Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Wakar Hattara 'Yan Siyasa Ta Malam Ahmad Makari

Takarda Wadda aka Gabatar a Taron Ƙarawa Juna Sani na Ƙasa a kan Rayuwa da Gudummawar Sheikh Ahmad Sa’idu Maƙari a Sashen Fasaha da Nazarin Al'adu na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya Tare da Haɗin Guiwar Gidauniyar Ilimi ta TANMIYA Dake Nijeriya, Daga 29 ga Watan Janairu 2025 Zuwa 30 ga Watan Janairu 2025.

NAZARIN WAƘAR HATTARA 'YAN SIYASA TA MALAM AHMAD MAƘARI

Daga

Musa Muhammad Labaran
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero, Kano.
08161747863
muhammadmusalabaran@gmail.com

Da

Hifzullahi Ahmad Muhammad
Sashen Koyar da Kimiyar Harshe da Harsunan Ƙasashen Waje
Jami’ar Bayero, Kano.
08133393733
hifzullahiahmad@gmail.com

Tsakure

Rubutattun waƙoƙin Hausa sun biyo bayan zanguna aƙalla guda uku. Wato lokacin zuwan addinin Musulunci da zuwan Turawa da kuma lokacin siyasa da sojoji. Wannan ya sa a farkon ƙarni na ashirin (Ƙ20) aka fara samun waƙoƙin siyasa masu jigogi daban-daban. Kuma yawancinsu suna da zubi da tsari da salo da sarrafa harshe irin na waƙoƙin ƙarni na goma sha tara (Ƙ19), wato lokacin masu Jihadi. Wannan waƙa tana cikin waƙoƙin da aka rubuta a cikin ƙarni na ashirin (Ƙ20). Babbar manufar wannan bincike ita ce yin nazarin waƙar hattara ‘yan siyasa domin fito da jigon da aka gina waƙar a kansa tare da ƙananan jigogin waƙar da kuma zubi da tsari da salo da sarrafa harshe. An zaɓi mazahabar Ɗangambo (2007 da 2011) a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a kansa. An yi amfani da dabarar bincike bi-bayani wajen yin sharhi da ƙalailaice saƙonnin da waƙar take ƙunshe da su da sauran matakan nazari a matanonin waƙar. Binciken ya gano cewa, mulkin soja shi ne ya fara haifar da ɓarna da rashin tsaro da ake fama da shi a Nijeriya tun daga wancan lokaci, har ya yo naso izuwa yanzu. Haka kuma, binciken ya gano cewa, adalci shi yake haifar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da yalwar arziƙi a tsakanin al’umma. Amma duk lokacin da aka rasa adalci daga shugabanni, to duk wasu ƙofofin ɓarna sun buɗe.

Keɓaɓɓun Kalmomi: Nazari, Ahmad Maƙari, waƙa, siyasa, hattara.

1.1 Gabatarwa

Waƙoƙin Hausa Hausa sun zama wasu mazubai waɗanda ake zuba saƙonni muhimmai na gyaran hali ko faɗakarwa ko nusantarwa da kuma adana tarihi domin hasko rayuwar magabata mai kyau domin a yi koyi da su, da kuma saɓanin haka domin a guje mata. Wannan ya sa waƙoƙin Hausa, musamman rubutattu suke ƙunshe da jigogi daban-daban, ciki har da na siyasa da tsarin mulki.

Tun lokacin da aka bawa Nijeriya 'yancin-kai a shekarar 1960, akwai fararen hula da sojoji wadanda suka yi mulki a matakai daban-daban. Waka Bahaushiya tana tafiya ne tare da al'adu da ɗabi'un Hausawa wadda kuma ta ratsa zanguna aƙalla guda hudu. Wato lokacin zaman farko (lokacin Maguzanci) da bayan zuwan addinin Musulunci da lokacin Turawa da Zamanin siyasa da sojoji. Wannan dalili ya sa wannan waƙa ta keɓanci ambato a kan yanayin yadda sojoji suka gudanar da mulki na ɓarna kuma ta yi kira ga 'yan siyasa a kan su ƙauracewa irin ɗabi'u da halayen mulki irin na sojoji.

A wannan takarda, an yi nazarin wannan waƙa mai suna 'hattara 'yan siyasa' ta Sheikh Ahmad Maƙari, nazari na gaba ɗaya. An kawo ma'ana da samuwar rubutacciyar waƙa ta Hausa. Haka kuma, an kawo tarihin marubucin waƙar a taƙaice da salsalar waƙar da kuma shekarar da aka rubuta Waƙar. Sannan an kawo ma'anar jigo da kuma bayanin jigon waƙar da zubi da tsari da salo da sarrafa harshe na waƙar. A ƙarshe kuma aka kawo kammalawa da manazarta.

An yi amfani da Mazahabar rubutacciyar waƙa ta Ɗangambo ( 2007 da 2011) a matsayin ra'in da aka dora wannan takarda a kansa. Kuma ra'i ne wanda shimfiɗa wasu matakai na yadda za a yi nazarin rubutacciyar waƙa ta Hausa.

1.2              Taƙairaccen Tarihin Samuwar Rubutacciyar Waƙa a Ƙasar Hausa

Masana irin su Ɗangambo (1984) da Sa’id (1981) da Yahaya (1979) da Gusau (2003) da (2008) da Auta (2017) sun tabbbatar da cewa kafin zuwan addinin musulunci, Hausawa ba su da ilimin karatu da rubutu. Wannan ya sa babu wata rubatacciyar waƙa da Hausawa ke da ita kafin zuwan musulunci. Tun a wajejen ƙarni na (10) ne zuwa (11) ake zaton Musulunci ya fara zuwa ƙasar Hausa. Sai dai tarihi ya nuna cewa, Musulunci ya zo ƙasar Katsina ne a lokaci mulkin Muhammadu Korau 1320-1353. Sannan ya zo Kano ne a lokacin mulkin Yaji Dantsamiya 1349 -1355. Bayan zuwan musulunci ne, Hausawa suka duƙufa wajen koyon ilimin addini da na Larabci. Bayan da suke sami ilimi addini da na Larabci, sai kuma suka fara sarrafa harufan Larabci wajen rubuta harshensa da shi, wato ajami wanda da shi ne aka fara rubuta rubutattun waƙoƙi na Hausa . Tarihi ya nuna cewa, an fara samun rubutacciyar waƙar Hausa ne a ƙarni na (17). Wato a wannan lokacin ne ake samu waƙar yaƙin Badar. Sai kuma a ƙarni na 18, aka samu wasu malamai waɗanda suka rubuta waƙoƙi da dama, kamar Malam Shitu ɗan Abdurra’uf da Malam Muhamamdu n a birnin Gwari. A ƙarni na 19 kuma aka sami bunƙasa da haɓakar rubutattun waƙoƙi. A sanadiyar Jihadin Shehu Usman Ɗanfodio. Shehu Usman ya rubuta waƙoƙi da dama tun kafin jihadi, haka lokacin jihadi, sannan ya rubuta bayan jihadi. Sannan mabiyansa da almajiransa ma sun rubuta waƙoƙi da yawan gaske. Kamar Abdullahi Ɗan Fodio da Nana Asma’u da Isan Kware da Muhammmad Bello da sauransu.

Rubutattun waƙoƙin Hausa sun bazu, sun fantsama saƙo da loko na ƙasar Hausa, ta hanyar rerewa a masallatai da wuraren wa’azi da makaranta da kuma wurin bara ga mabarata.

1.3 Ma’anar Rubutacciyar Waƙa

Masana da manazarta irin su Yahaya (1984) da Ɗangambo (1981 da 1984 da 2007) da Umar (1982) duk sun bayyana ma’anar waƙa. Misali, Ɗangambo (2007) yana cewa “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta sauti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa–amo (kafiya), da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidata kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

Yahaya ((1984) na cewa “ Waƙa maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba, wanda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu.

Waɗannan kaɗan kenan daga masanan da suka bayyana ma’anar rubutacciyar waƙa. Za a iya bayyana rubutacciyar waƙa da cewa, waƙa wani azanci ne da ake shirya shi tare da tsarawa bisa bin wasu keɓaɓɓun ƙa’idoji da sharaɗu domin isar da wani saƙo cikin ɗangwaye da baitoci ta amfani da hawa da saukar murya ko kari kuma a rera ta.

1.4 Bayanan Sharar Fage

1.4.1 Taƙaitaccen Tarihin Marubuci

An haifi malam Ahmad Sa'idu a 08-08-1947 a cikin garin Kusfa dake garin Zariya a Jihar Kaduna. Sunan mahaifinsa malam Sa'idu ɗan malam Ahmad Badikko. Asalinsu mutanen Ƙasar Libya ne wanda daga baya suka koma ƙasar Morocco. Haka kuma, daga baya kakanninsa suka yiwo ƙaura zuwa ƙasar Katsina, wasu kuma suka fantsama zuwa ƙasar Kano kamar zuriyar Sharif Hamza da sauransu. Daga nan ne mahaifinsa malam Ahmad ya tafi izuwa garin Zariya neman ilimin addinin Musulunci, inda a nan ne ya haɗu da manyan malamai na addinin Musulunci kuma ya karanta Fannonin ilimin addinin Musulunci daban-daban a wurinsu. Wanda kuma a nan ne aka haifi malam Ahmad Maƙari.

Zuriyar malam Ahmad Maƙari ta tuƙe har kan Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, ta kan Sayyidi Hassan ɗan Aliyu ɗan Abu Ɗalibi ɗan Sayyida Faɗima 'yar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam.

1.4.1.1 Neman Iliminsa

Malam Ahmad Maƙari ya fara neman Iliminsa ne tun yana da ƙananan shekaru a wajen mahaifinsa malam Sa'idu, har sai da ya cika shekara talatin (30). Haka kuma, ya samu ilimai daban-daban a Fannonin Musulunci da kuma harshen Larabci a wurin manyan malamai daban-daban dake cikin garin Zariya.

A ƙoƙarinsa na ci gaba da neman ilimi, ya shiga makarantar Shehu Tasi a shekarar 1957. Bayan wasu shekaru kuma ya wuce izuwa Kwalejin Koyar da Malamai ta Larabci (ATC) dake Katsina a shekarar 1973. A shekarar 1977ne malam ya samu shaidar daukar ɗalibi na karatun Difloma a Sashen Koyar da Harshen Larabci da Addinin Musulunci dake Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. Sannan ya ƙara samun wata shaidar daukar karatun na Difloma a kan harshen Hausa da Larabci da kuma addinin Musulunci a Jami'ar Bayero dake Kano a 1981. Wanda kuma ya kammala digirinsa ne a Jami'ar ta Bayero a shekarar 1986.

Malam Ahmad Maƙari malami ne da ya shawara wajen bada gudummawa ga al'umma da koyarwa a matakan ilimi daban-daban. Haka kuma, masani ne a kan fannoni ilimai na kimiyar harshe da rubutun waƙoƙi da sauransu. Haka kuma, ya shawara wajen yin rubuce-rubuce a kan sha'anin addinin Musulunci kamar ilimin matanin Hadisi da kimiyar Hadisi da ilimin zance da Aruli da sauransu.

Malam Ahmad Maƙari yana da ɗalibai masu yawa, wasu daga cikinsu su ne:

Farfesa Arsalan Muhammad, Sashen Koyar da Harkar Shari’a, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

Farfesa Ibrahim Ahmad Maƙari, Limamin Masallacin Ƙasa dake Abuja.

Farfesa Yahuza Suleman, Shugaban NBAIS

Farfesa Nasiru M. Ibrahim, Sashen Koyar da Harshen Larabci, Jami’ar Jihar Kaduna.

Farfesa Mustapha Yusuf, Sashen Koyar da Harshen Larabci, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa Jihar Katsina.

Alhaji Jafar Miftahu Yahaya CEO, Alaƙat Construction and Property Deɓelopment.

Justice A.S Yarima, Kadi, Shari’a Court of Appeal

Justice Mahadi Muhammad Siraj, Kadi Shari’a Court of Appeal Kaduna.

Da sauransu.

1.4.2 Salsalar Waƙar

An samu wannan waƙa ce a cikin kundin waƙoƙin Sheikh Ahmad Maƙari, wanda kundi ne wanda ya ƙunshi waƙoƙinsa waɗanda ya rubuta da harshen Larabci da kuma harshen Hausa. Haka kuma, an samu wannan kundi ne ta hannun malam Dayyib.

1.4.3 Shekarar da aka Rubuta Waƙar

Wannan waƙa, waƙa ce wadda aka rubuta ta a shekarar 1990. Wato a lokacin da sojoji suke ƙoƙarin miƙa mulki ga farar hula kafin kuma daga bisani su sake ɗanewa kan karagar mulkin. Wato ita wannan waƙa babu ramzi a cikinta na shekarar da aka rubuta, mawallafin ya bayyana shekarar da ya rubuta ta ƙarara a ƙasan takardar da aka buga waƙar a ciki.

2.1 Jigo

Masana masu yawa sun bayyana ma’anar jigo a fannin nazarin adabin Hausa. Daga cikinsu akwai Gusau (1983) da Ɗangambo (2007 da 2008) da Mukhtar (1984) da Buhari (1988) da ‘Yar’aduwa (1999) da Chamo (2011) da Halima, Ɗangambo (2012) da Labaran (2024) da sauransu. Labaran (2024) yana cewa, “ jigo shi ne saƙon da mawallafi ya gina waƙarsa a kansa kuma yake burin isar da shi ga waɗanda (wanda) abin ya shafa”. Wato jigo shi ne haƙiƙanin manufa wanda ta sanya marubuci ya rubuta waƙarsa domin isar da saƙon dake cikin waƙar ga al’umma ko waɗanda abin ya shafa kai tsaye.

Babban jigon wannan waƙa mai suna ‘Hattara ‘yan Siyasa’ shi ne illar ‘mulkin Soja’.

2.1.1 Furucin Gundarin Jigo a Waƙar Hattara ‘Yan Siyasa

Furucin gunfarin jigo na nufin muhalli na farko da mawaƙi ya fara bayyana jigon waƙarsa a cikin wani baiti ko ɗango. Wato wuri ne wanda mawallafi ya fara ambaton ainihin gundarin saƙon da yake so ya isar ga jama’a. Ɗangambo (2007) yana cewa “ jawabin jigo, ƙwayar jigo ce da ke iya samu ƙunshe cikin wasu baitoci da ke nuna tabbacin manufar mawallafin…” mawaƙa kan iya iya ambaton gundarin saƙon waƙoƙinsu tun a farkon waƙar, wasu kuma sai a tsakiyar waƙar. Sai dai akan samu wasu daga cikin mawaƙa da kan yi amafni da hikima wajen ɓoye manufar da suke son isarwa. Wato ba sa fitowa ƙarara su nuna saƙon da waƙar take ƙunshe da su. Ga mai nazari, idan aka samu waƙa mai irin haka, zai bi waƙar ne lungu-lungu ya tattaro dukkan wasu saƙonni waɗanda za su iya bada haske a kan gundarin saƙon waƙar, sannan ya bayyana jigon waƙar.

Wannan waƙa ba a bayyana gundarin jigonta ba ƙarara, hasalima sai a tsakiyar waƙar muwallafin ya bayyana jigon waƙar a cikin wasu baitoci. Ga muhallan da aka bayyana gundarin jigon waƙar a ƙasa:

Mun sha wuya mun farace lokacin Soja,

Allah ya sa kar a maimaito irin na jiya.

In munka sake shiga ni-‘yasu sai saura,

Ya taho ya wargaza tsarin nan na Tarayya.

(Baiti na 39-40)

Allah ka sa mun yi ban-kwana da sojoji,

Sai dai mu gan su a Bariki banda kan hanya.

(Baiti na 58)

Sun ɓata tsari na kirki wanda sunka taras,

Sun sace ɗimbin kuɗi sun kai gurin ajiya.

(Baiti na 3)

Idan aka lura, za a ga a cikin waɗannan baitoci na 39-40 da 58 da kuma na 3 muwallafin ya bayyana dalilin rubuta waƙarsa. Wato yana bayyana irin illa da ɓarnar da mulkin soja ya yi a Nijeriya har ta kai yana addu’ar kada Allah ya dawo da mulkin Soja. Haka kuma, yake yin kira ga ‘yan siyasa kada su bi sahun irin yadda Sojoji suka yi mulkin zalunci da ɓata ƙasa a Nijeriya idan sun karɓi mulki. Kar ku ma su yi abin da har Soja zai ƙara yin sha’war dawowa mulkin Nijeriya, domin kuwa idan suka sake dawowa, to sai sun ruguza ƙasar baki ɗayanta saboda ɓarnar da za su ci gaba da yi.

Idan aka karanta waƙar, za a ga ya kawo wasu miyagun laifuka da ɓarnace-ɓarnace aƙalla guda 10 waɗanda aka fare su ko aka yawaita aikata su a lokacin mulkin Soja saboda irin zaluncin da suke yi wa al’umma da sakaci da kuma karya tattalin arziƙin ƙasa da sace kuɗin al’umma kuma suka bar su cikin yunwa da fatara.

Bayan wannan babban jigo na ‘illar mulkin Soja’, akwai kuma ƙananan jigogi waɗanda aka yi amfani da su wajen gina babban jigon waƙar. Wato akwai jigon nasiha da wa’azi da ta’aziya da gargaɗi da janhankali da sauransu.

2.1.2 Jigo a Gajarce

Wannan wata dabara ce ta taƙaita abubuwan da aka faɗa cikin waƙa domin fayyace manufofin da waƙar ke ɗauke da su. Ɗangambo (2007) ya faɗa cewa “ a nan, za a bi waƙar ne a taƙaice, ana taƙaita baiti bayan baiti. Za a yi hakan ne ba tare da bayyana ra’ayi, sharhi ko wani dogon bayani ba”. A taƙaice, wannan wata dabara ce da ake yi domin taƙaice duk abin da waƙa ta ƙunsa dangane da manufofi bisa tsarin jadawali wanda zai ƙara haskawa ko fitowa da mai karatu dukkanin saƙonnin da waƙar ke ƙunshe da su, a taƙaice.

A wajen gajarta jigo, ana dubawa a ga cewa shin waƙar tana da jerin tunani, ko kuma an yi tafiyar kura a cikinta wajen ƙuƙƙula saƙonninta.

Wannan waƙa ta ‘Hattara ‘yan Siyasa’ ba ta da jerin tunani, wannan ya sa aka taƙaita jigonta ta amfani da hanyar taƙaita jigo ta biyu, waro kamar haka:

1.Kira ga ‘yan siyasa a kan daina murna domin za su hau mulkin Nijeriya, domin Sojojin sun ɓata ƙasar, sun bar musu babban aiki na gyara: baiti na 1, 2, 7.

2.Furucin gundarin jigo: baiti na 3, 39-40, 58.

3.Bayyana makircin sojoji domin idan sun miƙa mulki ga farar hula, daga baya kuma su ƙara dawowa su ce ai farar hula sun gaza. Saboda daman sun san sun ɓata ƙasar, farar hula ba za su iya gyara ta ba: baiti na 4.8.

Bayyana irin abubuwan da mulkin Soja ya haifar na ɓarna a Nijeriya kamar fashi da makami da yankan-kai da ƙungiyoyin asiri da masu hana haƙar man fetur (Ogani) da rikicin manoma da makiyaya da fataucin miyagun ƙwayoyi da damfara ta 419 da rikicin Bukasi da kuma ayyukan Shia: baiti na 8-17,19,28.

4.Bayyana irin yadda mulkin Soja ya ɓata tattalin arziƙin ƙasa wanda hakan ya haifar da tsadar takin noma da ƙarancin man fetur da ɓata tsarin masarautin gargajiya da karya darajar naira da ciyon bashisshika da sauransu: baiti na 20,23,27.

5.Magana a kan yadda mulkin Soja ya lalata harkar ilimi a Nijeriya har ta kai ana samun yawaitar yajin-aiki na malamai da sauran ma’aikatan Gwamnati. Haka kuma, da amfani da takardun bogi: baiti na 24,26,30.

6.Bayyana yanayin yadda mulkin Soja ya yi sanadiyar samuwar cin hanci da rashawa: baiti na 25.

7.Bayyana yadda Gwamnatin Soja ta sace kuɗaɗen ƙasa suka kai su ƙasar waje: baiti na 31

8.Yin nasiha ga ‘yan siyasa a kan su tsaya su yi abin da ya dace idan sun karɓi mulkin Nijeriya: baiti na 33-36,40-41.

9.Bayyana halin ‘yan siyasa na son zuciya da sace kuɗin talakawa: baiti na 43-47,52.

10.Tona asirin ƙasashen Turai na irin yaudararsu a kan ƙananan ƙasashe ta fuskar taimako kuma su sace dukkanin dukiyarsu: baiti na 48-51,53-55.

11.Yin addu’a ga ƙasa da yan ƙasa a kan halin da ake ciki da kuma yin neman afuwa da gafara a kan waɗanda suka mutu (Musulmai) a sanadin halin da ƙasa ta shiga: baiti na 56-60.

12.Baitin ƙarshe da yin nasiha ga waɗanda ya rubuta waƙar domin su, a kan su yi amfani da nasihar: baiti na 61.

2.1.3 Warwarar Jigo

Wannan waƙa an gina jigonta a kan faɗakar da wani rukunin al'umma, wato 'yan Siyasa a kan irin illar da mulkin sojoji ya yi a ƙasa Nijeriya a lokuta mabambanta. Wato Waƙar ta yi kira a kan idan mulki ya dawo hannun farar hula, su dauri su kyautata wa al'umma kuma su yi aiki tuƙuru domin ciyar da ƙasa gaba. Wannan ne kawai zai sa Soja ya kasa ƙara dawowa kan karagar mulkin Nijeriya ballanta har ya sake yin irin ɓarnar da ya yi a baya. Idan ka dubi wannan baitin dake ƙasa za a ga yana cewa:

Mun sha wuya mun farace lokacin Soja,

Allah ya sa kar a maimaito irin na jiya.

Sojoji sun yi mulki a lokuta daban-daban kusan sau shi da ko bakwai a cikin cikakken juyij mulki guda biyar. A 15-01-1966 wasu matasan sojoji suka yi juyin-mulki inda a lokacin ne aka kashe wasu manyan Arewa, ciki har da Tabawa Ɓalewa da Ahmadu Bello da wasu daga manyan Kudu kamar irin su Akintola da sauransu. Haka kuma, suka ɗora Johnson Aguiyi Ironsu a matsayin shugaban kasar Nijeriya na Soja. Tun wannan lokaci ne aka fara samun ɓarna a Nijeriya da zalunci da ƙudurce ramuwa da ta-zaunar-tsaye musamman a kan abin da ya shafi shugabanci. Kashe su Sardauna ya yi wa mutanen Arewa ciyo sosai, wannan ya sa suka shirya juyin mulki na ramawa, wato Soja ya ƙwaci mulki a hannun dan'uwansa soja ta ƙarfin tuwo. Wato a 26-07-1966 ne sojoji suka ƙwaci mulki a hannun dan'uwansu Ironso inda kuma suka ɗora sabon shugaba wato Yakubu Gawon.

Bayan da ƙasa ta koma hannun sojoji sai abubuwa suka taɓarɓare, ƙasa ta fara lalacewa, wannan ya sa wasu gungun sojoji suka yi sanarwar juyin mulki a 29-07-1975 a lakacin da Yakubu Gawon ya tafi taron haɗa kan Afirka wanda aka yi a Kammala. Wanda daga nan ne suka ɗora Birgediya Murtala Muhammad. Sai kuma a 13-02-1976 aka ƙaƙarin juyin mulki har aka kashe Shugaban Ƙasa Murtala Muhammad amma wannan juyin mulki bai yi tasiri ba. Wannan ya sa mataimakinsa Olusegub Obasanjo ya ɗare kujerar ya ci gaba da tafiyar da ita har zuwa wani lokaci. Bayan wannan, sojoji sun yanke shawarar mayar da mulki ga farar hula wanda a ƙarshe aka yi zaɓe, kuma shugaban Ƙasa Shehu Shagari ya samu nasara. Amma a 31--12-1983 wasu sojoji suka ƙara yin yujin mulki inda suka ɗora shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A lokacin Buhari, yunwa ta yawaita da yajin aiki daga malamai da ma'aika da karya 'yan kasuwa da rigingimu da ƙungiyoyin lauyoyi da ta'addanci irin na su Maitatsine a Kano da sauran abubuwan ɓarna da suka cika Nijeriya. Wadannan dalilai suka sa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Muhammadu Buhari juyin a mulki a 27-08-1985.

A lokacin da Babangida ya hau kan mulki an yi amfani da kuɗaɗen ƙasa wajen yin wasu aikace-aikace na raya ƙasa na manyan ayyuka. Amma kuma a lokacin ne Nijeriya ta samu kanta a yanayin da bata taɓa zata ba na lalacewa da taɓarɓarewar al'amura. Tun daga wancan lokaci abubuwa ƙara gaba suke yi na lalacewar ƙasar har zuwa yanzu. Wannan ya faru ne kuwa saboda irin mulkin da sojojin wannan lokaci suka yi, inda har ta kai an hofantar da ɓangaren noma aka dogara kawai a kan ɗanyen man fetur, kuma a ƙarshe man taƙi samuwa ga 'yan ƙasa, wannan ya sa aka fara samun rashin tsayayyen farashi. Haka kuma, duk wani ɓangare da ake samun kuɗin shiga, sai da suka hofantar da shi, suka koma kan man fetur kawai. Wannan shi ne ya yi sanadiyar mutuwar noma a yankin Arewa. Sannan, aka ciyo manyan basussuka daga ƙasasehn waje da karya darajar naira, wato dai mulki Babu ƙwarewa wajen tafiyar da shi. Wannan ya sa talauci da yunwa suka ƙaru a ƙasar da ayyukan ta'addanci da cin zarafin ƙananan mutane da yawaita da yaɗuwar cututtuka da taɓarɓarewar harkar ilimi da kwararowar 'yan ƙauye cikin birane saboda rashin abubuwan more rayuwa da talauci da kuma yunwa. Wannan ya sa malam yake cewa,

Sun ɓata tsari na kirki wanda sunka taras.

Wato kafin zuwan mulkin sojoji a 1966, Nijeriya ba ta fuskantar dukkanin irin waɗannan matsaloli. Wato wannan tsari na sojoji shi ne silar haifar da talauci a Nijeriya wanda har ya yi sanadiyar samar da wasu ayyukan ta'addanci da ɓarna. Wannan ya sa za a ga malam yana cewa,

Ga 'yan fashi da makami kowane hanya,

Da dare da rana suna ta fashi ga mai tafiya.

Sabon salon damfara sunarsa 419,

Ya zam ruwan dare ya game ko wane shiyya.

'Yan ƙungiya na asiri masu yankan kai,

Sun kasa yin maganinsu bare farin kaya.

Wato yunwa da talauci da mulkin sojoji suka haifar a wancan lokaci ya sa kowa ya nema wa kansa mafita domin ya rayu, wasu ta hanya mai kyau wasu kuma ta hanya marar kyau kamar dai yadda malam ya ambata a cikin waɗannan baitoci dake sama.

A shekarar da aka rubuta wannan waƙa ce, wato 1990 aka shirya yi wa shugaban ƙasa na Soja wato Babangida juyin mulki amma ba a samu nasara ba. Bayan wani lokacin 'yan siyasa da manyan ƙasa suka matsawa shugaban ƙasa lamba a kan a dawo mulkin farar hula saboda taɓarɓarewar da ƙasa ta yi a lokacin. Wannan dalili ya sa Babangida ya yi murabus daga kujerar shugaban ƙasa, kuma ya ba wa Ernest Shonekan shugabancin Nijeriya na riƙon ƙwarya kafin a yi zaɓe a 26-08-1993. Amma Shonekan watanni uku kawai ya yi a kan mulki Janar Abacha ya yi masa juyin mulki a 17-11-1993.

Bayan rasuwar Janar Sani Abacha a shekarar 1998, aka yi zaɓe a 1999 inda daga nan har zuwa yau ake gudanar da mulkin Nijeriya a kan tsarin mulkin farar hula. A lokacin da Janar Babangida yake ƙoƙarin miƙa mulki ga farar hula, malam ya yi kira ga 'yan siyasa a kan kada su yarda su bi irin tsarin mulkin sojoji na ɓata ƙasa da cin hanci da ɓarna idan sun karɓi mulki, shi ne malam yake cewa,

In Kun ci sa'a ku Kai aiki na san barka,

Naijeriya za ta dawwama Babu jayayya.

In kun bi tsari na 'yan jarinka ne hujja,

Kuka sake tatse Ƙasarku za ku sha kunya.

Amma duk da wannan faɗakarwa da jan hankali da aka yi wa 'yan Siyasa, amma sai da suka dinga yin ɓarnar da har 'yan ƙasa suna buri da kiraye-kiraye ga sojoji domin su yi juyin mulki su karɓi ƙasar. Lalle idan mai karatu yay i la’akari da abubuwan da aka ambata na ɓarna da sojoji suka yi lokacin da suke mulki da kuma irin kiraye-kirayen da 'yan ƙasa suke yi a yau, to za a gane cewa, 'yan Nijeriya suna cikin wani matsananci hali wanda ya fi na sojoji masifa a gare su. Abin da ya koro ɓera daga rami zuwa wuta, ya fi wutar zafi, inji Hausawa.

Shugabanin siyasa na Nijeriya aa yau, sun miƙa wulayarsu duka ga Turawa, wannan ya sa suka haɗa kai da su wajen cutar da al'ummar ƙasa ta fuskoki daban-daban. Idan aka duba za a ga malam ya yi kira ga 'yan siyasa cewa kada su aminta da Turawa a matsayin waɗanda za a riƙa domin kawo taimako. Za a ga yana cewa,

Manyan ƙasashe dake cewa suna yaƙi,

Domin su 'yanto ƙasashe wanda ke baya.

Ƙaryar tsiya, marasa tausai da imani,

Waɗanda kan sa ruwan bashi a kasa biya.

Gidanmu na kan tudu su sun yi nasu kwari,

Komi ya kucce a gunmu gare su za ya tsaya.

Idan aka dubi waɗannan abubuwa da malam ya faɗa tun a wancan lokaci, su ne suke faruwa a yanzu kwabo da kwabo kuma su ne suka saka ɗan ƙasa a halin da yake ciki a yanzu na yunwa da talauci da cuta da ta'addanci da zalunci da damfara da sata da mace-mace a sanadiyar yunwa, har ta kai ɗan ƙasa ba ya iya cin abinci sau biyu a rana. An taɓarɓa harkar ilimi da kasuwanci da noma da sana'o'i dama tattalin arziƙin gaba ɗaya. 'Yan siyasa sun ɓata Nijeriya sama da yadda sojoji suka ɓata ta sau ninki ɗari. Allah ya gyara mu ya kuma gyara ƙasarmu, amin.

3.1 Zubi da Tsarin Waƙar Hattara ‘yan Siyasa

3.1.1 Zubi da Tsari na Gaba Ɗaya

Wannan waƙa mai suna ‘hattara ‘yan siyasa’, marubucin ya jeranta saƙonnin cikinta ta yadda mai karatu zai kai ga inda ake so ya kai, kai tsaye ba tare da ya sha wuya ba. Haka kuma, ya yi amfani da kalmomi masu makusanciyar ma’ana da juna da jumloli dogaye da kalmomin fannu da tsofaffi da sauransu.

Wannan waƙa, waƙa ce wadda take ɗauke da baitoci sittin da ɗaya (61). Haka kuma, tana da ɗangwaye bibbiyu, wato waƙa ce ‘yar tagwai. Tana kuma da ƙafiya guda biyu. Wato babba da ƙarama. Babban ƙafiyar waƙar ita ce, ‘ya’. Wato waƙar ‘yayiya’ ce. Sannan tana da ƙananan ƙafiya mai sauyawa a cikin kowane baiti. Waƙar ta ƙunshi ƙananan ƙafiyoyi na ki, ri, ras, wa, ko, ka, na, ya, sa, kai, a, ma, wo, to, ra, su, ba, ta, ƙi, ne, sur, mu, ci, ni, ja, mi, she, da, ce da kuma do. Amma kuma ba ta da mabuɗi da marufi.

3.1.1.1 Gangara

A cikin wannan waƙa akwai baitoci inda aka samu gangara a cikinsu. Wato saƙonni da aka ƙullo a cikin ɗango na farko, ba a cika ma’anarsa ba sai a cikin ɗangon da yake biye da shi. Ga misalan wasu baitoci da suke ƙunshe da wannan dabara ta gangara:

Sabon Salon damfara sunarsa (419).

A wannan ɗango, mawallafin ya fara bayanin wata sabuwar damfara da ta shigo Nijeriya. Saboda haka, da za a bar wannan ɗango a haka, ma’anarsa ba ta cika ba saboda ana buƙatar a ji menene dalilin ambatar sunan damfarar? Wannan ya sa sai a ɗango na biyu ya bayyana dalilin faro ma’anar a ɗango na ɗaya, inda yake cewa:

Ya zam ruwan dare ya game kowane shiyyya.

Za a ga cikin wannan ɗangon aka cika ma’anar ɗango na ɗaya. Haka nan, a baiti na 38 an ƙara samun iirn wannan gangara, inda yake cewa:

Mulki idan dai da zalunci yake tafiya.

A wannan ɗango, ya fara bayanin halin da mulki da zalunci yake kasancewa, amma bai cika ma’anarsa ba sai a ɗango na biyu, inda yake cewa:

Allahu ba ya bari nasa kun ga kau aya.

Ma’ana, idan ana mulki na zalunci, Allah ba ya barin sa. Ashe kenan, a ɗango na ɗaya ya fara furta ma’anar sannan sai ya ƙarasa iyar da ma’anar a ɗango biyu.

An samu gangara da yawa a cikin wannan waƙa kamar a baiti na 10, 13, 16, 17, 38, 40, 60 da kuma 61.

3.2.1.2 Saɓi-Zarce

A cikin wannan waƙa, a wuri ɗaya ne kawai aka samu saɓi-zarce. Wato tsakanin baiti na 15 zuwa na 16. Marubucin ya fara saƙa wata ma’ana a cikin baiti na goma sha biyar (15) amma bai ƙarasa ba sai a cikin baiti na goma sha shida (16). Ga waɗannan baitoci a nan ƙasa:

Kuma ga shi mu da maƙota ‘yan’uwan juna,

A Bukasi an jibge sojoji ana niyya.

(Baiti na 15).

Sai an zubar da jinin juna sabo da zato,

Wai yankunan na da ɗimbin mai da za a siya.

(Baiti na 15).

Idan aka kalli waɗannan baitoci za a ga cewa, mawallafin ya fara shirya wata ma’ana ce a cikin baiti na goma sha biyar (15), wato bayani a kan faɗan yankina Bakasi da ake ƙoƙarin yi a tsakanin ƙasar Nijeriya da kuma Kamaru. Amma bai cika ma’anar da ya faro ba sai da ya tsallaka izuwa baiti na goma sha shida (16).

4.1 Salo da Sarrafa Harshe a Waƙar Hattara ‘yan Siyasa

4.1.1 Salo

Salo zaɓi ne ko wani ‘yanci da marubuci yake da shi wajen yin amfani da wasu ayyanannun dabaru ko hanyoyin domin sarrafa kalmomi da jumlolin da ya yi amfani da su wajen shirya waƙarsa. Ɗangambo (2007) ya bayyana salo da cewa, “ salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi, yanayi, hanya ko tunani a maimakon wani”.

Akwai ire-iren salo wanda ya haɗa da miƙaƙƙen salo da lamin salo da salo mai kashe jiki da salo mai karsashi da tsohon salo da sauransu.

Wannan waƙa marubucinta ya yi amfani da miƙaƙƙen salo wajen isar da saƙon da waƙar take ƙunshe da shi. Wato ya yi amfani da yanayin saƙa jumlolin waƙar cikin yanayi mai sauƙi ta yadda duk wanda ya karanta zai gane abin da ake nufi. Ga wani misalin baiti a ƙasa:

Rikicin tsakanin manoma su da mai kiwo,

Ɓarna suke yin ma juna ba batun diyya.

Idan aka karanta wannan baiti, za a ga yana da sauƙin ganewa a kan abin da yake magana, wato yanayin yadda ake samun rigingimu tsakanin manoma da makiyaya, har ta kai da ana salwantar da rayuka. To, dukkanin ragowar baitocin waƙar a haka ya tsara su cikin wannan salo mai sauƙi kuma miƙaƙƙe.

3.1.1.1 Dabarun Jawo Hankali

Dabarun jawo hankali wani salo da marubuta suke amfani da shi wajen kwatanta abubuwa biyu ko sama da haka ta fuskar yanayi ko kuma tasiri. Akwai dabarun jawo hankali na kamantawa na daidaito da fififko da gazawa da sauransu.

Marubucin wannan waƙa ya yi amfani da dabarun jawo hankali na kamantawa ta daidaito a cikin baiti na 39 da kuma 46. Ga yadda baitocin suke a ƙasa:

Mun sha wuya mun farace lokacin soja,

Allah ya sa kar a maimaito irin na jiya.

(Baiti na 39).

Idan aka dubi ɗango na biyu na wannan baiti, kalma ta biyun ƙarshe, ya yi amfani da dabarar jawo hankali ta kwatanci na daidaito. Wato ya yi ƙoƙarin kwatanta mulkin soja wanda ya wuce da kuma mulkin soja wanda bai zo ba. Wato ya nuna cewa kenan, tasirinsu iri ɗaya ne babu wani sauyi duk da cewa ba lokaci guda aka yi su ba, kuma ba mutum guda ne ya yi ba.

Haka nan a cikin baiti na 46 an sami irin wannan dabara ta kwatantawa. Ga shi misalin baitin a ƙasa:

Dun ta riga ta zame mana ma kamar Sunna,

Koko a ce (Wajiba), sata a kai ajiya.

(Baiti na 46).

A wannan baiti ma, an sami wannan dabara ta kamantawa. Wato an kwatanta abubuwa guda biyu. Mawallafin ya yi ƙoƙarin kamanta yanayin muhimmancin sata da sunna ko wajibi a wajen ‘yan siyasa. Wato ya nuna yadda sunna ko wajibi yake a wajen Musulmi, haka sata da zambo suka zama a wajen ‘yan siyasa. Dukkanin yadda ka amincewa ɗan siyasa, sai ya yi sata matuƙar ya hau kan kujerar mulki.

3.1.1.2 Siffantawa

A cikin baiti na 20 an samu doguwar siffantawa wadda marubucin ya yi amfani da ita wajen siffanta wani nau’in kuɗi na da kai tsaye. Ga abin da yake cewa:

Ga kasuwar cunku ya kasha kasuwar Naira,

Darajar sule goma yau, shi ne kwabo a jiya.

(Baiti na 20).

A nan, marubucin ya siffanta sule goma da kwabo ɗaya ta hanyar ɗaukar darajar kwabo ɗayan kuma ya ɗora ta a kan sule goma. Wato ya siffanta kwabo ɗaya kai tsaye da sule goma domin nunawa al’umma irin yadda mulkin soja ya lalata kuɗin Nijeriya ta hanyar karya darajarsa.

3.1.1.3 Samarwa da Korewa (I, A’a)

Wannan ita ma dabara ce ta jan hankali wadda mawallafi kan yi amfani da ita don samun yarda daga makaranci ko mai sauraro (Ɗangambo 2007, sh.53). Wato ya yi amfani da kore wani abu kuma ya tabbatar da wani domin janyo hankalin mai sauraro ko karatu ya fahimci saƙon da yake so ya isar cikin sauƙi.

Samarwa da korewa su ne iyaye a cikin wannan dabara ta jan hankali, amma sun haifar da ‘ya’ya da jikoki kamar yadda za a kawo ƙasa.

Samarwa + Samarwa

Sun ɓata tsari na kirki wanda sunka taras. (bait na 3, ɗango na 1)

Ga jahilan nan matasa masu yin Shi’a. (baiti na 12, ɗango na 1)

Korewa + Korewa

Kowa ya kama gabansa a daina Tarayya. (baiti na 28, ɗango na 2)

Ƙaryar tsiya, mara sa tausai da imani. (baiti na 49, ɗango na 1)

Samarwa +Korewa

Taki akwai shi, idan kasaye shi ba riba. (baiti na 23, ɗango na 1).

Ga kasuwar cunku ya kasha kasuwar Naira. (baiti na 20, ɗango na 1).

Korewa

Allahu ba ya bari nasa kun ga kau aya. (baiti na 38, ɗango na 2).

Dun kar ku ce muguwar fata nake niyya. (baiti na 42, ɗango na 2).

Samarwa

In mai makami a hannu da kansa ya koka. (baiti na 7, ɗango na 21).

Ya zam annoba a wannan nahiya ku jiya. (baiti na 21, ɗango na 2).

4.2 Sarrafa Harshe

Sarrafa harshe na nufin yanayin yadda marubuci ya yi amfani da wata dabara wajen zaɓen kalmomi da jumlolin da ya yi amfani da su wajen rubuta waƙarsa ta hanyoyi daban-daban. Lamiɗo da Bara’atu, Maikadara (2024) sun bayyana sarrafa harshe da cewa, “ wannan ya shafi gwanintar harshe a waƙa, ta yadda za a yi amfani da wasu dabaru a sarrafa shi ko a aiwatar da shi cikin hikima domin burge masu sauraro (ko karatu)”.

Daga cikin abubuwan da ake dubawa a nazarin sarrafa harshe akwai kalmomin aro da tsofaffin kalmomi da masu zurfin ma’ana da kalmomin fannu da karin harshe da zaɓaɓɓen kalmomi na rukunin nahawu da sauransu.

4.2.1 Kalmomin Aro

Kalmomin aro ko baƙin kalmomi su ne kalmomin da makaɗi ya ara daga wasu harsuna ko wani harshe guda ya tsattsarma a cikin wadiyan waƙarsa domin ya burge masu sauraro (Lamiɗo da Bara’atu, Maikadara 2024, sh.211).

A wannan waƙa, an yi aron kalmomi daga harsuna daban-daban, amma manya daga cikinsu su ne Larabci da Turanci. Daga cikin kalmomin Larabcin da aka yi amfani da su akwai; mulki, jahilai, shi’a, diyya, kunya, kasuwa, daraja, sharri, nahiya, haƙƙi, ilimi, Alƙawar, kullun, hujja, hisabi,galabaita, zalunci, aya, Allahu, Sa’ili, hali, sunna, wajib, imani, rahama, nasiha da kuma zayyana. Haka kuma, akwai kalmomin Turanci waɗanda aka yi amfani da su a wannan waƙar kamar irin su ; kananzir, soja, naira,bariki da sauransu.

4.2.2 Tsofaffin Kalmomi

Tsofaffin kalmomin su ne kalmomin da ake amfani da su a da, wanda kuma aka sauya su da wasu kalmomin daban sakamakon sauyawar zamani. Daga cikin tsofaffin kalmomi da aka yi amfani da su a wannan waƙar akwai; dauri, fatauci, cunku, sule, kwabo, farace da kuma tafarki.

4.2.3 Kalmomin Fannu

A kowane fanni ko jigo za a iya samun kalmomin da amfani da su ya keɓanta ga wannan fannin (Ɗangambo 2007, sh.50). Ma’ana, kowane jigo mutum ya ɗauka ya gina waƙarsa a kansa, akwai kalmomin da suka dace da wannan jigo, kuma ana sa ran a ga sun bayyana a cikin wannan waƙa. alal misali, jigon addini, ana sa ran a ga kalmomi irin nasu Allahu da wa’azi da nasiha da sauransu.

Wannnan waƙa. waƙa ce wadda take da jigo wanda ya shafi siyasa kai tsaye. Saboda haka an yi amfani da kalmomi waɗanda suka dace da wannan jigo. Daga cikin kalmomi akwai; mulki, tsari. Farin-kaya, rikici, kotu, man fetur, cin-hanci, takarda, ƙarya, bashi, Nijeriya, ƙasa, jari-hujja, zalunci, kuɗi, buƙata da kuma Taryya.

4.2.4 Sauya Sifar Kalma

Sauya sifar kalma shi ne ragi da mawaƙa kan yi a farki kalma ko tsakiyarta ko kuma ƙarshenta domin taƙaitawa ko daidaita karin waƙarsu. Ɗangambo (2007) yana cewa “ mawaƙa sukan yi amfani da ‘yancin waƙa ko lalurar waƙa su sarrafa kalma da sake wa kalmomin siffa da sauransu”. Akwai wurare a cikin wannan waƙa inda aka sauya ƙirar kalma. Ga wasu misalai a ƙasa:

Giɓin Kalma

Cikakkiyar Kalma

Baiti Ɗango

Ɗau

Ɗauki

1 2

Bar

Bari

5 1

Zam

Zamo/zama

10 2

Kau

Ko

38 2

 

Idan aka dubi waɗannan kalmomi za a ga mawallafin ya taƙaita su yayin furta su domin daidaita karin waƙarsa ko kuma wata lalurar waƙa.


4.2.5 Amfani da Jumla a Wa
ƙar Hattara 'Yan Siyasa

Jumla na nufin jerin wasu kalmomi masu ma’ana wuri guda bisa wani ƙayyadajen tsari da harshe ya tanadar. Wannan waƙa gaba ɗayanta an gina gangar jinita da dogoyen jumloli. Alal misali:

Dama ku daina rawan kai za ku hau mulki.

(Baiti na 1).

Kuma ga shi mu da maƙota ‘yan’uwan juna.

(Baiti na 15)

Ga masu yaji na aiki dun biɗar ƙari.

(Baiti na 30).

In kun ci sa a ku kai aiki na san barka.

(Baiti na 35).

Allah ka yafe dukan laifinsu kai rahama.

(Baiti na 8).

Idan aka dubi waɗannan ɗangwayen baitoci, an zaɓo su daga farko da tsakiya da kuma ƙarshen waƙar. Saboda haka, za a ga dukkaninsu dogaye. Wato dai ba a yi amfani da gajeru da matsakaitan jumloli ba a cikin waƙar.

4.2.6 Giɓin Jumla a Waƙar Hattara ‘Yan Siyasa

Ɗangambo (2007) yana cewa “ sau da yawa za a ga akwai wurare a cikin waƙa inda za mu iya cewa an bar giɓi wanda ake fatan mai karatu ko mai sauraro ya cike da fahimtarsa. Wannan giɓi yakan shafi tsarin jimla”.

An samu wurare da dama a cikin wannan waƙa inda aka samu giɓin jumla, wanda mai karatu da kansa zai ƙarasa ko ya ƙaddara abin da ake nufi a wurin domin samun tabbatacciya kuma ingantacciyar ma’ana. Ga misalan wasu jumloli waɗanda aka samu giɓi a cikinsu:

Domin ku sake shiri, kar ku zaman ƙarya.

(Baiti na 8, ɗango na 2).

Idan aka dubi wannan jumla, za a ga an samu giɓi musamman a gurbin aiki na ‘yi’. Wato jumla ya kamata ta kasance kamar haka; domin ku sake shiri kar ku yi zaman ƙarya.

In an yi yau kotu ce ke tabbatar da shiya.

(Baiti na 18, ɗango na 2).

Idan aka dubi wannan ɗango, za a ga akwai giɓi a cikinta musamman idan aka yi la’akari da ita ta fuskar cikar ma’ana. Jumlar ya kamata ta kasance kamar haka; in an yi tsarin sarautu, amma a yau kotu ce ke tabbatar da shiya.

Bayar da hanci da goro wajen biɗar haƙƙi

(Baiti na 25, ɗango na 1).

Haka nan, wannan ɗango ma an samu giɓin ma’ana ta fuskar gundarin aiki mai madanganci da kuma gurbin doguwar nasaba. Ma’ana, an cire wata kalma a cikin ɗango domin daidaita kari, kuma aka barwa mai karatu ya ƙarasa da kansa. Ɗangon ya kamata ya kasance kamar haka; Bayar da cin hanci da na goro wajen biɗar haƙƙi

Gidan mu na kan tudu su sun yi nasu kwari.

(Baiti na 50, ɗango na 1).

A wannan ɗango dake sama, an samu giɓin kalma na bayanau. Wato ya kamata ɗangon ya kasance kamar haka; Gidanmu na kan tudu su sun yi nasu a cikin kwari.

Allah mun ɗaga hannayenmu dube mu.

(Baiti na 56, ɗango na 1)

Haka shi ma wannan ɗango, an samu giɓi a cikinsa ta fuskar wakilin suna. Ga dai yadda ya kamata ɗangon ya kasance; Allah mun ɗaga hannayenmu ka dube mu.

3.1.2.7 Karin Harshen Waƙar Hattara ‘Yan Siyasa

Karin harshen a nufin wasu ‘yan sauye-sauye da ake samu a tsakanin al’umma ɗaya masu amfani da harshe ɗaya ta fuskar tsarin sauti da kalma da kuma tsarin ginin jumla. A cikin wannan waƙa an yi amfani da wasu kare-karen harshen Hausa. Ga wasu misalai a cikin jadawali:

Kananci

Daidaitacciyar Hausa

Zazzaganci

Daidaitacciyar Hausa

Sakkwatanci

Daidaitacciyar Hausa

In

Idan

Dun

Don

Tausai

 

Mai i

Mayar

Shashi

Sashe

Biɗa

 

Me

Menene

 

 

Tai

 

Ba

Babu

 

 

Daɗa

 

Sukai

Suka yi

 

 

Ishe

Tarar

Yai

Ya yi

 

 

 

 

Kullun

Kullum

 

 

 

 

 

4.1 Kammalawa

Waƙoƙin Hausa, musamman rubutattu, suna ƙunshe da wasu saƙonni na musamman. Wannan ya sa waƙa ta zama wata hanya ta musamman wajen koyar da al'umma wasu keɓaɓɓun ilimai a rayuwar yau da kullum da faɗakar da su a kan wasu muhimman abubuwa ta fuskar nusantarwa da jan-hankali da gargaɗi da kuma kwaɗaitarwa.

A wannan waƙa, an faɗakar da al'umma a kan illar da mulkin sojoji yake da shi, musamman idan aka yi la'akari da yadda suka yi mulki a Nijeriya, kuma suka taɓarɓara tsarin ƙasar daga mai kyau zuwa mummunan yanayi. Haka kuam, waƙar ta yi kira ga 'yan siyasa da kuma sauran 'yan ƙasa a kan kar su yadda su bari soja ya ƙara dawowa ya mulki Nijeriya. Wannan ya sa ya mawallafin ya bayyana irin ɓarnar da sojoji suka yi iri daban-daban yayin da suke mulki.

Wannan takarda ta yi nazarin wannan waƙa mai baitoci sittin da ɗaya (61) ta fuskar jigo da zubi da tsari da kuma salo. Wato, an yi nazarin gundarin jigon waƙar, wato jigon faɗakarwa da taƙaita jigo da kuma warwarar jigo. Haka kuma, an fitar da zubi da tsarin waƙar ta duban yanayin yadda mawallafin ya tsara carbin tunaninsa wajen sassaƙa saƙonnin da waƙar take ƙunshe da su. Sannan aka fito da muhallan da aka samu gangara da saɓi-zarce a cikin waƙar. Haka kuma, an bayyana salon waƙar gaba ɗaya da cewa salo ne miƙaƙƙe kuma mai armashi ta yanayin yadda aka yi amfani da dabarun jawo hankali na kamantawa da siffantawa da samarwa da korewa da zaɓen kalmomi na aro da tsofaffi da na fannu da sauransu.

Takardar ta gane cewa, mulkin Soja shi ne ya fara ɓara duk wani kyakkyawan tsarin da ƙasa Nijeriya take da shi tun bayan da ta samu 'yancin-kai. Haka kuma, ya taɓarɓara tattalin arziƙin ƙasar tun daga wancan lokaci har zuwa yau. Haka kuma, an fahimce cewa, mawallafin ba ya amfani da dabarun jawo hankali na jinsintarwa a cikin waƙarsa, wannan ya sa waƙar ba ta ɗauke da zambo ko habaici kai tsaye.

Manazarta

Auta, L.A. (2017). Faɗakarwa a Rubutattun Waƙoƙin Hausa. BUK Press.

Bugaje, M.H. (2011). Wa’azi a Rubutattun Waƙoƙin Mata na Ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri na

Ɗaya. Zariya: Sashen Koyar da Harsunan Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano. Jami’ar Bayero ta Kano.

Chamo, I.Y (2011). “Jigo a Fina-Finan Hausa”. A cikin Algaita Journal of Humanities

Sashen Koyar da Harunan Nijeriya da Kimiyar Harshe, Jami’ar Bayero, Kano Vol.12. No.1 (sh. 66).

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kano: Kdg Publishers.

Ɗangamob, H.A. (2012. “Salon Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa”. kundin Digiri na uku

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S.M (2014). Mu Koyi Ibada. Kano: Century Res/earch and Publishing Limited.

Lamiɗo, I., da Maikadara, B.I (2024). “Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru:

Nazari a Waƙar Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda”. Takarda Wadda aka Gabatar a Cikin Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings From the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa’idu Faru. Sashen Koyar da Harshe da Al’adu, Jami’ar Gwamnatin Tarayya, Gusau.

Labaran, M.M. (2024). Waƙa Maƙunsar Ilimi: Nazarin Jigon Koyar da Ibada a Wasu Waƙoƙin

Malam Nasiru Kabara. Takarda Wadda aka Gabatar a kan Rayuwa da Gudummawar Malam Nasiru Kabara. Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano.

Ilyas, A.H. (2023). Sheikh Ahmad Maƙari Sa’idu Zariya: An Icon of Education and Social Transformation. Tanmiya Education Foundation.

Sani, M.A.A. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. Ibadan Uniɓersity Press.

Siyasa

Post a Comment

0 Comments