𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Hadisin da ya ce:
حَقٌّ لِلَّهِ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ أَنْ يَغْتَسِلَ فِي كُلِّ
سَبْعَةِ أَيَّامٍ، يَغْسِلُ رَأْسَهُ وَجَسَدَهُ
Haƙƙi ne na Allaah a kan kowane musulmi ya yi wanka a cikin kowaɗanne kwananki bakwai, ya wanke kansa da jikinsa. Menene
sahihancin wannan Hadisin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Al-Imaam Muslim ya riwaito shi (lamba: 849) daga
malaminsa Muhammad Bn Haatim, ya ce: Bahzu ya ba mu hadisi, ya ce: Wuhaib ya ba
mu hadisi, ya ce: Abdullah Bn Taawus ya ba mu hadisi, daga babansa, shi kuma
daga Abu-Hurairah, daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« حَقٌّ لِلَّهِ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ أَنْ يَغْتَسِلَ فِي كُلِّ
سَبْعَةِ أَيَّامٍ، يَغْسِلُ رَأْسَهُ وَجَسَدَهُ »
Haƙƙi ne na Allaah a kan kowane musulmi ya yi wanka a cikin kowaɗanne kwananki bakwai, ya wanke kansa da jikinsa.
Kasantuwan wannan hadisi yana cikin Sahih Muslim
ya isa ya tabbatar da sahihancinsa. Sannan kuma ga shi ma Al-Imaam Al-Bukhaariy
ya riwaito shi da gajeren isnadi (Al-Isnaadul Aalee) a cikin Sahih Al-Bukhaariy
(897) da wannan lafazin:
«حَقٌّ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ، أَنْ يَغْتَسِلَ فِي كُلِّ سَبْعَةِ
أَيَّامٍ يَوْمًا يَغْسِلُ فِيهِ رَأْسَهُ وَجَسَدَهُ»
Haƙƙi ne a kan kowane musulmi a yini guda a cikin kowaɗanne kwanaki bakwai ya yi wanka, ya wanke kansa da
jikinsa a cikinsa.
Kuma a cikin riwayar da ya yiwo ta daga Mujaahid,
shi kuma daga Taawus (lamba: 898) ya zo da wannan lafazin:
«لِلَّهِ تَعَالَى عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ حَقٌّ، أَنْ يَغْتَسِلَ
فِي كُلِّ سَبْعَةِ أَيَّامٍ يَوْمًا»
Allaah Ta’aala yana da haƙƙi a kan kowane musulmi, ya yi wanka a yini guda
daga cikin kowaɗanne kwanaki
bakwai.
Don haka wannan hadisi ya samu daraja mafi girma
wurin sahihanci, domin yana cikin manyan littafan da suka fi kowane littafin
hadisi inganci, waɗanda kuma duk
hadisin da ya fito daga cikinsu ya gama hayewa, in shaa’al Laah.
Kodayake a cikin dukkan lafuzzan ba a ambaci wace
rana ce daga cikin ranakun na mako ba, amma a cikin waɗansu riwayoyin an fayya ce hakan. Kamar riwayar Jaabir a
cikin Sunan An-Nasaa’iy (lamba: 1377) mai cewa:
«عَلَى كُلِّ رَجُلٍ مُسْلِمٍ فِي كُلِّ سَبْعَةِ أَيَّامٍ غُسْلُ
يَوْمٍ، وَهُوَ يَوْمُ الْجُمُعَةِ»
Wajibi ne a kan kowane mutum musulmi a cikin kowaɗanne kwanaki bakwai ya yi wanka a yini ɗaya, kuma shi ne yinin Jumma’a.
Haka ma ya kawo shi da wannan lafazin a cikin
Sahih Ibn Khuzaimah: (lamba: 1746).
A cikin Al-Musannaf na Ibn Abi-Shaibah (lamba:
4989) daga riwayar Al-Baraa’ Bn Azib (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
«إِنَّ مِنَ الْحَقِّ عَلَى الْمُسْلِمِينَ أَنْ يَغْتَسِلَ أَحَدُهُمْ
يَوْمَ الْجُمُعَةِ، وَأَنْ يَمَسَّ مِنْ طِيبٍ إِنْ كَانَ عِنْدَ أَهْلِهِ، فَإِنْ
لَمْ يَكُنْ عِنْدَهُ طِيبٌ فَالْمَاءُ لَهُ طِيبٌ»
Lallai yana daga cikin haƙƙi a kan musulmi cewa ɗayansu ya yi wanka a ranar Jumma’a, kuma ya shafa turare
idan akwai a gidansa. Idan kuma babu, to ruwa ma dai turare ne gare shi.
Wannan hadisin da dukkan lafuzzansa da aka ambata
a nan da waɗanda ba a kawo ba kamar:
«غُسْل يوم الجُمُعة واجبٌ على كلِّ محتلم»
Wankan ranar Jumma’a wajibi ne a kan kowane
baligi. (Sahih Al-Bukhaariy: 879, Sahih Muslim: 846).
Waɗannan duk nuni
suke yi a fili cewa, wajibi ne a kan musulmi ya yi wanka a kowace ranar
Jumma’a.
Haka ma ƙissar Umar Bn Al-Khattaab da Uthman Bn Affaan (Radiyal Laahu Anhumaa) take
nunawa. A cikinta, Uthman ya zo ya tarar da Umar yana cikin huɗuba a ranar Jumma’a, sai ya zarge shi a kan zuwa a
makare. Sai shi kuma ya ba da uzurin cewa ayyuka ne suka ɗauke masa hankali, don haka da ya ji kiran sallah bai ko
iya komawa gida ba, sai ya yi alwala kawai ya zo. Sai Umar ya ce:
والوضوء أيضاً! وقد عَلِمْتَ أنَّ رسول الله - صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - كان يأمُرُ بالغُسْل
Sannan kuma alwala ka yi! Alhali ka san cewa
Manzon Allaah ya yi umurni da yin wanka ne! (Sahih Al-Bukhaariy: 878, Sahih
Muslim: 845).
Waɗansu malamai sun
kafa hujja da wannan ƙissar a kan rashin wajibcin wankan Jumma’a, tun da dai ga babban Sahabi Uthman bai yi ba!
Amma waɗansu malaman
irin su Is’haaq Bn Rahwuyah ba su yarda ba. Ga abin ma da ya ce:
قِصَّةُ عُمَرَ وَعُثْمَانَ تَدُلُّ عَلَى وُجُوبِ الْغُسْلِ،
لَا عَدَمِ وُجُوبِهِ، مِنْ جِهَّةِ تَرْكِ عُمَرَ الْخُطْبَةَ، وَاشْتِغَالِهِ بِمُعَاتَبَةِ
عُثْمَانَ، وَتَوْبِيخِ مِثْلِهِ عَلَى رُؤُوسِ النَّاسِ، فَلَوْ كَانَ تَرْكُ الْغُسْلِ
مُبَاحاً؛ لَمَا فَعَلَ عُمَرُ ذَلِكَ، وَإِنَّمَا لَمْ يَرْجِعْ عُثْمَانُ لِلْغُسْلِ
لِضِيقِ الْوَقْتِ، إِذْ لَوْ فَعَلَ؛ لَفَاتَتْهُ الْجُمُعَةُ، أَوْ لِكَوْنِهِ كَانَ
اغْتَسَلَ كَمَا تَقَدَّمَ
Ƙissar Umar da Uthman tana nuna wajibcin yin wankan ne ba wai rashin
wajibcin ba. Ta fuskar yadda Umar ya bar huɗubar, ya shagaltu da zargin Uthman. Sannan kuma da yadda
ya zargi mutum mai girma irinsa a gaban mutane. Idan da barin yin wankan halal
ne da Umar bai yi wannan ɗin ba. Abin da
kawai ya sa Uthman bai koma don yin wankan ba, sai domin ƙurewar lokaci. Domin in da ya yi hakan, to da kuwa
Jumma’ar ta kuɓuce masa. Ko
kuma bai koma ba ne saboda ya riga ya yi wankan, kamar yadda ya gabata (tun da
safe). (Fat-hul Baariy: 2/362).
A kan wannan wankan na Uthman akwai riwaya da ta
tabbatar da hakan a cikin Sahih Muslim, daga bawan gidansa mai suna Humraan Bn
Abaan, ya ce:
كُنْتُ أَضَعُ لِعُثْمَانَ طَهُورَهُ فَمَا أَتَى عَلَيْهِ يَوْمٌ
إِلَّا وَهُوَ يُفِيضُ عَلَيْهِ نُطْفَةً .
Na kasance ina ajiye wa Uthman ruwan tsarkinsa.
Kuma yini guda ba ya zuwa masa face ya zuba wani abu a jikinsa. (Sahih Muslim:
231).
An-Nawawiy ya ce: Wato, yini guda bai wucewa a
gare shi, sai ya yi wanka.
Tun da dai yana yin wanka a kowace rana to shi ne
Ibn Hazm ya ce:
فَيَوْمُ الْجُمُعَةِ يَوْمٌ مِنَ الْأيَّامِ بِلَا شَكٍّ ...
Ranar Jumma’a kuwa ɗaya ce daga cikin ranaku, ko shakka babu… (Al-Muhallaa:
2/21).
Daga cikin riwayoyin da suke ƙara ƙarfafa wajibcin wankan Jumma’a akwai fatawar
Sahabi Abi-Qataadah wacce ɗansa Abdullah ya
riwaito cewa: Babana ya shigo wurina alhali ina wanka a ranar Jumma’a sai ya
ce: Wankan janaba kake yi ko na Jumma’a? Na ce: Na Jumma’a. Ya ce: Ka ƙara wani wankan ban da
wannan. Na ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa:
«مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ؛ كَانَ فِي طَهَارَةٍ إِلَى
الْجُمُعَةِ الْأُخْرَى»
Wanda ya yi wanka a ranar Jumma’a zai zama a cikin
tsarki har zuwa wata Jumma’ar. (At-Tabaraani a cikin Al-Ausat, da Ibn Khuzaimah
suka fitar da shi, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin As-Saheehah: 2321).
Malaman da suke ganin rashin wajibcin wankan
Jumma’a sun kawo dalilai masu yawa. Mafi ƙarfin hujjarsu, kamar yadda Ibn Daqeeq Al-Eid ya ambata dai ita ce: Hadisin
Samurah Bn Jundub cewa, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya ce:
«مَنْ تَوَضّأَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ؛ فَبِهَا وَنِعْمَتْ، وَمَنِ
اغْتَسَلَ؛ فَالْغُسْلُ أَفْضَلُ»
Wanda ya yi alwala a ranar Jumma’a to madalla da
hakan, amma wanda ya yi wanka, to wankan shi ya fi falala. (Ahmad (20177) da
An-Nasaa’iy (1380) da Abu-Daawud (354) da At-Tirmiziy (497) da Ibn Maajah
(1091) suka tiwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).
Suka ce: A nan, cewa ya yi wankan ya fi, amma ba
wai wajibi ba ne!
Amma waɗansu malaman sun
rinjayar da hadisan wajibcin wankan Jumma’a a kan waɗanda suke nuna mustahabbanci, kamar waɗannan:
1. Ibn Daqeeq Al-Eid ya ce:
وَلَا يُقَاوِمُ سَنَدُهُ سَنَدَ هَذِهِ الْأَحَادِيثِ
Isnadinsa bai kai ƙarfin isnadin waɗannan hadisan (da suke nuna wajibci ba).
Har zuwa inda ya ce:
فَلَا تَقْوَى دَلَالَتُهُ عَلَى عَدَمِ الْوُجُوبِ، لِقُوَّةِ
دَلَائِلِ الْوُجُوبِ عَلَيْهِ.
Don haka, dalilin da ke cikinsa bai kai ƙarfin nuna rashin
wajibci ba, saboda rinjayar ƙarfin dalilin wajibcin a kansa. (Ihkaamul Ahkaam Sharh Umdatul Ahkaam:
1/332).
2. Shi kuwa Ibn Hazm cewa ya yi:
لَمْ يَكُنْ فِيهَا نَصٌّ وَلَا دَلِيلٌ عَلَى أَنَّ غُسْلَ
الْجُمُعَةِ لَيْسَ بِوَاجِبٍ، وَإِنَّمَا فِيهَا أَنَّ الْوُضُوءَ نِعْمَ الْعَمَلُ،
وَأَنَّ الْغُسْلَ أَفْضَلُ، وَهَذَا لَا شَكَّ فِيهِ
A cikinsa ba bu nassi ko dalili a kan cewa wankan
Jumma’a ba wajibi ba ne. Abin da ke cikinsa kawai shi ne cewa: Ita alwala
madalla da ita, kuma cewa wanka ya fi falala. Wannan babu ko shakka a cikinsa.
Daga nan kuma sai ya ce:
وَقَدْ قَالَ اللهُ تَعَالَى: {وَلَوْ آمَنَ أَهْلُ الْكِتَابِ
لَكَانَ خَيْراً لَهُمْ} ؛ فَهَلْ دَلَّ هَذَا اللَّفْظُ عَلَى أنَّ الْإِيمَانَ وَالتَّقْوَى
لَيْسَ فَرْضاً؟! حَاشَا للهِ مِنْ هَذَا.
Allaah Ta’aala ya ce: ‘Idan da Ahlul-Kitaab sun yi
imani da ya fiye musu alkhairi.’ (Surah Al-Imraan: 110). Yanzu wannan lafazin
ya nuna kenan cewa, imani da taqawa ba wajibai ko farillai ba ne?! Allaah ya
kiyaye hakan. (Al-Muhallaa: 2/25).
Tun kafin nan da ma ya ambaci cewa:
وَكُلُّ مَا أَخْبَرَ - عَلَيْهِ السَّلَامُ - أنَّهُ وَاجِبٌ
عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ وَحَقُّ اللهِ تَعَالَى عَلَى كُلِّ مُحْتَلِمٍ؛ فَلَا يَحِلُّ
تَرْكُهُ، وَلَا الْقُوْلَ بِأنَّهُ مَنْسُوخٌ، أَوْ أنَّهُ نُدْبٌ؛ إِلاَّ بِنَصٍّ
جَلِيٍّ بِذَلِكَ مَقْطُوعٌ؛ عَلَى أنَّهُ وَارِدٌ بَعْدَهُ مُبَيِّنٌ أنَّهُ نُدْبٌ،
أَوْ أنَّهُ قَدْ نُسِخَ؛ لَا بِالظُّنُونِ الْكَاذِبَةِ الْمَتْرُوكِ لَهَا الْيَقْين.
Duk abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya ambaci cewa shi wajibi ne a kan kowane baligi, kuma cewa shi haƙƙin Allaah Ta’aala ne a kan kowane musulmi, to bai halatta a bar shi
ba. Kuma bai halatta a ce wai shi shafaffe ne, ko kuma wai shi mustahabbi ne
ba. Sai dai in akwai nassi a fili yanke, wanda ya zo a kan hakan, cewa a bayan
wancan ɗin ne ya zo yana bayanin cewa shi ɗin mustahabbi ne, kuma cewa wancan ɗin an shafe shi. Amma ba da zace-zace na ƙarya waɗanda saboda su a ce an bar zance na yaƙini ba! (Al-Muhallaa:
2/21).
3. Al-Ameer As-San’aaniy kuma ya ce:
أنَّ وُجُوبَ غُسْلِ يَوْمِ الْجُمُعَةِ أَقْوَى مِنْ وُجُوبِ
عَدَدٍ مِنَ الْمَسَائِلِ الْفِقْهِيَّةِ الْمُخْتَلَفِ فِيهَا.
Wajibcin wankan Jumma’a ya fi ƙarfi fiye da wajibcin
mas’alolin Fiqhu da dama waɗanda malamai suka yi saɓani a kan su. (Subulus Salaam: 1/156).
4. As-Shawkaaniy kuma abin da ya ce shi ne:
بِهَذَا يَتَبَيَّنُ لَكَ عَدَمُ انْتِهَاضِ مَا جَاءَ بِهِ
الْجُمْهُورُ مِنَ الْأَدِلَّةِ عَلَى عَدَمِ الْوُجُوبِ، وَعَدَمِ إِمْكَانِ الْجَمْعِ
بَيْنَهَا وَبَيْنَ أَحَادِيثِ الْوُجُوبِ؛ لِأنَّهُ وَإِنْ أَمْكَنَ باِلنِّسْبَةِ
إِلَى الْأوَامِرِ؛ لَمْ يُمْكِنْ بِالنِّسْبَةِ إِلَى لَفْظِ (وَاجِبٌ) وَ (حَقٌّ)؛
إلاَّ بِتَعَسُّفٍ لَا يُلْجِئُ طَلَبُ الْجَمْعِ إِلَى مِثْلِهِ. وَلَا يَشُكُّ مَنْ
لَهُ أَدْنَى إِلْمَامٍ بِهَذَا الشَّأْنِ أنَّ أَحَادِيثَ الْوُجُوبِ أَرْجَحُ مِنَ
الْأحَادِيثِ الْقَاضِيَةِ بِعَدَمِهِ ... ".
Da wannan yake bayyana maka cewa, dalilan da
jumhuur suka kawo ba su isa su nuna rashin wajibci ba, ko kuma a iya haɗe kansu da hadisan da suka nuna wajibcin ba. Domin
kodayake hakan zai iya yiwuwa dangane da (awaamir), amma ba zai yiwu ba dangane
da lafazin (wajibun) da (haqqun), sai tare da wahala wanda ƙa’idar neman haɗe kan nassoshi
ba ta komawa gare shi. Ba shakka dai duk wanda yake da fahimta kome ƙanƙantarta a cikin wannan ilimin ya san cewa, hadisan
da suke nuna wajibcin sun fi rinjaye a kan hadisan da suke hukunta rashinsa.
(Nailul Awtaar: 1/292).
5. Haka shi ma Ahmad Shaakir cewa ya yi:
الْحَقُّ الَّذِي نَذْهَبُ إِلَيْهِ وَنَرْضَاهُ: أنَّ غُسْلَ
يَوْمِ الْجُمُعَةِ وَاجِبٌ حَتْمٌ، وَأنَّهُ وَاجِبٌ لِلْيَوْمِ وَللِاجْتِمَاعِ،
فَمَنْ تَرَكَهُ؛ فَقَدْ قَصَّرَ فِيمَا وَجَبَ عَلَيْهِ، وَلَكِنْ صَلَاتُهُ صَحِيحَةً
إِذَا كَانَ طَاهِراً.
Gaskiyar da muka zaɓa kuma muka yarda da ita a nan ita ce: Wankan ranar
Jumma’a wajibi ne yanke! Kuma shi wajibi ne domin yinin da kuma taron. Don
haka, wanda ya bar shi to lallai ya taƙaita a cikin abin da ya wajaba a kansa. Amma dai sallarsa ta inganta, idan
dai yana da tsarki.
Sannan kuma ya ce:
فَإنَّ الْأَصْلَ فِي الْأَمْرِ أنَّهُ لِلْوُجُوبِ، وَلَا يُصْرَفُ
عَنْهُ إِلَى النَّدْبِ إلاَّ بِدَلِيلٍ، وَقَدْ وَرَدَ الْأَمْرُ بِالْغُسْلِ صَرِيحاً،
ثُمَّ تَأيَّدَ فِي مَعْنَى الْوُجُوبِ بِوُرُودِ النَّصِّ الصَّرِيحِ الصَّحِيحِ بِأَنَّ
غُسْلَ يَوْمِ الْجُمُعَةِ وَاجِبٌ، وَمِثْلُ هَذَا الَّذِي هُوَ قَطْعِيُّ الدِّلَالَةِ،
وَالَّذِي لَا يَحْتَمِلُ التَّأوِيلَ؛ لَا يَجُوزُ أَنْ يُؤَوَّلُ لِأَدِلَّةٍ أُخْرَى،
بَلْ تُؤَوَّلُ الْأدِلَّةُ الْأُخْرَى إِنْ كَانَ فِي ظَاهِرِهَا الْمُعَارِضَةُ لَهُ،
وَهَذَا بَيِّنٌ لَا يَحْتَاجُ إِلَى بَيَانٍ"
Domin a asali a cikin umurni ana ɗaukar sa na wajibi ne, kuma ba a juyar da shi zuwa ga
mustahabbanci sai da dalili. Kuma umurni da yin wankan ya zo ne a fali ƙarara, sai kuma ya ƙarfafu a cikin ma’anarsa da zuwan nassi sarihi sahihi mai cewa: Wankan
ranar Jumma’a wajibi ne. Irin wannan nassi da manufar
dalilinsa yake a yanke, wanda kuma ba ya ɗaukar tawili ba
ya halatta a juyar da shi zuwa ga wata ma’anar ta daban. Amma sauran dalilan ne
ake juyar da su gare shi, waɗanda ake ganin
sun saɓa wa wannan ɗin a zahiri.
Wannan dai a bayyane ya ke, ba ya buƙatar wani bayani. (Ta’aleeq ga
littafin Ar-Risaalah na Al-Imaam As-Shaafi’iy, shafi: 307).
6. Al-Albaaniy kuma ya ce:
وَجُمْلَةُ الْقَوْلِ أَنَّ الْأَحَادِيثَ الْمُصَرِّحَةَ بِوُجُوبِ
غُسْلِ الْجُمُعَةِ فِيهَا حُكْمٌ زَائِدٌ عَلَى الْأَحَادِيثِ الْمُفِيدَةِ لاسْتِحْبَابِهِ،
فَلَا تَعَارُضَ بَيْنَهُمَا، وَالْوَاجِبُ الْأَخْذُ بِمَا تَضَمَّنَ الزِّيَادَةُ
فِيهَا.
Taƙaitacciyar magana dai ita ce: Hadisan da suka zo da bayanin wajibcin wankan
Jumma’a a fili, a cikinsu akwai hukunci da ya ƙaru a kan hadisan da
suke fa’idantar da mustahabbanci. Don haka babu cin karo
da juna a tsakaninsu. Abin da yake wajibi dai shi ne yin riƙo da abin da ya ƙaru a cikin hakan.
(Tamaamul minnah, shafi: 12).
7. A ƙarshe dai, Ibn Al-Munzir ya samo amincewa da cewa, wankan Jumma’a wajibi ne daga mamai irinsu: Abu-Hurairah da Ammaar
(Radiyal Laahu Anhum). Al-Khattaabiy kuma ya samo daga: Al-Hasan Al-Basariy da
Maalik (Rahimahulnal Laah). Haka ma Ibn Munzir ya samo daga Maalik (Rahimahul
Laah). Duk kuwa da cewa jumhur na malamai sun zaɓi cewa mustahabbi ne. (Nailul Awtaar: 1/290).
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.