Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Tarawihi Da Tahajjud Wanne Ya Fi Falala?

Akwai 'yan bidi'a da yawa da suke sukar Tahajjud, wasu har da Tarawihin suke suka, kamar Rafidha 'yan Shi'a. Wasu kuma Ahlus Sunna ne, amma sun shahara da sukar Tahajjud, duk da cewa akwai Hadisai karara da suke tabbatar da Annabi (saw) ya yi Tahajjud, a Masallaci, tare da Sahabbansa cikin jam'i. Su wadannan 'yan Izalar - duk da cewa Tahajjud yana cikin "al-Muwadda" ta Imamu Malik, kuma su Malikiyya suke bi - sun wayi gari cikin masu sukar Tahajjud din.

To, Allah ya shirye su, da mu gaba daya.

Miye Tarawihi?

Miye Tahajjud?

Tarawihi shi ne: Sallar dare a dararen Ramadhan, wacce ake yi a farkon dare, bayan idar da Sallar Isha’i.

Tahajjud shi ne: Sallar dare, wacce ake yi cikin dare zuwa karshen dare, ko bayan an yi bacci an tashi. Musamman a dararen goman karshe na Ramadhan. Shi ya sa A'isha (ra) ta ce:

(وأيقظ أهله).

Wato Annabi (saw) yana tashin iyalansa daga barci, don su yi Tahajjud, a goman karshe.

Duka biyu ana yinsu a cikin jam'i, ko a daidaiku.

Hadisai sun zo suna nuni cewa; Annabi (saw) ya yi Tahajjud, ya yi jam’i wa mutane, a Masallaci. Akwai Hadisin A’isha (ra), a cikin “al-Muwadda” da “Sahihul Bukhari” da “Sahihu Muslim”.

Da kuma Hadisin Abu Zarr (ra), a wajen “Ash’abus Sunan” da Ahmad da Ibnu Khuzaima da Ibnu Hibban.

Da kuma Hadisin al-Nu’uman bn Basheer (ra), a wajen al-Nasa’iy, da Ahmad, da Ibnu Khuzaima da al-Hakim.

Annabi (saw) ya yi jam’i wa mutane na tsawon kwana uku, sai ya dena fitowa, amma ya fadi dalili kamar ya zo a "al-Muwadda" kamar haka:

«قد رأيت الذي صنعتم، ولم يمنعني من الخروج إليكم، إلا أني خشيت أن تفرض عليكم» وذلك في رمضان.

موطأ مالك ت عبد الباقي (1/ 113)

A Sahihul Bukhari kuma ya zo cewa:

«أما بعد، فإنه لم يخف علي مكانكم، ولكني خشيت أن تفترض عليكم، فتعجزوا عنها»، فتوفي رسول الله صلى الله عليه وسلم والأمر على ذلك".

صحيح البخاري (3/ 45)

Ma'ana: Annabi (saw) ya dena fitowa ne don tsoron kar a farlanta sallar, sai kuma su kasa yi.

Tun da aka dena Tahajjud a zamanin Annabi (saw) ba a sake yi ba, sai a tsakiyan zamanin Sayyidina Umar (ra) aka cigaba da yi:

"قال ابن شهاب: فتوفي رسول الله صلى الله عليه وسلم، والأمر على ذلك ثم كان الأمر، على ذلك في خلافة أبي بكر وصدرا من خلافة عمر بن الخطاب".

موطأ مالك ت عبد الباقي (1/ 114)

A zamanin Sayyidina Umar (ra) sai ya tara mutane a karkashin Limami guda daya, suka fara jam’i, suna Tahajjud a Masallaci, saboda dalilin da ya sa Annabi (saw) ya dena fitowa Tahajjud ya gushe, saboda Annabi (saw) ya rasu, an rufe kofar farlantawa:

حدثني مالك، عن ابن شهاب، عن عروة بن الزبير، عن عبد الرحمن بن عبد القاري، أنه قال: خرجت مع عمر بن الخطاب في رمضان إلى المسجد، فإذا الناس أوزاع متفرقون. يصلي الرجل لنفسه، ويصلي الرجل فيصلي بصلاته الرهط. فقال عمر: والله إني لأراني «لو جمعت هؤلاء على قارئ واحد لكان أمثل»، فجمعهم على أبي بن كعب قال: ثم خرجت معه ليلة أخرى، والناس يصلون بصلاة قارئهم، فقال عمر «نعمت البدعة هذه»، «والتي تنامون عنها أفضل من التي تقومون» يعني آخر الليل وكان الناس يقومون أوله.

موطأ مالك ت عبد الباقي (1/ 114 - 115)، صحيح البخاري (3/ 45)

Kafin Sayyidina Umar (ra) ya sa su fara Tahajjud, mutane Tarawihi suke yi, wato a farkon dare suke Sallar, kuma a rarrabe, kucul-kucul. Sai ya tara su karkashin Limami guda daya, kuma a karshen dare. Shi ya sa ya ce:

«والتي تنامون عنها أفضل من التي تقومون» يعني آخر الليل وكان الناس يقومون أوله.

"Sallar da kuke yi mata bacci ta fi falala a kan wacce kuke yinta".

Yana nufin Sallar karshen dare ta fi ta farkon dare. Mutane sun kasance a farkon dare suke yin Sallar.

Don haka da farko mutane Tarawihi suke yi, wato a farkon dare, sai Sayyidina Umar (ra) ya mayar da su yin Tahajjud, wato Sallah a karshen dare. Shi ya sa Ibnu Abdilbarr ya ce:

"وفيه دليل على أن قيامهم كان أول الليل، ثم جعله عمر في آخر الليل".

الاستذكار (2/ 66)

Don haka Tahajjud Sunnar Annabi (saw) ne, ya kwadaitar, kuma ya yi ta a aikace, kamar yadda Ibnu Abdilbarr ya ce:

"وهذا كله يدل على أن قيام رمضان جائز أن يضاف إلى النبي عليه السلام، بحضه عليه وعمله به، وأن عمر إنما سن منه ما سنه رسول الله".

الاستذكار (2/ 64)

"Wannan abin da ya gabata gaba dayansa yana nuna cewa; ya halasta a jingina Tahajjud ga Annabi (saw), saboda ya kwadaitar a kai, kuma ya aikata a aikace, kawai shi Sayyidina Umar (ra) ya sunnanta abin da Manzon Allah (saw) ya sunnanta ne".

Kuma da waccar magana ta Sayyidina Umar (ra) malamai suka tabbatar da cewa; Tahajjud ya fi Tarawihi falala. Saboda Sallah a karshen dare ya fi a farkon dare. Shi ya sa ma Annabi (saw) Tahajjud ya yi, ba Tarawihi ba.

Ga maganganun Malamai a kan haka:

Ibnu Baddal da Ibnul Mulaqqin suka ce:

"وقوله: (والتي ينامون عنها أفضل): يعني: القيام آخر الليل؛ لحديث عائشة أنه - عليه السلام - كان ينام أول الليل ويحيي آخره. وأيضا فهو وقت التنزل واستجابة الرب تعالى في ذلك الوقت لمن دعاه".

شرح صحيح البخارى لابن بطال (4/ 147)، التوضيح لشرح الجامع الصحيح (13/ 557)

Ma'ana; Tahajjud ya fi falala, saboda Annabi (saw) yana bacci a farkon dare, sai ya yi Sallah a karshen dare. Kuma saboda karshen dare lokacin saukowan Allah ne, yana amsa addu'ar wanda ya kira shi.

Haka Ibnu Abdilbarr ma ya fada:

"وأما قوله: "والتي ينامون عنها أفضل" فلِما جاء في دعاء الأسحار، وقد أثنى الله على المستغفرين بالأسحار".

الاستذكار (2/ 68)

Haka al-Bajiy ya fada:

"وقوله: "والتي ينامون عنها" يريد الصلاة آخر الليل، أفضل من التي يقومون يريد مع الإمام أول الليل، لأن الصلاة في النصف الآخر أفضل منها في النصف الأول، لما روي عن عائشة - رضي الله عنها - «أن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - كان ينام أول الليل ويحيي آخره».

المنتقى شرح الموطإ (1/ 208)

Haka al-Iraqiy ya fada:

"وقوله والتي ينامون عنها أفضل ليس فيه ترجيح الانفراد ولا ترجيح فعلها في البيت وإنما فيه ترجيح آخر الليل على أوله كما صرح به الراوي بقوله يريد آخر الليل".

طرح التثريب في شرح التقريب (3/ 96)

Haka Ibnu Hajar ya ce:

"قوله: "والتي ينامون عنها أفضل" هذا تصريح منه بأن الصلاة في آخر الليل أفضل من أوله، لكن ليس فيه أن الصلاة في قيام الليل فرادى أفضل من التجميع".

فتح الباري لابن حجر (4/ 253)

Saboda haka Sallar Tahajjud, wacce ake yi a cikin dare zuwa karshen dare, bayan an yi bacci an tashi, ta fi falala a kan Sallar Tarawihi, wacce ake yi a farkon dare, ana idar da Sallar Isha’i. Saboda karshen dare ya fi farkonsa falala, kuma saboda Annabi (saw) Tahajjud yake yi.

Saboda haka a cikin wannan akwai raddi ga masu cewa; Tahajjud bidi’a ne. A’a, sam, Tahajjud Sunnar Annabi (saw) ne, kamar yadda ya gabata daga Ibnu Abdilbarr. Kuma har ma Tahajjud din ya fi Tarawihi falala.

Da wannan za ka fahimci kuskuren masu cewa; -wai- Shaikh Abdallah al-Khalifiy ne ya fara yin Tahajjud a Haramin Makka. Shaikh Isyaka Rabi’u kuma ya fara yi a Nigeria. A’a, ba haka ba ne, tun zamanin Annabi (saw) an yi, sai aka dena, sai aka cigaba da yi a zamanin Sayyidina Umar (ra), har zuwa yau, saboda abin da ya sa Annabi (saw) ya dena ya kau.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments