Ticker

6/recent/ticker-posts

Takaitaccen Tarihin Hassan Sarkin Dogarai Kano

TAƘAITACCEN TARIHIN HASSAN SARKIN DOGARAI KANO

Hassan Adamu, da aka fi sani da Hassan sarkin Dogarai, shi ne sarkin Dogarai na uku da marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya naɗa a mastayin shugaban dogaran sarki a shekarar 1990.

Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya; Dan-Wudil da Adamu, kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan, sannan shi ma bayan mutuwarsa aka nada sarkin Dogarai na yanzu, Danbala.

Saidai sabanin sarkin dogarai Adamu da Dan-Wudil, Hassan ba bafade bane. Asalinsa direba ne dake sana’ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga galadiman Kano, Marigayi Tijjani Hashim, mutumin da ya fara nada shi a matsayin shamakinsa kuma ya zama silar shigar sa cikin fadar Kano.

A shekarar 1990 ne, bayan mutuwar sarkin Dogarai Dan-Wudil, Marigayi Tijjani Hashim ya roki sarkin Kano Ado alfarmar ya nada Hassan a matsayin sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyar sa da kuma jarumtar sa, sannan ga soyayya da yake nunawa ga sarkin.

Marigayi Hassan na zaune ne da iyalinsa a unguwar Sagagi, kusa da gidan mahaifiyar Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma unguwar gidan sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, daf da gidan sarkin Kano.

Hassan ya yi shura a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda ƙarfi da jarumta da kuma tsananin biyayyarsa ga sarkin Kano Ado.

Hassan sarkacecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya.

Wani ɗan asalin unguwar Dogarai, Ibrahim Mu’azzam Sadauki, da ya san marigayi Hassan, ya shaidawa shafin tarihin kano cewar, Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausa, Alh DR Mamman Shata, yayin da yake sana’ar sa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama sarkin Dogarai ne, Shata ya rera masa waƙar “Hassan Sarkin Dogarai”, waƙar da ta kara ɗaukaka sunan Hassan a faɗin Duniya.

Yanzu haka iyalan Hassan sun koma gidansa dake unguwar Sagagi inda suka cigaba da rayuwa bayan mutuwar mahaifinsu.

An ɗauko wannan labari daga zauren WhatsApp na amsoshi.com.

Hassan Sarkin Dogarai

Post a Comment

0 Comments