Ticker

6/recent/ticker-posts

Waka Makunsar Ilimi: Nazari Da Sharhi A Kan Jigon Koyar Da Ibada A Cikin Wasu Wakokin Malam Nasiru Kabara Kano

Takardar da aka gabatar a wurin Taron Ƙasa da Ƙasa a kan Rayuwa da Gudummawar Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, Wadda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci ta Jami’ar Bayero ta Shirya Daga 26 ga Watan Nuwanba, 2024 Zuwa 28 ga Watan Nuwanba, 2024.

WAƘA MAƘUNSAR ILIMI: NAZARI DA SHARHI A KAN JIGON KOYAR DA IBADA A CIKIN WASU WAƘOƘIN MALAM NASIRU KABARA KANO

Daga

Musa Muhammad Labaran
Ɗalibi a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero, Kano.
Lambar Waya: 08161747863
Imel: muhammadmusalabaran@gmail.com

Tsakure

Malam Nasiru Kabara ya shahara a ƙasar Hausa, wajen rubuce-rubuce a kan sha’anin addinin Musulunci. Kusan a iya cewa, tun bayan wucewar masu jihadi (Shehu Usman Ɗanfodiyo da muƙarrabansa), ba a samu wani wanda ya yi rubuce-rubuce masu tarin yawa a kan Musulunci ba kamar malam Nasiru Kabara. Daga cikin rubuce-rubucensa akwai rubutattun waƙoƙin Hausa masu ɗauke da jigogi daban-daban na addini. Babbar manufar wannan takarda ita ce, yin nazarin jigon koyar da ibada a cikin wasu waƙoƙin Malam Nasiru Kabara domin a ƙalailaice su, kuma a bayyana muhallai da yanayin yadda yake sassarƙa saƙonni a cikinsu domin ya samar da jigon ibada na kaɗaita Allah da tsoron Allah da salla da azumi da zakka da salatin Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam da kuma neman ilimi. An zaɓi Mazahabar Rubutacciyar Waƙa ta Ɗangambo (1975 da 1981 da 2007 da 2011) a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a kansa. Haka kuma, an yi amfani da hanyar bincike ta bi-bayani, wato hanyar sharhantawa wajen yin sharhi da ƙalailaice baitocin waƙoƙin nasa masu ɗauke da manya da ƙananan saƙonni na ibada a cikinsu. Takardar ta gano cewa, malam Nasiru Kabara yana kallon ibada ta fuska uku wajen koyarwa. Wato ibada ta dole da ta sunna da kuma wanda aka so a aikata ta. Haka kuma, takardar ta gano ana amfani da sauƙaƙan kalmomi da jumloli a duk lokacin da ya rubuta wata waƙa wadda take ɗauke da jigon koyar da ibada saɓanin yadda yake shirya kalmomi da jumloli masu tsauri a ragowar waƙoƙinsa na yabo da sufanci da makamantansu.

Keɓaɓɓun Kalmomi: ilimi, ibada, jigo, waƙa, malam Nasiru Kab


 

1.1              Gabatarwa

Ana zaton rubutacciyar waƙa ta farko da aka fara samu ta Hausa ita ce ‘Waƙar Yaƙin Badar’ wadda Wali ɗan Masani ya rubuta ta. Kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa ba su da wata tsayayyiyar hanyar karatu da rubutu. Wannan ya sa da Musulunci ya zo, sai Hausawa suka kama shi hannu biyu, kuma suka koye shi sosai. Wannan ya ba su damar da har suka fara samar da hanyar rubuta sautukan harshe Hausa cikin Larabci, wato ajami. An samu waɗanda suka yi rubuce-rubuce cikin Hausa da harufan Larabci (ajami) a wajejen ƙarni na 17, irin su Shitu ɗan Abdulra’uf da Wali ɗan Marina da sauransu. Cikin rubuce-rubucen nasu har da rubutattun waƙoƙi.

Rubutattun waƙoƙi sun samu bunƙasa ne a ƙarni na goma sha takwas (Ƙ18), wato lokacin da Shehu Usman ɗan Fodiyo ya bayyana, yana wa’azi da koyar da ilimi. Shehu Usman ya rubuta waƙoƙin cikin harshen Hausa amma da ajami, haka ma, ƙaninsa Abdullahi ɗan Fodiyo da ‘yarsa Nana Asma’u da ɗansa Isan Kware da ɗalibinsa Abdullahi mai Boɗingo da sauran masu Jihadi. Masu Jihadi sun gina waƙoƙinsu bisa jigon addini kawai, sai kuma ilimi na shari’a da na mulki da kuma na kimiya.

Malam Nasiru Kabara an yi shi ne a ƙarni na sha tara (19), amma ya ɗauko yanayi da sigar rubuta waƙoƙi irin na masu Jihadi. Waƙoƙin Malam Nasiru Kabara suna da siga da jigo da zubi da tsari iri ɗaya da na masu Jihadi. Wannan dalili ya sa kusan dukkanin waƙoƙin malam Nasiru Kabara yana gina su a bisa jigon addini. Ko dai jigonsu ya kasance na ibada ko wa’azi ko nasiha ko yabon Allah da Annabinsa ko yabon waliyai ko zikiri ko salatin Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam da sauran ayyukan alheri.

Wannan takarda ta yi nazarin wasu jigon ibada na “neman ilimi” da “shika-shikan Musulunci” wanda ya haɗar da tauhidi da sallah da tsarki da alwala da zakka da kuma azumi a wasu waƙoƙin Malam Nasiru Kabara guda huɗu, wato waƙar Jalalullahi da ta Kamalullahi da ta Tauhida da Zikiri da kuma waƙar Shika-shikan Musulunci. An yi amfani da Mazahabar Rubutacciyar Waƙa ta Ɗangambo (2007) a matsayin Mazahabar da aka ɗora wannan takarda. Wato an fito da wurare inda mawaƙin ya ambaci gundarin jigon waƙoƙin nasa. Sannan, an yi warwarar manya da ƙananan jigogin da mawaƙin ya gina jigon ibada da su a cikin waƙoƙin nasa. Haka kuma, an yi amfani da hanyar bincike ta bi-bayani, wato hanyar sharhantawa wajen yin sharhi da ƙalailaice wasu ɗangwaye masu ɗauke da ƙananan saƙonni na ibada.

1.2 Bayanan Sharar Fage

1.2.1 Tarihin Malam Nasiru Kabara

Zuriyar Shehin Malami Nasir Muhammad Al-Mukhtar Kabara ta fito ne daga garin Kabara na Timbuktu, wanda ke a Ƙasar Mali ta yau. Kakansa na uku Malam Umar (Omar), shi ne ya taso daga garin Kabara ta Timbuktun Ƙasar Mali. Malam Umar ya fara zama a Unguwar Adakawa da ke Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano, kafin ya yi ƙaura zuwa Unguwar Kabara da ke cikin Birnin Kano a yau, unguwar da sunanta ya samo asali daga inkiyar malamin.

A cikin shekarar 1787 da Malam Umar ya shiga Unguwar Kabara ta Kano, ya mayar da zauren gidansa makaranta wacce a yau ɗin nan ta zama katafariyar Cibiyar Ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka baki ɗaya,Wannan cibiya tana daga cikin daɗaɗɗun makarantun soro a Kano(Mujahid 2003, sh.9).

1.2.2 Haihuwar Malam Nasiru Kabara

An haifi Shehin Malami Nasir Muhammad Al-Mukhtar Kabara a ranar Alhamis, a watan Afrilu, a shekarar 1912, a garin Guringawa da ke Kano a Najeriya. Sunan mahaifinsa Malam Muhammdu Mukhtar, mahaifiyarsa kuma, sunanata malama Maryam Al-Azra’u ( Kabara 1988, sh.1 da Mujahid 2003, sh.10).

1.2.3 Rayuwar Malam Nasiru Kabara ta Karatu

Malam Nasiru Kabara ya sauke Alƙur’ani mai girma yana ɗan shekara tara (9) a wurin Malam Muhammadu Soron Ɗinki a garin Kano. Haka kuma, ya yi karatun littattafai a wurin malamai daban-daban. Ya karanta littattafan fiƙhu a wurin malaminsa kuma mariƙinsa malam Ibrahim Natsugune, inda ya karanta ‘littafin Ahalari’ da ‘Askari’ da ‘Risali’ da ‘Mukhtasar’ a wurinsa. A wurin nasa dai, ya karanta littattafan ‘nahawu’ da ‘Arabiya’.A nahawu ya karanra ‘Mulhamatil i’irab’ da ‘Ajurimiya’ da ‘Alfiya’ ta ‘Ibn Malik’. A Arabiya kuma, ya karanta ‘Mu’allaƙatul Sittata’ da ‘Muƙamatul Hariri’. Haka kuma, ya karanta ‘ilimin Hisabi’ da ‘ilimin zance (Manɗiƙ)’ a wurin nasa. Haka kuma, ya karanta ilimin Sufanci a wurin nasa, inda ya karanta ‘Alhakhu’ na ɗan Aɗa’ullahi da ‘Shuruhi’ na Abbadu da ‘Iƙazul Hamam’ da ‘Sharƙawiy’ da ‘Sharnabiy’ da sauransu. Sannan ya karanta littattafai guda hamsin na Tauhidi a wurin nasa. Daga cikinsu akwai ‘Bad’ul Amaliy’ da ‘Muhassilul Maƙasidi’ da ‘Nazmul Kubra’ da ‘Ida’atul Dajinnatu’ da ‘Dalilil Ƙa’idu’ da ‘Al-Munhalul Azab’ da ‘Minhajul Faridi’ (Furaidi) da ‘Matanul Sunusiyyatil Sab’u’ da ‘Manzumul Sunusiyyatil Khams’ da sauransu. Haka kuma, ya karanta littattafan Hadisi a wurinsa, irin su ‘littafin Ashafa’ da ‘Muwaɗɗa’ da ‘Muslim’ da ‘Bukhari’ da sauransu.

Malam Nasiru Kabara ya zauna a nan, a gaban Malam Ibrahim Alƙalin Alƙalai na Kano, inda ya karanta ‘Tafsiril Jalalaini’ da ‘Diya’ul Ta’awil’ da littafin ‘Mugni Alfiya’ ta ɗan Maliku da ‘Alfiya’ ta ɗan Mu’uɗi da ‘Alfiya’ ta Siyuɗi da ‘Ƙafiyatu’ ta ɗan Maliku da (mai baiti dubu uku) da littafin ‘Ƙawa’idil i’irab’ ta ɗan Hisham da ‘Manzumarsa’ da ‘Sharhin Manzumar’ tasa da littafin ‘Shuzurin Zahab wa Ƙaɗrul Nada’, duk a ilimin Larabci. Sannan ya karanta ‘Usulul fiƙhi’ a wurinsa, inda ya karanta ‘Kaukabul Saɗa’I’ da ‘Jam’il Jawami’I’. Haka kuma, ya karanta ‘ilimin zance’ da na ‘Aruli’ a wurinsa da kuma ilimin balaga, inda ya karanta ‘Tauharul Maknun’ da ‘Uƙudul Jiman’. A ilimin luga kuma, ya karanta ‘Ƙamusul Muhiɗ’ da ‘Masahil Munir’ da ‘Mukhtarul Sahhahu’ a wurinsa. A adabi ma ya karanta ‘Daliya’ da ‘Tahƙiƙul Mudud’. Haka kuma, ya karanta Al-Mu’allaƙatul Sittata da Ƙira’atul Tahƙiƙ wa Tadƙiƙ da sauran littattafi da ya karanta da yawa a wurin malamai daban-daban ( Kabara 1988, sh.1-4).

Malam Nasiru a lokacin yana neman ilimi, ya lazumci ziyartar manyan ɗakunan karatu irin na su:

1, Gidan Mataimakin Limamin Masallacin Birni wanda yake da zama a Unguwar Daneji.

2, Gidan Malam Ibrahim Babban Alƙalin Kano wanda ke Unguwar Yakasai.

3, Gidan Alhaji Musɗafa Kurawa Alƙalin Kotun Bichi wanda ya ke a unguwar Kurawa.

4, Gidan Mallam Abdulkarim wanda aka fi sani da Mallam Sambo da ke Unguwar Ciromawa.

5, Gidan Malam Inuwa Babban Limamin Zawiyya da ke Unguwar Mayanka.

Malam Nasiru Kabara ya kasance mai girmamawa da kwantar da kai ga malamansa a yayin karatu da kuma neman ƙarin haske, wannan ya sa malaman suka zamo suna maraba da shi a duk lokacin da yake da buƙata.

A wajejen 1940, Malam Nasiru Kabara ya mayar da hankali kan haɗa kan ƙungiyar Ƙadiriyya a Kano a ƙarkashin jagorancinsa, daga nan ya cigaba da buɗe masallatai da dama a duk faɗin ƙasar Hausa a matsayin ɓangaren ƙadiriyya, wanda hakan ya sa kuma ya zama jagoran Ƙadiriyya a Afirka (Shehu 2014, News Africa Hausa).

1.2.4 Shigar Malam Nasiru Kabara Ƙadiriya da Zamansa Muƙaddami

Lokacin da Malam Nasir Kabara yake da ƙananan shekaru, ya nemi a ba shi Ɗariƙar Ƙadiriyya, inda ya je wurin shehin wancan lokaci a Masallacin Halla-Halla a garin Kano. Amma saboda ƙanana shekarunsa, sai suka koro shi, suka kuma hana shi. Bayan wani lokaci da ya karɓi ɗariƙar Ƙadirya, ya zamo sanadin yaɗuwa da ɗaukakar Ɗarikar Ƙadiriyya a Afirka. A shekarar 1937, an yi tururuwar shiga Ɗariƙar Ƙadiriyya a cikin Birnin Kano. Daga cikin mutanen da suka samu karɓar Ɗarikar Ƙadiriyya a wannan shekara har da Malam Nasiru Kabara. Duk da cewa, Malam Ibrahim Natsugunne ya so a ce Malam Nasiru ya samu zamowa mamba na Ɗariƙar Ƙadiriyya a wannan shekarar, amma hakan ba ta samu ba, saboda ƙarancin shekarunsa, a lokacin yana da shekara goma sha bakwai (17) a duniya, sai Shehu Malam Sa’ad ya damƙa masa wazifa, duk kuwa da zuzzurfan ilimi da shi Nasir Muhammad yake da shi a fannin sufanci.

Malam Nasiru Kabara yana da salsalar karɓar Kalmar ‘La’ilaha Illallahu’ wadda ita ake ba wa mutum yayin da zai shiga Ƙadiriya. Malam Nasiru Kabara ya ƙarɓi Ɗariƙar Ƙadiriya ne daga ShehunsaMuhammadu Mujittafa’, shi kuma daga ‘Ni’imatullahi Muhammad Algaus’ daga ‘Mustafa Ma’ul’ainaini’ daga ‘Muhammadul Fadil’ daga ‘Muhammadu Maminu’ daga ‘Muhammadu Ɗalib’ daga ‘Akhyar Ahlu’ daga ‘Mukhtar Jayyi’ daga ‘Muhammadul Habibu’ daga ‘Ɗalibu A’al’ daga ‘Yahyal Sagir’ daga ‘Ahmadu Zuruƙ’ daga ‘Yahya Hadramiy’ daga ‘Aliyul Wafa’ daga ‘Muhammadu Wafa’ daga ‘Daudul Bakhiliya’ daga ‘Ahmadu ɗan Aɗa’ullahi Al-iskandariya’ daga ‘Abul Abbas Mursiy’ daga ‘Abul Hassan Aliyul Shazali’ daga ‘Abdulsalam ɗan Mashish’ daga ‘Muhammadu ɗan Abi bakar’ daga ‘Abu Najibu Al-Sabrurdiy’ daga ‘Aliyu ɗan Haitiy’ daga ‘Muhyidin Abu Muhammad Abdulƙadiri Jilani’ daga ‘Abul Wafa Kakisu Tajul Arafina’ daga ‘Nurul Arafina Abubakar Shubki’ daga ‘Ɗa’ifatul Sufiyati Abul Ƙasimu Junaid Alƙawaririy’ daga ‘Wakhaliy Sirri Al-saƙɗiy’ daga ‘Ma’aruf ɗan Kharran Buzil Karkhiy’ daga ‘Habibul Ajamiy’ daga ‘Hasanul Basari’ daga ‘Abul Hassanaini Aliyu ɗan Abu Ɗalib Aliyu’ (A.S) daga ‘Annabi Sallallahi alaihi wa alihi wa sallam’ (Kabara 2017, sh. 37-39)

A cikin wata shekara da Mai Martaba Sarkin Kano Abdullahi Bayero zai tafi aikin Hajji, sai Malam Nasiru Kabara ya rubuta wasiƙa ta hannun Wali Sulaiman zuwa ga Halifan Ƙadiriyya na wancan lokacin Shehi Abu al-Hassan as-Samman, yana mai roƙonsa da ya yi masa izinin zamowa muƙaddamin zawiyarsa. Mamaki ya yi matuƙar kama Shehi Abu al-Hassan da ganin irin wannan baƙon abu daga wannan mutum. Saboda haka nan-take ya aiko masa da kyautar riga jubba da hula da kuma rubutacciyar takardar naɗa shi muƙamin muƙaddamin na Ɗariƙar Ƙadiriyya Sammaniyya.

1.2.5 Gamuwar Malam Nasiru Kabara da Manyan Shehunan Ƙadiriya na Duniya

A shekarar 1949 Malam Nasiru Kabara ya samu zuwa aikin hajji da kansa, inda ya samu ganawa da Halifa Shehi Hashim da Shehi Muhammad dukkan su daga Murtaniya. A kan hanyarsa ta dawowa gida, ya biya ta ƙasar Sudan, inda ya samu ganawa da Sayyadi Shehi Muhammad al-Fatih ɗan Shehi Ƙaribullah, babban Shehin Sammaniyya ta Sudan, inda a nan ma ya sake karɓar izinin zama Muƙaddimin Sammaniyya-Ƙaribiyya a karo na biyu.

Tun kafin sannan, Malam Nasiru Kabara ya karɓi ijazarsa ta asali a Ɗariƙar Ƙadiriyya Kuntiyya da kuma Ahl al-Dar daga hannun babban malami Malam Ibrahim Natsugunne, wanda ya yi zamaninsa daga 1867 zuwa 1941.

Malam Nasiru Kabara ya samu ganawa da tushen gidajen Ƙadiriyya da ke a garuruwan Khartoum ta ƙasar Sudan da Timbuktu ta ƙasar Mali da kuma asalin tushen Ƙadiriyya da ke a Bagadada ta ƙasar Iraƙi a tsakankanin shekarar 1935 zuwa 1955. Ziyararsa zuwa Bagadada a shekarar 1953 ita ce tubalin zamowarsa Majimin Baƙadire da zaman shugabanta na Afirka, wanda wannan ce ta ba shi dama ta kafa masallacinsa na Ƙadiriyya.

Dukkan gidajen Ƙadiriyya na ciki da wajen Kano da ma faɗin Najeriya sun zama a ƙarƙashinsa tun daga shekarar 1958 har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

1.2.6 Wasu Daga Muƙamai da Matsayai da Malam Nasiru Kabara ya Riƙe

1, Ya zamo muƙaddamin Ɗariƙar Ƙadiriyya al-Sammaniyya a tsakankanin shekarar 1937 zuwa sama da ita.

2,Ya sake zama Muƙaddamin Ɗariƙar Ƙadiriyya al-Sammaniyyal-Ƙaribiyya a shekarar 1949.

3, Ya zamo mamba na majalisar mashawartan Mai Martaba Sakin Kano Abdullahi Bayero a shekarar 1949.

4, Ya zamo ƙwararren mai ba da shawara a harkar shari'a a kotun Musulunci ta Arewacin Najeriya a shekarar 1954.

5, Ya zamo ɗaya daga cikin mutane biyu da suke gabatar da tafsiri a Fadar Masarautar Kano tun daga 1954 har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

6, Ya zamo shugaban Makarantar Shari'a da Labirare ta Shahuci a shekarar 1958.

7, Ya kafa babbar makarntar firamare ta Islamiyya a shekarar 1961 a Gwale.

8, Ya sake zamowa mashawarcin Mai Martaba Sakin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero a shekarar 1963.

9, Ya zamo mamba na Majalisar Malamai ta Kaduna a shekarar 1963.

1.2.7 Rasuwar Malam Nasiru Kabara

Malam Nasiru Kabara ya rasu a ranar 21 ga watan Jumada Auwal, hijira ta 1417 wadda ta yi daidai da 4 ga watan Oktoba na shekarar 1996. Kuma ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki masu yawa.

2.1 Waƙa

Masana da manazarta irin su Yahaya (1996) da Ɗangambo (2007) da Ƙaura (1994) da Bunza (1988) da Habibu (2001) da Zurmi (2006) da Sani da Wasu (2022) da saursansu, sun bayyana ma’anar waƙa. Ɗangambo (2007) yana cewa “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta sauti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa–amo (kafiya), da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidata kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

Sani da wasu (2022) sun kawo cewa , “ Waƙa wani furuci ne (lafazi ko saƙo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi (Ɗangambo, a Cikin Habibu 2001).

Za a iya bayyana rubutacciyar waƙa da cewa, waƙa wani azanci ne da ake shirya shi tare da tsarawa bisa bin wasu keɓaɓɓun ƙa’idoji da sharaɗu domin isar da wani saƙo cikin ɗangwaye da baitoci ta amfani da hawa da saukar murya ko kari da kuma tsarin rerawa.

3.1 Jigo a Waƙoƙin Malam Nasiru Kabara

Kalmar jigo ta samo asali ne daga wani abun ban-ruwa, wanda masu noman rani suke amfani da shi, wajen yin ban-ruwan lambu. Halima (2012) ta kawo cewa, Abrahams (1968) yana cewa “ Jigo shi ne itacen da ake amfani da shi wajan ban-ruwan rani, wato lambu…”. Bunza (2009) yana cewa, “jigo daɗaɗɗiyar kalma ce wadda Hausawa masu aikin fadama ke amfani da ita wajen ban-ruwan kayan lambu da ita”. Wato a wannan ma’ana, jigo wani ita ce ne da masu aikin noman rani ke samarwa ta hanyar kafa itatuwa bisa rijiya, su kuma ɗaura guga a jiki domin su rinƙa ɗebo ruwan suna shayar da lambu. Ta fuskar mu’amalar yau da kullum kuma, kalmar jigo na iya kasancewa ‘shugaba’ ko’ ‘jagora’ ko ‘miji’ ko ‘maigida’ a wurin iyalansa. A taƙaice, jigo a lugga shi ne abin da wani aiki ko al’amari ke tabbata da tabbatuwarsa, yake kuma rushewa da rushewarsa.

Masana irin su Ɗangambo (2007) da Gusau (1983) da Halima (2012) da Auta (2017) da Bunza (1988 da 2009) da sauransu sun bayyana ma’anar jigo ta fuskar ilimi, wato isɗilayi. Ɗangambo (2007, sh.14) yana cewa “Abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa, ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai”

Jigo shi ne saƙon da mawallafi ya gina waƙarsa a kansa kuma yake burin isar da shi ga waɗanda abin ya shafa. Malam Nasiru Kabara yana gina wasu daga cikin waƙoƙinsa, bisa jigon ibada da hanyoyin da za a bauta wa Allah. Wannan jigo na ibada yana da ƙananan jigogi waɗanda yake sassarƙa su a cikin ɗangwaye daban-daban na waƙoƙin nasa domin gina babban jigon, wato jigon ibada. Daga cikin ƙananan jigogin da yake amfani da su wajen gina jigon ibada akwai jigon neman ilimi da na shika-shikan Musulunci wanda ya haɗa da kaɗaita Allah da salla da zakka da azumi da sauransu.

3.1.1 Furucin Gundarin Jigo

Furucin gunfarin jigo na nufin muhalli na farko da mawaƙi ya fara bayyana jigon waƙarsa a cikin wani baiti ko ɗango. Wato wuri ne wanda mawallafi ya fara ambaton ainihin gundarin saƙon da yake so ya isar ga jama’a. Ɗangambo (2007) yana cewa “ Jawabin jigo, ƙwayar jigo ce da ke iya samu ƙunshe cikin wasu baitoci da ke nuna tabbacin manufar mawallafin…”

Wannan takarda ta mayar da hankali wajen fitar da jigon koyar da ibada a cikin waƙoƙin Malam Nasiru Kabara. Ga misalan wasu baitoci masu ɗauke da wannan jigo na ibada:

Ibadodi mu san su sani sahihi,

Kamar ‘ya’yanmu domin Allah Allah.

(Jalalullah. Bt. 14).

Sanin addini shi ne ci gabanmu,

Da yadda ake ibada Allah Allah.

(Kamalullahi, Bt. na 11).

Idan aka lura da waɗannan baitoci, za a ga dukkaninsu suna bayani ne a kan yadda za a bauta wa Allah yadda ya kamata ta hanyar neman ilimin yadda ake bauta masa daidai. Kuma mawaƙin a cikinsu ne ya tsoma ambaton jigon koyar da ibada a cikinsu ta hanyar kira da horo a kan al’umma a kan su samu ilimin yadda ake bauta wa Allah a bisa tsari da ƙa’idar da addini ya tanada.

3.1.2 Warwarar Jigon Koyar da Ibadan a Waƙoƙin Malam Nasiru Kabara

A nan, za a yi sharhi ne kan jigo gaba ɗayansa. Za a duba shi dangane da jawaban jigo, da kuma abin da waƙar ta faɗa a taƙaice. To amma muhimmin abin shi ne za a duba lungu-lungu na waƙar dangane da jigo tare da ƙarin bayani daga dukkan abin da za iya danganta waƙar da shi. Misali, ana iya kawo ƙarin bayani dan kafa hujjoji da misalai daga Alƙur’ani, Hadisi, littatafai, muƙala da ra’ayoyin iri daban- dabam da dai sauran bayanai da za su taimaka wajan gane abin da waƙar ta ƙunsa da inda ta dosa (Ɗangambo 2007, sh. 18-19).

Kamar yadda bayani ya gabata, wannan takarda ta yi nazari da sharhi ne a kan jigon ibada a cikin wasu waƙoƙin Malam Nasiru Kabara. Ibada (tilo) ibadoji (jam’i), Ƙamusun Hausa (2006, sh.204) ya bayyana ibada da “bautawa Ubangiji a ƙarƙashin wani addini”. Kalmar ibada kalma ce ta Larabci wadda take nufin bauta da Hausa. Kalma ce wadda wajen Larabawa suke amfani da ita tun kafin zuwan addinin Musulunci, wadda kuma take nufin hanyar sadaukarwa ga abubuwa waɗanda suka ba da gaskiya da su a matsayin majiɓinta lamuransu. Bayan bayyanar addinin Musulunci, ya ci gaba da amfani da wannan kalma a matsayin hanyar ɗayanta Allah a cikin dukkanin al’amura. Khazinu (BS, sh. 506) yana cewa, “ Duk inda Kalmar ibada ta zo a cikin Alƙur’ani tana nufin kaɗaita Allah”. Haka shi ma Lawan (2018) yana cewa “ Haƙiƙar ma’anar ibada a addinin Musulunci ma’ana ce da ta game dukkanin abubuwan alheran duniya da lahira. Domin haƙiƙanin ibada suna ne da ya haɗe dukkanin wasu maganganu ko ayyuka waɗanda Allah ke son su kuma ya yadda da su”. Gusau (1994) ya bayyana cewa “ Ibada ita ce ayyukan addini da gaɓoɓin jiki tare da kyautata yi a lokacin gudanar da ita da kuma neman aƙibar aikin wato a samu sakamakon ayyukan da ake aikatawa tun nan duniya da kuma gobe lahira”. Kalmar bauta a Musulunci tana nufin yin wani motsi ko ƙuduri a zuciya wanda Allah yake so ko ya yi umarni a yi shi da nufin tsarkake shi da girmama shi da miƙa wuya gare shi a cikin dukkanin al’amura da aikata wani aiki mai kyau domin girmansa da cancantarsa da jingina wannan aiki mai kyau gare shi da kuma kiyaye aikata abubuwan da ya haramta.

Wannan baiti dake ƙasa, Malam Nasiru Kabara ya saƙa wani muhimmin saƙo a cikinsa, wanda yake kira ga al’umma a kan su kiyaye ibada da aiwatar da ita yadda ta dace ta hanyar neman ilimin yadda Musulunci ya yi umarnin aiwatar da ita. Ga abin da yake cewa:

Ibadodi mu san su sani sahihi,

Kamar ‘ya’yanmu domin Allah Allah.

(Jalalullah. Bt. 14).

Baitin waƙar yana haska wa mutane muhimmancin sanin kowane ɓangare na ibada da wajabcinsa. Baitin yana yin horo a kan sanin ibada domin aiwatar da ita yadda take, saboda haka, mawaƙin ya kusantar da tunanin mai sauraro ga iyalinsa domin ya fahimci saƙon da kyau.

Wato Malam Nasiru Kabara ya yi kira ga al’umma a kan su san ibada tamkar yadda suka san ‘ya’yansu ko ma sama da haka. Malam Nasiru Kabara ya yi wannan kwatance ne saboda irin kusantacciyar alaƙar da take tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ta ƙut da ƙut. Babu wani abu da zai iya mantar da mutum ga barin ‘ya’yansa. To, ta haka ne yake kira da mutane su nemi ilimin sanin yadda ake yi ibada irin sanin da suka yi wa ‘ya’yansu ko ma sama da haka.

Ibada a Musulunci iri biyu ce, akwai ibada ta wajibi, wato wajibau (Farilla) da kuma ibada ta kai da kai (Nafila).

4.2 Ibada Wajibau (Farilla)

Ibada wajibau ita ce nau’in bauta wadda Allah yake yin hukunci na azaba idan bawa ya ƙi aikata ta. Haka kuma, ya yi sakayya ta alheri ga duk wanda ya aikata ta. Bauta wajibau ta rabu gida biyu dangane da aiwatarwa. Akwai bauta wajibau wadda Musulunci ya wajabta a kan kowane Musulmi. Ita irin wannan bauta, ba ta rusa Musuluncin mutum, sai da janyo azaba da taɓewa da fushin Ubangiji. Haka kuma, akwai bauta wajibau ta rukunan Musulunci, wadda ta haɗa da kaɗaita Allah a zuci da zahiri da yin salla da azumi da zakka da kuma ziyarar ɗakin Ka’aba. Ita irin wannan bauta, ita ce wadda Allah ya yi umarni ga dukkanin wani Musulmi ya aiwatar da ita, domin yin ta shi ne tabbatar Musuluncinsa, rashin aikata ta kuwa, shi ne rushewar Musuluncin nasa. Wato ita ce bautar da mutum yake yi a kira shi da Musulmi.

Wannan takarda ta mayar da hankali ne wajen yin nazarin nau’o’in bauta wajibau ta neman ilimi da kuma ta aiwatar da shika-shikan Musulunci.

4.2.1 Neman Ilimi

Ƙamusun Hausa (2006, sh. 205) ya bayyana ilimi da cewa “ Sani musamman na shari’a da addini”. Ilimi shi ne sanin wani abu wanda da ba ka sani ba. A ta fuskar Musulunci kuwa, ilimi na nufin sanin yadda za a bauta wa Allah da sauran ayyukan addini da na kasuwanci da na zamantakewa da wasu fannonin kimiya da fasaha da sauransu.

Malam Nasiru Kabara yana yawan tsarma jigon ilimi a cikin waƙoƙinsa, domin ya nuna wa al’umma da faɗakar da su cewa, neman ilimin bauta wa Allah, wajibi ne ga dukkanin Musulmi. Haka kuma, da sauran ayyuka waɗanda suke sun zama wajibi ga mutum, to neman ilimin yadda za a gudanar da wannan abu shi ma ya zama wajibi. Malam Nasiru Kabara yana faɗa cewa:

Sanin addini shi ne ci gabanmu,

Da yadda ake ibada Allah Allah.

(Kamalullahi, Bt. na 11).

Wannan baiti yana haska wa mutane muhimmanci da wajabcin neman ilimi. Kamar yadda salla take wajibi a kan kowane Musulmi, haka shi ma neman ilimin yadda za a yi sallar yake wajaba a kan kowane Musulmi. Mawaƙin yana nusantar da hankulan al’umma kan su fahimci cewa, akwai ɓangarorin ilimi da yawa a doron ƙasa waɗanda mutane suke yi domin kawar da jahilci a kansu. Amma ilimin addinin Musulunci shi ne wanda ya wajaba a bawa fifiko kuma a mayar da hankali wajen ganin an yi shi yadda yake. Domin sai da shi mutum zai san yadda zai bauta wa Ubangijinsa. Haka kuma, yana faɗakar da al’umma a kan su gane cewa, kowane irin ilimi mutum ya yi, amma ba shi da ilimin addininsa, to mutum bai ɗauko hanyar ci gaba da wayewa a rayuwarsa ba. Wato Malam Nasiru Kabara yana kira zuwa ga al’umma kan su fifita ilimin addinin Musulunci a bisa kowane irin ilimi, ya zama shi ne ilimi na farko da mutum zai fara yi a rayuwarsa kafin shiga kowane fagen ilimi. Dalilin haka kuwa shi ne, ilimin addini Musuluncin shi ne yake yi wa mutum jagoranci wajen gane daidai da ba daidai ba. Haka kuma, ya yi hani da horo a kan aikata ɓarna wadda kan iya cutar da mutum ko waninsa ta ɓangarori daban-daban.

Baitin yana ƙara haska mutane cewa, bauta wadda Allah yake karɓa, ita ce wadda aka yi ta a bisa wani tabbataccen ilimi. Bauta wa Allah ba da ilimi ba kuwa, jahilci ne mai illa da kan jayo rushewar duk wani aikin bauta da mutum ya yi. Wannan dalili ya sa Malam Nasiru Kabara ya faɗakar da mutane kan illar bauta wa Allah da jahilci, inda yake cewa:

Ibada da Jahlu zama kan wuta ne,

Ba ta samu hanyar shiga ko kaɗan.

(Kamalullahi, bt. na 6).

Baitin da yake sama, ya haska wa mutane irin illar dake tattare da bauta wa Allah a cikin jahilci. A cikin baitin, Malam Nasiru Kabara ya siffanta yin ibada a cikin jahilci da cewa tamkar zama a kan wata wuta ce gagaruma. Ma’ana, duk kyan abu da ingancinsa, matuƙar a kan sanya shi a cikin wuta, to sai ya ƙone, kuma ya lalace. Haka ita ma ibada, duk kyan ibadar mutum, idan ya yi ta a bisa jahilci, to ba za ta zamo mai amfani gare shi ba, kuma babu ta hanyar da Allah zai ƙarɓe ta, tunda daman ta riga ta lalace. Bauta wa Allah a cikin jahilci, tamkar mutum ya kai kansa ga halaka ne.

A taƙaice, baitin ya yi horo ga al’umma a kan lalle su nemi ilimin sanin yadda za a bauta wa Allah, domin tsira da mutunci da kuma imani. Dalila kuwa, idan mutum ya yi bauta ba yadda addini ya yi umarni ba, Allah ba zai karɓa ba, kuma azaba ta riske shi a dalilin rashin sanin yadda zai yi ta daidai. An rawaito a Hadisi daga Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam yana cewa “ Neman ilimin wajibi ne a kan kowane Musulmi (da Musulma)”[1]. Gusau (2014) ya yi sharhin wannan Hadisi a cikin wasu baitoci, inda yake cewa:

Jama’a mu daure gun koyon,

Ilimin ibada mui gaya.

Da maza da mata danginmu,

Danginmu yara har manya.

A biɗe shi ilmi farlun ne,

Na sanin ibada je koya.

(Waƙar Mashiga, bt. na 9-11)

Waɗannan baitoci na Gusau, sun yi kira ga mutane da su koyi ilimin addinin Musulunci, a ko’ina yake a faɗin duniya, domin neman ilimi wajibi ga Musulmi, musamman ilimin yadda za a bauta wa Allah daidai. Haka kuma, baitocin suna haska wa al’umma kan cewa, su koyar da ‘ya’yansu ilimin yadda za a bauta wa Allah tun suna ƙanana, domin su koyi yadda ake bauta wa Allah daidai.

Sannan Gusau (2014) ya ƙara ƙarfafar nasihar Malam Nasiru Kabara a kan illar yin bautar Allah a bisa jahilci, inda yake cewa:

In kai ibada ba ilmi,

Banza kake yi sai jinya.

Ba za a sam wata lada ba,

Sai dai zunubi don ƙuiya.

(Waƙar Mashiga, bt. na 9-11).

Waɗannan baitoci suna ƙara haska wa al’umma illar da take cikin bauta wa Allah ba tare da ilimi ba. Wato, komai yawan bautar Allah da mutum ya yi a bisa jahilci, ba zai samu komai na lada ba. Ana saka ran ma, zunubi ya biyo bayan wannan ibada da mutum ya yi.

Wajabcin neman ilimi yadda za a bauta wa Allah, yana farawa ne a daidai lokacin da mutum ya balaga. Ahalari (BS) yana cewa, “ Farkon abin da ya wajaba ga wanda ya balaga shi ne sanin yadda zai kaɗaita Allah da tsarkake shi da sauran abubuwan da suke wajaba a kansa”. Ma’ana, a lokacin da mutum ya balaga, ibadar neman ilimi ta hau kansa, kuma wajibi ne ya cika wannan ibada, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

4.2.2 Shika-Shikan Musulunci

Shika-shikan Musulunci wasu ƙayyadaddun ibadu ne guda biyar (5) waɗanda Allah ya sanya su domin su zama wasu ginshiƙai masu riƙe da addinin mutum. Wato wasu ibadu ne waɗanda idan suka rusa su ko ya wulaƙantar da su, ya rusa addininsa. Haka kuma, mutum ya fita daga cikin tafarkin Musulunci. Waɗannan ibadu na shika-shikan Musulunci su ne; ‘ Kaɗaita Allah da ‘Salla’ da ‘Azumi’ da ‘Zakka’ da kuma ‘Hajji’.

Malam Nasiru Kabara ya ambaci waɗannan rukunan Musulunci a cikin wasu baitoci, inda yake cewa:

Tauhida salla zakka azumi hajji na biyar,

Su ne ƙawa’iu haƙƙan inji Ƙur’anu.

Tauhidi ne kansu haƙƙan dole ne ku sani,

Masaninsa shi mumini ne babu tammanu.

Du wanda bai san shi ya kafurta babu rufi,

Naman jahannama ne shi inji Ƙur’anu.

(Waƙar Kamalullahi, bt. 2-4).

A cikin waɗannan baitoci, Malam Nasiru Kabara ya bayyana wa mutane rukunan Musulunci guda biyar, waɗanda su ne suke tabbatar da Musuluncin mutum. Wato su ne “Tauhidi” da “Salla” da “Azumi” da “Zakka” da kuma “Hajji”. Haka kuma, ya yi nuni da cewa, duk a cikinsu, tauhidi shi ne mafi girma. Duk wanda ya san shi, shi ne cikakken mumini kuma ya tsira daga azabar Allah. Haka kuma, duk wanda bai san shi ba, Allah zai yi masa a zaba a cikin wutar Jahannama.

4.2.2.1 Kaɗaita Allah (Tauhidi)

Tauhidi kalma ce ta Larabci wadda kuma da Hausa take nufin ‘kaɗaita Allah a cikin komai’. Ƙamusun Hausa (2006, sh.433) ya bayyana Kalmar Tauhidi da cewa “ Gasgata ɗayantakar Ubangiji Allah, Tabaraka wa Ta’ala”. Wali (1953, sh. 5 ) yana cewa “ Ilimin kaɗaita Allah ilimi ne da ake sanin Allah da shi da siffofinsa da aikace-aikacensa da ɗaukakarsa da wadatuwarsa ga barin wata halitta…” Malam Nasiru Kabara ya yi amfani da hanyar waƙa wajen koyar da al’umma ta yadda za su san Ubangijinsu kuma su tsarkake shi daga dukkanin wata tawaya, haka kuma su bauta masa. Yana faɗa cikin wani baiti inda yake cewa:

Abin da ya wajibta gun baligi,

A farko ya san khaliƙin Ahmadan.

(Kamalullahi, bt.na 10)

Malam Nasiru Kabara ya yi wa mutane nuni a baitin a kan abun da ya wajaba a kan dukkanin wani musulmi, shi ne ya san wane ne Ubangijinsa. Ana kuwa sanin Allah ne ta hanyar sanin sunayensa da siffofinsa da kuma aikace-aikacensa. Ahalari (BS, sh.1 ) yana cewa “ Farkon abin da yake wajaba ga baligi[2] shi ne ya inganta imaninsa”. Wato ya san Allah.

Akwai wasu hujjoji ko dalilai waɗanda mutane suke sanin Allah da su. Wasu daga cikin waɗannan dalilai, Allah ya aiko Annabawansa da su, wasu kuma, ana gane su ta hanyar yin tunani a cikin abubuwan da Allah ya halitta.

4.2.2.1.1 Dalilan Samuwar Allah

Dalilan samuwar Allah na nufin wasu hujjoji da suke tabbatar da kasantuwar Ubangiji (Allah) kuma mahaliccin kowa da komai, wanda kuma ya cancanci bauta daga halittun sammai da ƙassai. Wali (2007, sh.7) ya nuna cewa, za a iya kallon dalilan samuwar Allah ta fuska biyu, wato ta fuskar nassi da kuma hankali.

4.2.2.1.1.1 Dalilan Samuwar Allah ta Nassi

Ƙamusun Hausa (2006, sh.358 ) ya bayyana nassi da cewa su ne “ Ayoyin Alƙur’ani da hadisai”. Nassi shi ne duk wani zance ko kalma wadda aka jingina ta ga Allah a matsayin ayar Alƙur’ani ko zance mai tsarki (Hadisi ƙudusi) ko zancen Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam kai tsaye.

Akwai ayoyin Alƙur’ani da zancen Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam masu yawa waɗanda suka tabbatar da samuwar Allah Tabaraka wa Ta’ala. Daga cikinsu akwai faɗin Allah:

“ ka ce Allah ɗaya ne tak, kuma shi ne abin nufi da buƙata, (wanda) bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Kuma wani kini bain kasance a gare shi ba. ( suratul Ikhlas, aya ta 1-4).

“ Ku bautawa Allah, kuma kada ku haɗa wani da shi” (Suratul Nisa’, aya ta 36).

“ Kuma ku bi Ubangijinku,ya hukunta kada ku bauta wa kowa face shi “(Suratul Isra’i, aya ta 23).

“ Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tare da Allah, har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe. (Suratul Isra’i, aya ta 22).

“ Na’am, Ubangjinka yana halittar abin da yake so, kuma yake zaɓar (abin da ya so). Zaɓi bai kasance a gare su ba. tsarki ya tabbata ga Allah ga barin tarayya shi da wani (abu). (suratul Ƙasas, aya ta 68)

“ Sannan kuma ka ce, godiya ta tabbata ga Allah, wanda bai riƙi ɗa ba, kuma wani abokin tarayya bai kasance a gare shi ba a cikin mulkinsa…” (Suratul Isra’i, aya ta 111)

“ Kuma abin da (duk) ke cikin sammai da ƙassai na Allah ne, kuma zuwa gare shi ake mayar da al’amura. ( suratu Ali Imrana, aya ta 109).

“ Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi (ne) rayayye kuma tsayayye bisa komai. Gyangyaɗi ba ya kama shi bare (ya yi) bacci. Abin da (duk) ke cikin sammai da ƙassai na ƙarƙashin ikonsa (da mulkinsa)…..” (Suratul Baƙara, aya ta 255).

“ Kuma lalle idan ka tambaye su, wane ne ya halicci sammai da ƙassaui? Haƙiƙa za su ce Allah ne…” (Suratur Zumar, aya ta 38).

Baya ga waɗannan ayoyi na Alƙur’ani da aka ambata a sama, akwai wasu ayoyin masu tarin yawa da suka tabbatar da samuwar Allah, kuma shi ne mahaliccin kowa da komai.

4.2.2.1.1.2 Dalilan Samuwar Allah a Hankalce

An samu kalmar ‘hankalce’ ne daga kalmar ‘hankali’. Ƙamusun Hausa (2006, sh.194) ya bayyana “ ‘hankalce’ da ‘hankalta’, hankalta na nufin gane yadda aka aikata wani abu ko fahimtar wani abu”. Hankali wani halitaccen abu ne a ƙwaƙwalwa da yake tantance daidai da kuma ba daidai ba a rayuwar yau da kullum. Ashe kenan, dalilan samuwar Allah a hankalce na nufin yin aiki da hankali wajen sanin ubangiji da kasantuwarsa da kuma fahimtarsa dangane da aikace-aikacensa. Wani mawaƙi yana cewa;

A cikin komai akwai wata alama,

Da ke tabbatar da ɗayantuwar Allah.

Baitin yana yin nuni da cewa, duk wani hankali lafiyyayye, zai tabbatar da akwai mahalicci a koyaushe ya yi duba a cikin abubuwan duniya. Dole hankali zai kawo, tabbas akwai wanda ya samar da wannan abu da ido ya gani.

Akwai wasu baitoci da malam Nasiru Kabara yake tabbatar da samuwar Allah a hankalce, inda yake cewa:

Yaro akwai ka ashe akwai ni,

Na’am akwai ka kamar akwai.

Domin akwai ka ka san akwai,

Da ba akwai da babu kai.

(waƙar haƙiƙa, bt. 1-2)

Malam Nasiru Kabara ya yi kira zuwa ga hankulan mutane, waɗanda suke lafiyayyu, a kan lalle su gane akwai mahaliccinsu. Wato yana nuni ga cewa, tun da akwai ni samamme kuma na tabbata akwai ni. Haka kuma, kai ma ka tabbata akwai ka samamme, to tabbas ba mu ne muka yi kanmu ba, dole akwai wanda ya yi mu. Domin sanin akwai ni samamme, shi ya tabbata min akwai wanda ya samar da ni. Sannan, da kuwa babu wanda ya samar da ni, to da ba zan kasance a samamme ba. Haka yake ga dukkanin halittu, sun tabbata akwai su, suna rayuwa, tun da haka ne kuwa, to tabbas akwai wanda ya yi su, domin da babu wanda ya yi su, to da su ma kuwa babu su.

Malam Nasiru ya cigaba da koyar da al’umma yadda za su tsarkeke Ubangiji a cikin wasu baitoci, inda yake cewa:

Ƙadimi mawajin masanin halitta,

Tsayayye da kai nasa tun a can gaba.

(Kamalullah, bt. na 12)

A wannan baitin, Malam Nasiru Kabara yana ƙoƙarin ribatar hankulan mitane ne a kan lalle su san cewa, shi Allah akwai shi, tun babu halittu sai shi kaɗai a zatinsa, kuma wanda yake tsaye da zatinsa babu wani mai agaza masa wajen tabbatuwarsa.

Mawaƙin ya ƙara nuni da kaɗaituwar Ubangiji a cikin wani baiti, inda yake cewal:

Kaɗai yake ba shi da mai ja da shi,

Buwayi Gwani shugaban Ahmadan.

(Kamalullah, bt. na 12)

Baitin ya yi nuni a kan cewa, tabbas Allah shi kaɗai ne a cikin zatinsa, da hukuncinsa da mulkinsa. Saboda haka, ba ya yin wani aiki ko hukunci wani ya ce masa don me aka yi? Ko me yasa aka yi? Ko kuma kar a yi abu kaza. Dalili kuwa, shi ne mahallicin kowa da komai ba tare da wani misali ya rigaya a gare shi ba. Kuma shi yake da iko a bisa abubuwan da ya halitta, kuma yake sarrafa a bisa ikonsa da ƙudurarsa. Duk abin da ya nufa a kan bayinsa, babu wanda zai hana shi aiwatar da wannan abu, ko saka shi, ballanta a yi masa dole ko tursasawa. Dukkanin halittu ba su da iko a kan kansu, ballanta su yi iko a cikin mulkin Allah da ƙudurarsa.

Ku san shi kaɗai yake tun babu kowa,

A tun fil azal haka har abadan.

(Kamalullah, bt. na 14 )

Baitin yana haska wa mutane a kan lalle su fahimci ce, Allah shi kaɗai ya kasance tun babu motsi da ji da tunani, ballantana halitta. Haka kuma, zai ci gaba da kasancewa har Abada a cikin wannan sifa tasa ta kaɗaitaka. Akwai saɓani tsakanin malamai, a kan bayan tashin ƙiyama da hisabi, ‘yan aljanna sun shiga aljanna, ‘yan wuta sun shiga wuta, za a dawwama a haka ko kuwa za a ƙare? Wasu na ganin ba za a dawwama ba, saboda idan aka ce za a dawwama, to an yi tarayya da Allah a cikin rashin ƙarshe. Wasu kuma na ganin za a dawwama. Amma Allah ne masani.

Tabaraka babu makani gare shi,

Babu zamani ga mai Ahmadan.

(Kamalullah, bt. na 16 ).

Malam Nasiru Kabara yana nuni a wannan baiti, a kan siffar Allah wadda ta saɓawa da kowace irin halitta.Wannan ya sa babu wani wuri da yake ɗaukar Allah ko yake riƙarsa. Haka kuma, babu wani zamani da zai kasance yana kewaye da Allah, domin shi ne mahallincin zamanin kuma yana nan tun kafin halittar zamanin. Baitin yana nusantar da al’umma, lalle su ƙudurce Allah ba halitta ba ne irin ka ko irin abin da ka taɓa gani ko ka ji ko ka taɓa ko ka raya a ranka ko ka taɓa yin tunininsa ko mafarkinsa. Allah ya wuce haka, wannan ya sa babu wani wuri da za a ce nan ne muhallin Allah inda yake zaune ko kuma wani zamani ya riske shi saboda shi ne mahaliliccin kowane bigire kuma mahaliccin zamanai, kuma yana nan tun kafin ya samar da bigirai da zamanai.

Tabaraka babu misali gare shi,

Babu shabihi ga mai Ahmadan.

(Kamalullah, bt. na 16).

Wannan baiti, yana faɗakarwa da mutane a kan su gane cewa, shi Allah a sifarsa da zatinsa da ɗayantuwarsa da suna, babu wani abu da ya yi kama da irin abin da ya yi kama da shi. Babu wani wanda ya yi kama da Allah a cikin komai. Allah maɗaukakin Sarki yana cewa “ Babu wani abu da ya yi kama da irin abin da ya yi kama da Allah”.

Da iko da mulki da ƙarfin sarauta,

Abin da ya kyare shi ba ya kaɗan.

(Kamalullah, bt. na 17).

A nan, Malam Nasiru Kabara yana koyar da al’umma cewa, su san kowane irin iko da mulki da ƙarfi irin na Sarauta na Allah ne. Duk wani mai iko da Sarauta da ƙarfi ba irin na Allah ba ne, kuma na halitta ƙararre ne.

Gani nasa ji nasa sun san da komi,

Ya gan mu ya ja mu gwanin Ahmadan.

(Kamalullah, bt. na 18).

Baitin yana nusantar da al’umma a kan su gane wasu siffofi tabbatattu kuma wajibabbu ga Allah, domin girmama shi da tsarkake shi da kuma kiyaye saɓa masa. Wannan ya sa yake faɗa cewa, Allah yana gani ba da ido irin na wata halitta ba, yana ji ba da kunne irin na wata halitta ba, kuma masanin komai ne ba da ƙwaƙwalwa irin ta wata halitta ba. Allah shi ne mahaliccin dukkanin waɗannan siffofi ga mutane. Saboda haka, Allah yana ji, yana gani, kuma masani ga komai, tun kafin ya halicci halitta. Allah yana gani kuma yana jin motsin tafiyar jaririn kiyashi a kan yashi, a cikin baƙin duhu. Kuma ya san buƙatarsa da dukkanin abin da yake buƙata, kuma ya yan kokensa, yana biyan buƙatarsa. Wato baitin yana koyar da mu cewa, mu roƙi Allah a duk inda muke kuma a kowane hali muke, yana jin mu kuma ya san da mu. Wannan yasa Malama Nasiru Kabara yake faɗa a cikin wani baiti, inda yake cewa:

Idan kai asiri cikin zuciyarka,

Yana jin ka jalla Gwanin Ahmadan.

(Kamalullah, bt. na 20).

Baitin yana kira ga al’umma a kan su tsantsance niyya ga Allah, domin shi masani ne da abin da yake ɓoye a cikin zuciyar kowace halitta. Haka kuma, duk wani abu da mutum ya ɗarsa a cikin zuciyarsa mai kyau ko marar kyau, Allah ya san shi kuma zai yi sakayya ta gari ga wanda ya yi kyakkyawan ƙuduri. Wato Allah yana jin ƙiftawar zuciyoyin halittu ba a rarrabe kuma a kodayaushe.

A wannan baitin kuma cewa yake yi:

Siffofinsa babu bidaya gare su,

Bare su nihaya gwanin Ahmadan.

(Kamalullah, bt.na 19).

A wannan baiti, Malam Nasiru Kabara yana kira ga dukkanin Musulmi ya ƙudurce cewa, da Allah da siffofinsa masu tsarki ba su da farko ko mafari kuma ba su da ƙarshe, ballanta su ƙare. Yaya abin yake? Allah shi kaɗai ya barwa kansa sani.

Allah Maɗaukakin Sarki yana da wasu siffofi waɗanda ake son kowane Musulmi ya san su, kuma ya ƙudurce tabbatuwarsu ga zatin Ubangiji a cikin zuciyarsa. Siffofin Allah ba su da farko kuma ba su da ƙarshe. Wato siffofi ne da suke liƙe da zatinsa, ba su ne Allah ba, kuma ba a rabe suke da Allah ba. Samuwar Allah, tare yake da samuwarsu, haka dawwamarsa, it ace dawwamarsu. Wannan ya sa Malam Nasiru Kabara yake faɗa a wannan baiti cewa siffofinsa ba su da farko kuma ba su da ƙarshe.

Wali (1953, sh. 8) ya ayyana wasu siffofi tabbatattu ga zatin Allah da kuma korarru gare shi. Wato ta waɗannan siffofi ne ake gane wane ne Allah. Duk wata halitta da ta yi ikirarin ita ce Allah, to sai a ɗora mata waɗannan siffofi, idan sun tabbata a kanta, to tabbata Allah ce, idan ba su tabbata ba, to shaiɗan ce mai kaiwa ga halaka. Haka kuma, korarrun siffofi, duk wanda aka samu ya liƙu da ɗaya daga cikinsu, to ba Allah ba ne. Tabbatattun siffofin su ne, ‘samuwa’ da ‘rashin farko’ da ‘wanzuwa’ da ‘saɓawa’ ga halitta a cikin komai da ‘tsayuwa da zati’ da ‘ɗayantaka’ a cikin komai da ‘iko’ da ‘nufi’ da ‘sani’ da ‘rayuwa’ da ‘ji’ da ‘gani’ da kuma ‘zance’. Waɗannan tabbatattun siffofi babu wata halitta da ta keɓanta da su, kaɗai Allah maɗaukakin Sarki ne ya keɓanta da su. Haka kuma, da sauran siffofi da suke korarru ga haƙƙin Allah. Wato su ne; ‘rashi’ da ‘faruwa’ da ‘ƙarewa’ da ‘kamantuwa’ da ‘halitta’ da ‘buƙatuwa’ izuwa wata halitta da ‘abokin tarayya’ da ‘gazawa’ da ‘tilastuwa’ da ‘rashin sani’ da ‘mutuwa’ da ‘makanta’ da ‘babentaka’ da kuma ‘kurmanta’. Waɗannan siffofi da suke korarru ga haƙƙin Ubangiji. Kowane abu aka ɗauka za a ga ya siffantu da ɗaya daga cikin waɗannan siffofi amma banda Allah tabaraka wa Ta’ala.

4.2.2.2 Salla

Ƙamusun Hausa (2006, sh. 385) ya bayyana salla da cewa ita ce “ Ibadar da musulmi ke yi sau biyar a rana, wadda ta haɗa da ruku’u da sujjada. Salla ta ƙunshi furuci na zikirai da motsin gaɓoɓi ta hanyar yin ruku’u da sujjada. Salla iri biyu ce, akwai ta wajibi da ta nafila. Salla ta wajibi bauta ce wadda Allah ya wajabta ta ga dukkanin Musulmi domin girmama shi da miƙa wuya gare shi kai tsaye. Gusau (2014,sh.30) yana cewa, “ Salla ta farilla ita ce aka tilasta yin ta ga dukkanin Musulmi mazansu da matansu, balagaggu, masu hankali da imani da Allah da Manzonsa, an umarce shi da yin salla. Ƙin yin salla ga mutum Musulmi ko daina yin ta, ko ana yi ana hutawa ko ƙin yin ta bisa yanayinta, dukkan ɗayan waɗannan abubuwa suna cikin manyan laifuka, ga zunubi kuma da za a iya ladabtarwa a kan haka”.

Jigon salla na ɗaya daga cikin jigogin da Malam Nasiru Kabara yake gina waƙoƙinsa a kansa. Idan muka dubi baitin da ke ƙasa, za mu ga yana cewa:

Mu san salla sanin kirki da zakka.

(Jalalullahi, bt. na 16)

A wannan ɗango Malam Nasiru Kabara yana kira ne ga al’umma, wajibi ne su san yadda ake yin Salla, salla ba ta yuwuwa sai an san rukunoninta da sharuɗanta da ƙa’idojinta da tsarinta da kuma dukkanin wani abu da ya dangance ta. Kurɗabi (BS) yana cewa “ Salla tana ƙunshe da aikace-aikace har guda dubu goma sha biyu (12000)”. Daga cikin abubuwan da salla ta ƙunsa akwai sharuɗan wajabcinta kamar Musulunci da balaga da hankali da shigar lokaci da kuma isar kiran Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam (ga mutum). Haka kuma, akwai sharaɗin ingancinta kamar tsarki da fuskantar Alƙibila da suturce al’aura da barin zance da kuma barin aiki mai yawa. An ɗauki wasu daga cikin waɗannan abubuwa da aka kawo a sama kuma aka a yi bayaninsu, domi taƙaitawa kuma su ne waɗanda Malam Nasiru Kabara ya ayyana a cikin wasu baitoci. Wato tsarki da sanin lokacin salla da duban alƙibila da kuma aikace-aikacen cikinta.

4.2.2.2.1 Tsarki

Tsarki shi ne abu na farko da mai salla zai fara yi domin tsarkake jikinsa daga dukkan najasa da dauɗa, wanda hakan ne zai ba shi damar yin ingantacciyar salla. Allah tabaraka wa Ta’ala yana faɗa a cikin wani zance mai tsarki cewa, “ haƙiƙa Allah mai tsarki, kuma ba ya karɓar wani aiki sai mai tsarki (tsarkin zuciya da na jiki)[3].

Malam Nasiru Kabara yana faɗa a wani baiti cewa:

Mu zan tsarki gaban tamu ƙalƙale shi,

Mu tsefe alwala don Allah Allah.

(Jalalullahi, bt. na 42).

Malam Nasiru Kabara yana yin nuni a cikin wannan baiti ga al’umma cewa, tsarki wajibi kafin a yi kowace irin sallah. Haka kuma, yin tsarki wajibi ne a kowace salla, sallah ta wajibi ko kuma ta nafila. Sannan ya haska wa al’umma cewa, bayan an yi tsarki domin yin salla, abu na biyu da za a yi ita ce alwala. Haka kuma, ya yi kira a cikin baitin a kan al’umma su inganta alwalarsu ta hanyar tsattsefe ta da yin ta yadda addini ya tanada.

Tsarki da ake yi domin yin salla iri biyu ne, wato akwai tsarki na najasa da na alwala. Tsarki na najasa, shi ne wanda ake amfani da ruwa ko hoge domin kawar da wata najasa da ta samu mutum[4]. Tsarki na biyu kums, shi ne yin alwala[5]. Gusau (1994 da 2014) yana cewa “Alwala tsarki ne na ruwa da aka danganta shi da wasu ayyanannun gaɓoɓi na jikin mutum tare da kyautace yin niya. Alwala tana sa mai ibada ya zama mai tsarki da zai ba shi damar kusantar Ubangijinsa cikin hali da yanayi mai kyau…” Akan yi aron tsarki yayin da bukatar alwala ta zo kuma babu ruwan yin alwalar ko ba zai isa ba, ko gudun kamuwa da wata cuta ko fama ciwo da sauransu. Wato akan yi taimama a maimakon alwala. Idan mutum ya tsinci kansa cewa, ɗaya daga cikin waɗannan najasoshi sun same shi, wajibi ya yi tsarki cikakke kuma nagartacce, sannan ya yi salla. Idan mutum ya yi salla ba tare da tsarki ba, Allah ba zai karɓi sallarsa ba.

Alwala ita ce wanke wasu gaɓoɓin jiki na fuska da hannuwa da ƙafafuwa da kuma shafar kai domin samun tsarkakuwa daga dukkanin wani zunubi yayin da za a gaida Allah.

4.2.2.2.2 Lokutan Salla[6]

Kalmar ‘Auƙatu’ jam’i ce ta ‘Al’waƙtu’, wato ‘lokaci’ kenan da Hausa. Shigar lokacin salla yana ɗaya daga cikin sharuɗan salla wanda idan babu shi babu salla. Wannan dalili ya sa, Malam Nasiru Kabara ya nusantar da al’umma muhimmanci da wajabcin sanin lokacin kowace salla a cikin wani baiti, inda yake cewa:

Mu san auƙatu tahaƙiƙan mu duba,

A farko lokaci mu kiyayi Allah Allah.

(Jalalullahi, bt. na 42).

Baitin yana yin nuni a kan wajabcin sanin lokacin salla, domin kowace salla akwai wani ƙayyadajjen lokaci da Allah ya ajiye a yi kowace salla a cikinsa. Haka kuma, wajibi ne kowane Musulmi ya san lokutan salla, domin yin ta a farkon lokacinta. Kowace salla tana da lokuta guda biyu, wato zaɓaɓɓe da kuma laluri. Zaɓaɓɓen lokaci shi ne wanda Malam Nasiru Kabara yake kiran al’umma a cikin baitin da ke sama, domi su yi salla a cikinsa, wanda kuma a cikinsa ne Musulunci ya fi san kowa ya yi salla, sai idan akwai wani muhimmin uzuri. Laluri lokaci kuma, shi ne wanda ake yin salla a cikin bayan fitar zaɓaɓɓen lokaci a bisa wani muhimmin uzuri[7].

4.2.2.2.3 Ayyukan Cikin Salla Wajibabbu

Wajibabbun ayyuka a cikin salla, su ne waɗanda idan babu su salla ke rushewa. Waɗannan ayyuka sun haɗa da yin niya da kabbarar shiga salla da ruku’u da sujjada da kuma sallama. An karɓo wani zance daga Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam cewa, “ Idan za (kai) salla, ka yi kabbara, sannan ka karanta abin da ya sawwaƙa a gare ka na a Alƙur’ani ( fatiha da/ko sura). Sai ya yi ruku’u har ya samu nutsuwa a cikin ruku’un, sannan ya ɗago har ya daidaita a tsaye. Sannan ya yi sujjada har ya samu nutsuwa a cikin sujjadar, sannan ya ɗago har ya samu nutsuwa a zaune, sannan ya yi sujjada har ya samu nutsuwa a cikin sujjadar. Haka zai aikata a dukkanin sallarsa[8]”. Idan aka dubi wannan sallar da Annabi Sallallahi wa alihi wa alaihi wa sallam ya koyar, za a ga ya taƙaita ne kawai a kan abubuwan da suke wajibai, kamar dai yadda Malam Nasiru Kabara ya bayyana a cikin baitin da ke ƙasa:

Idan mun niyyata mu gare shi Allah,

Idan mun kabbara mu gare shi Allah.

(Jalalullahi, bt. na 45).

Baitin yana yin nuni da horo a kan cewa, abu na farko da mutum zai, yayin fara salla, ita ce niya. Niya wajibi ce a cikin kowane aiki. Niya ita take rarrabe tsakanin aiki da aiki ( misali, sallar azahar da la’asar suna da siga da zubi da tsari iri ɗaya amma niya ce take bambance su). An karɓo Hadisi daga Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam cewa, “ Kowane aiki ba ya tabbata sai da niya, kuma kowa akwai abin da ya niyata[9]…” muhallin yin niya ita ce zuciya.

Aiki na biyu a cikin salla, shi ne yin kabbarar shiga salla (Kabbarar Harama). Kabbarar shiga salla ita ce kabbara ta farko da mai yin salla zai yi, kuma wajiba ce, idan babu ita, babu salla. Sallar azahar da la’asar da isha suna da kabbarori ashirin da ɗaiɗai. Sallar magariba kuma tana da kabbarori goma sha biyar, haka ita ma sallar asuba tana da kabbarori goma sha ɗaya. Amma ɗaya ce wajiba a cikinsu, wato ta farko.

Karatun fatiha shi ne aiki na uku a cikin salla, kamar yadda Malam Nasiru Kabara bayyana a baitin da ke ƙasa:

Karatun fatiha shi ne ya motsad,

Da harshen namu shi ne Allah Allah.

(Jalalullahi, bt. na 47).

Baitin yana yin nuni a kan aikin da yake na biyu a cikin salla. Haka kuma, baibtin ya faɗakar da mutane tare da sanar da su muhallin yin karatun fatiha a cikin salla da yadda ake yinsa. Malam Nasiru Kabara ya haska wa mutane cewa, ana yin karatun fatiha ne a cikin salla ta hanyar motsa harshe yayin karanta ta. Sannan, ba a yin karatun fatiha a cikin zuciya. Karatun fatiha wajibi ne a kowace salla, kuma a kowace raka’a.

Aiki na huɗu da na biyar a cikin salla, su ne yin ruku’u da kuma sujjada. Baitin da yake ƙasa ya koyar da mutane yadda ake jeranta waɗannan ayyuka na cikin salla kamar haka:

Ruku’u shi cirawa shi sujuda,

Da ɗaukewar sujuda Allah Allah.

(Jalalullahi, bt. na 48).

Wannan baiti yana yin nuni da cewa, bayan mai salla ya yi karatun fatiha (da na sura), abu na gaba da zai yi shi ne ruku’u. Haka kuma, bayan ya ɗago daga ruku’u, sai ya yi sujjada tare da ayyukan da ake yi a cikinta (na zikiri da tasbihi da kuma addu’a). Nutsuwa a cikin ruku’u da sujjada da daidaituwa bayan an ɗago daga gare su, ita ma wajibi ce a cikin salla.

Zaman yin tahiya da karatun yin tahiyar, su ne ayyuka na ƙarshe a cikin salla. Malam Nasiru Kabara ya ayyana waɗannan ayyuka a cikin wannan baiti da ke ƙasa, kamar haka:

Tahiya shi salati shi salami,

Da dukkan ayyukan nata Allah Allah.

(Jalalullahi, bt. na 49).

Wannan baiti, yana nuni da cewa, zama da karatun tahiya[10] su ne ayyuka na ƙarshe a cikin salla. Haka kuma, ya bayyana yin salati da sallama ga Annabi Sallallahi wa alaihi wa alihi wa sallam, a matsayin wajibabbua cikin salla. Karatun tahiya a cikin salla ba wajibi ba ce, amma saboda kasancewar wasu ayyuka wajibabbu a cikinta, sai Malam Nasiru Kabara ya kawo ta a cikin jerin abubuwan da suke wajibai a cikin salla. Wato a cikinta akwai salati/salami da kuma sallamar fita daga salla da kuma zama domin yin ta.

4.2.2.2.3 Azumi

Shika (2008, sh.5) yana cewa, “ Azumi wata ibada ce da Musulmi ke yi, yana barin buƙatar ransa don neman yardar Allah. Ta hanyar azumi, bawa ke samun kusanci ga Allah da kuma samun lada. Ibn Hajar ya fassara azumi da kamewa ko barin wasu abubuwa keɓantattu, a wani zamani keɓantacce, da wasu sharuɗa keɓantattu”. Wato azumi ya ƙunshi rashin cin abinci da shan abin sha da saduwa da mace da kamewa daga ƙarya, tun daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana da niyar bauta wa Allah. Gusau (2014, sh.47) ya bayyana azumi da cewa, “ azumi shi ne kame baki daga dukkan abin ci ko abin sha ko kowace irin sha’awa daga ɓullowar Alfijir zuwa faɗuwar rana. Azumi kuma ya ƙunshi karatun Alƙur’ani da salati da zikiri da kame kai da sauran ayyuka na ibada da kauce wa ayyuka na alfasha”.

Malam Nasiru Kabara yana kira ga al’umma a kan lalle su zamto sun san ibadar azumi da yadda ake yin ta domin samun yardar Allah da kusanci zuwa gare shi. Yana faɗa a cikin wani baiti cewa:

Mu san salla mu san azumi,

Mu ambaci Jalla Rahamani.

( Waƙar Falalar Zikiri, bt. na 1).

A wannan baiti da ke sama, Malam Nasiru Kabara ya saki kalmar azumi ne saki-ba-ƙaidi. Wato a nan kalmar azumi da ya ambata za ta iya ɗaukar nau’o’in azumi na wajibi da na nafila kamar azumin litinin da alhamis da na arfa da na watan Rajab da watan Sha’aban da guda shida na watan Shawwal da guda uku a kowane wata da sauransu.

Amma idan aka dubi sigar yadda ya tsara ɗangon, za a ga ya jeranta salla da azumi, wannan zai nuna cewa yana Magana ne a kan azumi na wajibi. Wato azumin watan Ramadan. Za a ƙara gane hakan ne idan aka duba wannan baitin da yake ƙasa inda yake cewa:

Azumci Ramalana,

Lillahi billahi.

(Waƙar shika-shikan Musulinci, bt. na 10)

A wannan baitin, Malam Nasiru Kabara ya fito ƙuru-ƙuru, ya nuna azumin watan Ramadana yake kira ga al’umma su yi domin cika wajibinsu da kuma kaucewa fushin Allah.

Ga ma’azumta, matuƙar mutum yana so ya samu cikakken lada da daraja waɗanda Allah ya yi tanadi ga masu azumi, to bayan ya bar ci da sha da saduwa da iyali, sai kuma ya kiyaye gaɓoɓinsa daga aikata dukkanin wata alfasha da kiyaye ganinsa da jinsa. Haka kuma, sai ya kiyaye harshensa daga furta duk wata mummunan kalma irin su ƙarya da zagi da batsa da gulma da munafurci da sauran manya da ƙananan zunubai. Wannan ya sa Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam yake cewa “ wanda duk bai bar ƙarya ba ( a cikin watan Ramadana) da aiki da ita ba, Allah ba ya buƙatar daina cin abinsa da abin shansa[11]”.

4.2.2.2.4 Zakka

Zakka ita ce fitar da wani kaso daga cikin dukiya ( na kuɗi ko dabbobi ko hatsi) domin ba wa mabuƙata da nufin cika wani sharaɗi na zama Musulmi da kuma neman yardarm Allah. Zakka ita ce sadakar da addinin Musulunci ya umarci a riƙa fitarwa daga dukiya ko amfanin gona ana bai wa matalauta (Ƙamusun Hausa 2006, sh,488). Gusau (2014) yana cewa, “ wajibi ne ga wanda Allah ya ba ikon abin yin zakka ya fitar da ita, kuma ya ba da ita ga waɗanda suka cancanta. Daga cikin sharuɗan zakka akwai balaga da hankali da karɓar Musulunci wanda ba shi da waɗannan kuwa ba zai yi zakka ba saboda ba ta rataya a wuyansa ba. Har wayau ba za a yi wa abu zakka ba sai an mallake shi, mallaka ta haƙiƙa, kuma shi wanda zai fitar da zakka ya zama ɗa ne ba bawa ba”.

Akwai nau’o’in abubuwan da ake fitar musu da zakka kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Gusau (2014) ya kawo wasu daga cikin nau’o’in abubuwan ake fitar musu da zakka kamar haka:

a-Zakkar Zinari da azurfa (kuɗi)

b-Zakkar kayan saye da sayarwa, wato ciniki ko kasuwanci

c-Zakkar hatsi

d-Zakkar dabbobi

e-Zakkar gidaje

f-Zakkar sauran abubuwa

Malam Nasiru Kabara ya bayyana wa al’umma abubuwan da suke wajabta zakka a kan mutum da kuma abubuwan da ake fitar musu da zakka da kuma waɗanda za a bawa zakka. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitoci da suke ƙasa:

Guda huɗu su ne farillan zakatu,

Nisabi cikar shekara niyyatan.

Ka fara da ‘yanci ana wanda ya ce.

Ba zai ba da zakka ba yai ƙamƙami.

Ana soya namansa ranar ƙiyama,

Ana babbaka shi cikin Hawuya.

A ba da khiyari a bai ganin ‘yan Adam,

Sari’an a ɓoye ganin ‘yan Adam.

A bai wa ƙaribi a jinkirta nesa,

A bai wa Kano kan a kai Makkatan.

Ana son du’a’i ga wand aka baiwa,

Gama mustajaba tana nan a nan.

(Kamalullahu, bt. na 94-99).

A cikin waɗannan baitoci, Malam Nasiru Kabara ya faɗakar da mutane kan su san cewa akwai farillar zakka guda huɗu. Wato su ne, nisabi da cikar shekara da niya. Haka kuma, ya bayyana mutanen da ake so a ba zakka a Musulunce. Waɗannan mutane sun haɗa da miskini da mabuƙaci da matafiyi da kuma makusanci. Sannan baitocin, sun yi nuni da cewa, ana iya bayar da zakka aɓoye ko kuma a sarari. Haka kuma, baitocin sun yi horo a kan masu hana zakka, domin su sani Allah zai ƙona su a cikin wutar hawiya.

Malam Nasiru Kabara ya bayyana irin nau’o’in abubuwan da ake fita musu da zakka a cikin wata waƙar daban, inda yake cewa:

Zakkar hatsi shi ne,

Lillahi billahi.

Buhu biyar ka ji.

Lillahi billahi.

Rabin buhu shi ne,

Lillahi billahi.

Na ba wa miskini,

Lillahi billahi.

Gyaɗa da wajenka,

Lillahi billahi.

Dawa da geronka,

Lillahi billahi.

Zakkar kuɗi shi ne,

Lillahi billahi.

Cikin Sina ashara.

Lillahi billahi.

Junaihu ma’asisi,

Lillahi billahi.

Ka ƙara sulayani,

Lillahi billahi.

Sulai shida su ne,

Lillahi billahi.

Sisin kwabo ma’ahu,

Lillahi billahi.

Gudan anininsa,

Lillahi billahi.

Shi ka ba she shi,

Lillahi billahi.

Komai yawa mali,

Lillahi billahi.

Haka za ka fisshe shi

Lillahi billahi.

(Waƙar Shika-shikan Musulunci, bt. na 15-31)

Malam Nasiru Kabara ya yi nuni da cewa, ana fitarwa da hatsi zakka. Yana cewa, kowane irin hatsi mutum ya noma[12], to a duk buhu biyar, zai fitar masa da rabin buhu, shi ne zakkar wannan hatsi. Wato ita zai ɗauka ya ba wa miskini ko ɗaya daga cikin waɗanda Allah ya ce a ba su zakka. Idan buhu goma ya noma, to biyu ɗaya zai fitar na zakka. Haka kuma, idan buhu arba’in ya noma, buhu huɗu zai fitar na zakka. Wato a taƙaice, zakkar hatsi ana fitar da kaso goma bisa ɗari na adadin buhuhhunan da mutum ya noma ne.

Haka kuma, idan aka dubi ragowar baitocin, za a ga ya yi nuni da yadda za a fitar da zakkar kuɗi daki-daki. Amma za a ga ya buga nisabin zakkar ne a bisa kuɗi irin na dauri. Amma a taƙaice, idan za a fitar da zakkar kuɗi, mutum zai raba dukiyarsa wadda yake juyawa idan shekara ta zagayo zuwa gida arba’in, to sai ya cire kaso ɗaya shi ne zakkar wannan dukiya. Misali,

Zakkar dubu ɗari (10000), zai kasance kamar haka:

#100000÷40=#2500. Wato, duk dubu ɗari za a fitar mata da zakkar naira dubu biyu da ɗari biyar.

Zakka ba ta wajaba a kan mutum sai an samu wasu sharaɗai na wajbaci da inganci. Wato akwai “niya” da “cikar shekara” da “kai wa nisabi”. Haka kuma, akwai laduban zakka yin zakka kamar haka; ba da ita cikin daɗin rai da killace ta daga idanun mutane da kuma kasancewarta zaɓin dukiya. Akwai wasu nau’o’in mutane da addini ya yi umarni a ba wa zakka. Daga cikinsu akwai: “mabuƙata” ko “miskinai” ko “masu aiki a kan zakka” ko “waɗanda ake rarrashin zuƙatansu” ko “fansar wuyaye” ko “mabarata” ko “aiki a cikin hanyar Allah” ko kuma “ɗan tafarki”, ma’ana matafiyi.

Bayan zakka ta wajibi, akwai zakkar fidda kai wadda ake fitar da ita a duk shekara a ƙarshen watan azumin ramadana. Haka kuma, akwai zakkar jikin ɗan adam. Shi ma jikin mutum ana fitar masa da zakkarsa. Zakkar jikin mutum ita ce yin ambaton Allah.

4.2.2.2.4 Hajji

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, waɗanda addini ya yi umarni ga kowane Musulmi ya yi domin ingantar Musuluncinsa. Ƙamusun Hausa (2006) ya bayyana Hajji da cewa, “ “ .

Malam Nasiru Kabara bayyana wa Musulmi abubuwan da suke wajiba a cikin aikin Hajji. Inda yake cewa:

Farillan Ihrami tabbata niyya,

Ɗawafi da tsaiwa a kan Arafan.

Da Sa’ayi tsakanin Safa’u da Marwa,

Idan ka kula za ka san Khamsatan.

Da aski da jifa rashin datse farce,

Fitar da tufafi barin judalan.

Iyalu ya tsefe ya kai su ga hamsin,

Uban Malikawa na Marakishan.

(Kamalullahi, bt. na 100-103).

A cikin waɗannan baitoci, Malam Nasiru Kabara ya yi nuni ga wasu abubuwa guda biyar waɗanda suke su ne wajibabbu a cikin aikin Hajji. Wato su ne, “yin harami” da “yin niya” da “ɗawafi” da “tsayuwa (a dutsen Arfa) da kuma “safa da marwa”.

Haka kuma, baitocin sun yi nuni ga sunnoni aikin Hajji. Waɗannan sunnoni sun haɗa da yin aski ko saisaye da jafan jamra da rashin yanke farce da kuma rashin tuɓe kaya.

4.3 Ibada ta kai da kai (Nafila)

Bauta ta kai da kai (Nafila), bauta ce wadda Allah da Annabinsa suka yi umarni a yi ta amma bada sigar wajabci ba. Allah ba ya hukunta mutum da azaba a dalilin rashin aikata ta, sai dai mutum yana nisantar kusanci da Allah. Ita irin wannan bauta ta kan ƙara samar da kyakkyawar alaƙa da kusanci tsakanin Allah da bawansa. Irin wannan bauta ta haɗa da yin salla da azumi da zakka da ziyartar ɗakin Allah amma na nafila. Haka kuma, da ambaton Allah ta sigogi daban-daban da sauran ayyukan alheri.

Daga cikin ibada ta nafila akwai yin zikirin Allah (Wuridi) ta sigogi daban-daban. A cikin wani baiti, Malam Nasiru Kabara yana faɗakar da al’umma a kan su kiyaye ladabi a yayin da suke ambaton Allah, inda yake cewa,

Ku kama zikiri ya ‘yan’uwa da gaskiya,

Ku so wanda ya so Annabinmu Muhammadu.

(Waƙar Zikiri, bt. na 2).

Baitin ya yi kira ga Musulmi da su ƙanƙame zikiri da gaske, domin shi zikiri yana daga cikin manyan ibadu waɗanda Allah ya yi umarni da a yi su ta sigogi daban-daban. Zikiri tamkar sabule ne da yake wanke dukkanin wani datti da yake tattare a cikin zuƙatan mutane. Wannan ne ma ya sa, Allah ya ambaci mai yin zikiri da wanda ba ya yi, kamar matacce ne da kuma rayayye. Haka kuma, ƙin yin zikiri, alama ce ta munafurci a Musulunci. Saboda haka, baitin yana haska wa mutane muhimmancin zikiri da kuma horo a kan kada a yi wasa da shi. Amma duk da wajabcin da yin zikiri yake da shi a Musulunci, rashin yin sa ba ya rusa Musuluncin mutum, sai da ya janyo azaba mai raɗaɗi.

5.1 Kammalawa

Waƙoƙin Malam Nasiru Kabara, waƙoƙi ne da suka shahara a ƙasar Hausa, musamman garin Kano da arewacin Nijeriya, wajen koyar da al’ummar Musulmi addininsu da yadda ake aiwatar da shi da wa’azi da gargaɗi da faɗakarwa a kan al’amuran addini masu yawa. Waɗannan waƙoƙi nasa sun yi tasiri sosai, musamman a wancan lokaci da ake da ƙarancin makarantun Islamiyoyi, na manya da na yara. Waƙoƙinsa su ne suka zamar wa al’umma tamkar makaranta, kar ma dai waƙar Kamalullahi ta ji labara.

Wannan takarda ta yi taƙaitaccen tarihin malam Nasiru Kabara. Haka kuma, ta yi bayanin ibada a dunƙule. Sai sai ta yi bayanin wasu jigogin waƙoƙinsa waɗanda suka haɗa da jigon ibadar neman ilimi da shika-shikan Musulunci, wanda ya haɗa da kaɗaita Allah da salla da tsarki da lokutan salla da azumi da kuma zakka.

Wannan takarda ta gane cewa, Malam Nasiru Kabara yana yin amfani da salon hira a waƙa domin samun sauƙin isar da saƙo ga mai sauraro. Haka kuma, takardar ta fahimci yanayin yadda Malam Nasiru Kabara yake amfani da falsafa wajen kiran hankulan al’umma izuwa ɗayanta Allah da kuma horo da hani wajen aikata ayyukan ɓarna. Haka kuma, takardar ta gano cewa, waƙoƙin Malam Nasiru Kabara, waƙoƙi waɗanda aka cika su da nassin Alƙur’ani da Hadisi amma ta hanyar baddala. Domin daidaita tunanin al’umma a bisa abin da yake daidai na rayuwar addini.

Haka kuma, wannan takarda, tana bada shawara, musamman ga manazarta a kan a bibiyi waƙoƙin Malam Nasiru Kabara domin cike giɓin da aka bari a fagen ilimi, musamman idan aka yi la’akari da jogogi irin na wa’azi da yabo da kirari da sufanci da kariya ga Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam da kuma sauran fagagen ilimi, musamman salo da sarrafa harshe da falsafa da aruli da al’ada da sauransu.

Manazarta

Auta, A. L. (2017). Faɗakarwa a Rubutattun Waƙoƙin Hausa. BUK Press.

Abubakar, A.U. (BS). Bugyatul Muslim wa Kifayatul Wa’izina wal Muta’azina. Lebenon: Maktabatul Shu’ubatu.

Ahlari, A. (2009). Kitabul Akhdari. Kano:” Baba Ƙusa.

Bunza, A.M. (1988). Nason Kirari Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin.

Takarda Wadda aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre.

Bukhari, M. (2009). Sahihul Bukhari. Lebenon: Darul Fikr.

Bugaje, M.H. (2011). Wa’azi a Rubutattun Waƙoƙin Mata na Ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri na Biyu. Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano. Jami’ar Bayero ta Kano.

Chamo, I.Y (2011). “Jigo a Fina-Finan Hausa”. A cikin Algaita Journal of Humanities

Sashen Koyar da Harunan Nijeriya da Kimiyar Harshe, Jami’ar Bayero, Kano

Vol.12. No.1 (sh. 66).

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kano: Kdg Publishers.

Furniss, G. (1996). Peotry, Prose and Popular Culture in Hausa. USA: Smithsonian Institution Press.

Ɗangambo, H.A. (2002). “Nazari a kan Jigon Faɗakarwa na Adabin Baka”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo, H.A. (2012). “Nazarin Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa”. Kundin Digiri na uku,

Sashen Koyar da Harsunan Nijriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S.M (2014). Mu Koyi Ibada. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S.M. (1983). Waƙoƙin Noma na Baka: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S.M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Habibu, L. (2001). Bunƙasa Rubutattun Waƙoƙin Hausa a Ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri na

Ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Hashimi, S.M. (2017). Mukhtarul Hadis wal Hikamil Muhammadiya. Alƙahira: Maktabatul Darabal Atrak.

Ibn Maja, A.A (2013). Sunani Ibn Maja. Alƙahira: Darul Fajri Lilturath.

Ƙaura, H.I. (1994). Ƙawancen Salo a Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Kabara, A.N. (2017). Riyadil Jannati. Kano: Rijalul Khidimati.

Kabara, N.M. (1988). Ihsanul Mannan. Kano: Maiƙukari Amaktaba al Ƙadiriya.

Khazinu, A. (2009). Tafsirul Khazinu Li-BabiTa’awili fi Ma’anil Tanzili. Lebenon: Darul Fikr.

Mujahid, S.M. (2003). “Gudummawar Shehu Malam Nasiru Kabara ga Adabin Hausa: Nazarin Diwanin Waƙoƙinsa na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Magaji, B. (2012). “Nazarin Jigo da Salon Amfani da Nassin Alƙur’ani a Cikin Waƙoƙin Alhaji

Mudi Spikin”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Munziri, Z.A. (2010). Mukhtasar Kitabul Targib wal Tarhib. Alƙahira.

Nawawi, A.Y. (BS). Riyadul Salihina. Al-Azhar: Maktabatul Iman Bil Mansura.

Sani, A-U.; Hamma, A.; Aliyu, I. & Aliyu, K. A. (2022). Mawaƙa a idon Hausawa: Ƙorafi a cikin waƙar ranar mawaƙa ta Fati Da Kasim. Scholars International Journal of Linguistics and Literature, 5(7), 209-216.  www.doi.org/:10.36348/sijll.2022.v05i07.002.

Suyiɗi, A. (2009). Tanwirul Hawaliki Ala Muwaɗɗal Imami Maliki. Alƙahira: Darul Ibn Haisami.

Shika, A.H. (2008). Bayani a kan Azumi. Zariya: (BM).

Shaukani, M. (2008). Nairul Auɗar. Aƙahira: Shirkatul ƘudusLiltijarati.

Tanko, Y. (2005). Muhimmancin Lokaci a Musulunci. kfg Limited.

Wali, N. (1953). Giza’ul Wildan fi Aƙa’idil Iman. Kano: Durusul Arabiya.

Yahaya, A.B. (1996). Jigo Nazarin Waƙa. Kaduna. Fisbas Media Serɓice.

Zubaidi, A.A. (2005). Tajridul Sarihu Li Ahadisil Jami’il Sahihi. Alƙahira: Darul Hadis.

Zahabi, S.M. (2007). Alkba’ir. Lebenon: Darul Fikr.

Zarnuji, B. (BS). Ta’alimul Muta’allimi fi Ɗariƙil Muta’allumi. (BM).

Zurmi, A.D. (2006).Tsoratarwa a Cikin Waƙoƙin Wa’azi na Nana Asma’u. Kundin Digiri na

Ɗaya. Sashen Koyar da Harsuna Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.



[1] A duba cikin Mukhtasar Al-Targibu wal Tarhibu lamba ta 35 da Ibn Maja lambta ta 264 da Ɗabarani lamba ta 22 da Abu Ya’ala lamba ta 2903 da sauransu.

[2] Malamai sun ƙarawa junansu sani a kan lokacin da yaro (yarinya) yake balaga[2]. Wasu na ganin idan yaro ya fara yin mafarki yana saduwa da mace ko idan ya fara gashin gaba ko na hammata ko kuma idan ya cika shekara goma sha takwas (18). Wasu kuma na ganin shekara goma sha biyar (15) ne shekarun balaga. Ma’ana idan yaro ya tsinci kansa da ɗaya daga cikin abubuwan da aka ambata a sama, to ya balaga. Haka kuma, mace tana balaga ne idan ta fara al’ada ko fitar ƙirji ko gashin mara ko idan ta kai shekara goma sha huɗu(14). Saboda haka, idan yaro ya tsinci kansa a ɗayan waɗannan abubuwa da aka zayyano a sama, to abu na farko da zai fara yi shi ne ya san wanene Ubangijinsa, sani na sakankancewa da yin imani da shi da gasgata shi. Ɗayanta Allah ita ce bauta ta farko kuma mafi girma da mutum zai yi yayin da ya balaga. Wannan ya sa koda kafiri idan ya shigo Musulunci, abu na farko da ake buƙatarsa da ya fara yi shi ne kaɗaita Allah a zuci da zahiri ta hanyar karanta kalmar shahada[2]. Wannan ya sa Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam yake cewa, “ mafi girman abin da na faɗa, ni da Annabawan da suke gabanina ita ce la’ilaha illallah[2]”. Wato kalmar tauhidi.

[3] A duba Muslim lamba ta 1015 da Timizi lamba ta 2989.

[4] Yanayin samuwar najasa ya rabu gida biyu, akwai wadda take fita a al’adance kamar gayaɗi ko bauli ko maziyi ko wadiyi ko maniyi ko jinin al’ada ko jinin haihuwa ko jinin cuta da sauransu. Haka kuma, akwai samuwar najasa wadda take aukuwa nan take kamar saukar wata najasa a jikin mutum ko fatarsa ko muhallin yin salla da sauransu. Wajibi ne idan ɗaya daga cikin waɗannan najasoshi ya samu mutum sai ya san yadda zai kawar da ita ta hanyar yin tsarki na wankewa ko wanka ko yayyafa ruwa ko kuma gogewa.

[5] . Alwala ita ce wanke wasu gaɓoɓin jiki na fuska da hannuwa da ƙafafuwa da kuma shafar kai domin samun tsarkakuwa daga dukkanin wani zunubi yayin da za a gaida Allah.

[6] Tanko (2005) yana cewa “ wata ƙila babu wata kalma guda ɗaya a Hausa da za ta fassara ‘lokaci’ illa Kalmar ‘zamani’. Hasanul Basari yana cewa, lokaci tari ne na kwanaki”. A ɓangaren Malaman kuwa, harshe Lokaci na nufin sa’ar wanzar da wani aiki. Lokutan salla suna nufin wasu ƙayyadaddun sa’o’in yin salla ne waɗanda addini ya sharɗanta yin salla a cikinsu a cikin dare da rana. Akwai lokutan salla guda biyar na salloli biyar masu ƙunshe da wasu sa’o’i na musamman waɗanda ake wanzar da salla a cikinsu.

Shigar lokacin salla yana ɗaya daga cikin sharuɗan salla wanda idan babu shi babu salla. Kowace salla (salloli biyar ɗin nan) ba ta wajaba a kan mutum har sai lokacinta ya shiga.Wannan ya sa da mutum zai yi salla kafin shigar lokacinta, sallarsa ba ta yi ba, ma’ana Allah ba zai karɓi sallarsa saboda ya saɓawa ɗaya daga cikin sharuɗan karɓar salla. Saboda haka ne malam Nasiru Kabara yake nusar da al’umma muhimmancin sanin lokacin salla wanda ya dace a yi salla a cikinsa da kuma hanyoyin da za su fahimci lokutan salla. Ga abin da yake faɗa a cikin wannan baiti da ke ƙasa:

[7] Zaɓaɓɓen lokaci shi ne lokacin yin salla wanda Allah ya fi so a yi salla a cikinsa, wato shi ne farkon lokacin yin salla. Shi ya sa malam Nasiru Kabara yake faɗa a cikin baitin da ke sama cewa ‘ a farko lokaci’, ma’ana zaɓaɓɓen lokaci. An karɓo hadisi daga Annabi Sallallahi alaihi wa alihi wa sallam cewa “ aikin da Allah ya fi so, shi ne yin salla a farkon lokacinta (zaɓaɓɓen lokaci)[7]” a wani Hadisi kuma, “ a kan lokacinta”.

Zaɓaɓɓen lokaci ya rabu gida uku. Wato akwai:

a- zaɓaɓɓen lokaci na farko

b- zaɓaɓɓen lokaci na tsakiya

c- zaɓaɓɓen lokaci na ƙarshe

A kowane ɗaya daga cikin waɗannan lokuta mutum ya yi salla, ya yi ta a cikin lokacinta. Za a ƙara gane haka ne idan aka dubi wani zance da aka karɓo daga Annabi sallallahu alaihi wa alihi wasalla cewa ” [7]farkon lokacin salla yardar Allah ce, tsakiyar lokacin (salla) rahamar Allah ce. ƙarshen lokacin (salla) afuwara Allah ce”. Wato Zaɓaɓɓen lokacin salla yana da tsawo (musamman na sallar Azahar da La’asar da kuma Isha), wannan ya sa aka raba shi gida uku dangane da falalal kowace sa’a. Zaɓaɓɓen lokaci da laluri lokuta ne masu yalwa. Domin ƙarin bayani a duba Ibn Maja lamba ta 227 da Nairul Auɗar, Juz’i na 1, a lamba ta 417,418 da ta 419 da kuma Tanwiril Hawalik sh. 50, a lamba ta 1.

Lalurin lokacin salla yana farawa ne bayan fitar zaɓaɓɓen lokaci. Lalurin lokaci, Lokaci ne wanda musulunci ya yarjewa mutum ya yi salla a cikinsa bisa wasu muhimman uzurai. Wato dai babu laifi idan mutum ya yi salla a cikinsa sai dai ladaddakin da za a bawa wanda ya yi a cikin zaɓaɓɓen lokaci shi ba zai same su ba.

Zaɓaɓɓen lokacin sallar azahar yana farawa ne daga karkatar rana ta yamma ( lokacin da inuwa mutum ta zama a cikinsa) zuwa ƙarshen ƙama (lokacin da inuwar mutum za ta yi daidai da tsawonsa). Wato dai daga misalin ƙarfe 12:15nr zuwa 3:25nr. Lalurinta kuma yana farawa ne daga farkon zaɓaɓɓen lokaci na la’asar zuwa gab da fatsi fatsin rana. Zaɓaɓɓen lokaci na sallar la’asar kuma yana farawa ne daga ƙarshen ƙama zuwa ( lokacin da inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa da ɗani ɗaya) zuwa jajatar rana (lokacin da inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa sau biyu. Lalurinta kuma yana farawa ne daga ja-ja-jan rana zuwa faɗuwarta. Lokacin lalurin sallar azahar da na la’asar kusan suna ƙarewa ne a tare, wato bayan faɗuwar rana. Haka kuma, zaɓaɓɓen lokacin sallar magariba yana farawa ne daga daga faɗuwar rana zuwa gwargwadon fara sallar da kammalata ( wasu na ganin sai bayan kamala zikiran bayan sallar). Shi kuma zaɓaɓɓen lokaci na sallar Isha yana farawa ne daga ɓoyuwar shafaƙi ( ɓoyuwar ja-ja-jan rana gaba ɗaya) zuwa ukun dare na farko ( kamar 10:00nd a yanzu). Lalurin sallar magariba da na isha suna tafiya ne kusan a tare, kuma su ƙare a tare. Wato suna ƙarewa ne bayan ɓullowar alfijir na gaskiya. Haka shi ma zaɓaɓɓen lokaci na sallar asuba, yana farawa ne daga ɓullowar alfijir na gaskiya zuwa fatsi-fatsi maɗaukaki (wato lokacin da mutum zai iya gane ɗan’uwansa). Lalurinta kuma yana kasancewa har zuwa ɓullowar rana.

Duk wanda ya yi salla ba a cikin ɗaya daga waɗannan lokuta (zaɓaɓɓe da laluri) ba, to ya yi ta ne a cikin lokacin ramuwa[7]. Wato lokacin da aka hana a yin salla a cikinsa. Ahalari (2007) yana faɗa cewa, “ duk wanda ya jinkirta salla har lokacinta ya fita, ya aikata zunubi mai girma, sai dai idan ya kasance yana da uzuri na mantuwa ko bacci”.

[8] A duba Mukhtarul Hadis lamba ta 161.

[9] A duba Arba’una Hadisi lamba ta 1 da Riyadul Salihina lamba ta 1.

[10] Yin salati a cikin salla ba wajibi ba ne a mazahabar Mailkiya saboda haka, sai malam Nasiru ya yi amfani da fatawar Imamu Shafi’i ta ayyana wajabcin yin salatin Annabi Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam a cikin salla. Imamu Shafi’i yana faɗa a cikin wasu baitoci cewa:

Ya ‘ya’yan gidan Annabin Allah son ku,

Farilla ne da Allah ya saukar a Ƙur’ani.

Ya ishe girman abin alfahari cewa ku,

Duk wanda bai yi salati a gare ku ba shi da salla.

An karɓo hadisi cewa, Sahaban Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam bayan ayar umarni a kan salati ta sauka sai suka tambayi cewa, mun san yadda za mu yi maka sallam, amma ba mu san yadda za mu yi maka salati ba. Sai ya ce “ ku ce ya Allah mai dubun sunaye, ka yi salati ga Muhammadu da Ahalinsa[10]”. Ahalin gidan Annabta kuwa su ne ma’abota barko, wato su ne Annabi da kansa da Nana Faɗima da Hassan da Hussaini da kuma Aliyu, kamar yadda wani zance na Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya bayyana[10].

Saboda haka, wannan baitoci na Imamu Shafi’i sun nuna wajabcin yin salatin Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam a cikin salla. Wanda kuma duk ba yi ba, to ba shi da salla a wurin Imamu Shafi’i. Wannan dalili ya sa malam Nasiru Kabara ya ayyana tahiya a cikin jerin ayyuka salla wajibabbu. Haka kuma, sallama da ake yi ta fita salla daga salla, wajiba ce da kuma zama domin yin ta. Lafazin sallarmar shi ne Assalamu alaiku ba ‘salamu alaikum ba’ kamar yadda wasu suke yi. Kuma sallama ta farko ita ce wajibi. Wannan ya sa a Mazahabar Malikiya sallana ɗaya ake yi yayin fita daga salla ba guda uku ba kamar na sauran Mazahabobin.

[11] A duba Tajridul Sarihu lamba ta 925.

[12] Idan mutum noman damuna ya yi , zai fitar da kaso ashirin ne bisa ɗari na adadin buhuhunan da ya noma. Idan kuma noman rani ne, to kaso goma zai fitar kammar yadda aka ambata a sama.

Faɗakarwa da ilimantarwa

Post a Comment

0 Comments