Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarawihi Da Tahajjud A Gida Ko Masallaci Wanne Ya Fi Falala?

A jiya mun ga cewa; ya halasta mutum ya yi Tarawihi - amma ban da Wutri - sai kuma ya yi Tahajjud duka a dare daya. Wannan shi ne Mazhabar Imamu Ahmad, dogaro da fadin Anas bn Malik (ra):

«لا بأس به إنما يرجعون إلى خير يرجونه، ويبرءون من شر يخافونه»

مصنف ابن أبي شيبة (2/ 167)

"Babu laifi ga komawa yin Tahajjud bayan Tarawihi, ai masu yin hakan suna komawa ne ga alheri da suke fata, kuma suke gudun wani sharri da suke tsoro".

Kuma da ma sananne ne yana cikin "Usul" na Mazhabar Ahmad daukar Fiqhu daga maganar Sahabi.

Haka mun ga magana a kan yawaita raka'o'i, cewa; Sahabbai ba su fahimci Annabi (saw) ya kayyade yawan raka'o'in Qiyamu Ramadhan ba. Wannan ya sa tun zamanin Umar (ra) raka'a 20 ake yi a Masallacin Annabi (saw) har yau din nan, haka Ishaq bn Rahuya ya fada cikin:

مسائل الإمام أحمد وإسحاق بن راهويه (2/ 839)

To abin da ya saura shi ne; me ya fi falala tsakanin yin Sallar Tarawihi da Tahajjud a gida da yi a Masallaci?

To ga amsa a kan haka daga Imam Ahmad bn Hanbal.

Imam Abu Dawuda ya ce:

سمعت أحمد، وقيل له: أن يصلي الرجل مع الناس في رمضان أو وحده؟ قال: يصلي مع الناس

وسمعته أيضا، يقول: يعجبني أن يصلي مع الإمام ويوتر معه، قال النبي صلى الله عليه وسلم: «إن الرجل إذا قام مع الإمام حتى ينصرف كتب له بقية ليلته»

مسائل الإمام أحمد رواية أبي داود السجستاني (ص: 90)

"Na ji Imamu Ahmad an tambaye shi: Mutum ya yi Sallah a Ramadhana tare da mutane ko ya yi shi kadai?

Sai ya ce: "Ya yi tare da mutane".

Kuma na ji shi yana cewa: "Ina fifita mutum ya yi Sallah tare da Liman har ya yi wutri tare da shi, saboda Annabi (saw) ya ce:

(Lallai mutum idan ya yi Sallar Qiyamu Ramadhan tare da Liman har ya idar to za a ba shi ladan Sallar daren gaba dayanta)".

Hadisin da ya ambata Hadisi ne ingantacce; Abu Dawud, Tirmiziy, Nasa'iy da Ibnu Majah duka sun ruwaito shi.

Wannan ya sa Shaikhul Islam ya ce:

وبهذا الحديث احتج أحمد وغيره على أن فعلها في الجماعة أفضل من فعلها في حال الانفراد، وفي قوله هذا ترغيب لقيام شهر رمضان خلف الإمام

اقتضاء الصراط المستقيم (2/ 94 - 95)

"Da wannan Hadisi Imamu Ahmad da waninsa suka kafa hujja a kan cewa; yin Tarawihi a cikin jam'i shi ya fi falala a kan yinta mutum shi kadai. Kuma a cikin Hadisin akwai kwadaitarwa ga yin Qiyamu Ramadha tare da Liman a Masallaci".

Saboda haka, wannan shi ne abin da wasu cikin magabata suka fahimta, wato yin Qiyamu Ramadhan (Tarawihi da Tahajjud) a Masallaci tare da Liman ya fi falala, saboda in ka yi tare da Liman tun daga farko har karshe, to kana da ladan daren gaba dayansa.

Don haka, ta yaya za a ce: hada Tarawihi da Tahajjud, ko yi cikin Jam'i a Masallaci, ko yin raka'a fiye da 11 bidi'a ne?!

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments