abu da mai magana, jinsin mace ko namiji ‘wannan’, kuma sau 1 marubucin ya ambace shi a waƙarsa. Haka kuma, a baiti na 33, ɗango na 1 “Sauran waɗancan don karamar Annabi” marubucin ya kawo wani daga cikin wannan nau’i na wakilin suna nunau mai nuni da nisan abu da mai magana, kuma mai nuna jam’i. 008

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka kalli bayanan da wannan hotona taswirar kara-tsaye (bar chart) yake ɗauke da su, za a ga cewa hoton yana bayyana adadin wakilin suna nunau da marubucin wannan waƙa ya yi amfani da su wajen isar da saƙonsa ga al’umma. A taƙaice hoton ya nuna yadda marubucin ya yi amfani da kalmar‘wannan’ da kuma ‘waɗancan’ kacal a matsayin wakilin suna nunau a waƙarsa.

4.7 Wakilin Suna Kaikaitau

Shi kuma irin wannan nau’i na wakilin suna, wasu kalmomi ne ake amfani da su domin a ɓoye sunan wanda ake magana a kan sa ko waɗanda ake magana a kan su. Wato kalmomin da ake amfani da su ba su bayyana wanda ake magana a kan sa kai tsaye, sai dai ta raragefe. Irin wannan nau’i na wakilin suna ya bayyana a cikin waƙar sau 1 kacal. Ma’ana, marubucin wannan waƙa ya yi amfani da wannan nau’i na wakilin suna kaikaitau sau 1 ƙwal, wato a baiti na 19, ɗango na 2 “Ba na ɗariƙar wane ko ƙwaya ɗaya”. Wakilin sunan da ya yi amfani da shi kuwa shi ne ‘wane’.  Za a iya ganin wannan bayani a cikin hoton da yake a ƙasa. 009

Kididdigar Wakilin Suna

Idan aka lura da bayanan da suka zo a cikin wannan hoto na taswirar kara-tsaye da yake a sama, za a ga yana nuna cewa, daga cikin ire-iren wakilin suna kaikaitau marubucin ya yi amfani da guda 1 ne kawai, kuma shi ma sau 1 ƙwal aka ambace shi. Kenan, ba a ambaci sauran wakilan sunayen a wannan waƙar ba.

Sakamakon Bincike

A sakamakon ƙididdigar da bincike ya yi a kan wakilan sunayen da suke a cikin waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikaan sarki Agadasawa. Bincike ya gano cewa, marubucin waƙar ya yi amfani da wakilan sunaye guda casa’in da huɗu (94) wajen isar da saƙonsa ga al’umma. Don marubucin ya yi ambaci wasu nau’o’in wakilin suna rakaɓau sau 23. Sannan ya ambaci wasu nau’o’in wakilin suna zagin aikatau har sau 45. Hakazalika, marubucin ya yi ambaci wakilin suna mallakau sau 15. Hakazalika, marubucin ya yi amfani da wakilin suna dogarau sau 4. Har ila yau, ya yi amfani da wakilin suna gama-gari sau 4. a waƙar tasa. Dangane da abin da ya shafi wakilin suna nunau kuwa, marubucin ya ambace sau 2 rak a cikin waƙar. Inda kuma ya ambaci wakilin suna kaikaitau sau 1 ƙwal a cikin waƙar tasa. Bugu da ƙari, za a iya ganin waɗannan bayanai a cikin wannan hoto na taswirar kara-tsaye (bar chart) da yake a ƙasan waɗannan bayanai. 010

Kididdigar Wakilin Suna

Kammalawa

Wannan takarda ta yi nazari tare da ƙidddige yawa ko adadin wakilan sunayen da marubucin wannan waƙa ta Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya Nasiru Jikan Sarki Agadasawa ya rubuta. Sannan takardar ta yi nasarar bayanin ire-iren wakilan sunayen da marubucin ya yi amfani da su wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Daga cikin wakilan sunayen da takardar ta gano kuma ta ƙididdige yawansu akwai wakilin suna rakaɓau da wakilin suna zagin aikatau da kuma wakilin suna mallakau. Har ila yau, takardar ta fito da wakilin suna gama-gari da wakilin suna dogarau da wakilin suna nunau da kuma wakilin suna kaikaitau.

Manazarta

Andersen, S. (2014). Pronouns: Cohesion within Praghraph. www.sjsu.edu/writingcenter

Caulfield, J. (2022). What is pronoun? Definition, types and eɗamples. www.scribbr.com/pronoun

Garba, F. A. (2021).  “A Study on tha Comparatiɓe Analysis of Hausa and Jar Pronouns of Northern Nigerira.” International Journal of Language and Linguistics, 9(3), 100-105. https://www.sciencepublishingcomp.com/i/ijll

Gelderen, E. (2022). Pronouns. Oɗford Bibliographies. www.oɗfordbibliographies.com

Hikima Kulob, (1979). Waƙoƙin Hikima. Ibadan: Uniɓersity Press.

Nkopuruk, I. & Odusina, K. S. (2018). The English pronoun and their Usage. www.researchgate.net/publication/327542058

Sani, M. A. Z. (2005). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. Ibadan: Uniɓersity Press.

Traffis, C. (2021). What is Relatiɓe Pronoun and how does it work? www.grammarly.com/blog/relatiɓe-pronoun

Wren (1983). High School Englishe Grammar and Composition (34thedt.). New Delhi: S. Chard & Co Ltd.

Wiharjokusumo, P. (2015). The Analysis of Pronoun in English Ɓiewed fron Syntactical Perspectiɓe. Journal of Darma Agung Medan, ƊƊIII(1), 96-101. www.gogle.com/journaldarmaagung

Zaria, A. B. (1981). Nahawun Hausa. Ikeja, Lagos: Thomas Nelson Nigeria Limited.

Zarruk, R. M., Kafin Hausa, A. A. & Al-Hassan, B.S.Y. (2005). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. Ibadan: Uniɓrsity Press.

Ratayen Waƙar ‘Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya’ ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa

1. Bismil Ilahi Jalla na biɗi taimako,

A gare ka ya Allahu Sarki kai ɗaya.

2. Kuma nai salati ga Annabinmu Muhammadu,

Manzonka ne kuma shugaban duka anbiya.

3. Kai ne da komai duniya har lahira,

Ka yi mu ne don shugabanmu abin biya.

4. To ‘yanuwana sai ku saurarar ku ji,

Kowa ya saurare ni babu hayaniya.

5. Da na yi niyya zan taho da yabon Kano,

Amma fa yanzu ba za ku ji shi ba ko ɗaya.

6. Domin akwai wata ƙaddara da ta afku ne,

Ƙudurar Ta’ala ta wuce haka kun jiya.

7. Jirgi ya taso tun a Saudi Arebiya,

Da ya zo Kano kuma sai ya faɗi gaba ɗaya.

8. Da faɗuwarsa wuta ta kama ciki nasa,

Amma mutane arba’in sun sha wuya,

9. Mutum ɗari biyu cikinsa haƙiƙatan,

Ɗari da sittin sun mace baki ɗaya.

10. Ya Rabbana ya Rabbana ya Wahidin,

Ya Rabbana ka ji ƙansu ya Sarki Ɗaya.

11. Ya Rabbi sa rahama cikin ƙabari nasu,

Ni’ima ta tabbata gunsu yamma da safiya.

12. Ya Rabbana kai gafara a gare su du,

Domin Rasulillahi manzon gaskiya.

13. To ‘yan’uwa wannan fa aya ce haka,

Ita ce isharar wanda yai mu baki ɗaya,

14. Sun ƙare yin bautarsu tun a ƙasar Maka

Suka zo Kano aka karɓi ransu gaba ɗaya.

15. Kowa ya gane wagga aya ‘yan’uwa,

Mu tsaya ga Allah wanda yai mu gaba ɗaya.

16. Istingifari du mu dinga kula da shi,

Har ma salati ga Annabinmu abin biya.

17. Safe da rana dare mu roƙi Ubangiji,

Yai gafara a gare mu du baki ɗaya.

18. Haɗa kan Musulmi dole ya zama wajibi,

In dai muna ƙaunar Rasulu da auliya.

19. Kar wai ka ce ni ai ɗariƙata daban,

Ba na ɗariƙar wane ko ƙwaya ɗaya.

20. Dukkan ɗariƙun Shehunanmu ku tabbata,

Hanya guda ɗaya ce haƙiƙar gaskiya.

21. Sun ce idan muka bi su tsira za mu yi,

A gidan ƙiyama to mu bi su da gaskiya.

22. Ku matso mu ƙanƙame Shehunanmu da kyau mu san,

Sun kai mu hanya wadda ba mai shan wuya.

23. Ni ne fa Nasiru naku Jikan Sarki,

Baba ga Dauda har Hadija gaba ɗaya.

24. Wannan mutane Rabbana ka ji ƙansu du,

Domin Rasulillahi manzon gaskiya.

25. Ya Rabbi gafarta wa baba Abubakar,

Domin karamar auliya’u gaba ɗaya.

26. Dukkan Musulmi Rabbi gafarta mana,

Ya Rabbana ka jiƙanmu ya Sarki ɗaya.

27. Haɗarin da ke afko irinsa daban daban,

Ya Rabbana sawaƙe shi du baki ɗaya.

28. Ya Rabbana kai ne Mujibu ga mai kira,

Kai ne Sami’u Ƙaribu ya Sarki ɗaya.

29. Ya Rabbana kai ne Hafizu da ba i kai,

Na nan kiyayewa gare ka lahiya.

30. Kai ne Ƙadiru bisa ga komai ka isa,

Ya Rabbana Allah ka amsa du’a’iya.

31. Waɗanda du suka tsira zan masu addu’a,

Ya Rabbana Allah zubo musu lafiya.

32. Ka ba su sauƙi Rabbana ya Rabbana,

Domin Rasulillahi manzon gaskiya.

33. Sauran waɗancan don karamar Annabi,

Ya Rabbana ka nufa su dawo lafiya.

34. Dukkan bala’i Rabbana kare mana,

 Domin karamar auliya’u gaba ɗaya.

Post a Comment

0 Comments