Ticker

6/recent/ticker-posts

Tatsuniya a Mahangar Mawaka: Nazarin Siffofi Da Muhallan Tatsuniya a Rubutattun Wakokin Hausa

Citation: Anka, Y.H. and Jangebe, S.A. (2024). Tatsuniya a Mahangar Mawaƙa: Nazarin Siffofi da Muhallan Tatsuniya a Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 515-520. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.063.

TATSUNIYA A MAHANGAR MAWAƘA: NAZARIN SIFFOFI DA MUHALLAN TATSUNIYA A RUBUTATTUN WAƘOƘIN HAUSA

Yuhanazu Halilu Anka

Da

Shu’aibu Abdullahi Jangebe

Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Kimiyya Da Fsaha (ZACAS), Gusau, Jihar Zamfara

Tsakure

Marubuta waƙoƙin Hausa kan yi amfani da siffar tatsuniya a cikin waƙoƙinsu domin kawo nishaɗi, da wurin faɗakarwa da ilmantarwa. Haka kuma a waɗansu lokuta sukan riƙa bayyana halayyar rayuwar mutane a cikin waƙa ta hanyar sanya muhallin tatsuniya don bayyana hoton rayuwa a cikin bayani. Abin shaawa tattare da wannan, shi ne a kan sami marubucin waƙa ya shirya waƙarsa domin ilmantarwa ko nishaɗi ko faɗakarwa sai a ci karo da tun a farkon waƙar ya tsara ta cikin sigar tatsuniya ko kuma cikin waƙar sai a ci karo da wasu baitoci da ke ɗauke da sigar tatsuniya.

Fitilun Kalmomi: Tatsuniya, Mawaƙa, Siffofi da Muhallai, Rubutattun Waƙoƙi

Gabatarwa

Masana da manazarta sun bayyana abin da ake cewa tatsuniya, wata hanya ce ta dabara, wadda ake sarrafa harshe tare da ƙuƙƙula wasu maganganu na basira cikin azanci domin isar da wani saƙo ko cimma wani buri (Muhammad 2003:5). Haka kuma tatsuniya ƙagaggen labari ne da aka shirya game da ‘gizo’ ko waninsa da ya ƙunshi wani darasi ko ya cim ma wata manufa ta musamman cikin hikima (Ɗangambo1978:28). Haƙiƙa waɗannan ma;anoni sun fito da ma’anar tatsuniya. Don haka, tatsuniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musammamn tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare. Maƙasudin nazarin shi ne ya duba ire-iren tatsuniya da marubuta waƙa sukan sa cikin waƙoƙinsu. Da yadda mawaƙa ke amfani da siffofin tatsuniya ta hanyar gutsure su da yin ishara gare su wanda kan tunatar wa mai saurare da tatsuniya da makamantan haka. Haka kuma, bincike zai yi ƙoƙari wajen gano wuraren da ake samun tatsuniya tare da kawo muhimmancin tasuniya a cikin rubutattun waƙoƙi.

1.0.Ire-Iren Tatsuniya Da Aka Fi Samu A Rubutattun Waƙoƙi

Mafi yawancin masana adabin Hausa sun karkasa tatsuniya zuwa gida biyu, tatsuniyar labari da tatsuniyar kacici-kacici. Dalilin wannan kaso na da alaƙa da lokacin da ake yin waɗannan abubuwa ya zama kusan kamar ɗaya ne, amma idan aka dubi ma’anarsu da yanaye yanayensu sun sha banban da juna.

2.1 Tatsuniyar Labari

Tatsuniya mai labari, ita sauraro kawai ake yi, a ji, ba tare da an nemi a ba da amsa ba. Misali tatsuniyoyin da suka shafi ba da labarin dabbobi ko tsuntsaye kamar gizo da ƙoƙi, dodo, zaki, zalɓi, damo da sauransu da yawa. Cikin irin waɗannan tatsuniyoyi akan sami mutane da sauransu. Akan kuma nuna yadda dabbobi ko dodanni, ko abubuwa ke magana ko hulɗa da mutane da sauransu.

2.1.1 Sifofi Da Muhallan Tatsunyar Labari Cikin Rubutacciyar Waƙa

Kamar yadda bayanai suka gabata, daga cikin muhallan tatsuniya su ne ambaton wani ƙursungumin daji, ko bishiyoyi, ƙoramu da falalen dutse, ko kogo ko rami da sauransu. Haka kuma ana ambaton tsuntsaye da dabbobi. A cikin waƙarsa ta “Tutocin Shaihu da waninsa”, Mu’azu Haɗeja ya kawo wasu baitoci (baiti na 43 zuwa na 46) da ke ɗauke da siffar tatsuniya kamar yadda zamu gani a waɗannan baitoci kamar haka:

Ga ƙura can a dawa,

Wata ƙila har da guguwa,

Iska tanakaɗa dawa,

Itatuwa suna rawa,

Allah raba mu lafiya.

Kura ta buɗe baki,

har akuya ta yi kaki,

Sannan ta tofa a ciki,

har ma ta sa kanta ciki,

Ta fid da shi lafiya.

Ka ji abin mamaki,

Ungulu zai kashe maiki,

Dawa za ta ci doki,

kare yi sannu da zaki,

Don juyi na duniya.

Ga kura ga zaki,

Ga ungulu ga maiki,

Ga wani mushen doki,

‘Yan kallo ka ja jiki,

 Ku zakuɗa waje ɗaya.

Haƙiƙa idan muka yi la’akari da tsarin waɗannan baitoci, za mu tabbatar cewa Mu’azu Haɗeja ya kawo siffofin tatsuniya domin yin ishara ga mai sauraro, wanda hakan kan tunatar da mai sauraro ko karanta waƙar da cewa waɗannan baitoci ɗauke suke da siffar tatsuniya. Ya ƙara kawo wani baiti (baiti na 52) duk a cikin waƙar da ke ɗauke da siffar tatsuniya kamar haka:

 

Abin ga ko da gaskiya,

Kura ta iske tunkiya,

Ta ce su je su tsariya,

Akwai tuwo akwai miya,

Su yi shagali na duniya.

Wannan baiti ɗauke yake da siffar tatsuniya, da yake tunatar da mai karatu tatsuniya. Domin mafi yawan siffar tatsuniyar labari ba ta wuce tsakanin kura da wata dabbar kamar tunkiya da aka ambata.

Haka kuma, cikin waƙarsa ta “Gaskiya Ba Ta Sake Gashi”. Mu’azu Haɗeja ya ƙara kawo wasu baitoci masu ɗauke da siffar ta tatsuniya a muhallin waƙa, kamar yadda zamu gani a baiti na 74-75.

Da abin dariya da na mamaki,

Ba sa ƙarewa ba shakka,

Wakura ce aka ce ta tu-

Ba da sata don tsoron halaka.

Makiyayi sai ya amince har,

Ya kafa mata turke cikin maruƙa.

Waɗannan baitoci sun fito ƙarara sun tunatar da mai karatu tatsuniyar labarin kura da halayenta na ƙarya da saɓa alƙawali. Ke nan waɗannan baitoci ɗauke suke da siffar tatsuniya.

Wannan siffa tatatsuniya ta ƙara fitowa a cikin wata waƙa mai suna “waƙar tsuntsayen zamani”. Ta Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu. Ga abin da yake cewa:

Bayan haka za ni bayani,

Bisa tsuntsayen zamani,

Na san har masu muƙami,

Na san halinsu yaƙini,

 Ya ahi luro da ishara

Na zo yawo can daji,

Sai na iske wani gamji,

Da gije yay o masa gamji,

Daga nesa kamar wani juji,

 Tsuntsaye gasu kasiran.

Can nig ga abin mamaki,

Don ga tsuntsayen kirki,

Jinjimi gaba ga maiki,

Mis sa kolo shi yi mulki,

 In ban da hali na tijara.

Idan aka duba waɗannan baitoci za mu ga cewa an ambaci sunayen tsuntsaye da yanayin zamansu a daji da bishiyoyi, wanda duka siffa ce daga cikin siffofin tatsuniya.

A cikin waƙar “Azancin Waƙa” wadda Audu Sha’iri Gwandu ya rubuta. Ya kwao baitoci da dama da ke ɗauke da siffar tatsuniya da ke iya tunatar da mai karatu da tatsuniya, kamar yadda za mu gani a waɗannan baitoci (baiti na 11 da 12):

Ƙarya da ta kai ga halin suka,

Ta kilme kunya da son taimaka,

Da nuna sai gaskiya ta fake,

Nan ƙeta ta zamna ta haskaka,

 Dut galibin diddigi ya zaka.

Ta ɗan yaƙinta za ta hari,

Ƙaramcinta algushshu kakari

Barden lifiddanta alfahari,

Shi ya ci mai yaƙi don kuɗuri.

An sake kawo irin wannan misali a baiti na 16 layi na ɗaya da na biyu kamar haka:

Algargi ya tashi ya zabura,

Gungumaɗa ta shigo ɗamara.

A nan, an yi amfani da siffar tatsuniya ta hanyar amfani da wasu nau’in tsuntsaye wato, Algargi da Gugumada. Ya ɗara kawo wasu baitoci (baiti na 19 da 20 ) da ke ɗauke da muhallin tatsuniya kamar haka:

Kururuwa ta bi hanya zuwa,

Dan kwarmato caka kai guguwa,

Ta ɗaura son jan kurum kokewa,

Shi bai taɓa ba da ya yi nawa,

 Ta iske ance suna hauhawa.

Ta gangara za ta bata zama,

Birninta shakka k azan fahima,

Soronta babaguma rigima,

Ta hau kilishin yawan tantama,

 Tana ba da batun karam.

Waɗannan baitoci an yi amfani da siffar tatsuniya wajen nuna cewa kururuwa ta kama hanya za ta je wajen kwarmato.Wanda ya nuna cewa kururuwa ba mutum bace amma a muhalli na tatsuniya ya nuna cewa kururuwa ita ce ke yin halayya ta mutane. Wannan waƙa an gina ta kan muhallin tatsuniya ta hanyar amfani da kalmomin shaguɓe domin habaici ga wasu gungun mutane. A nan za a iya cewa kalmomin shaguɓe da habaici suna ɗaya daga cikin azancin harshe wanda tatsuniya na ɓangaren adabin baka.

Cikin waƙarsa ta “Maraba da ‘yanci”, Alhaji Na’ibi Sulaiman Wali, ya kawo wasu baitoci da ke ɗauke da siffar tatsuniya kamar haka:

Kuma na ga tsuntsaye suna waƙa tasu,

Ganyayyakin bishiya suna tafa musu,

Waƙa da tafi babu sulu ba musu,

Kowa ya ji su lakan yana sara musu,

 Bishiyar cikin rafi tana yin rausaya.

Har ƙoramu dai ka ga sun saka gudu,

‘Yar-yar kamar mai tona ramin kurkudu,

Tamkar macizai ƙanƙanan na gudu,

Jejjere an koro su sun yi wajen kudu,

 Don razana a cikinsu ba mai waiwaya.

Tsuntsu ina so in ji amsa ka jiya,

Shin mai ya sassaka su, nai maka tambaya,

Koni na sake ne nace duk duniya?

Amsa da tsuntsun nan ya bani farat ɗaya,

 Ya ce da ni ‘yancin Arewa gaba ɗaya.

A nan, mun ga cewa wata siffa da tatsuniya take ɗauke da ita na ambaton tsuntsaye da ƙwari da macizai da ƙoramu da ake yi a cin tatsuniya. A waɗannan baitoci ya bayyana mana yadda tsuntsaye ke magana, ga ƙoramu suna gudana tare da bishiyoyi, wanda hakan yana faruwa ne a cikin tatsuniyoyinmu na Hausa.

2.2 Tatsuniyar Kacici-Kacici

Ita wannan tatsuniya tana ƙunsar tambaya ne da amsarta. Amsar tambayar sau da yawa tana yin kama da tambayar, dangane da sauti da ma’ana. Wannan nau’in tatsuniya yar ganuwa mai tambaya da amsa, ana samun wasu daga cikin rubutattun waƙoƙin Hausa da ke ɗauke da siffar tatsuniya yar ganuwa, wato tatsuniyar kacici-kacici. Kamar yadda za mu gani a cikin waƙarsa mai suna “waƙar ƙalubale”, Aƙilu Aliyu ya buɗa waƙar da wannan siffar ta tatsuniyar kacici-kacici. Inda yake cewa:

Ƙulin ƙulufit abu dunƙule,

Ƙalau naƙala ƙalubale.

Ka-cici ka-cici miye abin,

Da ke yaɗo kuma dunɗule?

Ya watsu ya barbazu tattare?

Da rassa ga shi a mulmule?

Haƙiƙa, waɗannan baitoci sun fito ƙarara ɗauke da siffar tatsuniyar kacici-kacici. Wanda marubucin ya yi amfani da muhallin tatsuniya tun a baiti na farko na waƙar. Ko a cikin waƙarsa mai suna “Kadaura Babbar Inuwa” ya ƙara kawo wasu baitoci ta amfani da muhallin tatsuniyar kacici-kacici kamar haka:

Jama’a musa natsuwa a zuci da kunne,

Ya zuwa abin da Aƙilu ke tsarawa.

Taro, ka-cinci-ka-cinci, ko a cinta,

Wace ce ƙazamar rayuwa, mara yalwa?

Ƙam-ta-ƙalai gashi babu mai ko naso,

Dafa babu romo, ko na ɗan lasawa.

A nan, marubucin ya kawo mana siffar tatsuniyar kacici-kacici, wato mai tambaya da amsa. Salihu Kwantagora shi ma ya kawo kwatankwacin haka a cikin waƙarsa mai suna “Ƙulin Ƙulihita” kamar haka:

Ƙulin ƙulihita (gauta),

Matar ƙulihita (yalo),

Ƙulin ƙulihita gauta,

 Maza an sanku da mata.

Ƙulin ɗulihita (gauta),

Matar ƙulihita (yalo),

Matar ƙulihita yalo,

Goge ka rio ko molo,

Tuwo da miya ta kabewa,

A haɗa da muƙakka kalwa.

A nan, mun ga yadda muhallin tatsuniya ya kasance cikin wannan waƙa, ta hanyar tambaya da amsa.

3.0 Muhimmancin Tatsuniya Cikin Rubutattun Waƙoƙi

Tatsuniya wata hanya ce ta dabara, wadda ake sarrafa harshe tare da ƙuƙƙula wasu maganganu na basira cikin azanci domin isar da saƙo ko cimma wani buri. Cikin rubutattun waƙoƙin Hausa a kan ci karo da marubucin waƙar ya yi amfani da muhallin tatsuniya wajen siffanta wani abu domin faɗakarwa ko don ilmantarwa ko don nishaɗantarwa kamar yadda suka zo cikin waƙoƙi mabanbanta kamar haka.

3.1 Faɗakarwa

Faɗakarwa na ɗaya daga cikin muhimmancin tatsuniya a cikin rubutattun waƙoƙi. Tatsuniya tana faɗakarwa zuwa ga yara da ma manya masu saurare, mun ga haka ya fito a waƙar “Azancin Waƙa” wadda Audu Sha’iri Gwandu ya rubuta. Ya kwo baitoci da dama da ke ɗauke da siffar tatsuniya da ke faɗakarwa ga jama’a yara da manya illar ƙarya da kwarmato kamar yadda ya nuna a waɗannan baitoci (baiti na 11 da 12).

Ƙarya da ta kai ga halin suka,

Ta kilme kunya da son taimaka,

Da nuna sai gaskiya ta fake,

Nan ƙeta ta zamna ta haskaka,

 Dut galibin diddigi ya zaka.

Ta ɗan yaƙinta za ta hari,

Ƙaramcinta algushshu kakari

Barden lifiddanta alfahari,

Shi ya ci mai yaƙi don kuɗuri.

An sake kawo irin wannan misali a baiti na 16 layi na ɗaya da na biyu kamar haka:

Algargi ya tashi ya zabura,

Gungumaɗa ta shigo ɗamara.

Ya ƙara kawo wasu baitoci (baiti na 19 da 20 ) da ke ɗauke da muhallin tatsuniya kamar haka:

Kururuwa ta bi hanya zuwa,

Dan kwarmato ca ka kai guguwa,

Ta ɗaura son jan kurum kokewa,

Shi bai taɓa ba da ya yi nawa,

 Ta iske ance suna hauhawa.

Ta gangara za ta bata zama,

Birninta shakka k azan fahima,

Soronta babaguma rigima,

Ta hau kilishin yawan tantama,

 Tana ba da batun karam.

Haƙiƙa an yi amfani da wannan nau’i na tatsuniya cikin waƙa don faɗakar da mutane illar ƙarya da kwarmato.

 

3.2 Ilmantarwa

Ilmantarwa na ɗaya daga cikin manufofin tatsuniya da take isarwa zuwa ga al’umma. Wannan siffa haka take ga rubutattun waƙoƙin Hausa waɗanda ke ɗauke da siffar tatsuniya. Irin wannan misali na ilmantarwa ya fito a cikin waƙoƙi mabambanta da muka kawo cikin wannan muƙala.

Kamar yadda za mu gani a cikin waƙarsa mai suna “Waƙar Ƙalubale”, Aƙilu Aliyu ya yi amfani da wannan siffar ta tatsuniya ta hanyar tambayar mai sauraro da nufin nemo amsa ta hanyar yin zurfin tunani wajen gano amsa kamar haka:

Ƙulin ƙulufit abu dunƙule,

Ƙalau naƙala ƙalubale.

Kaccinci ka-ci: miye abin,

Da ke yaɗo kuma dunɗule?

Ya watsu ya barbazu tattare?

Da rassa ga shi a mulmule?

Muhimmancin ilmi ya sake fitowa duk a cikin misalan da aka bayar na siffar tatsuniyar kacici-kacici, wanda waƙarsa mai suna “Kadaura Babbar Inuwa” ta ƙara tabbatar da haka:

Jama’a musa natsuwa a zuci da kunne,

Ya zuwa abin da Aƙilu ke tsarawa.

Taro, ka-cinci-ka-ci: ko a cinta,

Wace ce ƙazamar rayuwa, mara yalwa?

Ƙam-ta-ƙalai gashi babu mai ko naso,

Dafa babu romo, ko na ɗan lasawa.

Waɗannan baitoci da aka kawo ɗauke suke da siffar tatsuniya mai ilmantarwa zuwa ga yara da manya. A nan, buƙata ake da mai sauraro ya gano amsar tambayar.

3.3 Nishaɗantarwa

Marubuta waƙoƙin Hausa suna da hanyoyi da dama na samar da raha da nishaɗi ga al’ummarsu. Ba abin da ke da muhimmanci a irin waɗannan waƙoƙi da aka cusa tatsuniya ciki illa sa nishaɗida ban dariya, duk kuwa da cewa waƙoƙin ba na ban dariya ba ne gaba ɗayansu ba, sai dai ana samun ɓurɓushin ban dariya da ke ƙara wa waƙar armashi ga mai karanta ko sauraron waƙar.Mu’azu Haɗeja ya kawo wasu baitoci cikin waƙarsa ta “Tutocin Shaihu da Waninsa”.

Kura ta buɗe baki,

Har akuya ta yi kaki,

Sannan ta tofa a ciki,

Har ma ta sa kanta ciki,

 Ta fid da shi lafiya.

Ka ji abin mamaki,

Ungulu zai kashe maiki,

Dawa za ta ci doki,

Kare yi sannu da zaki,

 Don juyi na duniya.

Ga kura ga zaki,

Ga ungulu ga maiki,

Ga wani mushen doki,

‘Yan kallo ka ja jiki,

 Ku zakuɗa waje ɗaya.

Ya ƙara kawo wani baiti (baiti na 52) kamar haka:

Abin ga ko da gaskiya,

Kura ta iske tunkiya,

Ta ce su je su tsariya,

Akwai tuwo akwai miya,

 Su yi shagali na duniya.

Waɗannan baitoci da aka kawo ɗauke suke da nishaɗI ta hanyar sanya raha da ban dariya ga mai sauraro. Da abin mamaki da dariya a ce kura da kanta za ta buɗe baki har akuya ta yi kaki cikin bakinta ba tare da cutarwa ba, ga kuma ungulu za ya kashe maikida ma haɗuwar manyan dawa tare da ƙananan dawa wurin cin mushe an san akwai cakwakiya.

4.0 Kammalawa

Wannan maƙala ta fito mana da siffofi da muhallan tatsuniya a rubutattun waƙoƙin Hausa. Nazarin ya gwada fitowa da ire-iren tatsuniya da ake ganin suna samuwa a cikin waƙoƙi rubutattu da suka haɗa da tatsuniyar labari da tasuniyar ‘yar ganuwa wato kacici-kacici.Muƙalar ta kawo misalan waɗannan nau’o’in tatsuniya cikin waƙa tare da kuma muhimmancin tatsuniya cikin waƙoƙin da suka haɗa da faɗakarwa da ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa. Daga ƙarshe wannan nazari zai taimaka ga manazarta samun madafa wajen faɗaɗa bincike.

Manazarta

Adamu, A (2012) “Sharhin Azancin Waƙa”. Champion of Hausa cikin Hausa, A Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad. Zaria: Ahmadu Bello University press.

Aliyu, A. (1976) FasahaAƙiliya. Zaria: Nothern Nigerian Publication Company.

CNHN/BUK. (1979) Waƙa A Bakin Mai Ita. Zaria: Nothern Nigeria Publication Company.

CNH/JUƊS. (2006) Wa’azu Gonar Malam: Diwanin Waƙoƙin Alhaji (DR) Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu (1916/2000). Sakkwato: University Press.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triump Publishing Company

Ɗan Sidi, A. S. Z.(1980)Waƙoƙin Aliyu Ɗan Sidi Sarkin Zazzau. Zaria: NNPC

Kwantagora, S. (1978) Yula Rubutattun Waƙoƙin Hausa Don Ƙanann Makarantun Firamare Na Jihohin Arewacin Nigeria. Ibadan: Oxford University Press.

Koko, H. S. (2009) JagoranNazarin Tatsuniya. Sakkwato: Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari.

Mu’azu, H. (1970) Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja. Zaria: The Northern Nigerian Publishing Co. Ltd.

Muhammad, Y. M. (2003) Adabin Hausa. Kaduna:Ɗan Idi Publishers.

Na’ibi, S. W. Da Wasu (1972) Waƙoƙin Hausa. Zaria: Nothern Nigerian Publishing Company Ltd.

Omar, S. (2013)Fasahar Mazan Jiya: Nazari A Kan Rayuwa Da Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja. Sokoto: Garkuwa Media Service.

Salihu, K. (1972) Kimiyya da Fasaha Waƙoƙin Hausa guda 5. Zaria: Nothern Nigerian Publishing Company Ltd.

Umar, M. B. (1987) Dangantakar Adabin BakaDa Al’aun Gargajiya. Kano: Triump Publishing.

Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa.kaduna: Fisbas Media Service.

Tatsuniya

Post a Comment

0 Comments