TAƘAITACCEN TARIHIN GIDAN SU MARIGAYI SHEIKH (DR.) ALIYU NAMANGI DA SANADIYANR RASA IDANUNSA
Bincike ya nunar da cewa asalin garin Kakannin Aliyu Namangi shi ne Jibiya da ke cikin Jahar Katsina a yanzu. Sun taso sun komo kasar Zazzau ne a zamanin mulki sarkin Zazzau Hammada, wato a wajen shekara ta dubu daya da dari takwas da arba'in da shida, 1846. Masihiyya. Malam Muhammudu Attammu, wato Kakan Aliyu Namangi shi ne ya fara zuwa Zariya da zama.
Zuriyar Muhammudu
Attammu, wato Kakan Aliyu Namangi suna
daga cikin magadan sarautar Jibiya. Saboda kalubale da surkulle da ke cikin
neman sarauta shi ne ya sabbaba masu bari garin Jibiya inda suka watsu cikin
duniya. Wasu sun nufi wajen Kano wasu kuwa suka danno zuwa Zariya. A cikin wadanda suka nufo Zariya har da Kakan
Aliyu Namangi Muhammudu Attammu. A yayin da suka iso Zariya sun zauna ne a
Anguwar Limanci a cikin birnin Zariya.
Ba wani abu ya dawo
da Iyayen Aliyu Namangi, garin Mangi da zama ba, illa nadin da aka yi wa Kakan
Aliyu Namangi, wato Muhammudu Attammu da sarkin Mangi mai ci a wancan lokacin
ya yi masa a matsayisa sarkin yara Magajin gari Mangi, Mangi na wannan lokacin
mai mulki ana kiransa Magaji Daudu.
Mahaifin Aliyu
Namangi Malam Ishaka ya sami sarautar Mangi bayan an fitar da Magajin Mangi
wanda ya gaji Daudu, wato Isa. Sarkin Zazzau Yero ne ya nada shi a matsayin
Magajin Mangi.
Malam Ishaka mahaifin
Aliyu Namangi bayan da ya yi aure ya dauki tsawon lokaci, Allah bai ba shi
haihuwa ba. Wannan ya sa Malam Ishak ya damu kwarai da gaske saboda rashin
haihuwa matarsa. A matsayisa na dan sarki kuma ga shi magajin gari, in har ba
shi da dan lallai zai kasance ba shi da magaji kenan a nan gaba.
Akwana a tashi wata
rana sai wani bako ya ziyarci Malam Ishak. Saboda rashin dan sai Malam Ishaka
ya rinka yi wa bakon nan hidima da kansa a cikin gida a matsayinsa na magajin
gari. Bayan wani lokaci sai malamin nan ya lura da cewa bai ga yara suna Zirga-Zirgan
a cikin gidan Malam Ishaka ba, kamar yadda ake yi a sauran gidan masu sarauta.
Sai bakon Malamin nan ya ce Wai babu yara a gida nan ne? Sai Malam Ishaka ya ce ai ni Allah bai taba
ba ni haihuwa ba. Sai Malamin ya ce Allah Sarki, akwai wata Addu'a wacce idan
na yi ta da yardan Allah matarka za ta dauki ciki. Sai Malam Ishaka ya ce To
Malam ai sai a taimaka mana, Malami ya ce To za a kokarta a cikin dare da
yardar Allah.
Bayan da gari ya waye
sai Malam Ishaka ya kawo wa bakon nan abincin karyawa. Bayan da ya gama kalaci
sai ya tambayi Malamin nan Malam ko an
sami damar yin addu'ar kuwa? Sai Malamin
ya ce lallai kam na yi addu'a kuma za ka sami dan da yarda Allah amma kuma abin
da aka nuna mani makaho ne Allah zai ba ka A lokacin da ake yi wa Malam Ishaka
wannan bushara ta samun dan makaho suna tare da wani abokinsa ne. Sai wannan
abokin nasa ya budi ya ce Yallabai me za ka yi da makaho?
Sai Malam Ishaka ya
ce Ni a wurina in dai makahon nan mai albarka ne, to na gode wa Allah. Bayan
kwana yan kwanaki sai Malamin nan ya koma inda ya fito.
A kwana a tashi ran
nan sai matar Malam Ishak Huraira ta sami ciki bayan wata tara sai ta haifi
danta namiji sambalele. Koda aka duba sai aka gan shi da idanuwansa guda biyu
tangararan. Sai Malam Ishak ya ce Allah da ikonsa Malamin nan ya ce Za a haifi
makaho amma ga shi an sami mai gani, Da
rana ta kewayo aka rada wa jariri suna Aliyu.
Haƙƙin
Mallaka: "ƘASAR ZAZZAU JIYA DA
YAU"
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.