Ticker

6/recent/ticker-posts

Tun Lokacin Da Aka Yi Mana Baiko Da Saurayina Harkokin Kasuwancin Sa Suke Jan Baya Sai Yake Gani Kamar Daga Ni Ce

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam, ina nema shawara, ina da saurayi har anyi baiko tsakanin mu, to tin lokacin da aka yi muna baiko kullum kasuwanci shi naci baya, abubuwan na tabarbarewa, kuma muna garin da ada kananan maganganu, duk abinda yaci baya da wanda zaka aura sai ace daga kaine, afara magana akanka, kuma kullum cikin gayamin halin da ya ke ciki yake, da bahaka yake ba, amma yanzu abubuwa dik canza masa, sai naga kamar yana fada minne abin daga nice, wlh malan duk randa ya fadamin bana iya kwana, Allah nike ina roka mishi Allah, amma yanzu abin ya fara damuna saboda kullum kara fadamin sabbin abubuwa naci baya da yasamu, har nafara tinanin rabuwa da shi, dan Allah ya zanyi, Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:

Toh shakka babu indai bai ji tsoron Allah ya Dena ba sa'annan ya tuba ya cire komai a zuciyar sa ba, toh kiyi gaggawar rabuwa da shi domin za ki zauna da Miji Wadda yake yin Shirka zuwa ga Allah ne wannan.

Dãman su nau'ukan yin Shirka zuwa ga Allah kala-Kala ne, Manyan Shirka zuwa ga Allah shi ne mutum ya haɗa bautar sa da Allahu Subhanahu Wa Ta'ala shi ba zai taɓa yin ibada ma Allah shi kaɗai ba sai ya haɗa shi da wani abun daban, ko kuma mutum ya bautawa wani gumki ko Ɗan Adam ko ma bayan Allahu Subhanahu Wa Ta'ala. Duk waɗannan Shirka ce.

Ko Kuma mutum yayi tsammanin wani cutarwa daga wani ɗan Adam ko Jinnu ko ma bayan Allah, ko samun sa ne harkan Kasuwancin sa ya ce ai ko rashin samun sa ya ce ai daga wani Ɗan Adam ne ko ma bayan Ubangijin sa, toh waɗannan dukkan su duk Musulmin da ya sanya su a cikin zuciyar sa yake kwana da su yake ta shi da su, toh ya tabbatar cewa lallai ne yana yin Shirka zuwa ga Allahu Subhanahu Wa Ta'ala.

Domin babu wani wadda ya isa ya cutar da wani, babu wani wadda ya isa ya wadatar da wani ko ya amfanar da wani sai Allah kaɗai, toh daga lokacin da Ɗan Adam ya fara tunanin cewa a'a ai dalilin na kasance da wane, shiyasa hanyoyin sa suke Kara bumkasa, ko kuma dalilin ya kasancewa da wata ko wane shiyasa hanyoyin samun sa suka fara yin baya, toh shakka babu ya ɗauki hanyar yin Shirka zuwa ga Allah, da duk Waɗanda suke tunanin cewa ai dalilin rashin samun sa ai sabida ya kai baikon sa ne zuwa ga wacce, ga shi tun bai Aure ta ba kasuwancin sa ya fara yin baya dãman dangin su haka suke, su ce, Ina ga Kuma ya Aure ta ai zata talautar da shi domin ita ɗin mai Bakar Kafa ce, toh duk wadda zai yi irin wannan tunanin har ya furta shi, toh Shi ma yayi Shirka zuwa ga Allah, da shi wadda abun yake faru da shi.

Kai a naka tunanin Allah bai isa ya jarraba samun ka ko abun da ka mallaka ba, a'a ai wane ne ya min ko Kuma a'a dalilin na Kai Baikon ta ne shiyasa ai Mai Bakar Kafa ce wannan Yarinyar, toh wannan Shirka ce.

Allahu Subhanahu Wa Ta'ala yana cewa;

الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَٰئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ

"Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãnin su da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu."

Allahu Subhanahu Wa Ta'ala ya ce waɗannan mutanen zai Amintar da su daga Azabar cikin qabari, zai Amintar da su zuwa ga yi musu Hisabi me Sauki, dalilin shi ne ba su yin irin wannan tunanin irin na saurayin ki, shin tunanin sa me yake jawowa ko yake nunawa a kanki? Shi ne Shirka zuwa ga Allah.

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya ce duk wadda ya mutu Yana Shirka zuwa ga Allah toh ba zai shiga Aljannah ba, shin ke kin yarda ki Auri Namiji me irin wannan tunanin tun a waje? Sa'annan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya ce duk wadda ya mutu bai taɓa yin Shirka zuwa ga Allah ba, toh Lallai Aljannah ta tabbata gare shi (Bukhary), kenan indai Miji Nagari kike so shin wannan da yake da irin waɗannan tunanin ya dace da Miji Nagari ne ya dace ki Aure shi?

Allahu Subhanahu Wa Ta'ala yana cewa duk wadda ya mutu yana yin Shirka bai tuba ya nema Gafarar Allah ba, toh makomar sa Wuta ce sa'annan zai dawwama a cikin sa. Shirka yana da hatsari sosai kuma a yanzu mafi Yawancin Al'umma suna aikata shi ba tare da ma sun San cewa Shirka bane, ko kuma sun sani amma sai a take sanin a juya abun ta wani hanyar daban zuwa ga yin Shirka ga Allah, kamar yadda a yanzu shi Saurayin ki yake gaya miki, ya fito Fili ne ya ce miki ga shi tun da ya kawo Baikon ki kasuwancin sa komai nashi yake yin baya a dalilin ki, yana gudun ya furta miki hakan ne domin kada ki ce ya zage ki, amma shi ko a yanzu idan kin ce za ki rabu da shi sabida irin abubuwan da ya ga suke faruwa da shi, toh da gudu zai yarda ku rubu, kai ko ba ki Faɗa cewa ku rabu ba, toh a aje aje idan Bakin Jama'a suka yi masa Yawa, shi ma tunanin sa ya Kara tafiya gaba akan haka ɗin ne, toh abun da zai ce miki kenan zai ce kawai ai ya ga tunda ya kawo baikon ki yake Haɗuwa da masifu daban daban da kuma kariyar kasuwancin sa, sabida haka shi ba zai iya Aure ki ba, domin idan ya Aure ki abun zai fi haka. A karshe shi zai ce ku rabu kin ga kenan wannan ya fada cikin Shirka ga Allah ɗin gadan-Gadan wallahi.

Akwai masu yin Shirka zuwa ga Allah a gurin yin ibadar su don neman abun duniya, sai Allahu Subhanahu Wa Ta'ala yake cewa;

مَنْ كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لَا يُبْخَسُونَ

Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawar ta, Munã cika musu ayyukan su zuwa gare su a cikin ta, kuma a cikin ta bã zã a rage su ba.

Wato duk abun da mutum yake so na rayuwar domin yana yin sa domin Jama'a don ya samu abun duniya toh zai same shi komai Allah ya ce zai cika masa shi bai rage masa komai daga cikin sa ba, amma kuma fa bai rabo a Ranar Alqimaya.

Har yanzu Allah ya sake cewa;

أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الْآخِرَةِ إِلَّا النَّارُ ۖ وَحَبِطَ مَا صَنَعُوا فِيهَا وَبَاطِلٌ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ

Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã´an ta a cikin ta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne.

Kin gani duk abun da mutum yake so zai samu kuma Allah zai cika masa ayyukan sa ma'ana yana neman duniya ne, shi kuɗi yake so rayuwar sa da duniyar sa, shiyasa yake yin irin waɗannan ayyukan, toh Allah ya ce zai ba shi Ladan sa gaba ɗayan sa tun anan duniya ba zai rage masa komai ba sai ya gama cinye su gaba ɗayan sa, amma kuma makomar sa Wuta ce, sa'annan duk wasu ayyukan sa kamar su Azumi ne, Zakkah, aikin Hajji da sauran su, duk sun Lalace bai da wani aikin Lada wadda zai sa Allah yayi masa Rahma zuwa Aljannah, Domin ya gama cinye komai nashi tun anan duniya Wuta ce Kaɗai makomar sa.

Sa'annan akwai wani Shirkan da Jama'a suke aikatawa ba su ma San cewa Shirka bane, shi ne Shirka na So wato Shirka ta soyayya. Kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana ɗayan ku bai shiga Aljannah ba, Sai ya so ni wato kin so Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam fiye da yadda yake son kanki, fiye da yadda yake son iyayen sa fiye da yadda yake son Yaran sa, fiye da yadda yake son Matar sa fiye da yadda kike son Mijin ki ko Saurayin ki, fiye da yadda yake son komai na duniya.

Amma kina iya samun wasu Mazãjen sabida son Matar sa da yake yi, ko tana cikin jinin haila babu Ruwan sa, sabida yayi mata abun da take so haka zai yarda yayi Jima'i da ita Alhalin tana cikin jinin hailar fa, kin ga anan me? Ga dokar Allah nan an take shi yanzu sabida irin yadda yake son Matar sa akan ya ce mata ta yi hakuri Haramun ne, a'a ba zai fada mata ba gara yayi Jima'in da ita sabida Hankalin ta ya kwanta shikenan.

Wani Kuma za ki ga an yi saki Ukku Allah ya Sanya musu soyayya sosai a tsakanin su kin ga babu Aure a tsakanin su sai ta Auri wani Sahihin Aure, amma haka za suyi ta yin Karya har su komar da Auren su an ba su Fatawar karya, ko kuma kullum su je suna ta yin Zina babu wadda ya sani sun manta cewa Allah na ganin su, kin ga yanzu ga dokar Allah nan sun take shi dalilin soyayyar da suke yiwa Junan su, hakan ya hana su bin dokar Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, a nasu tunanin babu wadda ya sani amma sun manta cewa Allah ya sani, kin ga wannan ma Shirka ce Kuma Jama'a dayawa suna aikata shi sosai.

Haka Matar Aure ce za ki ga Mijin ta Mazinaci ne babu wadda bai sani ba Kuma ya qi ya tuba ya Dena, ga abun da Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suka ce Mazinaci sai Yar uwar sa Mazinaciya a gurin yin Aure, ga shi Mijin ya qi ya tuba ya dena yin Zinar, sai ki ji Mace ta ce ai zata zauna da shi don Yaran ta, ko Kuma iyayen ta su ce, toh Ina ruwan ki da Zinar sa laifin ai nashi ne bawai naki ba, ko kuma Ina ruwan ki Zinar sa zai shafe ki ne ko Yaran ku? Ki bar sa mana ai qabarin kowa da nashi. Kin ga yanzu kokarin su shi ne kada ta rabu da shi ta ci gaba da Zama da shi a hakan, ga shi kuma sai Saɓawa Allah yake yi na yin Zina ko aikata wani abun Haramun, tana son shi a hakan zata zauna da shi, ba za ta iya rabuwa da shi ba dalilin uban Yaran ta ne kuma tana son sa ita, yanzu kin ga anan tana son zama da shi ne domin tana son sa ne, ita babu Ruwan ta kawai ya ci gaba da yin Zinar sa ko Saɓawa Allah daidai ne akan ta rabu da shi, tafi yarda ta ci gaba da zama da shi a hakan yana Saɓawa akan ta rabu da shi, kin ga su a nasu tunanin gara a take dokar Allah tunda Zunubin ba a kanta zai sauka ba tunda akan sa ne, toh babu komai ta zauna da shi don tana son sa, ga dokar Allah nan cewa Mazinaci sai Mazinaciya Yar uwar sa, ga shi ya qi ya tuba ya Dena, kika ce a'a Uban Yaran ki ne kina son sa wallahi za ki zauna da shi a hakan, toh wannan ma Shirka ce. Kuma ke kin manta cewa Ciwo zai kama ki ne? Kwanan Hakan ya faru Mijin Mazinaci ne ta qi ta rabu da shi karshe ta sama masa HIV ga shi ya mutu, ya bar ta da Ciwo sai mu ga ta tsiya kuma, ko dai za ki bi shi da Yaran zuwa cikin qabarin sa ne tunda Uban Yaran ki ne kuma kina son sa? Indai kina son sa sai ki bi wallahi da Yaran dukka Nan ne za a gane kina son sa sosai.

Haka kuma za ki ga Uba yana ganin Yar sa tana Saɓawa Allah, tana yin duk abun da take so a rayuwar ta wadda ba daidai bane, amma sabida baya son fushin Yar sa yana son ta sosai, kada ya ce ta Dena ta shiga cikin tashin hankali da damuwa yana son ta sosai, baya Jin maganar kowa indai a kanta ne, domin irin yadda yake son Yar sa, ko Kuma mu ce Matar sa shiyasa akan ya hana ta Saɓawa Allah gara kawai ya bar ta ta ci gaba yin komai, domin kada ya bakan ta mata Rai, sai ya ce ai idan lokacin shiryuwan ta yayi ai zata Dena, toh wannan ma Shirka ce ma Allahu Subhanahu Wa Ta'ala, shi ne Shirkan soyayya.

Wallahi akwai wadda irin yadda yake son Yan kwallon Kafa, Arna Makiya Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Makiya Addinin sa, ko Yan Films wato Fina-Finan Hausa ko Nigerian Films, toh akan ki zage su gara kin Zagi iyayen sa, za ki Zagi iyayen su ba za su ce komai ba, za ki yi Ɓatanci ga Addinin Musulunci ko a jikin su, amma da kin Zagi waɗannan mutanen ko kin yi ɓatanci a kansu, sai Hankalin sa ya tashi, kai wani ma har fada sai Kun yi da shi, dalilin kawai kin Zagi Yan kwallon Kafa ko Yan Films, Hankalin sa na tashi idan an taɓo su, toh wannan ma Shirka ce ga Allah ta soyayya. Toh waɗannan abubuwan sun yiwa a cikin zuciyar Jama'a wadda ba su ɗauke shi bakin komai ba, alhalin Shirka ce zuwa ga Allah, shiyasa Allahu Subhanahu Wa Ta'ala yana cewa;

وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَتَّخِذُ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْدَادًا يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ اللَّهِ ۖ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَشَدُّ حُبًّا لِلَّهِ ۗ وَلَوْ يَرَى الَّذِينَ ظَلَمُوا إِذْ يَرَوْنَ الْعَذَابَ أَنَّ الْقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا وَأَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعَذَابِ

Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so ga Allah. Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cewa lalle ne Allah Mai tsananin azãba ne.

Sa'annan yana da cikin Shirka zuwa ga Allah shi ne rashin ɗaukar abun da Allah ya hukuntawa wannan Bawan nashi, Abu zai Sami mutum sai Rika Jin haushin kansa, ina ma da yayi kaza ai da Abu kaza Bai same shi ba, ko kuma irin yadda a yanzu shi Saurayin ki ya kawo Baikon ki, shikenan kasuwancin sa suke yin sa Allah ya jarrabe shi yana yin baya a yanzu, sai ya Koma zargi da tunanin cewa ai dalilin neman ki da yake yi, dalilin zai Aure ki dalilin ya kawo Baikon ki shiyasa komai nashi yake komawa baya, yanzu ke kanki ya fara Jin haushin neman Auren ki da yake yi, domin a nasu tunanin da shi Saurayin naki kene silar Lalacewar komai nashi, sa'annan yana Jin haushin Ubangijin sa, ai meyasa kasuwancin sa yake yin baya me yayiwa Allah? zai Rika yin irin waɗannan tunanin, jama'a ko Yan Uwan sa, su Rika cewa ai ga dalilin nan domin za ka auro wannan me Bakar Kafar ce, toh gara ka rabu da ita tun yanzu in ba haka ba zata talauta ka, ai wane ma haka da Auri wacce, shi ma da me Arziki ne Amma yanzu Bai da komai, a yi ta zuga shi, duk waɗannan abubuwan Shirka ce zuwa ga Allah ga duk masu tuna irin wannan.

Ko Kuma mutum ya fara tunanin ai dalilin wannan abun da ya same shi, ai wani ne ya min ko su wane ne suka min wannan abun, an San cewa akwai Sihiri kuma Sihiri gaskiya ne, toh amma shi Musulmi ba zai taɓa tuna cewa ai su wane ne suka min ba wai har ma ya Koma yin gaba da su, har ma ya Koma bin Malamai ko Bokaye wai shi ma zai kare kansa, duk Shirka ce wannan.

Sabida haka wannan saurayin naki bai siffantu da mijin da Mace ta Aure shi ba ta ji daɗi ko ta zauna lafiya da shi ba, duk Namijin da tun a waje ba a ma Yi Auren ba, amma tun yanzu ga irin abubuwan da yake ta cewa a kanki, toh Ina ga kuma ya Aure ki yana da iko akan ki? Kin ga kenan Zagi da tozarci da cin Mutunci har da iyayen ki, duk ba su tsira ba idan ya tashi yin Zagin sa da tsinuwar sa, Kuma ba za ki taɓa samun jin daɗi ko kwanciyar hankali ba, sa'annan kullum kin Rika shan Zagi da tsinuwa kenan, domin da kin yi magana bani Abu kaza ko Siya min Abu kaza, toh zai zage ki ya ce ai kene silan Lalacewar Arzikin sa ko kasuwancin sa.

Don haka ki zauna kiyi tunani me kyau ga wadda za ki Aura ki sanarwa iyayen ki idan kin Yanke Hukunci, Amma dai wannan saurayin naki matukar bai ji tsoron Allah yayi gaggawar tuba ya cire wannan mummunar tunanin a Zuciyar sa ba, toh lallai ne ya kama Hanyar da babu kyau, kawai shawarar da zan ba ki Ki rabu da shi. Allah ya shirya ya tsare. Dafatan Kin gane ko???????

WALLAHU A'ALAMU

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments