Ticker

6/recent/ticker-posts

Tubalan Ginin Turke Cikin Wakokin Yabo Na Ahmad Muhamm

Citation: Alhassan, B.A. (2024). Tubalan Ginin Turke Cikin Waƙoƙin Yabo Na Ahmad Muhammad (Shehi). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 506-514. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.062.

TUBALAN GININ TURKE CIKIN WAƘOƘIN YABO NA AHMAD MUHAMMAD (SHEHI)

Badariyya Aliyu Alhassan

Dept of Nigerian Languages, Bayero University Kano

Tsakure

Daidai da faɗar Hausawa ko da iska ta zo, ta iske kaba na rawa, domin kuwa, masana da manazarta sun yi shekaru suna baje-kolin tunaninsu da fasaharsu da tarken tubalan waƙoƙin baka na Hausa. Ta haka ne, wannan takarda ke da muradin fayyace yadda Ahmad Muhammad Shehi yake bayyana wa masu sauraransa irin yabon da yake yi wa annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama a ɗiyan waƙoƙinsa. An gina wannan takarda ne bisa ra’in Waƙar Baka Bahaushiyya (WBB). A ɓangaren dabarun gudanarwa kuwa, an yi amfani ne da fasalin bincike sharhantacce. Domin wannan takarda ta ginu a kan fayyace yadda shehi ya ke gina waƙoƙinsa, inda yake bayyana girma da matsayin annabi Muhammad, sallallahu alahi wa sallama a gurin allah subhanahu wa ta’ala da kuma irin soyayyar da yake yi masa a cikin zuciyarsa.

Fitilun Kalmomi: Tubala, Ginin Turke, Waƙoƙi, Yabo, Ahmad Muhammad (Shehi)

Gabatarwa

Waƙar baka tana da ɗaɗɗen tarihi a rayuwar Hausawa. Wannan a bayyane yake cewar makaɗan baka na Hausa suna da wani giɓi na adabi da suke cikewa a rayuwar al’umma ta hanyar yin amfani da baiwar hikima azanci na fasahar shirya zantuka da allah ya huwace musu. Waƙa babban reshe ce ta adabin Hausa, musamman na waƙar baka wacce ita ta fara samuwa tun lokaci mai tsawo kafin rubutacciya. A wannan bincike an yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) da Gusau (2003 da 2011 da 2014) ya gabatar a ayyukansa. Wannan ra’i na ƙunshe da wasu matakai ko dabarun na turken waƙar baka. Har ila yau ra’in WBB na magana ne a kan tsarin waƙa a ƙungiya da kan ƙunshi jagora wanda ke ƙulli da kuma ‘yan amshi waɗanda sukan yi wa jagora ƙari wajen isar da saƙo. Wannan bincike an ɗora shi a kan sharhantaccen bincike (ƙaulitatiɓe research) wata hanya ce ta tattara bayanai da nazarin tare da rubutu rahoto mabambanta daga dabarar bincike ta adabi. Wannan bincike ya tattaro bayani tare da ƙididdiga da samo hanyoyi yayin gudanar da shi.

1.1 Taƙaitaccen Tarihin Ahmad Muhammad (Shehi)

An haifi ahmad Muhammad sabi’u shehi mai tajid’izzi, a unguwar dukawa ta tsakiyar birnin kano a ƙaramar hukumar birni da kewaye a shekarar 6/2/1995. Tun yana ƙarami ya taso da hazaƙa da saurin haddace abu aƙwakwalwarsa. Ya fara karatun addinin musulunci a hannun mahaifiyarsa, kasancewar gidansu gidan malamai ne. Ana yi masa laƙabi da shehi mai tajid’izzi.

Shehi ya fara koyon karatu da rubutun boko tun a gida kafin ya shiga makarantar firamare ta ‘yan awaki a shekarar 2004 ya gama a shekarar 2010. Daga nan ya shiga ƙaramar sakandare da ke sabuwar ƙofa a shekarar 2010. Daga nan ya tafi babbar sakandare ta ƙofar nasarawa inda ya gama a shekarar 2016. Tun kafin ya gama makaranta yake tare da masu gudanar da waƙoƙin yabo na annabi Muhammad sallallahu alaihi wa salam. Hakan ya ba shi damar haddace waƙoƙi masu yawan gaske, waɗanda yawancin duk na yabo ne. Sannan ko a makarantar islamiyya shehi gwani ne wajen iya tsara waƙoƙin yabo musammman a lokacin bukukuwan maulidi. Ya yi ƙungiyoyin yabo da yawa a matsayin masu kula da kayan sauti, daga baya ya zama daga cikin masu yin amshi. Bayan ya gama makarantar sakandare sai ya shiga harkar waƙoƙin yabo, inda ya kafa tasa tawagarsa ta ƙashin kansa. Ya kafa tawaga mai ƙarfin gaske, wacce in dai game da harkar yabo ce, ana iya cewa ya tsere sa’o’insa. A yanzu ahmad shehi ya wallafa waƙoƙin yabon annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam, masu yawan gaske. Haka kuma akan kira shi wurin bukukuwan aure ko suna domin ya rera waƙoƙin yabo a ciki da wajen jihar kano. Shehi yana da halaye na ƙwatance ma’ana yana da kyawawan ɗabi’u, waɗanda sun cancanci a yi koyi da su; kamar son ibada da karatun addini da son fiyayyen halitta annabi Muhammad, sallallahu alahi wa sallama. Mutum ne mai yawan fara’a da barkwanci, sannan ma’abucin sa suturar alfarma, mai girmama mutane ne da baƙi da maƙwabta.

2.1 Ma’anar Turke ta Lugga

Turke ta fuskar lugga na nufin itace ko wani ƙarfe mai tsawo wanda ake ɗaure dabba da shi, ko ɗaure wani abu (Gusau, 2008:369).

Ɗaure wani abu (Gusau, 2002:295).

Turke shi ne riƙe mutum ko kafe shi har sai ya faɗi wata maganar da ya shirya, ko a tona masa asiri kan wata ƙarya da ya yi ko kuma a riƙe shi sai ya yi wani aiki da ake buƙatar ya yi (Bargery,1934:1034) (CNHN, 2006:446).

2.2 Ma’anar Turke a Fannin Ilimi

Gusau (2008:370) ya ce turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba. Gusau (2008:370) ya kuma bayyana yanayin turke a waƙoƙin baka suna da manyan manufofi a kowace waƙa za a sami turke guda wanda aka gina ta a sababiyyarsa. Akwai kuma ƙananan manufofi inda akan kawo wasu maganganu don su taimaka daɗa fito da babbar manufa wadda ita ce aka ba suna turke, ƙananan manufofin nan su ake kira tubalan ginin turke. Gusau (2008:371) ya bayyana manyan turakan waƙoƙin baka na Hausa sun haɗa da yabo zalla da zuga zalla da yabo surke da zuga da zambo da ta’aziyya da wayar da kai da tarihi da siyasa da kishin ƙasa da soyayya da wasa kai ko koɗa kai da taya murna da sauransu.

Kings (1980:29) ya bayyana ma’anar turke shi ne wanda ake harhaɗa ɗiya gwargwadon buƙata ana yi ana gwama dangantaka a tsakaninsu, ta kusa ko ta nesa, har su bayar da ma’ana bisa manufar da ake son isarwa.

Tubali ta Fuskar Lugga

Tubali ta fuskar lugga na nufin curin ƙasa da aka yi ya bushe dan gini (CNHN, 2006:440)

Tubali ta Fuskar Fannin Ilimi

Ma’anar tubali ta fuskar nazari, wato fannu, tubali na nufin wani ko wasu saƙonni da akan samo a cikin waƙa da makaɗa da mawaƙa ke tsattsarmawa a mabambantan gurare. Tubalan ginin waƙa wasu ƙananan saƙonni ne da ake gwamawa don ƙara ƙulla waƙa ta yi tsawo amma ba su ne babbar manufar waƙa ba. Kuma kowane babban turke akwai nau’o’in tubalan da suka dace da shi. Ƙaramin saƙo shi ne wanda ake ginawa a cikin ɗan waƙa ɗaya, ba kasafai ne yake zarcewa zuwa wani ɗan ba a zubi irin na waƙar baka. Za a iya samun waƙa ɗaya ta ƙunshi tubalai da dama gwargwadon yadda makaɗin ya tsara da kuma yadda yake tunanin zurfafa manufar. (Ɗangambo, 2007:14) da (Gusau, 2002:35) (Gusau, 2003:30) tubalan ginin turke ke nan suna nufin wasu maganganu da aka bi aka ƙuƙƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo, amma ba su ne babbar manufar waƙar ba. Misali idan turken waƙa na ‘yabo’ ne, a cikin waƙar za a iya kawo wasu abubuwa waɗanda ba lalle sai a kan yabo suke magana ba, amma za su iya ƙara wa waƙar kyau da armashi. (Gusau, 2003:30) ya bayyana kowane ‘turke’ da tubalan gininsa da suka fi dacewa da shi. Alal misali a turken yabo an fi amfani da ambaton addini da asali ko nasaba da karamci ko kyauta ko tarihi da sauransu a lokacin da ake ƙoƙarin faɗaɗa shi.

Satatima (2009:82) ya bayyana ma’anar tubali cewa ya yi cikin hikima ne mawaƙan baka sukan zaɓi turken waƙarsu su kuma ƙayatar da shi ta amfani da ƙananan turaku wato tubalan ginin turke, ko kuma raɓa dannin turke kamar yadda wasu sukan kirasu. Alal misali idan waƙar turkenta na yabo ne, to sai ka ga mawaƙi ya taɓo nasaba da riƙo da addini da kyauta ya tsara wannan yabo nasa da shi.

Umma (2021) ta bayyana tubali na nufin saƙonni da mawaƙan baka kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu domin taimakawa wajen fito da babban turke. Kaɗan daga cikin tubalan akwai yabo da zambo da habaici da zuga da kirari da makamantansu.

Tubalin ginin turke yana nufin ƙaramar manufa ko saƙo a zubin ɗiyan waƙa. Tubali shi ne ake sassarƙawa a fito da babbar manufa ta waƙa. Tubali shi ke kyautata tunanin makaɗa wajen samun manufar waƙa (CNHN, 2006: 446).

3.0 Tubalan Turke a Wasu Waƙoƙin Ahmad Muhammad Shehi

Binciken gaba ɗaya an yi shi ne a kan turken yabon ma’aiki da sahabbansa da iyalansa da kuma tubulan da aka yi amfani da su a ya yi gina wannan turken waƙoƙin. Daga cikin tubalan da wannnan takarda ta ɗauka za ta kawo misalansu sun haɗa da: tubalin mu’ujiza da jarumta da kyakkyawan asali da kyawon halitta da kyawun ɗabi’a.

3.1 Mu’ujiza

Mu’ujiza tana nufin wata baiwa ta musamman wanda kan faru ga wani annabi kamar tsagewar wata ga annabi Muhammad (CNHN, 2006:354).

Mu’ujiza kalma ce ta larabci kuma tana nufin gajiyawa, wani lokaci kuma ta ɗauki ma’anar wasu ayyuka na ban mamaki da ta’ajibi waɗanda babu mai ikon gudanar da su sai allah maɗaukaki, to sai ubangiji allah ya hore wa annabawa ko manzanni su dinga gudananr da su don ya gajiyar da mutanensu ko kuma don ya tabbatar musu da hujjar lallai shi annabi ne ko manzo, musamman waɗanda suka bijire masa suka ƙi gaskata shi. Mu’ujiza takan zama wani abin ta’ajibi wanda mutane ba za su iya aikatawa ba. Haka kuma mu’ujiza tana da sharuɗa da kuma ƙa’idoji da suka haɗa da:

Lallai ne ta zama ɗaya daga cikin ayyukan allah waɗanda babu wani daga cikin mutane wanda zai iya irinta;

Wajibi ne ta saɓa wa al’ada wato ta zama abin da mutane ba su gani ba;

Haka kuma wanda duk ba annabi ko manzo ba ba zai iya aikata irinta ba;

Sannan kuma, ta zamanto ta gudana ne a lokacin da aka yi jayayya, ko aka yi ƙure, ko kuma don ƙara wa jama’a imani;

Kuma lallai ne ya zama tafi to daga wajen mutumin da ya zo da saƙo na annabta ko na manzanci

(Adamu 2014:8-9) cikin (Nura da Ahmad 2018:169).

Mu’ujiza tana nufin abin da ya saɓa wa al’ada ta tafi da hankali ko mamaki wanda ta bambanta da ƙara ko duba ko sihiri ko rufa-ido da makamantansu. Kuma allah yana hore wa annabawa da manzanni ita, domin gaskata da kuma ƙarfafa abin da annabi ko manzo ya zo da shi. Haka kuma, akan sami mu’ujiza domin ƙalubalantar masu inkarin annabtar wani annabi ko manzo. Kuma annabawa da manzonni ne ke da mu’ujiza, wato babu wani wanda ke da mu’ujiza face annabi da manzo (Nura da Ahmad 2018:169).

3.2 Kyakkyawan Asali

Asali shi ne mafari ko salsala ta mutum ko wani abu. (CNHN, 2006:20).

Halima (2015:35) ta bayyana asali da cewa shi ne mafari ko fito da tushen wani abu domin a fahimci daga inda ya fito. Kyakkyawan asali shi ne tushen mutum ya zamo mai kyan. Jinsi wato ta yadda aka same shi ya zama abin alfahari a gare shi.

3.2.1 Kyawun Ɗabi’a

Ɗabi’a, musamman ta mutum (CNHN, 2006:191). Hali wani abu ne da bahaushe ke dangantawa da sababben abu. Hali yana da makusanciyar ma’ana da’’ al’ada’’ domin al’adar abu shi ne halinsa. Bahaushe ya lura da hali cikin jini yake har faufau ba a rabashi da shi, don haka yake hange hali da wasu fuskokin da yawa cikin zantukansa na yau da kullum irin su:

- Hali zanen dutse

- Mai hali ba ya barin halinsa

- Rai da hali ba a raba su

- Halin uwa ɗiya kan ɗauka

- Hali abokin tafiya (Bunza, 2009:6)

Ita ɗabi’a wata aba ce da mutane ko dabba ko wata halitta ta saba yi ko aikatawa (Satatima:147). Ɗabi’a asalinta kalma ce ta larabci, tana nufin wani abu da aka saba yi. Kyawon ɗabi’a ko halaye da wani ko wasu ke yi a zamantakewarsu da mutane wajen mu’amalantarsu. Ita ɗabi’a tana ɗauke da abubuwa da dama a ƙarƙashinta wanda duk siffofinta ne. Misali, jarumtaka da gaskiya da amana da halaye da sauransu.

3.2.2 Jarumtaka

Gusau (2008:387) ya bayyana kalmar jarumtaka tana nufin nuna juriya ko ƙarfin hali ko wata bajinta a lokacin aiwatar da wani abu. Idan an ce mutum mai jarumtaka ne, to ana nufin gwarzan namiji ne, mai taurin hali, ko mai nacewa ga al’amari ko maras tsoro wanda ba ya firgita balantana ya samu faɗuwar gaba. Mai jarumtaka yakan sa gabansa inda ya nufa ba tare da ya ja da baya ba, bai kuma yin waiwaye, bai karkacewa, sai ya kai inda ya dosa. Gusau (2007:387) ya kuma bayyana turken jarumta yana tafiya kafaɗa da kafaɗa da turken yabo mai surke da zuga. Bisa yawanci makaɗan jarumtaka sukan yabi gwarzayensu ne ko kuma su zuga su ta yadda za su ƙara bajinta. Domin haka, turken jaruntaka yana da dangantaka makusanciya da turken yabo mai haɗe da zuga.

Tubalan ginin turke a waƙoƙin shehi

A wajen ginin tubali a waƙar bege mawaƙa suna amfani da kaifin basira wajen fito da ƙananan saƙonni domin faɗaɗa babbar manufa a kowace waƙar yabo, tare da yin la'akari da wanda suke yi wa waƙar, domin yin taka-tsantsan wajen ƙwarewa tare da kiyaye mutuncinsa, tare da nuna tsananin soyayyarsu da ƙaunarsu a gare shi. Haka kuma

Kowacce waƙa na ƙunsar nau'o'in tubalai daban-daban da suka dace da babbar mabufa ta waƙar yabo.

Bugu da ƙari, ta wani ɓangaren tubali a waƙar yabo shi ne yadda mawaƙa da makaɗan yabo suke amfani da tubalan da suke ƙara wa al 'ummar Hausawa musulmai soyayyar annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama a cikin zukatansu. Da kuma son masoya annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam da kuma kyautata ɗabi'un jama'a ta hanyar yin koyi da annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama.

Tubalan da shehi ke amfani da su wajen gina waƙoƙinsa domin jan hankali da kuma isar da saƙon da yake san isarwa ga jama'a. Waɗannan tubalan sun haɗa da mu’ujiza da jarumta da kyakkyawan asali da kyawon halitta da sauransu.

4.0 Tubalin Mu'ujiza

Ahmad Muhammad Shehi makaɗi ne wanda yake da zalaƙar harshe domin isar da saƙo ga jama’a, kuma yana amfani da kalmomi masu nauyi cikin Hausar karin harshen kananci. Sannan yakan fayyace kyan ɗabi’u da kyawon fuska da kyauta da zamantakewarsa da jama’arsa annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama, ta amfani da gina tubalan ginin turke a waƙokinsa. Shehi a cikin waƙoƙinsa yana ambaton mu'ujiza ta annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama wanda ba a ba wa wani irinta ba. Misali a cikin waƙarsa mai suna ya gayatul huna yabon ka ba za ni bar shi ba.

Jagora: Har yau ban ga wanda ya kira yi wata ya tsaga shi ba,

:Har yau ban ga wanda ya yi magana da matacce ya bi shi ba,

:Har yau ban ga wanda abincinsa ya ya beshiba da kan shi ba,

:Har yau ban ga wanda raƙumi ya yi ƙara a gurinsa ba,

:Har yau ban ga wanda zaki ya zabure ya tare shi ba,

:Har yau ban ga wanda rai ya fice kuma ya mai da shi ba,

:Har yau ban ga mai mayar da itace takobi a hannunsaba,

:Har yau ban ga wanda rabbi ya ke hidima a gare shi ba,

:Har yau ban ga wanda in ba shi musulunci bai cika ba,

:Sai mai sirrin subuhun ƙuddusin ya mujitafa.

'Y/amshi: ya gayatul huna yabon ka ba za na bar shi ba.

(Waƙar Ya Gayatul Huna ɗa na 12 mp3).

A wannan ɗan waƙar Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana yadda mu’ujiza annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama ta ke wanda ya kira wata ya zo, sannan kuma ya tsage biyu. Wannan abin ya faru ne a lokacin da mutanen makka suka tambayi annabi da ya nuna musu wata aya da za su gaskata shi, shi annabin allah ne. Sai annabin Muhammad tsira da amincin allah su ƙara tabbata a gare ya kirawo wata sannan kuma ya tsage biyu. Sannan yana daga cikin mu’ujizar annabi ya yi magana da matacce. Shehi ya kuma kawo wata mu’ujizar annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama inda dabbobi suka kawo masa ƙarar iyayen gidansu kamar raƙumi da ya kawo wa annabi ƙara a kan mai kiwon sa zai yanka shi bayan tun yana da ƙarfinsa yake yi masa bauta, yanzu da girma ya kama shi zai yanka shi. Annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama ya yi wa wannan mutumin magana da ya rabu da shi. Shehi ya bayyana annabi ya mayar da itace takobi a hannunsa a lokacin yaƙin hunainu, sai annabi ya zari zangarniya sai ta zama takobi da ya kai sara sai dai kafirai su dunga faɗuwa. Kuma babu wanda rabbi yake hidima a kansa sai annabi, wanda idan ka yi wa annabi salati ɗaya allah zai yi maka goma. Shehi ya bayyana inda ba ka ambaci annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama a yayin kalmar shahada ba to musulunci aka bai cika ba. Har sai ka ambace shi sannan musulunci ya cika. Misali.

Jagora :Ya mai bayyana gaibu ya mai sanin fili ga baɗini,

:Mai magana da kafaɗar tunkiya an yanka tun tuni,

:Kai ke zanta zantuka da barewa ya mu'azzami,

:Haka rabbu ya yi maka baiwa ba za a sanka ba.

(waƙar ya gayatul huna ɗa na 13 mp3).

A nan, Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama ya san gaibu duk abin da zai faru ya san shi kafin ya faru. Wannan abin ya faru ne lokacin da aka kama abbas a matsayin bawa sai aka ce ya fanshi kansa, sai ya ce ba shi da kuɗi. Sai annabi ya ba shi labarin abin da suka yi da matarsa a kan kuɗin da ya bar mata, abbas ya yi mamakin abin da annabi ya faɗa don ya san babu wanda ya sani. Yana daga cikin mu’ujizar annabi ya yi magana da ƙafar/katarar akuya bayan an yanka

Ta, inda take faɗa masa an yi masa sihiri a cikinta ka da ya ci. Babu wanda ya yi wannan sai annabin ƙarshen zamani.

Bugu da ƙari shehi a cikin wata waƙarsa mai suna labbaika ya kuma bayar da ɗiyan waka da ke ɗauke da mu'ujizar annabin tsira alaihimul salatu wassalamu, kamar haka:

Jagora: Tsarki ya tabbata gurin ainun yaƙini farkon duba,

:Wanda aka baiwa biyar waninsa banji ya samu ba,

:Wanda girgije ya ke yi wa inuwa waninsa bai samuba,

:Mai rugurguje gunki da masu bautarsa basu tanka ba.

Jagora: Ma abocin mu'ujiza da take shedarka,

:Wacce duk sakan take nuna muƙaminka,

:Ga maziya ta kankanka a kayinka,

:Mai ƙarfi boye ya tsarata,

:Ga muƙami aliyu na zatunka,

:Wanda ko nubuwa ba ta samu a nan. (waƙar labbaika ɗa na 4 mp3).

A wannan ɗan waƙar yana jaddada wa akan tsarki ya tabbata a gurin annabi Muhammad wanda dama shi tsarkakakke ne shi ne farkon duba a gurin allah subahanahu wa ta’ala. Wanda allah ya baiwa salloli guda biyar da ya umarci al’ummarsa da yi, an bashi waɗannan sallolin ne lokacin da ya je ganawa da allah. Wanda babu wani annabi da ka ba wa. Shehi ya bayyana annabi Muhammad sallallahu alaika wa sallama sabo da mu’ujizarsa har girgije ne yake yi masa inuwa a lokacin da suka je sham da maisaratu yaran nana khadija. Shehi yana bayyana ita kanta mu’ujiza tana shaidawa shi annabin allah ne wanda har take nuna muƙaminsa a gurin allah subhanahu wa ta’ala.

5.0 Tubalin Kyakkyawan Asali

Shehi a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa ya kawo kyakkyawan asalin annabu muhammmad sallallahu alaihi wa sallama da yadda allah ya halicce shi da haskensa. Misali a cikin waƙar salamu alaika ga abin da shehi y ace:

Jagora :Ka zo kana ta kaɗaita buwayaar ainihin asalinka,

:Ka sanu daidaito da abin da ya zamo ainihinka,

:Ka samu yaƙinin ce wa an same ka,

:Ka wanzu kai ka yi fanadi har ka fito ka koma cikinka,

:Sunanka ya yi kama da abin da sufar jikinka ta ɗauka,

:Ka kore biyun ka kasa ɗaukar numbar biyunka.

J agora:A lokacin ba jijabai da suke rufe ɓuyanka,

:Ba wata ba rana ba mai sheda e da akwai ka,

:Sai dai haskenka da asalin haskenka.

Jagora :Tun babu sammai ba ƙassai ba bauta bare aljanna

:Ba malakai ba insi da jinni bare a ba su su zauna,

:Kana nan cikinsu kana ta yin sha’aninka.

(wakar salamu alaika ɗa na 13 da 14 da 16 da 17 mp3).

A nan, Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana allah ya halicci hasken annabi ne tun kafin ya halicci komai na duniya. Wato ba wata ba rana ba sammai da ƙassai ba mala’iku ba insi da jinni sai hasken annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama wanda da shi ne aka halicci komai na duniya.

Jagora: Kai ta bauta wa rabbul arshi cikin hijaban mulki,

:Ka kure bauta da daɗaɗɗan mamaki,

:Har sai da ibadar ta zamo siffar sunanka.

Jagora :Daga nan aka fara hijabai dan rufe matsayinka,

:Kai abin da ka yi a cikinka ta yadda ba mai biyo ka,

:To wa ma zai biyo ka bayan ba hanyar biyoka.

Jagora : Sai aka nufin samar da abin da babu a zati,

:Komai da komai ya samu cikin ƙudirar iklahil baiti,

:Ta wannan hasken da shi ne asalinka.

(waƙar salamu alaika ɗa 19 da 20 da 21 mp3).

A cikin wannan ɗiyan waƙar ya kawo inda allah ya halicci annabi yana ta bautawar allah a cikin hijaban ubangiji ya daɗe da halittarsa kuma yana bauta masa, har sai da allah ya mayar da ibadar ta zamo siffar sunansa. Wato lokacin da allah ya yi nufin halittar ɗan adam, sai aka halicce shi da siffar sunan annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama daga cikin hasken da allah ya halicce shi. Ga abin da shehi y ace:

Jagora: Aka fara ƙaddara Adamu domin fitar da jikinka,

:Aka yi masa suffa da irin sunanka,

:Mimun ha’un mimum dalun in dauwamarka,

Jagora: Sai ya hau aiki ya samu hauwa’u alfarka,

:Su ka shiga jannatul fiddausi gidan ni’imarka,

:Aka yi abin da aka yi sha’anin akwai wata harka.

(waƙa salamu alaika ɗa na 23 da 24 mp3).

A cikin waɗannan ɗiyan waƙa ya bayyana allah subahanahu wa ta’ala ya fara halittar annabi Adamu domin ya halicci ɗan adam a doran duniya, wanda duk mutanen duniya ta tsatson annabi Adamu suka fito. Kuma allah subahanahu wa ta’ala da ya halicce ɗan adam sai ya yi masa siffa da irin sunan annabin Muhammadu, sallallahu alaihi wa sallama cikamakin annabawa wato mimun ha’un mimun dalun. Daga nan sai allah ya halicci hauwa’u daga ƙashin kirjin annabi Adamu wannan duk ya faru ne alfarmar annabin tsira. Sai allah ya saka su cikin aljannar firdausi su zauna. Daga nan sai allah ya halicci shitu wanda hakan yana nunawa annabi Muhammadu sallallahu alahi wa sallama shi ne zai bayyana a ƙarshen annabawa.

Jagora : Tafiya tana tafiya aka haifo shitu ba shi da sani,

:Koma bayan yadda aka saba a cikin ikiwani,

:To a nan aka gane akwai babbar harka.

Jagora: Ya zahirin daga nan ne sai ka fara zagaya garinka,

:Ka na ta juyawa a mahaifa wadda ba ta shirka,

:Kana biyo zamanai domain cikar sharaɗinka.

Jagora :A kwana a tashi sai ibrahima ya ɗauka,

:Har ka ba shi salama randa ya haɗu da dabar shirka,

:Ba ka barshi ba har sai da ya gina maka daularka.

(waƙar salamu alaika ɗa na 26 da 27 da 29 mp3).

A nan, Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana allah subahanahu wa ta’ala ya halicci annabi Ibrahim wanda da ya haɗu da dabar shirka sai da allah ya ba shi mafita kuma ya kare shi daga wutar da suka sanya shi a ciki don su halakar da shi. Annabi ibrahim bai gushe ba har sai da ya gina ka’aba a makka wanda yanzu ake bautar allah a wurinta. Shehi ya kawo waɗannan:

Jagora :Daga nan sai babban baba ya ce da umma,

:A samu mai matar kirki ma’ana mai himma,

:Da ma da akwai haka lokaci ne ya sauka, jagora : aka yi juyi sai aka yi cikinsa akwai ƙasaita,

:Harka ya yi tajalli ina maganar annabta,

:Sai rabi’ul auwalu ta zo mana barka.

(waƙar salamu alaika ɗa na 31 da 32 mp3).

A wannan ɗiyan waƙoƙin Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana kakan annabi abdulmuɗallib ya ce a samo wa mahaifin annabi matar aure wanda bayan an yi masa aure aka sami cikin annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama wanda aka haife shi a watan rabi’ul auwal sha biyu ga ranar litinin. A wannan rana haƙiƙa anga abin mamaki a wannan rana da aka haifi annabin annabawa, wanda kowa albarkacinsa yake ci . Allah ka yi salati ga shugaba annabi Muhammad sallalahu alaihi wa sallama. Shehi ya ƙara da cewa:

Jagora: Sannu da zuwa ga ka ka zo arabiyyu abdayyu,

:Sannu da zuwa hashimiyyu arabiyyu ƙuraishiyyu,

:Barka da sauka mafi tsarkin nasaba mafi alfarma,

:Barka da sauka mai babban burni ƙiyasul umma,

:Barka da sauka mai tutar shiriya runfar salama,

:Barka da sauka ya gatan aiki baiti na ke ma,

:Barka da sauka ainin ni’ima da salama,

:Ka yarda na ganka cikin siffar girmanka.

(waƙar salamu alaika ɗa na 33 mp3).

A nan, Ahmad Muhammad Shehi ya yi wa annabi barka da zuwa wannan duniyar da kuma jinjina a gare shi. Sannan kuma ya bayyana annabi balarabe ne, kuma ɗan ƙabilar ƙuraishawa. Kuma annabi shi ne mafi tsarkin annabawa mafi alfarma. Shehi ya bayyana annabi aka ba wa tutar shiriya da al’ummarsa tare da salama. Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama shi ne ni’ima ga kowa sannan shi salama ne ga mutane baki ɗaya. Shehi ya yi roƙo da allah ya sa ya ga annabi cikin siffar girmansa.

6.0 Tubalin Kyawun Ɗabi'a

Ahmad Muhammad Shehi yana amfani da wannan tubalan gurin gina waƙoƙinsa. Yana

Faɗar kyawun ɗabi’ar annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama. Ga abin da ya ce:

Jagora : Kyan ɗabi’a sai saduƙul amin,

: Tausayi sai akramul akrami

: Haƙuri sai akramul amin,

: Duk kyan tadodi sun taru a gurinka.

‘Y/ amshi: Ya rasulullah musɗafal arabi labbaika.

(waƙar musɗafal arabi ɗa na 25 mp3).

A nan, annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama yana da kyan ɗabi’a ga tausayi ga al’ummarsa. Sannan ga haƙuri da duk mutanan da suka yi masa wauta. Kuma sai ya yi musu addu’a akan allah ya shirya su don ba su san shi annabin allah ba ne.

Jarumtaka:

Ahmad Muhammad Shehi a cikin waƙoƙinsa ya kan yi amfani da tubulin jarunta domin ya faɗi jarumtakar annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam a gurin yaƙi. Misali

Jagora : Sarkin yana burge ni idan na hango shi can da takobi,

:Wannan ke nan ya kuma idan ya yi danƙa da hannun rabbi,

:Sarki kusama ke nan kaga sirrin haske rabbi,

:Ya raƙibul ƙasuwa a hawanka ba irin na kowa ne ba.

Jagora : Sallama ga mafi ƙarfi a dantsan nan.

: Sallama ga mafi kashe kafire a gurin yaƙin nan.

(waƙar labbaika ɗa na 16 mp3).

A misalin ɗiyan waƙar da aka kawo a sama, Ahmad Muhammad Shehi ya nuna annabi yana burge shi a lokacin da ake bayar da tarihi ya ɗauki takobi, sannan kuma a lokacin da yaƙi allah da kansa ya ce shi ya yi wannan. Sannan ya kuma cewa allah ya ƙara sallama ga mafi ƙarfin dantsen wato annabi Muhammad shi ne yake da dantse da yafi na kowa. Sannan annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama shi ya fi kowa kashe kafirai a gurin yaƙi daga ya kai sara sai ɗai kawuna su dunga faɗuwa.

7.0 Tubalin Kyawon Halitta

A cikin irin waƙoƙin yabo da Ahmad Muhammad Shehi ya ke yi yana faɗar irin kyawun halitta da allah ya yi wa annabin ƙarshen zamani wato annabi Muhammad sallallahu Alaihi wa sallama wanda ba a yi wa wani annabi kafinsa ba. Shi ne ƙarshan kyau, duk wani mai taƙama da kyawo a ƙasansa yake. Misali :

Jagora : Mai mulkin duk duniya ƙiyama sarki ne kai munzali,

: Kai ne mai ido ga kyallin fuska ga ka da ƙyalƙyali,

:Ga ka da tsarin girarka ga idonka da tozali,

: Kyautar kyau kai ne ka fara ban ji waninka ba,

'Y/amshi : Ya gayatul huna yabonka ba za na bar shi ba.

(waƙar ya gayatul huna ɗa na 10 mp3).

Ga wani ɗa:

Jagora : Mai mabayyanin launi siffarka ba irin siffa ba,

: Ga ka da jiki sai dai ban ji jikinka ya yi inuwa ba,

: Ga shi in ka taka ƙasa sawunka ba zai yo sheda ba,

: Zai riƙa idanun shi zai ga duk abin da ake saƙawa.

'Y/amshi : labbaika masani wanda ilahu ya ke yi wa tarba.

(waƙar labbaika ɗa na 14 mp3).

A ɗiyan waƙoƙin da suke a sama Ahmad Muhammad Shehi ya bayyana annabi Muhammadsallallahu alaihi wa sallama shi ne mai mulkin duk duniya har da ƙiyama. Sannan kuma ga shi da kyawon ido, fuskarsa ɗauke da kyalkyali, kuma girar annbai mai tsari ba irin ta kowa ce ba. Annabi shi ya yi kyautar kyau. Ya kuma launin siffar annabi ba irin ta kowa ce ba, kuma jikin annabi ba ya inuwa kamar yadda na sauran mutane ya ke yin inuwa. Annabin tsiya idan ya taka ƙasa sawun ƙafarsa ba ya fitowa.

Ahamad Muhammad shehi a cikin waƙarsa ta musɗafal arabi ya kuma bayyana kyawon halitta na annabi Muhammad tsira da amincin allah su ƙara tabbata a gare shi. Misali

Jagora : Balaraben allah kuma mujauhari,

: Mai gogar giyar fata ja madorari,

:Antal zainun akyari,

:Babu gwanin da za ya bayyana kyawunka.

'Y/amshi: Ya rasulullah musɗafal arabi labbaika.

(waƙar musɗafal arabi ɗa na 23 mp3).

A nan, ya bayyana annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama balarabe ne, kuma bawan allah mujauhari. Annabi tsira ƙirar fatarsa mai kyau ce da kuma santsi ba irin ta kowa ce ba. Duk wani kyau na kyawon halitta ya tabbata a gurinsa.

8.0 kammalawa

A wannan takarda an yi magana ne game da tubalan ginin turke na waƙar Ahmad Muhammad Shehi ta yabon annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama. An kawo misalan ire-iren tubalan ginin turke da ke cikin wannan waƙa. Kamar yadda aka lura a takardar nan, Ahmad Muhammad Shehi yana amfani da dabaru na jefa ƙananan saƙonni a zubin waƙar. Ta haka ne ya saƙa ƙananan saƙonni waɗanda suka da ce da babban turke na wannan waƙa masu nuna irin daraja da matsayi da annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama da kuma son da yake yi wa annabi Muhammad, sallallahu alaihi wa sallama yana kuma bayyanawa mutane da su so shi domin shi ne mafita a duniya da lahira. Kuma addini baya cika sai an ambace shi.

Manazarta

Abbas, U.A. (2021). Warwarar tubalan ninin turken waƙar almajiri ta haruna aliyu ningi. yojallac: yobe journal of language literature and culture, 9 (1) 245:252

Adamu, T.M (2011). Nazarin a kan waƙoƙin yabon annabi sallallahu alaihi wa sallam. kundi na goma sha shida zuwa na goma sha bakwai, takardun tattaunawa ɗaliban hau 3304. sashin koyar da harsunan nijeria, jami’ar bayero.

Bargery, G.P (1934). Hausa english dictionary. Oɗford University press.

Bunza, A.M (20009). Narambaɗa. Ibrashi islamic

CNHN, (2006). Hausa dictionary. Jami’ar bayero kano.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar gadon feɗe waƙa (sabon tari): k.d.g publisher limited

Gusau, S.M (2002). Salihu jankiɗi: sarkin taushi. Baraka publisher limited

Gusau, S .M (2008a). Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Benchmark Publisher

Gusau, S .M (2008b). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa. Benchmark Publisher.

Gusau, s.m (2014). Waƙar Baka Bahaushiya. Bayero University, Publisher.

Gusau, S. M (2003). Jagoran Nazarin Waƙa. Benchmark Publisher Limited

Halima, I (2015). Tarken Turken Koɗa Kai Da Yabo A Waƙoƙin Alhaji Dr. Manman Shata.

Kundin digiri na biyu. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeria, Jam’ar Bayero, Kano.

King, A. Ɓ (1980). Statement restatement and extension: stanzaic structure in Hausa Court Songs’ takardar wadda ya gabatar Zaria: Sashen Harsunan Nijeria Africa Jami’ar Ahmadu Bello.

Lawan, N da Magaji, A (2018). Ƙalailaice Tubalan Ginin Turke a Waƙoƙin Bege na Hausa. Journal of Multi Disciplinary Studies v.3, no 1.

Satatima, I. G (2009). Waƙoƙin Ɗarsashin Zuciya na Makaɗan Baka. Kundin Digiri na Uku Sashin Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Rubutattun waƙoƙi

________________________

Ɓiew other publications of the Department of Nigerian Languages, UDUS at: https://www.dundaye.com

Post a Comment

0 Comments