Asalinsa Bagobiri ne domin Kakansa(wanda ya haifi Mahaifinsa) da ake kira Gandau ne ya taso daga Kurawa ta Sabon Birnin Gobir ya dawo garin Dunfawa dake Masarautar Moriki ta Jihar Zamfara ta yau.
Gandau wanda ya
na fawa ya na kuma Kiɗa ne ya haifi Muhammadu /Ahmadu Ganga a Dunfawa.
Muhammadu Ganga ne ya tashi daga Dunfawa ya koma Magarya dake cikin Masarautar
Zurmi inda ya haifi Kassu a shekarar 1910. Sunan Mahaifiyarsa Maimuna /Kande,
shi ne ɗansu na farko sun kuma haifi Balarabe da Nasara duk kuwa da yake sun
riga Kassu (yayansu/wansu) rasuwa.
Sunansa na yanka
shi ne Abubakar ana kuma yi masa kinaya da Mai Kasuwa ko Kassu saboda an haife
shi a ranar Lahadi ne, wato ranar da Kasuwar wani gari dake kusa da
garinsu da ake kira Dauran ke ci.
Ya girma a garin
Kadawa inda suka koma daga baya shi da mahaifinsu da sauran iyalin daga baya
kuma Mahaifin nasa ya baro shi a Kadawa ya sake dawowa Magarya. A Kadawa ne
Kassu ya ci gaba da rayuwa har ya zuwa wafatinsa sanadiyar jinyar da ya yi fama
da ita a shekarar 1983 yana da shekaru 73 a duniya, ya bar matan aure 4 da
'ya'ya 12, 6 Maza, 6 Mata. Wasu daga cikinsu sun rasu, waɗanda ke raye a halin
yanzu sune Mal. Namakka da Mal. Rabi'u (wanda Makaho ne) da kuma Mal. Aliyu
dake wa'azi a Masallacin Jumu'a na garin Kadawa kafin Limamin Masallacin ya
iso.
Ya yi karatun
allo amma bai yi na zamani ba. Ya soma Kiɗa da waƙa tun yana da kimanin shekaru
15 a duniya. Kiɗan noma ne ya fara dashi da Ganga kafin daga baya ya fara Kiɗan
Farauta da Tauri da na Ɓarayi.
Wanda ya fara
yiwa Kiɗan noma shi ne Ƙwazo ɗan Sani, Sarki Bahago ne ya fara yiwa Kiɗan
farauta, Garugaru ne Ɗan Tauri na farko da ya fara yiwa Kiɗan Tauri yayin da
ban samu Ɓarawon da ya fara yiwa Waƙa ta farko ba.
Bayan Kiɗa da
waƙa Kassu Zurmi ya na yin noma da kiyo domin rufawa kansa asiri. Tsakanin
Manoma da Mafarauta da Yan Tauri da Ɓarayi da wasu ɗaiɗaikun mutane Kassu Zurmi
ya waƙe fiye da mutane 800 duk kuwa da yake ba duka bane za a samu Waƙoƙinsa naɗe
a fayafayi ba.
Sanadiyar wani ɗan
Tauri da aka yi a Funtua ta Jihar Katsina mai suna Alhaji Isah ne ya sadu da
Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina har ma ƙauna da soyayya ta ƙullu a tsakaninsu
inda Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina ya biya masa kujera ya tafi Kasar Saudiya
ya yi aikin Hajji a shekarar 1973.
Duk da yake wasu
jama'a ciki kuwa har da masana ilimin zamani da manazarta suna yi masa wani
kallo na mutumen da bai kamata a karrama da irin wannan taro ba, sai ina ganin
wannan ra'ayi nasu ya ci karo da na wasu jama'ar, musamman waɗanda suka yi
dandazo a wannan Taro da aka yi a Jami'ar Jihar Sakkwato daga 18 zuwa 21 ga
watan Afrilun 2025 ko dai domin gabatar
da Muƙalunsu ko domin sauraren abubuwan da suka wakana.
Ana kiransa da
Kassu Zurmi a maimakon Kassu Magarya ko Kassu Kadawa domin Zurmi ce hedikwatar
Masarautar dake kula da Magarya da Kadawa. Ya gaji/gadi Kiɗa ne daga Mahaifinsa
Muhammadu Ganga/Ahmadu wanda shi ma ya gada ne daga Mahaifinsa Gandau.
Da wannan nike
fatar Maigirma Alhaji Dikko Bala Ƙofar Sauri, Katsina ya samu wani ɗan bayani
daga cikin bayanan da yake nema akan Marigayi Alhaji Abubakar Muhammadu /Ahmadu
Kassu Zurmi. Allah ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau
da imani, amin.
Daga alƙalamin:
Alh. Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
Alhamis,
24/04/2025.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.