Ticker

6/recent/ticker-posts

Tanadin Tatsuniyoyin Hausa Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya

Citation: Shehu, M and Aliyu, L. (2024). Tanadin Tatsuniyoyin Hausa wajen Tabbatar da Zaman Lafiya. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 188-197. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.022.

TANADIN TATSUNIYOYIN HAUSA WAJEN TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA

Musa Shehu
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

Lauwali Aliyu
Department of Hausa
Adamu Augie College of Education, Argungu

Tsakure:

Hausawa na cewa “zaman lafiya mai daɗi”. Tatsuniya tana daga cikin fannonin adabi da suka game duniya baki ɗaya, saboda a kowane harshe da ke cikin faɗin duniya komai ƙanƙantarsa da rashin yawan masu amfani da shi ana samun tatsuniya a cikinsa. (Dorson 1972 a cikin Koko 2009). Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu tatsuniyoyin Hausa a yi fashin baƙinsu dangane da saƙon zaman lafiya da suke ɗauke da shi. Saboda haka, takardar ta fito da wasu ginshiƙan samar da zaman lafiya  da ke cikin wasu tatsuniyoyin waɗanda suka haɗa da riƙon amana da adalci da haƙuri da alkawali da yafiya da kuma haɗin kai don a gudu tare a tsira tare.

Fitilun Kalmomi: Gudunmuwa, Zaman Lafiya, Tatsuniya

Gabatarwa

Tatsuniya na daga cikin manyan sassan adabin bakan Hausawa wanda suke taƙama da su tun zamanin zamunna. Tatsuniya ta kasance makaranta ta farko ta koyar da Hausawa tarbiyya tagari da kyakkyawar zamantakewar rayuwar duniya. Muhimmancin tatsuniya a rayuwar Hausawa abu ne da ya fi ƙarfin a bayyana, sai dai a faɗi albarkacin baki a shafa fatiha a watse. Tatsuniya tana ilmantarwa wajen shiryar da yara yanayin zaman duniya da halin rayuwa da iya zamantakewa da sanin tarihin wasu abubuwa da rayar da halayen al’umma daga kaka zuwa tattaɓa kunne. Haka ma, tana iya kasancewa hanyar sadar da ilimi, ma’adinin al’adu, haɓaka al’adu, matakan tsaro, madubin rayuwa, nishaɗi, iya siyasa, haɓaka harshe da raya shi, cusa tarbiyya ga yara da sauransu. Dangane da sha’anin zaman lafiya da sasantawa kuwa, tatsuniya ta yi rawar gani wajen daidaita akalar rayuwar Hausawa, domin kuwa akwai tatsuniyoyi masu tarin yawa waɗanda ke nuni da yadda ake zama lafiya da sasantawa idan wata matsala ta kunno kai.

Tatsuniya na daga cikin fannonin adabi da suka game duniya baki ɗaya, saboda a kowane harshe da ke cikin faɗin duniya komai ƙanƙantarsa da rashin yawan masu amfani da shi ana samun tatsuniya a cikinsa. (Dorson 1972 a cikin Koko 2009). Wannan kuwa bai rasa nasaba da cewa, kowace al’umma ta duniya tana da nata hanyar da take aiwatar da ilimin hikimominta waɗanda suka haɗa da ƙere-ƙere da magungunan gargajiya da sauransu. Ta ƙara da cewa, bincike ya nuna ba Hausawa kaɗai ke yin tatsuniya ba, al’ummun duniya na kusa da na nesa suna aiwatar da ita. Haka ma, ba abin mamaki ba ne a ce labarun da ke cikin tatsuniya suna yaɗuwa ne daga wannan al’umma zuwa waccan, amma kuma tushensu daga wata ƙasa ce ta daban wadda idan tatsuniyar ta zo ga al’umma sai su gyara ta ta yadda za ta dace da al’adunsu, sai ta zama tasu.

Ma’anar Tatsuniya

Masana da manazarta sun faɗi albarkacin bakinsu gwargwadon fahimtarsu. Yahaya (1971) yana cewa: “Tatsuniya wani ƙagaggen labari ne da al’adar Hausawa ta tanada domin nishaɗantarwa da kuma cusa tarbiyya ga ‘ya’yan Hausawa.” Calvin (1984) a cikin Salihu (2009) “Tatsuniya abu ce a tsarin al’adun Hausawa inda tsohuwa ce kan tara jikokinta ko yaran gida da dare ta riƙa yi musu tatsuniya.” Shi kuma Zaruk (1987) cewa ya yi: “Tatsuniya ƙagaggen labari ne da aka shirya game da gizo ko waninsa da ya ƙunshi wani darasi ko ya cimma wata manufa ta musamman cikin hikima”. Ita kuwa Hadiza (2009) tana da ra’ayin cewa: “Tatsuniya wasu labarai ne da mutane ke ƙirƙirowa cikin azanci don su tarbiyyantar da ‘ya’yansu  da kuma cimma wasu buƙatoci dangane da al’umma.” A tunanina kuwa, tatsuniya wani ƙirƙirarren labari ne da ake yi wa yara don karantar da su rayuwar duniya mai alfanu, da kauce wa marasa alfanu.

Dabarun Tabbatar da Zaman Lafiya a Tatsuniyoyin Hausa

Koko (2009) ta kawo jerin jigogi fiye da ashirin, wanda suka haɗa da girmama manya da mutunta su, da adalci da jaruntaka da tausayi da tawakkali da amana da haƙuri da juriya da zamantakewa da soyayya da tarihi da dabarun fitar da kai da kwaɗayi da illolinsa da sakamakon zamba da yaudara da wa’azi da ilimi da tsoratarwa da sana’o’in gargajiya da sakamakon cin amana da sakamakon mugunta da zalunci da sauransu. Idan aka yi nazarin waɗannan jigogi da ƙwaƙwalwar hankali da idanun basira za a ga cewa, wasu da dama daga cikin jigogin da aka ambata, matakai ne na wanzar da zaman lafiya musamman jigogi irin su amana da adalci da haƙuri da sana’o’i, da kuma tsare dokokin al’umma. A kan haka, za a kalli yadda wasu tatsuniyoyin Hausa ke koyar da  zaman lafiya da kuma sasanta rikice-rikice idan sun kunno kai. Daga cikin dabarun samar da zaman lafiya da za a iya tsinta a tatsuniyoyin na Hausa sun haɗa da.

Riƙon Amana

Kamar yadda aka bayyana a baya, riƙon amana na daga cikin ginshiƙan wanzar da zaman lafiyar al’umma, kamar yadda rashinsa a tsakanin al’umma ke haifar da rikice-rikice da tashe-tashen hankula masu hana zaman lafiya. Idan aka dubi yanayin da ake ciki na rashin zaman lafiya a ƙasar nan a yau, za a ga yana da nasaba da rashin amanar shugabanni da ɗaiɗaikun mutane. An danƙa wa shugabanni dukiyar talakawa domin kyautata rayuwarsu, da samar musu abubuwan more rayuwa, amma sun danne, sun bar su cikin talauci, babu aikin yi, ba a kula da lafiyarsu, an kasa samar musu hanyoyin sufuri masu kyau, ga rashin wutar lantarki da ruwa masu tsafta, ga su nan dai. Irin Wannan yanayi da aka jefa talakawa ya taimaka wajen wanzuwar ayyukan ta’addanci da ya hana al’ummarmu zaman lafiya a yau.

Za a iya kallon rawar da riƙon amana ya taka wajen wanzar da zaman lafiya a tatsuniyar “Abotar Zaki da Mutum” da aka kawo cikin  littafin Taskar Tatsuniyoyi  na Bukar Usman, wadda aka nuna an yi abota tsakanin ɗan zaki da ɗan mutum, kuma ɗan zaki ya riƙe amana ya ƙi gaya wa uwarsa cewa akwai ɗan Adam tare da su, domin yin hakan tamkar cin amana ne da zai iya haddasa rashin zaman lafiya a rayuwarsu. Ga yadda tatsuniyar take:

Tatsuniyar Abotar Zaki Da Mutum

  Wani maharbi ne ne kullum yakan tafi daji yawon harbi, idan ya harbo naman daji sai ya kawo gida. Ana nan, sai wata rana ya tafi daji yawon farauta bai samo komai ba har kusan faɗuwar rana, sai ya ga fara ya kama ya kai gida. Da isowarsa sai matarsa ta yi masa maraba ta kawo ruwa ya sha, sai ta ɗauki burgamensa tana buɗewa sai fara ta tashi sama ta gudu. Sai maharbi ya ce wa matarsa, “Kash! Abin da na samo ke nan tun safe, bi ta ki kamo ta duk inda ta kai, in ba haka ba mu kwana da yunwa.” Matar maharbin nan kuwa tana da ciki ta kusa haihuwa, sai ta tashi da ƙyar ta bi fara. Tana cikin bin fara sai naƙuda ya kama ta, sai ta ga wata ƙatuwar kuka mai kogo ta shiga gefe ɗaya sai ta haifi ɗa namiji, gefe ɗaya kuma ashe wata zakanya ke ciki ta haihu. Wata rana zakanya ta fita kiwo, ita ma matar nan ta fita neman abinci, sai ‘ya’yansu (ɗan matar nan da ɗan zakanya) suka fito bakin kogo shan iska suka ga juna Allah ya haɗa so tsakaninsu, suka ƙulla abota cikin aminci ba tare da ɗan zakanya ya tona masa asiri wajen zakanya ba. Ɗan zakanya a kullum yana yi wa ɗan matar nan kashedi da cewa, “kada ya kuskura uwarsa zakanya ta gan shi saboda za ta iya kashe shi.” Rannan sai zakanya ta fito ba tare da ɗanta ba, sai ta ci karo da matar nan sai ta bangaje ta ta faɗi ta mutu, ta ɗauko ta kawo bakin kogo ta aje sharab! Ko da ɗan zakanya ya gano cewa gawar uwar abokinsa ce, sai ya ce “ba zan ci wannan naman ba, na daina cin naman mutum. Ana nan, ranar sai ɗan zakanya ya ce wa uwarsa, “Inna bari in nuna miki na iya bangazar namun daji ki gani.” Sai uwar ta ce “to gwada mu gani in ka iya.” Sai ɗan zakanya ya ja da baya ya ba uwarsa karab, sai ta faɗi ta mutu. Sai ya ja ta ya kai wa abokinsa ya gani. Abokinsa ya tambaye shi yaya aka yi haka? Sai ɗan zakanya ya ce “Ni na kashe ta, yanzu mun zama daidai, za mu ci gaba da zaman duniya lafiya lau ba tare da wata fargaba ba, kuma Allah zai taimake mu da abin da za mu ci mu sha.” ...Haka suka ci gaba da rayuwa har lokacin da ƙaddara ta sami ɗan zakanya sarkin baka ya harbe shi da kibiya rai ya yi halisa.

Wannan ya nuna riƙon amana wani sinadarin wanzar da zaman lafiya ne, domin da tun farko ɗan zaki ya ci amanar ɗan matar nan ya faɗa wa zakanya halin da ake ciki, da zamansu ya yamutse. Haka ma, da bai yi adalcin kashe uwarsa zakanya ba, da ba su sami zaman lafiya mai ɗorewa ba. Don haka, da shugabanninmu na yau za su riƙi amanar talakawansu, su rufa musu asiri ta hanyar kyautata rayuwarsu, su samar musu maslaha a kan matsalolinsu, da ƙasar nan an zauna cikin ƙoshin lafiya, sai ɗan abin da ba a rasa ba. Har wa yau, wasu rikice-rikicen aure da suke faruwa tsakanin ma’aurata, suna da nasaba da cin amanar zamantakewa, ko dai ta gefen miji, ko ta gefen mace.

Bugu da ƙari, akwai wata tatsuniyar “Rimi da ‘yar Amana” a cikin littafin Taskar Tatuniya na Bukar Usman, wadda ke koyar da amfanin riƙon amana a rayuwar mutane. A tatsuniyar an nuna cewa, wata marainiya ce da ba uwa ba uba, amma kafin rasuwar iyayenta sai suka danƙa ta amana ga wani iccen Rimi wanda ya riƙa kula da ita har ta girma kyawonta ya fito sosai. Wata rana Gizo ya gan ta sai ya sheƙa ya gaya wa sarki, sai sarki ya turo fadawa don a kai masa ita. Da aka zo kama ta sai ta maƙale wa Rimi tana neman agajinsa. Daga nan sarki ya sa a sare itacen Rimin, amma aka kasaa saboda amanar yarinyar da ya riƙe. Ga labarin tatsuniyar kamar yadda aka kawo ta:

Tatsuniyar Rimi da ‘Yar Amana

  An yi wani gari mai yawan jama’a da Sarkinsu mutumin kirki. Akwai wani mutum mazaunin wannan gari shi da matarsa da ‘yarsu ɗaya. Wata rana ciwon ajali ya kama matar wannan mutum. Kafin ta rasu sai ta kira shi ta ce: “Maigida, ni fa ina jin ba zan tashi daga ciwon nan ba, amma ga amanar ‘yarmu nan ka kula da ita sosai, kada ka bari wani mugun abu ya same ta. Da matar ta rasu sai uban yarinyar ya ci gaba da renon ‘yarsa har ta yi wayo. Sai wata rana shi ma ciwon ajali ya kama shi, sai ya rasa yadda zai yi da ‘yarsa, kuma ba shi da kowa a garin. To amma akwai wata tsohuwar bishiyar Rimi a ƙofar gidansa, sai ya fito ya ɗauko yarinyar ya kawo ta gindin Rimin, sai ya dubi Rimin nan ya ce ya ba shi amanar ‘yarsa domin yana jin wa’adinsa ya kusa cika. Daga nan ya koma gida bai sake fitowa ba har ya rasu. Bayan rasuwarsa da ‘yan kwanaki, duk sanda yarinyar ta ji yunwa sai ta je wurin Rimin nan ta kama waƙa tana cewa: “Rimi, Rimi uwata, Rimi ubana ya ba ka amanar Allah, uwata ta ba ka amanar Allah.” Da ta yi wannan waƙa sai Rimi ya ba ta abin da take so. Wata rana Gizo ya fita yawo sai ya ga ‘yar budurwa tana wanki a gindin Rimi, to da ma sunanta Jummai. Da Gizo ya ga kyaunta sai ya garzaya gidan Sarki ya kwashe labarin yarinyar nan ya gaya masa. Da Sarki ya ji haka, sai ya tura fadawansa su ɗauko yarinyar. Da suka isa wurin Rimi sai yarinyar ta gan su ta kuma razana, sai ta je ta rungumi Rimi ta fara waƙa tana neman agajinsa. Sai ya ce mata, yi wankinki, cikin ɗari da goma, ɗaya ya koma. Da dogarai suka matsa kusa da ita sai duk suka mutu. Da Sarki ya ji labari sai ya sa a je a sare wannan Rimi. Da aka taru za a sare, idan aka sara jikin sai ya ƙara tohowa, har dai masu saran suka gaji suka haƙura. Har yanzu wannan Rimi da ya riƙe amana yana can a garin, mutane suna zuwa kallonsa.

Wannan ya nuna cewa, riƙon amana babban makami ne na zaman lafiya, domin yana kariya ga duk wata musibar da ka iya yi wa rayuwa barazana ga zaman lafiyarta.

Adalci

Wanzuwar adalci a cikin al’umma yana haifar da zaman lafiya da ƙaunar juna mai ɗorewa, kamar yadda rashin adalci ke jawo rikici da haddasa gaba a cikin al’umma. Akwai wata tatsuniya da aka kawo a cikin littafin Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza Salihu Koko, ta wani yaro mai suna “Daredi” wadda ke nuni da illolin da rashin adalci ke haifarwa na haddasa fitina da ruɗani, da kuma yadda za a sasanta domin a zauna lafiya.  Ga dai labarin tatsuniyar kamar yadda yake:

Tatsuniyar Daredi

A wani gari da ake kira Tunga, an yi wata yarinya mai kyau wadda ba ta son kowa duk garin sai wani yaro da ake kira Daredi. To su kuwa iyayen yarinyar nan suka yi tsayin daka suka ce ba su ba shi ita aure. Yarinya ta yi ta yi da su suka ƙiya. Sai rannan wata shawara ta zo mata, sai ta tafi ta kwashe duk ruwan da ke cikin rijiyoyi da gulaben garin, ta haye saman itace ta yi zamanta. Da mutanen gari suka matsu babu ruwan sha, sai aka roƙi iyayen yarinyar nan da su je su roƙe ta ta sako ruwa a samu a sha. Sai uwarta ta fara zuwa tana rera waƙa tana roƙon ta, amma ta ƙiya. Sai uwar ta faɗi ta mutu. Daga nan sai ubanta ya zo ya roƙe ta, amma ta ƙiya, shi ma sai ya faɗi ya mutu. Haka dai ‘yan’uwanta suka yi ta zuwa suna roƙon ta tana ƙiyawa, sai su faɗi su mutu. Kai har dai duk zuriyarsu ta ƙare. Sai mai gari ya zo da kansa yana rera waƙa yana roƙon ta. Sai nan take ya sa aka biɗo Daredi saboda lokacin da iyayen yarinyar suka hana masa ita sai ya bar gari don baƙin ciki. Daga nan sai Daredi ya fara rera waƙa yana roƙonta ta ba shi ruwa ya sha. Sai yarinyar ta sauko daga saman itaciya ta mayar musu da ruwa kowa ya sha. Sai mai gari ya sa aka ɗaura musu aure suka yi zamansu.

Wannan tatsuniya tana nuni da illar da rashin adalci ke haifarwa a rayuwar mutane, da kuma irin rawar da sarakuna za su iya takawa wajen sasanta rikici domin maido da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Haka ma, tatsuniyar na hannunka mai sanda ga iyayen da ke tilasta wa ‘ya’yansu mata auren dole, alhali suna da masoya na gaskiya waɗanda aka tabbatar da ba su da wata illa da za ta hana a ba su aure. Wannan matsala a yau tana daga cikin rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar Hausa wadda ta sha haifar da masifu iri daban-daban, har ma da rasa rayukan waɗanda abin ya shafa da ma waɗanda bai shafa ba. Bugu da ƙari, rashin adalcin da ake fuskanta a wajen mahunkunta, babu mai gaskiya sai mai abin hannunsa ko mai uwa a bakin murhu, ko a ware wasu mutane, hukunci bai hawa kansu sai marasa gata, yana taimakawa wajen ƙara haddasa wasu rikice-rikice da suke yawan aukuwa. 

Akwai wata tatsuniya a cikin Taskar Tatsuniyoyi  na Bukar Usman da ta yi ƙoƙarin bayyana adalcin shugabanni a matsayin sinadarin wanzar da zaman lafiya. Wasu tsuntsaye ne biyu, wato “Talipaku da Kurciya” suka haɗa kansu suna tafiyar da lamurransu lami lafiya. Daga bisani  Talipaku ta shirya yaudara ta sace ‘yar Kurciya ta gudu. Daga ƙarshe rikicin ya kai ga sarkin tsuntsaye wanda ya sasanta rikicin bisa adalci. Ga cikakken bayanin tatsuniyar:

Tatsuniyar Talipaku da Kurciya

  Wata rana tsuntsuwa Talipaku da Kurciya suka yi sheƙa a bishiya ɗaya. Da lokacin saka ƙwan da suka ɗauka ya zo, sai suka haɗa ƙwansu a wuri ɗaya. Bayan sun gama kwanci, sai suka ƙyanƙyashe suka sami ‘ya’yansu guda biyu. Suna nan a haka, kullum sai su fita neman abincin ‘yan tsakinsu. Kansu ya haɗu komai na tafiya rumui-rumui. To ashe ita Talipaku ba ta jin daɗi da bakin ‘yarta ya yi tsawo fiye da na ‘yar Kurciya wadda kyakkyawar gaske ce. Duk lokacin da za su fita neman abincin ‘ya’yansu, sai a karɓi renon ‘yar Kurciya, amma a bar ‘yar Talipaku a sama cikin sheƙa. Wata rana Talipaku ta yanke shawarar sace ‘yar Kurciya ta gudu da ita. Wata rana suna wurin neman abinci, sai Talipaku ta sulale ta je ta sace ‘yar Kurciya ta gudu da ita. Ko da Kurciya ta dawo gida ta shiga sheƙa, sai ta ga ba ‘yarta, sai ‘yar Talipaku. Sai ta fita ta kama cigiya. Sai aka ce mata ai an ga Talipaku ta ɗauki ‘yar Kurciya sun yi sama. Da jin haka sai Kurciya ta koma sheƙarsu ta ɗauki ‘yar Talipaku ta fito ta kama waƙa tana neman Talipaku. Ita kuwa Talipaku tuni har ta isa garin Sarkin tsuntsaye aka kai ta gidan Sarkin tsuntsaye mai suna Miki. Da ta je gaban Sarkin sai ya tambaye ta abin da ke tafe da ita. Sai ta ce ta zo ne ita da ‘yarta a ba su wuri a garin domin su zauna. Da Miki ya ji haka sai ya ce: “To ai ‘yar da kika zo da ita ba ta yi kama da ke ba, ba ‘yarki ba ce. Ina kika samo ta?” Ita kuwa Kurciya tuni ta haɗu da wasu mutane a jeji ta tambaye su ko sun ga Talipaku? Sai suka ce mata yanzu ta tambaye su hanyar gidan Sarkin tsuntsaye. Sai suka nuna wa Kurciya hanyar, suka ce ta yi sauri ko ta same ta a gidan Sarkin tsuntsaye. Tana zuwa gidan, sai ta tarar ana tambayar Talipaku inda ta samo ‘yar da ba ita ta haifa ba. Sai ta faɗi ta yi gaisuwa, sai ta yi wa Sarki bayani yadda suka yi da Talipaku. Sai Sarkin ya sa aka ƙwace ‘yar Kurciya daga hannun Talipaku a ba Kurciya, ita kuma Talipaku aka ba ta ‘yarta. Sarkin tsuntsaye ya ja kunnen Talipaku da kada ta sake satar ‘yar wani tsuntsu. Idan aka sake kawo ƙarar ta, to za a kashe ta. Sai aka sallame su, Kurciya ta ɗauki ‘yarta ta yi godiya ta tafi. Ita kuma Talipaku ta tafi da ‘yarta.

Wannan tatsuniya na koyar da mu cewa, samun shugaba nagari mai adalci tsakanin al’ummarsa wani mataki ne na zaman lafiyar al’umma. Da ƙasarmu za ta sami irin wannan managarcin shugabanci a yau, ba shakka da rikice-rikicen da ke addabarta sun ƙaranta. {asarmu a yau ta zama babu mai gaskiya sai mai abin hannunsa, ko mai uwa a bakin murhu, ko kuma wanda ake ɗasawa da shi. Don haka, da za a kawar da wannan mummunar ɗabi’a, a ɗauki ɗabi’ar Sarkin tsuntsaye, da kakarmu ta yanke saƙa.

Alƙawali

Ba shakka, alƙawali wani babban jigo ne da ke taimakawa ga wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma. Rashin cika alkawali abu ne da addini da al’ada suka yi tir da shi, kuma yana da tasa gudunmuwa wajen haifar da rikici da hana zaman lafiya. Akwai tatsuniyar wani mahaukaci wai shi Zarumi a  cikin littafin Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza Koko. Zarumi mahaukaci ne mai tarin suma da kwarkwata a cikinta. Wata rana Zarumi yana son fita neman abinci amma ya rasa mai tsare masa shukarsa (wake). Sai kwarkwatar da ke cikin sumansa ta ce, ta yi alkawalin tsare masa wakensa amana har ya dawo gida. Sakamakon haka, danƙon zumunci ya ƙaru tsakanin Zarumi da kwarkwata, ya kuma yi sanadin fitar kwarkwatar daga ƙangin suman Zarumi zuwa cikin kwalban zinari. Ga abin da tatsuniyar ke cewa:

Tatsuniyar Zarumi

 An yi wani mahaukaci da ake kira Zarumi. Zarumi bai zagin kowa balle bugu, sai dai yana da tarin suma mai kwarkwata a ciki. Wata rana yana kwance cikin bola sai ya ga wani wake ja mai kyau, sai ya ɗauka ya je gida ya shuka. A hankali wake ya girma ya yi ‘ya’ya sosai. Rannan Zarumi na son ya fita neman abinci sai ya rasa mai fake masa waken nan. Can daga cikin sumansa sai ji ana cewa “ni zan tsare maka gidan.” Ko da Zarumi ya duba sai ya ga ashe kwarkwatar da ke kansa ce ke magana. Sai Zarumi ya ciro ta daga sumansa ya ce “to na ba ki amanar gidana.” Sai kwarkwata ta ce “na yi alkawalin tsare maka, Allah ya dawo da kai lafiya.” Bayan fitar Zarumi, Gizo ya shigo bara. Da ya ji kamar ba kowa gidan sai ya ce, bari in ɗan ɗibi waken nan in je gida in dafa jinɓiri. Ko da Gizo ya taɓa wake sai kwarkwatar nan ta fara rera waƙa tana ce wa Gizo kar ya taɓa, waken Zarumi ne. Sai ya tsaya bai ga kowa ba. Ya kuma ƙara taɓawa ya ji an yi waƙa kuma bai ga kowa ba, sai ya fara rawa. Da Gizo ya ga haka, sai ya garzaya gidan sarki ya gaya masa ya tafi wani gida bara ya ga wake mai kyau, ko da ya sa hannu ya ɗiba sai ya ji waken na waƙa mai daɗi. Da sarki ya ji wannan bayani, sai ya aika fadawansa su je su ɗebo masa wannan wake. Ko da suka sa hannu su ɗiba sai suka ji ana waƙa sai suka kama rawa har rana ta faɗi. Ko da sarki ya ga ba su dawo ba sai rana ya ɓaci ya hau doki da kansa domin ya je ya ga abin da suke yi. Da zuwansa ya kama yi musu faɗa ya sauko ya sa hannu zai ɗebi wake sai wake ya kama waƙa. Sai sarki ya kama rawa tare da fadawansa da Gizo har Zarumi ya dawo ya iske gida ya cika da mutane har da sarki. Ko da ya tambaya aka ce masa wakensa ke waƙa mai daɗi. Sai Zarumi ya ce, ba wake ke waƙa ba, kwarkwata ce. Daga nan sarki ya ce yana son ya sayi kwarkwatar, sai ya ba Zarumi bawa goma da dinari dubu, Zarumi ya ba shi kwarkwatar, ya ce maaa abincinta shi ne man shanu. Sarki ya yi godiya ya koma gida ya sa kwarkwata cikin kwalbar zinari da auduga da man shanu ya rufe ya rataye a kan gadonsa. Duk lokacin da ransa ya ɓaci sai ya zo ya taɓa kwalbar nan sai kwarkwata ta fara yi masa waƙa har sai ransa ya yi sanyi.

Wannan tatsuniya tana karantar da mu cewa, riƙon amana da cika alkawali sinadarai ne na samar da ci gaba da wanzar da zaman lafiya a rayuwar al’umma, musamman idan aka yi la’akari da yadda Zarumi ya saka wa kwarkwata da alheri, daƙon zumunci ya ƙara ƙarfi tsakaninsa da kwarkwata har zuwa lokacin da suka rabu lami lafiya.   .

Yafewa

Yafe wa juna a kan wani saɓani da ya gudana tsakanin mutane, wani babban mataki ne na wanzar da zaman lafiya tsakanin mutane. Sau da yawa wasu rikice-rikice suke faruwa a sanadiyyar ɗaukar fansa musamman a rikice-rikice masu alaƙa da addini ko ƙabilanci ko siyasa, wanda galibi yakan haddasa gaba mai ɗorewa tsakanin al’umma. Akwai wata tatsuniyar kishiyoyi biyu da aka kawo a cikin littafin Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman, suna zaman lafiya ba su taɓa ɓata wa juna rai ba. Suna cikin irin wannan zama, sai ɗaya ta kwanta jinya har Allah ya ɗauki ranta, sai dai kafin ta rasu ta bar wa kishiyarta amanar ɗiyarta. Bayan rasuwar kishiyar, sai kishiyar ɗaya ta riƙe amanar marainiyar kamar yadda ta riƙe ɗiyarta na cikinta, kafin daga bisani wata tsohuwa ta zo ta hure mata kunne, sai ta fara azabtar da marainiyar har ta kore ta daga gidan ta shiga duniya. Da man Hausawa na cewa: “Mahaƙurci mawadaci.” Wannan kora da aka yi mata sai ya zamo mata alheri, domin a kan haka ne ta haɗu da ɗan sarki ya aure ta suka ci gaba da rayuwa mai daɗi. To sai dai kuma, duk da irin cin zarafin da kishiyar uwarta ta yi mata bai sa ta manta da ita ba, ko kuma ta ƙudurci aniyar ɗaukar fansa tun da ta samu dama. Amaimakon haka, sai ta shirya tare da mijinta  suka tafi suka gan ta, suka yi mata goma na arziki tare da yafe mata. Ga labarin tatsuniyar kamar yadda take:

Tatsuniyar Kishiyoyi Biyu

   An yi wasu kishiyoyi biyu masu zaman lafiya, ba su taɓa ɓata wa juna rai ba. Sai wata rana ɗaya daga cikinsu ta kwanta jinya. To da ma kowacensu tana da ‘ya mace, kuma sun yi kama da juna ainun, yadda ba kowa ne zai iya bambance su ba. Da mai jinyar nan ta ga alamun ciwon nata ba na tashi ba ne, sai ta kira kishiyarta, ta ba ta amanar ‘yarta. Kishiyar ta karɓa, kuma ta yi alkawali za ta kula da duk yaran biyu kamar ita ta haife su. Da mai jinyar ta rasu, sai kishiyar ta ci gaba da kula da yaran har suka girma suka zama ‘yan mata. Rannan sai wata tsohuwa ta ziyarce su, da ta lura da yanayin matar ta hanyar adalcin da take nunawa a tsakanin yaran, sai riƙa yi mata faɗa a kan yaya za ta riƙi ‘yar wata kamar nata. Sannu a hankali har ta fara karkata ga zancen tsohuwa. Daga nan fa sai ta fara gana wa ‘yar kishiyar nan tata azaba iri-iri, har ya kai in za su ci abinci sai ta ƙi zuba wa ‘yar kishiyar abincinta a akushi, sai ta zuba mata a ƙasa. Ana nan a haka, sai ta daina ba ta abinci sam-sam, har ma dai ta kore ta daga gidan, wai ta je can ƙabarin uwarta ta karɓi abinci. Da yarinya ta ji haka, sai ta yi ta kuka, ta kama hanya ta tafi bakin ƙabarin uwarta tana kuka. Wata rana da ta je ƙabarin uwar tana kuka, sai uwar ta fito ta rarrashe ta, ta ba ta abinci, ta ci ta ƙoshi. Kullum haka nan yarinyar take yi idan aka hana ta abinci. Nan da nan ta sake yin ƙiba ta yi kyau, abin gwanin ban sha’awa. Wata rana sai wasu samari suka je tambayar uwar cewa, ɗaya daga cikinsu yana son ya shiga neman auren marainiyar. Sai ta ce, sai dai su auri ‘yarta. Da marainiyar nan ta ga haka, sai ta gudu, ta shiga uwa duniya. Tana cikin tafiya sai ta ga hadari ya haɗu, sai ta hangi ‘yar bukka sai ta shiga. Bayan ta zauna sai ta ga wani babban kumurci a gefenta. Macijin nan ya riƙa rikiɗa yana komawa abubuwa masu ban tsoro, amma bai sa yarinyar ta razana ba. Daga ƙarshe ya rikiɗa ya koma yaro matashi kyakkyawa. Yarinyar ba ta sani ba ashe macijin nan ɗan Sarki ne yake neman aure, amma sai ya bi wannan hanya don ya sami mace mai hankali da amana. Nan da nan ya sa aka ɗauke ta a kan doki aka kai ta gidan Sarki aka ɗaura mata aure da shi aka sha biki. Wata rana sai amarya ta kwanta ɗaki ita kaɗai tana rusar kuka. Da mijin ya shigo ya tambaye ta abin da ya faru, sai ta ce tana tunanin gidansu ne da mahaifinta da kuma kishiyar mahaifiyarta wadda ta riƙe ta. Ta kwashe labarin gaba ɗaya ta gaya masa. Da ya ji bayaninta, ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya ce ta shirya su je su kai musu ziyara. Da suka isa garin, sai suka zarce gidan iyayenta suka shiga gidan. Da ‘yar’uwarta ta gan ta sai ta rungume ta, amma kishiyar uwarta da ƙyar ta gane ta saboda tsagun fuska da ta yi mata. Bayan amarya ta huta, sai ta kwashe labari tun daga fitarta gida zuwa lokacin da ta auri ɗan Sarki. Da ta gama ganin dangi ta yi wa kowa alheri, sai ita da mijinta suka yi musu sallama suka kama hanyar garinsu...    

Wannan yana koyar da mu yafiya a lokacin da aka zalunce ka bisa kuskure ko  da gangan, saboda yin hakan zai dawo da zaman lafiya da ƙaunar juna mai ɗorewa. Haka ma, tatsuniyar na nuni da yin taka-tsan-tsan da wasu mutane da ka iya kawo tashin-tashina a cikin al’umma.

Har wa yau, akwai tatsuniyar wasu abokai biyu, “Nasiru da Nisiru” a cikin Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman, wadda ke ɗauke da jigon yafiya a matsayin hanyar zaman lafiya da sasantawa. Tatsuniyar ta nuna cewa, mahaifiyar Nasiru suna zaune lafiya da kishiyarta ba a taɓa raba su ba.  Rasuwar  uwar Nasiru ke da wuya sai kishiyarta ta shiga azabtar da Nasiru da ma ƙoƙarin halaka shi, sai dai ɗan kishiyar uwar Nasiru mai suna Aliyu yana son Nasiru sosai. Wannan ya tilasta Nasiru barin gari tare da abokinsa Nisiru, suka koma wani gari da zama, inda aka nuna Allah ya azirta su sosai. Bayan sun yi arziki, sai suka yanke shawarar zuwa ganin gida, suka tarar da kishiyar uwar Nasiru cikin mawuyacin hali na talauci da tsufa. Nan take Nasiru ya ba ta dukiya mai tarin yawa, ya kuma kawo jari mai kauri ya ba ɗanta Aliyu. Tun daga wannan lokaci  duk sa’ad da uwar Aliyu ta zauna sai ta shiga tunanin ƙetar da ta shirya wa Nasiru da kuma irin alherin da ya saka mata da shi, sai ta yi da-na-sani ta roƙi gafararsa, ya yafe mata. Ga labarin tatsuniyar kamar yadda take:

Tatsuniyar Nasiru da Nisiru

 A can ƙasar Mazarƙwaila, an yi wani yaro ɗan Sarkin Zaƙi mai suna Nasiru. Yana da wani aboki wai shi Nisiru. A na nan sai mahaifiyar Nasiru ta rasu. Rasuwarta ke da wuya sai kishiyarta ta shiga ba Nasiru wuya. To amma ɗan kishiyar uwar mai suna Aliyu yana son Nasiru sosai, ba ya nuna masa ƙiyayya ko kaɗan. Wata rana sai Aliyu ya ce wa Nasiru da abokinsa: “Yau zan raka ku shan zuma.” Lokacin da Nasiru da Aliyu suka ji wannan maganar, ashe wata mata magulmaciya ta ji su, sai ta je ta ce wa uwar Aliyu: “Kin ga Nasiru da abokinsa Nisiru za su ja ɗanki daji su halaka shi.” Uwar nan na jin haka, sai ta nemi shawarar ‘yar zugar nan, sai ta ce: “Akwai wani boka wanda za mu je ya ba mu maganin da za mu kashe Nasiru kawai mu huta.” Uwar Aliyu na jin wannan gurguwar shawarar, sai ta ce: “To Shi ke nan mu je.” Da zuwansu wurin boka sai ya ba su magani ya ce su zuba a nono su ba Nasiru ya sha. Ya ce idan ya sha, nan take zai mutu. Da ta ba Nasiru sai ya koma can waje ya ba ɗan akuya ya sha, nan take ya faɗi ya mutu. Daga nan sai Nasiru ya faɗi yana shure-shure kamar da gaske. Da kishiyar nan ta ga haka, sai ta shiga murna, ta ɗauki Nasiru ta kai shi bayan gari ta jefar. Bayan ta wuce sai Nasiru ya tashi ya nemi abokinsa Nisiru suka yanke shawarar barin garin don gudun mugun halin uwan Aliyu. Daga nan suka koma wani gari mai babbar kasuwa da karkara mai dausayi, ga filayen noma nan sai an zaɓa. Da yake su duka muzakkarai ne, sai suka shiga neman abin kansu. Kafin shekara ta dawo kowanensu ya mallaki dukiyar da an jima ba a ga masu kamarta ba. Wata rana bayan shekara biya, Nasiru da abokinsa suka yanke shawarar zuwa ganin gida. Nan da nan kuwa suka yi laftun dukiya suka ɗora wa raƙuma, suka tafi da ita garinsu. Nasiru ya tarar da uwar Aliyu tana cikin mummunar talauci, sai ta yi da-na-sani ta roƙi gafararsa, ya yafe mata, ga tsufa ya kama ta, ƙanensa Aliyu kuwa ba ya komai sai baranta a gidan wani tajiri. Nan take Nasiru ya ba ta dukiya mai tarin yawa. Ta shiga cin daɗi, ba da daɗewa ba ta murmure. Ya kawo jari mai kauri ya ba ƙanensa Aliyu. Shi da abokinsa kuma suka shirya suka koma wurin sana’arsu. Ta roƙi gafararsa, ya yafe mata.

Wannan yana koyar da mu sha’anin sasantawa domin zaman lafiya, domin a maimakon Nasiru ya ƙuduri aniyar ɗaukar fansar azabar da kishiyar uwarsa ta yi masa a lokacin da ya sami damar yin hakan, sai ya yafe mata, ya kuma ba ta kyauta. Yin hakan shi zai kawar da duk wani zogin zuci da tashin-tashina, da samun zaman lafiya mai ɗorewa tsakaninsu. Haka ya kamata mutane su kasance masu yafe wa junansu ga duk wani saɓani da ya auku tsakaninsu, ba mutum ya ƙudurci ramawa ko ɗaukar fansa idan ya samu dama ba.

Bugu da ƙari, akwai tatsuniyar “Yelwa da Tsohuwa da Sarki” da ke cikin littafin Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman, wadda ke bayyana yafiya a matsayin matakin wanzar da zaman lafiya da sasantawa. Tatsuniyar ta nuna cewa, akwai wata yarinya mai suna Yelwa tana da ƙawaye da yawa. Wata rana Sarkin garinsu ya umurci ‘yan matan garin da su tafi kogi su kamo kifi kowa ya yi masa miya, kuma duk wadda miyarta ta fi daɗi ita zai aura. Da ma sauran ‘yan matan sun tsani Yelwa, da suka tafi kogi sai suka jefa ta ruwa suka kama nasu kifi suka koma gida. Tana cikin wannan yanayi sai Allah ya kawo wata Tsohuwa sai ta tsamo ta. A taƙaice dai Tsohuwar nan ta ba Yelwa kifi ta je ta dafa ta kai wa Sarki, sai ga shi miyarta ta fi ta sauran ‘yan matan nan  daɗi, sai Sarki ya aure ta, duk da cewa ba ta da iyaye duk sun rasu. Daga nan ƙawayen nan nata suka ji kunyar abin da suka yi mata suka nemi gafararta, Yelwa kuma ta yafe musu. Ga cikakken labarin tatsuniyar kamar yadda take:

Tatsuniyar Yelwa da Tsohuwa da Sarki

 An yi wata yarinya mai suna Yelwa, mai ƙawaye da yawa. Wata rana Sarkin garinsu ya umurci ‘yan matan nan su je rafi su kamo kifi bisa sharaɗin cewa duk wadda ta kamo ta yi masa miya mai daɗi, ita zai aura. Da ma sauran ‘yan matan sun tsani Yelwa, saboda haka, bayan sun kamo kifi sai suka haɗa baki suka jefa ta cikin kogin ta nutse. Sai ta yi sa’a wata tsohuwa ta zo ta tsamo ta. Wannan tsohuwa kuwa tana da baiwa, sai Yelwa ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta gaya mata. Tsohuwar nan ta ji tausayin Yelwa, nan da nan ta kama wani ƙaramin kifi ta ba ta, kuma ta ba ta wata ‘yar tukunya ta ce mata ta sa wannan kifi a cikin tukunyar ta rufe ta kiwata shi. Washe gari da Yelwa ta buɗe tukunyar sai ta ga wani babban kifi a ciki. Ta yi mamakin yadda kifin ya girma haka. Ta kama kifin ta dafa, ta ɗauka ta nufi fada. Kafin ta je an soma biki har an rufe ƙofa. Ta roƙi dogarai suka buɗe mata ta shiga. Kafin zuwanta Sarki ya riga ya ɗanɗana dukkan miyan da ‘yan matan suka kai, amma babu wadda ya gamsu da ita. Saboda haka, da Yelwa ta kai tata miyar, Sarki bai so ya ɗanɗana ta ba, sai da tsohuwar nan ta matsa kusa da shi ta raɗa masa cewa ya taɓa. Sarki ya taɓa ya ji miyar Yelwa zaƙi cakwai, abin ba dama. Ba da ɓata lokaci ba, washe gari Sarki ya bayyana mata buƙatarsa ta autenta. Ya ce in ta yarda ta je ta shaida wa iyayenta a ɗaura musu aure nan da kwana biyu. Yelwa ta tafi tana kuka saboda baƙin cikin maraici, domin tuni mahaifanta suka rasu. Ta fara batun zuci tana cewa: “Kaito, yaya zan yi da raina yanzu, ga ni ba ni da iyaye.” Can sai ga tsohuwar nan ta bayyana, ta ce mata ta daina kuka, kar ta damu, komai zai yi kyau. Ta umurce ta da ta je ta samo ƙwari biyu ta kawo mata. Da ta kawo sai tsohuwar ta mai da su mutane, mace da namiji, wato sun zama iyayen Yelwa ke nan. Daga nan suka tasam ma fada, aka ɗaura aure. Nan fa sai ƙawayen Yelwa suka ji kunya, suke nemi gafararta. Yelwa ta yafe musu saboda halinta na haƙuri. Ita da ƙawayen suka zauna lafiya har kowacensu ta yi nata auren. 

Ashe ke nan, duk lokacin da aka cuce ka kada ka ƙudurci aniyar ramawa, yin yafiya shi ne mafi alheri da kawo zaman lafiya. Haka ne kuma zai sa wanda ya cuce ka yin da-na-sani da jin kunya, don haka ba zai ƙara cutar da kowa ba. Haka ma, Allah kan musanya ma wanda aka cuta ya yi haƙuri da mafificin alherinsa, kamar dai yadda ya faru ga Yelwa a cikin wannan tatsuniya.

Haƙuri

Hausawa na cewa: “Haƙuri maganin zaman duniya”, kuma “Mai haƙuri mawadaci”. Haƙuri na daga cikin abubuwan da ke kawo zaman lafiya da sasantawa a rayuwar al’umma, kamar yadda rashinsa ke haifar da tashin-tashina da rikice-rikice masu cin zarafin rayuwa. Rikice- rikicen addini da ƙabilani da rikicin aure da siyasa waɗanda suke addabarmu a yau, duk suna faruwa ne a dalilin rashin kai zuciya nesa, wato rashin haƙuri. A kan haka, Hausawa sun samar da wasu tatsuniyoyi masu koyar da haƙuri domin a yi koyi da karantarwarsu don kyautata rayuwar  duniya da ma ta gobe ƙiyama. Akwai wata tatsuniyar “Tasalla mai kifi” da aka kawo a cikin Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman, wadda ta kasance mai haƙuri da yafiya bayan an zalunce ta. Tatsuniyar dai ta bayyana cewa, akwai wata mace mai suna Tasalla wadda ke kiwon kifi har suka saba da juna, sukan yi wasa tare a wasu lokuta. Wata rana Tasalla ta yi tafiya, sai mutanen ƙauyen suka kama kifin suka cinye. Bayan da Tasalla ta dawo ta nemi kifinta ƙasa da sama ba ta gani ba. Da ta yi cigiya ba ta sami bayanin komai ga kowa ba. Daga nan sai ta yi wani siddabaru wanda ya ƙarar da ruwan ƙuyen baki ɗaya aka rasa na sha balle na abinci. Wannan ya sa mutanen ƙauyen da Sarki da mahaifiyarta suka yi ta ba ta haƙuri, sai ta haƙura ta kuma warware siddabarun da ta yi, sai ruwa ya samu kowa ya wadata. Ga cikakken bayanin tatsuniyar kamar haka:

Tatsuniyar Tasalla Mai Kifi

      Tasalla mace ce wadda ke zaune a wani ƙauye mai suna Saladuna. Tana kiwon wani kifi babba har sun saba da juna. Tasalla tana ciyar da kifin a kullum gwargwadon ƙarfinta. Saboda sabon da suka yi da juna, har yakan riƙa yin tsalle cikin wasa da ita. Wata rana Tasalla ta yi tafiya, sai mutanen ƙauyen suka kama kifin nan suka cinye. Da Tasalla ta dawo ta nemi kifinta ko sama ko ƙasa, ya ɓace. Ta yi tambaya da cigiya ko ta ji wani abu game da da kifin, amma ba ta sami bayani daga bakin kowa ba. Nan take ta shiga kukan takaici. Wannan ya sa ta yi wani siddabaru da ya ƙarar da ruwan garin, kowa ya rasa ko ruwan wanke ido, balle na wanka da girki. To amma akwai wani mutum ɗaya da Tasalla ke jin nauyi, kuma tana matuƙar ƙaunarsa. Sai aka turo mata shi domin ya roƙe ta ko za ta warware siddabarn da ta yi suka rasa ruwan sha. Sai ya zo yana rera waƙa yana roƙonta amma ba ta mince ba saboda ta yi fushi. Sarkin garin da fadawansa suka ɗunguma suka je roƙonta, amma ta ƙi saurarensu. Sai can uwarta ta zo ita kaɗai ta roƙe ta ruwan sha. Saboda ƙaunar da take yi wa uwar, sai ta daina fushin da take yi. Nan take ta warware siddabarun, ruwa ya samu kowa ya wadata da shi. Daga bisani mutanen garin suka zo suna ba Tasalla haƙuri, kuma suka amince lallai sun yi mata laifi da suka cinye mata kifi. Sai ta yi haƙuri, ta bar ma Allah. Sai kuma mutanen garin suka ɗauki alƙawari za su nemo mata wani kifin. Bayan watanni suka samo mata wani kifin. Sabon kifin yana da ruwan zinari, kamar dai wanda aka cinye. Wannan ya sa zaman lafiya tsakaninta da su ya tabbata. Kifin ya girma, kuma ya dinga hayayyafa. Daga ƙarshe dai har kifin ya zama ya wadaci mutanen garin.   

Wannan tatsuniya ta nuna cewa, haƙuri da yafewa na kawo zaman lafiya da sasantawa a tsakanin al’umma, kamar yadda rashinsu ke haddasa gaba da rikici a rayuwa.         

Haɗin Kai

Ko shakka babu, haɗin kan al’umma wuri ɗaya yana haifar da ci gabanta  da kawo zaman lafiya mai ɗorewa, domin babu abin da rarrabuwar kawunan al’umma ke haifarwa face koma baya. A duk lokacin da mutane suka haɗa kai suka zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, ƙarya ne ‘yan hana ruwa gudu da masu haɗawa su gudu, su sami kafar haddasa husuma a cikinku. A ƙoƙarin Hausawa na yayata zaman lafiya ta hanyar haɗa ƙarfi da ƙarfe, sun samar da wasu tatsuniyoyi da ke bayyana amfanin haɗin kan al’umma wuri ɗaya domin a gudu tare, a tsira tare. Akwai wata tatsuniyar “Kurege mai wayo” da ke cikin littafin Taskar Tatsuniya na Bukar Usman, an bayyana cewa, an yi wani lokacin yunwa babu abinci. Sai Kura da Maciji da Alade da Kurege suka haɗa kai domin su yi noma tare su fita cikin bala’in da ke damun su. Hakan kuwa aka yi, inda aka raba wa kowa aikin da zai yi, hakan ya sa suka sami nasarar da suke buƙata na samun abinci suka fita daga ƙangin yunwa. Ga labarin tatsuniyar kamar yadda take:

Tatsuniyar Kurege Mai Wayo

   Akwai wani lokaci da aka yi yunwa, ba abinci. Wuya ta sa Kura da Maciji da Alade da Kurege suka haɗa kai domin su yi noma tare. Sai suka zaɓi wani fili a dajin da suke, suka gyara, ya zama gonarsu. Jim kaɗan kafin damana ta faɗi, sai Maciji ya ce shi zai yi sassabe. Alade ya ce: “Ni zan yi muna huɗa.” Kura ta ce: “Ni zan nome muna gonar. Kurege kuwa sai ya ce: “Ni kuma zan nemo muna irin shukawa.”A daidai lokacin da ya dace, sai Maciji ya tuge bishiyoyin gonar ya ƙone. Alade ya yi musu huɗa. Kura ta nome. Kurege ya tafi neman irin shuka a kasuwa, sai ya ga wata mata ta tara dawa da masara da gyaɗa da wake. Nan ya yi mata wayo ya samo iri aka zo aka shuka aka sami amfani...

Wannan ya nuna muna cewa, haɗin kai wani mataki ne na kawar da duk wata matsala da ta taso a tsakanin al’umma. Dubi yadda rikice-rikice suka dabaibaye addinin Musulunci a faɗin duniya musamman tsakanin mabiya Sunna da mabiya Shi’a. Wannan yana faruwa ne sakamakon rarrabuwar kawunan mabiya addinin. Da za su haɗa kai su zauna su sasanta a fahimci juna, da an kawo ƙarshen rikicin da ya share zamunna ana fama da shi. 

Kammalawa

Bisa ga misalan tatsuniyoyin da suka gabata, za a aminta da cewa, tatsuniya ta kasance wata taska ta adana tarsashin rayuwar Hausawa musamman a kan zaman lafiya da sasantawa wanda shi ne jigon ci gaban rayuwar kowace al’umma a duniya. Matsalar da ake fuskanta a yau na rashin zaman lafiya yana da alaƙa da watsi da tanadin al’adunmu na gargajiya da koyarwar magabata. Ba shakka, da za a waiwayi baya a sake yi tanadin al’adunmu karatun ta natsau, lallai za a samu sauƙi na mawuyacin halin da ake ciki.

Manazarta

Bunza, A.M. (2015)  “Zama  Lafiya  Ya  Fi  Zama  Ɗan  Sarki: Shirin  Tunkarar  Zaɓen  2015 a  Nijeriya” Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan kyautata zama lafiya a  zaɓen  da za  a gudanar a shekarar 2015 wanda  ƙungiyar Orphans and Huffaz Educational Foudation  Birnin  Kebbi ya shirya.

Bunza, A.M.  (2015) “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin Koyi ga Shugabannin Zamaninmu”. Takardar da aka gabatar a taron yini ɗaya da Centre for Intellectual Services on Sokoto Caliphate ta shirya na faɗakarwa a kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya.

Bunza, A.M.  (2015)  “Labarin Zuciya a Tambayi Fuska: Saƙon  Dariya  Ga  Sasanta  Tsaro  a Farfajiyar  Karatun  Hausa”. Takardar  da  aka  gabatar  a Makarantar Harsuna, Sashen Hausa na  Kwalejin  Ilimi  ta  Adamu Augie, Argungu.

Ezirim, G.E.  (2009) “The  Role of  Civil  Society  in  Conflict Management” in Peace Studies and  Conflict  Resolution  in  Nigeria: A  Reader,  Edited by  Ikejiani-Clark  M.  Ibadan: Spectrum Books Limited.

Francis, D.J. (2006) “Peace and Conflict Studies: An African Overview of Basic Concepts” in Introduction  to  Peace  and  Conflict  Studies in West Africa, Edited by Shedrack Gaya Best. Ibadan: Spectrum Books Limited.

Koko, H.S. (2009) Tatsuniyoyin Hausa a Rubuce. Sokoto: Makarantar Hausa Publishers.

Usman, B.  (2012)  Taskar  Tatsuniya: Littafi na Ɗaya zuwa na Goma sha Huɗu. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Sani, S. (2007) The Killing Fields: Religious Violence in Northern Nigeria. Ibadan: Spectrum Books limited, Spectrum House.

Tashin hankali

Post a Comment

0 Comments