Ticker

6/recent/ticker-posts

Cikin Kira Ake Dadi

Citation: Yaya, A.B. (2024). Cikin Ƙira Ake Ɗaɗi. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 1-12. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.001.

Cikin Ƙira Aka Ɗaɗi 

Daga 

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar da Harsunan Najeriya
Jami’ar Jihar Sakkwato, Sakkwato

Can dauri mallami a

Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
+2347031961302; bagidadenlema2@gmail.com

X.0 Gabatarwa

A goshin wannan muƙala nasiha ko shawara ce ake son a yi, ko a bayar dangane da abubuwan da taskace tarihi musamman na rubutu mu nan a ƙasar Hausa ko ma Musulmi gaba ɗaya ke fuskanta. Nasihohi uku ne da ake iya a dunƙule su zamo guda.

X.1 Ɗaɗi

X.1.1 A Kan Adabi Musamman Waƙoƙi

Adabinmu na Hausa kamar kowane adabin al’umma, madubi ne na al’ummarsa. Ashe kuwa ya dace ko ma tilas ne Hausawa su taskace shi su da kawunansu ta hanyoyin da suka haƙiƙance ba zai salwanta ba ko ba za a gurɓata shi ba. A zamanin da ƙasashenmu na Afirka ta Yamma suka fuskanci barazana daga Turawa ‘yan mulkin mallaka cikin ƙarni na 19 da na 20 dangane da addini da al’adu da adabi, kakannimmu sun yi zuzzurfan tunani dangane da yadda za su taskace ayyukansu na waɗannan fannonin ilmi.(http://en.m.wikipedia.org/wiki/Timbuktu_Manuscripts ) A zamanin ba su yi ƙarfin ‘yan mulkin mallakar ba, sannan babu wasu ingantattun hanyoyin da za su iya kare waɗannan fannoni. Hanya ɗaya ta rage wa kakanninmu baicin hardacewa. Hanyar kuwa ita ce su saka littattafansu cikin akwatuna masu inganci kamar na ƙarfe sannan su turbuɗe cikin ƙasa, har lokacin da ɓarnar Turawa ta lafa, ko kuma bayan wani zamani ya zo jikoki (kamar mu) suka zo. A ƙarnin nan na 21 ma Turawa ba su yi mana ɗahiri ba, domin da suka gane cewa littattafan kakanninmu ba a ƙwace ko sace su ba ta waɗannan hanyoyi ba, sai suka turo karnan farautarsu (Islamic rebels of Ansar Dine, ko kuma IS) suka shiga rusa ɗakunan karatu da masallatai inda ake samun waɗannan littaffai suna ƙona su. Malaman Timbuktu sun ci gaba da amfani da tsuhuwar hanya ta turbuɗe littaffai. To amma duk da haka an ɗauki wasu an fice da su da sunan zuwa wasu wuraren taskace kayan tarihi masu inganci, (ana kiran waɗannan hanyoyi da ‘digitization’ (na’urantarwa) cikin Inglishi). (http://en.m, wikipedia.org.>wiki). Za a yi magana kan abin da ya shafi wannan hanya ta digitization a ɓangaren Ɗ.0.2 nan gaba kaɗan.

Shawarar da ake bayarwa a nan ita ce tilas ne masana kimiyyarmu da fasahar ƙere-ƙere Hausawa mu himmatu har sai mun ƙirƙiro tamu hanya ta taskace kayammu, hanya wadda za ta iya daƙile satar ko lalata kayanmu da muka taskace da ita. Dogaro da hanyoyin da Turawa suka ƙirƙiro babban haɗari ne.

X.1.2 Na’urantarwa (Digitization)

Ina da ra’ayin cewa na’urantar da nus’hohin adabinmu (a nan ina nufin gami da na addini da ma kowane fanni) da Turawa ke ‘ƙoƙarin’ taimaka mana, hanya ce mai haɗarin gaske da za ta cutar da mu ƙwarai ba kaɗan ba. Na ce haka ne saboda a can ƙasashen Turan za a na’urantar da nus’hohin kuma a can ne za su tabbata, sai dai a turo mana kwafe idan muka nema. To a nan ne fa gizo ke saƙa, saƙa kuwa mai kauri wadda ta fi tarkon da akan yi wa giwa kauri, giwa bukkar daji. Za mu zamo da kuturi, mun ba su dokinmu ke nan! Bari in yi ta gwari-gwari. Misali, Turawa su zo mu ba su nus’har littafin Shehu Usmanu ɗan Fodiyo da ya kira, Ihya’us Sunnati wa Imadul Bidi’ati su na’urantar, su aiko mana da kwafen hoto; mu ba su Diya’ut Tawil na Mallam Abdullah ɗan Fodiyo su na’urantar sannan su aiko mana da kwafen hoto; haka Kitab al- rahma fil- tibb wal- hikma na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, shi ma mu yi haka nan da shi.

Babbar ayar tambaya ita ce, wane tabbaci ake da shi cewa bayan tsawon shekaru jikokinmu da tattaɓa kunnenmu za su iya samun sahihin kwafen hoton waɗannan littaffai daga ƙasashen Turai inda aka na’urantar da su? Wace amana ce waɗannan ƙasashe suke da da za ta tabbatar mana cewa haƙiƙanin littaffan kakanninmu za su ba tattaɓa kunnenmu, bayan a yau mun sha ganin yadda suka ci amanar wasu ƙasashe ƙiri ƙiri kamar ƙasar Falasɗinu kwana-kwanan nan?

Bari in ba ku wani misali da na sheda da kaina. A shekarun da nake karantarwa a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, tabbas tsakanin 2005 da 2006, wasu ‘yan Amerika sun kai ziyara a Jami’ar, suka nemi su gana da mataimakin shugaban jami’ar kamar yadda doka ta nemi a yi. Bayan sun gana da shi, shi kuma da yake masani ne mai tsananin basira da tsinkaya sai ya tattara manyan malaman jami’ar irin fafasoshi da doktoci ya ce wa baƙin nan su yi wa malaman nan bayanin abin da suke tafe da shi. Sai baƙin suka ce sun zo ne domin su yi mana bayani game da na’urantarwar nus’hohin ƙasar nan kuma suna fatar masu su su bayar domin su na’urantar da su yadda ba za su halaka ba har abada! Suka ƙara da nuna mana wasu nus’hohin da suka na’urantar waɗanda suka samu daga wani malami a Mali. Bayan da suka kammala sai Mataimakin Shugaban Jami’a ya ce to ya kamata duk mai wata tambaya ko neman ƙarin bayani ga baƙin yana iya ya yi. Ni kuwa sai na miƙe hannuna don a lura da ni a ba ni damar yin magana. Da aka ba ni izni sai na ce, lalle wannan hanyar taskace nus’hohi tana da kyawo kuma na yaba da ita. Tambayar da nake da ita ce, shin idan suka je da nus’hohin da suka samu suka na’urantar da su ko za su mayar da su gida ga masu su? Amsar da baƙin suka bayar cikin damuwa ita ce wai ba za su mayar ba sai dai su ba mai su hoton abin da suka na’urantar, su kuma na’urantattun nus’hohin su saka su cikin babban ɗakin karatu na Amerika domin masu nazari!!! Ni dai daga nan na yi shiru kuma ba a sami wani wanda ya ƙara wata magana ba har aka rufe taro.

Zamanin Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ne aka yi wannan taro. Da na shigo gari sai na samu wani wanda na san yana iya ya isar min da haufin da nake da shi game da bukatar waɗannan baƙi don haufina ya isa ga kunnen mai martaba Sarkin Musulmi. Abin da nake da yaƙini shi ne har zuwa wafatin mai martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ban ji an biya wa waɗannan baƙi da bukatunsu ba.

X.1.3 Dara ta ci Gida

Mai wannan muƙala yakan kai ziyara Gidan Adana Tarihi da Al’adu na Waziri Junaidu tun zamanin da yake da sunan Gidan Tarihi kurum. A wancan lokaci a Giɗaɗawa aka yi shi, yamma da ƙofar gidan Wazirin Sakkwato. Wannan gidan tarihi ya samu sauye-sauyen wuri har dai zuwa yanzu da yake kan titin Ali Aƙilu, dab da farkon hanyar da ke zuwa makarantar koyon aikin assibiti (School of Nursing, Sokoto), a shiyyar Unguwar Rogo. Nakan ziyarci wannan gidan adana kayan tariha a wasu lokuta ma tare da yarana. Wannan ziyara har yanzu nakan yi ta.

A wannan shekara na ziyarci Gidan Adana Tarihi da Al’adu na Waziri Junaidu. Na kuma san na taɓa zuwa tare da wasu daga cikin yara har na nuna musu hoton mahaifina domin ko da aka haife su ya daɗe da rasuwa. Abin mamaki da ya faru bana shi ne da na zo tare da wani ƙanena, wanda ya taɓa aiki a ofishin, sai ya zo ya ce mini ya duba wurin da ake liƙa hotunan malaman da suka shahara amma bai ga hoton mahaifinmu ba! Nan take na bi shi ya kai ni wurin wanda da ma na sha leƙawa wurin. Na duba sarai babu hoton. Sai na tambayi malaman da ke ofishin kuma aka dace da duk sun san da hoton. Suka ƙara duba wurin amma bas u ga hoton ba, sai suka ce lalle wani ya cire hoton domin ga na wani nan an liƙa inda hoton mahaifina yake!! Na ce musu zan ba su wani hoto domin su saka idan har ma ba su da wani ajiye, kuma haka aka yi.

Ba a nan matsalar ta tsaya ba. Dama a ranar na zo ziyarar ne domin in samu kwafen wata shari’a da mahaifin ya yi a 1967. To an share fiye da kwana goma da ni da ma’aikatan wurin ba a samu wannan fayil ɗin shari’ar ba. Ba kuma a nan ta ƙare ba. Fayil ko guda na shari’o’in da mahaifin ya yanke babu. Wani abin mamaki ƙwarai shi ne an samu ganin na shari’o’in wanda mahaifina ya gada tun daga shekarun 1950!! Su kuma na mahaifina akwati kurum aka gani amma babu kome ciki!!! Duk dai wanda ya ɗauke su watakila domin ya ɓatar da tarihi, to bai yi nasara ba, domin a sashen da littattafai da muƙalu suke bai kai gare su ba, a nan ne kuwa ƙanen nan nawa ya yi aiki. Ɓarawon bai fara gwada zuwa can don in har lokacin da ƙanena yake aiki ne to kuwa zai damƙe shi jabau!

Abin da wannan ke nuni shi ne ashe watakila ba Turawa kurum suke satar kayan tarihinmu ba, har da ‘yan ƙasa. Abu na biyu shi ne wannan gidan tarihi da ma sauran gidaje irinsa suna bukatar ƙarin tsaro kuma ƙwaƙƙwara.

Amsoshi

Post a Comment

0 Comments