ƘOƘARIN GANO MASU ƊAUKAR NAUYIN TA'ADDANCI DA SUNAN MUSLUNCI A DUNIYA
Bayanai suna ta kara bayyana, wadanda suke tona asirin masu daukar nauyin ta'addanci a Duniya, ta yadda zuwa yanzu, mutane da yawa sun fita daga tababa a kan haka.
Yanzu abin
da ya saura shi ne abin da ya shafi mabubbugar tunanin ta'addancin. Inda ake
yaudaran mutane masu yawa, ana ce musu -wai- tunanin ta'addancin ya fito ne
daga Ibnu Taimiyya da Muhammad bn Abdulwahhab. Alhali wannan ra'ayi ne wanda
aka gina shi a kan ta'assubanci, da karancin ilimi, da rashin bincike. Wannan
ya sa hatta cikin Malaman Sufaye a wannan zamani suke inkarin jingina bullar
tunanin ta'addancin ga Ibnu Taimiyya, saboda a iya saninsu ga Ibnu Taimiyya ba
su ga ta'addanci a cikin littatafansa ba. Irin su Aliy Gumu'a, tsohon Mufti a
Misra. Da kuma Shaikh Sharif Saleh, shugaban kwamitin Fatawa a Nigeria.
Hatta
jingina haifar da tunanin ta'addancin ga Saudiyya, duk wanda zai yi adalci ya
san cewa; ita Saudiyya sawun barawo ta taka. Ma'ana; tausayin rai ne ya sa ta
yi alaka da wadanda suka haifi tunanin ta'addancin. Asali wadanda manazarta da
Malamai suke danganta haifar da tunanin ta'addancin gare su su ne Sayyid Qutub
- abin da ya dauko daga al-Maududiy - da mabiya na Sayyid Qutub din, wato
Qutbawa suka yi ta renon tunanin har ya iso wannan zamani, aka samar da
al-Qa*ida, Bo.ko Har.am IS.IS da sauransu.
Duk wanda ya
bibiyi silsilan rubutu da muka yi a kan Sayyid Qutub, da "Tarihin Bullar
Ta'addanci" zai ga yadda muka yi bayani, bisa yadda su Dr. Yusuf
al-Qardhawiy, Dr. Muhammad Amarah da sauran manazarta da masana, da masu
bincike a tarihin kungiyoyi suka tabbatar. Haka mun kawo maganganun manyan
kwamandoji na kungiyoyin ta'addanci, wadanda suka tabbatar da cewa sun sha
wannan ra'ayi ne daga littatafan Sayyid Qutub. Kamar su Abdallah Azzam, Ai.man
Zaw.ahir.iy da sauransu.
Abin da ya
shafi Nigeria kuwa, mun tabbatar da cewa; shugabannin Muslim Brothers sun
tabbatar da cewa; sun dauko Akidun ta'addanci ne daga littatafan Sayyid Qutub.
Kuma daga
wancan tafiya Muhammad Yu.su..f ya dauko tunanin.
A takaice,
abin da ya faru da Saudiyya shi ne ta tausaya wa Qutbawa, irin su Muhammad
Qutub, da sauran 'yan Ikhwan, bisa muzgunawa da suke fiskanta daga Jamal
Abdunnasir, sai ta ba su mafaka, ta ba su koyarwa a makarantu da Jami'o'i, da
rike ma'aikatar ilimi. Har ta kai ga ana buga littatafan Sayyid Qutub a ma'aikatar
Gomnati. Haka kuma wadannan mutane, wato Qutbawa suka zama cikin masu tsara
Manhajar karatu. Wannan ya sa aka cakuda koyarwar Shaikh Muhammad bn
Abdulwahhab da na Sayyid Qutb, alhali sun yi hanun riga. Na farko yana tafiya
ne bisa Manhajin Salaf, Ahlus Sunnati wal Jama'a, na biyu kuma yana tafiya kan
Manhajin Khawarijawa. An dauki lokaci mai tsawo Qutbawa suna yada wannan
mummunan Manhaji, har sai bayan harin da aka kai Amurka a 11 Satumba aka gano
abubuwa masu yawa. Kuma tun daga nan Gomnatin Saudiyya ta dauki matakin kakkabe
wancan Manhaji da ake so ya samu gindin zama a Saudiyyan.
Ala ayyi
halin, duk wanda zai yi magana ta adalci, bisa ilimi da bincike na hakika, ya
san cewa; Sayyid Qutub shi ne tushen ta'addanci a wannan zamani, ba Manhajin
Ibnu Taimiyya ko Muhammad bn Abdilwahhab ba.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.