Citation: Muhammad, I.A. and Umar, M.M. (2024). ‘Kalma’ A Mahangar Malaman Harshe: Taƙaitaccen Tsokaci. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 198-204. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.023.
‘KALMA’ A MAHANGAR
MALAMAN HARSHE: TAƘAITACCEN TSOKACI
Isah Abdullahi
Muhammad
Muhammad Mustapha
Umar
Department of
Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Tsakure:
Tattaunawa a kan abin da ya shafi ‘kalma’, batu ne wanda
manyan malamai suka fi yin magana a kan sa. Daga ciki akwai Aronoff (1976) da
Bauer (1983) da Katamba (1994) da Haspelmath (2011). A Hausa ma, malamai ba su
ba batun wata kulawa ba. A taƙaice, wannan maƙala za ta mayar da
hankali ne a kan ‘kalma’ kawai, don cike wannan giɓi. Da farko an fara da kawo
ma’anarta wadda aka fi amfani da mizani na zahiri wajen bayyana ma’anarta da
nau’o’inta da matsayinta da siffofin kalma a Hausa da kuma yadda ake nazarin
ta. Sakamakon wannan nazari ya fito da ma’anar kalma da nau’o’inta da matsayinta
da siffofin kalma a Hausa da kuma yadda ake nazarin ta.
Fitilun Kalmomi: kalma, ma’anarta, nau’o’inta, matsayinta,
siffofinta
Gabatarwa
Muhimman
tubala da ake nazari a ilimin harshe, su ne: Ƙwayoyin sauti da ƙwayoyin
kalma da kalmomi da yankunan jumla da kuma jumloli. Abin da wannan binciken ya
mayar wa hankali, shi ne, ‘kalma’. Batu ne wanda manyan malamai suka fi yin
magana a kan sa. A
cikin ayyukan nazarin harshen Hausa, musamman a fagen ƙirar kalma, kamar na Abubakar (2000) da Sani (2002) da
Amfani (2007) da Fagge (2013) babu wadataccen bayani a kan ‘kalma’. Amma can
baya Mamman (1987) ya kawo ma’anar kalma a taƙaice, da wasu siffofin kalma a Hausa.Haƙiƙa kalma,
muhimmin tubali ne na ginin kowane harshe. Ganin matsayi da muhimmancinta a
nazarin harshe, ya sa aka ba da fage sukutum! Da ake nazarin kalma. Da
Ingilishi, shi ne ‘Morphology’, da Hausa kuma, ‘Ilimin ƙirar kalma’. Asali ‘kalma’
larabci ce, inda ake ake nufin lafazi ɗaya mai
ma’ana[1]. Da Ingilishi, ana kiran ta
‘word’.
Zancen
sanin ma’anar ‘kalma’ abu ne wanda ko a matakin kimiyyar harshe babu
bakandamiyar ma’ana ɗaya da za a ce, ita ce kalma a dukkan
harsuna. Wannan ya faru ne a dalilin shu’umcinta a wajen bayyana ma’anarta.
Wannan ya sa cikin gogaggun masana ƙirar
kalma Bauer (1983),
yake cewa duk abin da masu harshe suka aminta da shi a matsayin kalma, shi ne
kalma. Saboda irin matsalar da ta haifar ya sa malaman ilimin ƙirar
kalma, suke kauce mata ta hanyar ƙirƙiro wasu keɓaɓɓun kalmomi a nazarinsu. Kamar uwar kalma (lexeme) da
sigar kalma (word form) da tushen kalma (stem). Ba abu ne ɓoyayye
ba a kimiyyar harshe, kasancewar kalma a matsayin wata matsala mai wuyar
sha’ani. Wataƙila, wannan
ne babban dalilin da ya sa akasarin malaman ƙirar kalma a Hausa, ba su farawa da bayanin kalma, kafin
su tsunduma cikin nazarin ƙirar kalma,
gudun ruɗar da ɗalibai.
A taƙaice, wannan maƙala
za ta tattauna ne a kan ‘kalma’, a mahangar malaman harshe. Nazarin
zai fara da ma’anar kalma da nau’o’inta da matsayinta da siffofinta a
Hausa da kuma yadda ake nazarin ta. Don sauƙaƙa
gabatarwar, an kasa maƙalar zuwa
waɗannan sassa: Gabatarwa da kalma a mahangar malaman
harshe. Ƙarƙashinsa akwai, ma’anar kalma da nau’o’inta
da matsayinta da siffofin kalma a Hausa da kuma yadda ake nazarin ta. Sai a
kawo sakamakon nazari da kammalawa.
‘Kalma’ A Mahangar Malaman Harshe
Harshe wata
tsararriyar hanyar sadarwa ce ta ɗan adam. Tubalan da suka gina maganar da mutum yake yi,
ya ƙunshi: sautuka da kalmomi da kuma jumloli tare da ma’anar da suke
ƙunshe da ita. Wannan kalmomi suna daga
cikin muhimman tubalan ginin maganar ɗan adam.
To, wai mene ne kalma?
Ma’anar Kalma
Asali
‘kalma’ ararriya ce daga harshen larabci. A cikin larabci tana nufin, lafazi ɗaya
wanda yake da ma’ana. Lafazin
yana iya kasancewa suna ko aikatau ko kuma harafi (Jaarimi & Amin,
1973). A wurin malaman harshe, ba abu ne mai sauƙi ba, bayyana ma’anar kalma.
Bauer
(1983:8) ya ce:
‘The
definition of the word has been for a long time, a major problem for linguistic
theory’
Fassarar
marubuci:
‘Ma’anar
kalma wata matsala ce mai daɗaɗɗen tarihi a ra’in ilimin ƙimiyyar harshe’
Spencer
(1991:41) ya jaddada wannan magana da cewa:
The whole
chapter 1 was concerned with words, their formation and their inflection, yet
we have not explained what a word is and how one is to be recognized. This is
far from being trivial question; indeed, it is one of the most difficult and
important problems in morphological theory.
Fassarar
marubuci:
Babi na ɗayan
gaba ɗayansa, ya mayar da hankali ne a kan kalmomi, yadda ake
gininsu da kumburarsu, amma kuma ba a yi bayani ba a kan abin da ake nufi da
kalma da yadda za a gane ta in aka gan ta. Tabbas! Tambaya ce mai ma’ana, amma
haƙiƙa,
batu ne mai wuyar sha’ani matuƙa, a cikin
ra’in nazarin ƙirar kalma.
Haka ma,
Spencer (2006:101) shi me yana cewa:
‘The
concept of ‘word’ is notoriously difficult to pin down’
Fassarar
marubuci:
‘Batun
ma’anar kalma al’amari ne mai wahala wajen tabbatarwa’
Alal
misali, a Ƙamusun Hausa shafi 227-228, an ba da ma’anar
kalma, da:
‘Ƙwayar lafazi ko furuci mai cikakkiyar ma’ana’
Idan aka ɗora
wannan ma’ana a bisa faifan nazari, za a ga cewa ‘kalma’ ba ƙwayar furuci ba ce. Misali:
·
gidaa
·
noomaa
Waɗannan
dukkansu kalmomi ne, masu ƙunshe da
lafuzza ko furuci guda huɗu-huɗu. Wato furucin [g], [i], [d], [aa], [n], [oo], [m],
[aa]. Wataƙila, sai dai a ce wani ‘yanki’ ko
‘sashe’ ko ‘tubali’ na magana. Sannan duk a ciki, an siffanta kalma ‘mai
cikakkiyar ma’ana’. A fahintar malaman harshe ba dole ba ne kalma, ta kasance
mai ma’ana (content) tana iya zuwa mai wani aiki na nahawu (functional).
Misali:
·
Ali yaa
tafi makaranta
A nan ‘Ali’
da ‘tafi’ da ‘makaranta’, duk suna da ma’ana, kuma sun fito ne daga azuzuwan
kalmomi daban-daban. Amma ‘ya’, ba wata ma’ana take da ita ba, aikin da take
yi, shi ne fayyace sunan da ya gabace ta, ta fuskar ‘jinsi’, da ‘adadi’, da
‘mutum’ da ’muhalli’[2]. Mamman (1987:1) yana cewa:
“An fassara
kalma a matsayin zance maI cikakken ‘yanci kamilalle, wadda take iya dogara da
kanta a cikin jumla ta kuma yi ma’ana”.
Idan aka
duba ma’anar da kyau, za a lura cewa ba kowa ce kalma take da ‘yanci ba, domin
akwai kama ɗafi ‘clitics’, kamar ‘-r’da ‘ta’, ko ‘-n’ da ‘na’. Haka
ma, akwai ‘a’ a matsayin harafi, kuma a matsayin kalma in ta fito a cikin
jumla, za ta iya ba da ma’ana ne kawai, in an haɗa
ta da wata kalma. Misali:
·
a kan
kujera.
Haka ma,
Bunza (2002:xx) yana cewa:
‘Kalma:
Cunkoson baƙi da wasali wuri ɗaya
don su ba da ma’ana ɗaya, misali “mutum”, ”Yaro”’
Akwai wasu
kalmomi a Hausa, waɗanda ba su ƙunshe da cunkoson
baƙin da waslin, tsintsar wasula ne ko baƙaƙe kawai.
Misali:
·
a
kan teburi
·
dokin
Ali ne da doki na Ali ne.
·
rigar
Kande ce riga ta Kande ce.
A misalan
da suke sama, an ga inda harafin wasalin ‘a’ ya zo a matsayin kalma, haka ma
‘-n’ da ‘-r’ a matsayin kalmomin ‘na’ da ‘ta’ (Skinner, 1977: 74-75, Anderson,
2005, Spencer, 2012,). Wannan yana ƙara
fito muna da shu’umcin kalma a bayyane. To wai wace ma’ana
za a bai wa ‘kalma’?
Ga ta bakin Bauer (1983:9) inda yake cewa:
...whatever a word is, it is not the same thing in all languages: it may not be possible to provide, for this sense of ‘word’, a definition which is valid in all languages except ‘a word is what native speakers think a word is’ (see Matthews, 1972:§7-5). Such a definition would not be of any great value in linguistic analysis’
Fassarar
marubuci:
‘...duk
abin da ake nufi da kalma, tabbas! Ba abu ce mai siffa ɗaya
a duk harsuna ba, ba zai yiwu a samar da wata bakandamiyar ma’ana, wadda za ta
game dukkan harsuna ba, sai wata ma’ana hana-rantsuwa, inda aka ce ‘ kalma dai
ita ce wadda masu harshe suka aminta da kasancewarta kalma’ (Don karin bayani,
a duba littafin Matthews (1972, babi na 5 zuwa 7). Sai dai kash! Wannan ma’ana
lami ce a fagen nazarin kimiyyar harshe’
A ra’ayin
Di Scuillo & Williams (1987) sun nuna, ana iya ba da ma’anar kalma ce kawai
ta fuskar siffofinta. Inda suka kawo siffofi uku da kalma take iya zuwa da su
cikin harshe. Kamar haka:
a.
kalma a
matsayin mai ƙunshe da
tubalan ƙwayoyin kalma (morphological objects).
b.
kalma a
matasayin tubalin ‘yantacce na ginin jumla (syntactic units).
c. kalma a matsayin jerin gwanon kalmomi (listeme).
Haka ma, a
Haspelmath (2011) ya kawo hanyoyi har takwas da malaman harshe suka fi amfani
da su, wajen ba da ma’anar ‘kalma’. Kamar:
a.
ma’ana
b.
tsarin
sauti
c.
ƙa’idojin rubutu
d.
ƙirar kalma da ginin jumla
e.
fahimtar
masu harshe
f.
shu’umci
g.
yadda take
zuwa a cikin harshe
h. gwada duka waɗannan sharuɗa
Wataƙila, wannan fahimta ce ta yi tasiri a kan Anderson
(2015:12) har yake bai wa kalma wannan ma’ana:
‘...a word
is a fundamentally a unit of mutual association among several sorts properties
‘
Fassarar
marubuci:
‘...kalma
tubali ce ta gamin-gambiza daga abubuwa daban-daban’
Haspelmath
(2023:285) yana cewa:
“A word is
(i) a free morph, or (ii) clitics, or (iii) a root or a compound possibly
augmented by nonrequired affixes and augmented by required affixes if there
any”
Fassarar
marubuci:
“Kalma ita
ce (i) ‘yantacciyar ƙwayar kalma
ko (ii) kama-ɗafi ko (iii) saiwa ko kuma harɗantawa
mai iya zuwa tare da ɗofanen da ya dace, idan akwai”
A ƙarshe, daga abin da aka fahinta daga bayanin magabata,
ana iya cewa: ‘kalma’ wata tubali ce ta ginin magana a harshe, wadda ake
samarwa ta hanyar karo-karo. Sannan ba a sami wata musantawa ba daga harshe ko
masu harshe ko kuma ilimin harshe.
Nau’o’in Kalma
Masana sun
kasa kalmomi ta fuskoki daban-daban. Da farko akwai kalma sassauƙa da
mai sarƙaƙiya. Misali,
kamar:
·
bi da
biyayya
·
ƙi da ƙiyayya
·
so da
soyayya
A nan,
kalmomin ‘bi’ da ‘ƙi’ da
‘so’, dukkansu sassauƙa
ne sun ƙunshi ƙwayoyin kalma ɗaya-ɗaya.
Amma, amma ‘biyayya’ da ‘ƙiyayya’ da
‘soyayya’. Dukkansu masu sarƙaƙiya ne,
domin kowace kalma tana ƙunshe da ƙwayoyin kalma fiye da ɗaya.
Kalmar ‘biyayya’, tana ƙunshe da ‘bi’,
sannan ɗafin tsirau da aka liƙa mata wato ‘-yayya’.
Haka abin yake ga sauran kalmomi, wato kamar ga ‘ƙi’, da ɗafin ‘-yayya’, sai ‘so’, da ‘-yayya’. Wannan ya nuna cewa
a fasalin ginin kalmomin Hausa, ana samun haɗuwar
yantacciyar kalma da turkakkiya cikin kalma ɗaya
ko kuma turkakku tsintsa ko kuma ‘yantattu tsintsa.
Har wa yau, akan sami kalmomi masu buɗaɗɗen
tsari da masu rufaffen tsari. Masu buɗaɗɗen
tsari, kalmomi ne waɗanda a kullum suke samun ƙaruwar baƙuwar
sabuwar kalma. Misali kamar, suna da aikatau. Su ko masu rufaffen tsari, ya haɗa
da kalmomi waɗanda har abada ba su samun ƙaruwar sabuwar kalma a cikinsu. Kamar wakilin suna da
mallaka ko nasaba.
Malaman ƙirar kalma, sun ƙirƙiro wasu keɓaɓɓun kalmomin nazari, saboda rikicin da ‘kalma’ ta haddasa
wajen nazari. Waɗannan kalmomi, sun ƙunshi:
Uwar kalma (lexeme) da sigar kalma (word form) da tushen kalma (stem) da samammiyar kalma (existent word) da kuma
ƙiyastacciyar kalma (possible word).
Dukkansu nau’o’in kalmomi ne a nazarin ƙirar
kalma. Uwar kalma a nazarin ƙirar kalma
wata nau’in kalma ce wadda take a baɗini
(wadda ba a gani), amma kuma ita ce tushen waɗanda
ake gani a zahiri a matsayin kalmomi. Ana rubuta ta da manyan kalmomi. Misali:
·
YARO
·
yaro
·
yarinya
·
yara
A waɗannan
misalai da suke a sama, wadda aka rubuta da manyan baƙaƙe ce uwar
kalma. Sauran kuma, sigoginta ne na zahiri, tilonsu ‘sigar
kalma’. A lura cewa ita sigar kalma, ana samar da ita ne ta
fuskar ‘adadi’ wato yaro da yara, ko kuma ta fuskar jinsi, yaro da yarinya. Ita
ko tushen kalma ita ce kamannin farko na kalma. Misali, kalmar ‘yaro’ babu wata
kalma da za a ce an tsago ta ne daga wurinta. Amma, idan aka ce ‘yarinya’ ko
‘yara’, waɗannan kam, ana iya cewa daga ‘yaro’ ne aka fitar da su.
Ita ko samammiyar kalma, kalma da take a taskace cikin rumbun harshe. Misali
‘kwalba’, samammiyar kalma ce. Amma, ‘kwalbe’ ko ‘kwalbewa’, ƙiyastattu ne, ba dole ba ne a same su cikin rumbun
kalmomin Hausa. Wato dai, ƙirƙirarru ne daga baya. Duk kasancewar asalinsu daga ‘kwalba’
ne. A ƙarshe kuma, ana raba kalmomi zuwa
azuzuwan kalmomi. Musamman suna da aikatau da masu yi musu hidima.
Matsayin Kalma da Siffofinta
Nazarin kalmomi da jumloli, shi ne abin da
nahawu kowane harshe ya ƙunsa a taƙaice (Amfani, 2007).Wannan ya nuna kalma a matsayin wani
muhimmin ginshiƙi daga
cikin ginshiƙan nahawu. Har wa yau, manyan abubuwan
da ake nazari a harshe, su ne ‘sautuka’ da
‘kalmomi’ da ‘jumloli’.
Wannan ya nuna kalma a matsayin babban tubalin da ake nazari cikin harshe. Malaman
ilimin ƙirar kalma (Kamar Haspelmath, 2002) sun
nuna idan aka kalli fasalin kalmomin harsunan duniya, ana iya kasu su gida
biyu: Masu wararrun kalmomi (analytic) da masu ƙulallun kalmomi (synthetic)[3].
Wannan ya danganta a kan adadin ƙwayoyin
kalma da ake samu a cikin kowace kalma ɗaya. Inda
aka sami kowace ƙwayar ma’ana
a matsayin ƙwayar kalma ɗaya,
da Ingilishi, ita ce ‘agglutinating’. Inda aka sami ƙwayar kalma ɗaya da tarin ma’anoni, to, sai a kira shi da Ingilishi
‘fusional’. In kuma, aka sami harshe a cikin kalma ɗaya,
ana iya cire ƙwayoyin
kalma daban-daban, to kuma, ana ce masa ‘polysynthetic’.
Idan aka
waiwayi kalmomin Hausa, a zahiri, suna zuwa ne da siffa biyu: Siffa ta asali da
siffa ta musamman. Misali: ‘gida’ da ‘kama’, da ‘fari’ da ‘duƙe’ kalmomi ne masu siffa ta asali. Amma, ‘a’ da
‘fari-fari’, tuma-ƙasa da ‘agwagwa-da-buje’ da
‘a-kori-kura’, dukkansu kalmomi ne amma masu siffa
ta musamman.
Yadda Ake Nazarin ‘Kalma’
Masana
ilimin ƙirar kalma sun shimfiɗa
hanyoyin huɗu na nazarin kalma, kamar haka:
a.
Hanyar
bayanin ƙwayoyin kalma.
b.
Hanyar
bayanin siga da ma’ana.
c.
Hanyar
bayanin matsayin kalma ta fuskar tsira da kumbura.
d. Hanyoyin da aka bi wajen ƙera kalma (Abubakar 2000, Haspelmath 2002, Aronoff &
Fudemann 2005, Muhammad 2022).
Hanya ta
farko, wato nazarin kalma ta amfani da tubalin ‘ƙwayar kalma’. Inda ake fitar da ƙwayoyin kalma ɗaya bayan ɗaya,
tare da bayanin aikin da suke yi da kuma hukunce-hukunce na wasu fannonin
ilimin harshe ko ma waɗanda ba harshe ba a wajen ginin kalma. Misali:
·
daidaitaawarsu
a. Wannan kalma, tana ƙunshe
da ƙwayoyin kalma har guda biyar. Ta farko,
/daidai-/, ‘yantacciyar ƙwayar kalma
‘yar ajin suna mai nuni ga abin da yake kishiyar kure.
Sannan alamar ‘–‘[4], tana nuna
gurbin da ake wa kalma ƙari. Da
Ingilishi, ana ce masa ‘Pivot’[5].
Sai /-taa-/, ɗafa-ƙeya ne,
kuma a nan, ya yi aikin mayar sun ‘daidai’
zuwa aikatau ‘daidaitaa’. Sai kuma, ɗafa-ƙeya na biyu wato /-waa-/, wanda yake aikin mayar da
aikatau suna. Wannan ya sa ake kiran sa da suna
ɗan aikatau (deverbal
noun). Bayansa, akwai harafin kama-ɗafi /-r-/[6] mai aikin nuna mallaka. Sai
rufaffen ɗafi wato ƙwayar kalma
da take nuna masu mallakar wato /-su/. An ce masa rufaffen ɗafi
ne, saboda babu sauran ɗafin da za a ƙara a kan sa.
b. Sai kuma bayanin kalma, ta la’akari da ‘siga’ da
‘ma’ana’. Siga da Ingilishi ita ce ‘form’. Ita ko ‘ma’ana’ ‘meaning’. Idan aka
haɗa su, a wuri ɗaya, sai a
ce ‘form and meaning’. Sannan an fi yin irin wannan nazari ne a wajen yin
bayanin kumbura.
Misali:
·
yaaroo
·
yaarinyaa
·
yaaraa
Idan aka
dubi waɗannan misalai na kalmomi da kyau, za a ga cewa, dukkansu
sun yi tarayya ta fuskar ‘saiwa’ /yaar-/. Inda suka bambanta a ƙarshensu. Domin ta farko, ta ƙare ne da ɗafin /-oo/. Ta biyu, ta ƙare ne da ɗafin /-inyaa/. Ta uku, ta ƙare ne da ɗafin /-aa/. Wannan ne ya bambanta su ta fuskar siga da
kuma ma’anar kanta. Domin, ɗafin /-oo/, yana aikin nuna adadin tilo da jinsin namiji,
kuma shi ne madubi ga abin da zai biyo gaba. Haka ma, ɗafin
/-inyaa/ mai aikin nuna adadin tilo amma jinsin mace. Sai kuma ɗafin
/-aa/, mai aikin nuna jam’i. Wannan ne bayani ta fuskar siga da ma’ana. A
kodayaushe, a wannan hanyar nazarin ana kallon bambanci da tasirin da bambancin
siga ya haifar.
c. Hanyar nazari ta la’akari da ‘tsira’ da ‘kumbura’, ana
lura ne da matsayin da kalma ta sami kanta ta waɗannan
rassa na ilimin ƙirar kalma.
Misali:
·
yaaroo da
yaaraa
·
yaaroo da
yaarantaa
A waɗannan
misalai, layin farko ‘yaaroo da yaaraa’, kalmar ‘yaaroo’ ce ta kumbura ta
fuskar adadi (tilo ko jam’i) daga tilo zuwa jam’i. Kuma ƙaramar kumbura ce wadda take faruwa a matakin kalma (
Booij, 2007). Ita ko ‘yaroo da yarantaa’, tsira ce ta fuskar ma’ana.
Inda aka sami sabuwar ma’ana daga mutum wanda yake a zahiri zuwa ɗabi’a
wadda take a ɓoye (Scalise, 1984).
d. Sai kuma ta ƙarshe,
nazarin kalma ta la’akari hanyoyin da aka bi wajen samar da kalma. Misali:
·
yaarantaa
·
kaciici-kaciici
·
aikin-baban-giwa
Idan aka ba
da irin waɗannan jinsin kalmomi, hanyar da aka bi wajen gina su. Ta
farko, asalin kalmar ‘yaaroo’ ne, sai aka cire ɗafin
‘-oo’, sai aka maƙala ɗafin
‘-antaa’. Sai aka tayar da ginin kalmar ‘yaarantaa’. Ita ko ‘kaciici-kaciici’,
cikakken ninki ne (complete reduplication), inda aka maimaita kalmar ‘kaciici’.
Ita ko kalmar ‘aikin-baban-giwa’, harɗaɗɗiyar
kalma ce (compound word), inda aka ɗauko
kalmomi daban-daban, aka gina kalma ɗaya.
Wannan ya
nuna a nazarin ƙirar kalma,
duk wata kalma da za yi nazarin ta, ya kamata a lura da hanyar da ya fi dacewa
a bi a yi nazarin ta. Wato hanyar da za ta fito da fa’idojin da za a ƙaru da su.
Sakamakon Nazari
1.
Wannan
nazari ya fito da sarƙaƙiyar da take cikin bayyana ma’anar
kalma. Kamar yadda malaman harshe suka nuna.
2.
Ta fito da
ma’anar kalma.
3.
A rattabo
nau’in kalma.
4.
An bayyana
matsayi da siffofin kalma a Hausa.
5. An fito da yadda ake nazarin kalma a ilimin ƙirar kalma.
Kammalawa
Wannan maƙala ta yi bayani ne a kan ‘kalma’ a mahangar malaman
harshe. An yi
wannan bayani ne domin
cike giɓi. Saboda ba a cika kawo irin wannan batu ba, a cikin
ayyukan magabata. An fara da gabatarwa, ciki an bayyana ma’anar kalma da
nau’o’inta da matsayinta da siffofinta da ma yadda ake nazarin ta a fagen nazarin ilimin ƙirar kalma. Nazarin ya fito da sarƙaƙiyar da
take tattare da ba da ma’anar kalma. Sannan maƙalar ta kawo ma’anar kalma da nau’o’inta sai kuma yadda
ake nazarin ta, ƙarshe
kammalawa ce.
Manazarta
Abubakar, A.
(2001). An Introductory Hausa Morphology. Maiduguri: University of
Maiduguri.
Amfani, A.H. (2007). Hausa Morphology. In Basic
linguistics for Nigerian Languages Teachers (ed) Ore Yusuf. (Page 138-148).
Anderson, R. Stephen (2005). Aspects of the Theory of Clitics. Oxford: Oxford University Press.
Anderson, R. Stephen (2015). The Morpheme: Its Nature and
Use. In The Oxford Hand Book of
Inflection. (eds) Matthews Bearnman.pp11-33. Oxford: Oxford University
Press.
Aronoff, M. (1976). Word
Formation in Generative Grammar. MIT: Massachusets Institute of Technology.
Aronoff,
M. Fudeman, K. (2005).What is Morphology? Hong-kong: Blackwell
Publishing.
Bauer, L. (1983). English
Word Formation. Cambridge: Cambridge University Press
Bauer, L. (1988). Introducing Linguistics
Morphology. Edinburgh: Edinburgh University Press.
Bello, S. (Edts).(2006). Ƙamusun
Hausa Cikin Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano .
Booij, G. (2007). Grammar
of Words: An Introduction to Linguistic Morphology.
Bunza, A.M. (2002). Rubutun
Hausa: Yadda Yake Da Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Legas: Ibrash
Islamic Publication Centre.
Di Suillo, A. & Williams, E. (1984). On the Definition of Word.
London:MITPress.
Fagge,
U.U. (2013). Ƙirar Kalma A Hausa. Zaria: Maɗaba’ar Jami’arAhmadu Bello
Zaria.
Haspelmath, M. (2002). Understanding Morphology. London: Hodder Education.
Haspelmath, M. (2010). Understanding Morphology (Second Edition). London: Hodder Education.
Haspelmath, M. (2011). The Indeterminacy of Word
Segmentation and The Nature of Morphology and Syntax. Folia Linguistics. 45(1).pp31-80.
Haspelmath, M. (2023). Definin Word. WORD. 69:3, 283-297.
DOI:10.1080/00437956.2023.2237272.
Jaarimi, A.& Aminu, M. (1973). Annahawul Alwadhihu.Riyal:Ihyaul Atturathul Alwa Alislami.
Katamba, F. (1994). English
Words. London: Roultledge.
Mamman, M. (1987). Kalmomin Hausa Da Halayensu. Takardar
da aka gabatar a babban ƙawa wa juna
ilimi na huɗu a kan Harshe Adabi da Al’adu wanda Cibiyar Nazarin
Harsuna Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano, ta shirya.
Muhammad, I.A. (2020). Kalmar ‘Zamfaraa’ A Mizanin Ilimin
Ƙirar Kalma. A paper presented at Fourth
National Conference Theme: Zamfar Kingdom ‘Social and Political Transfomation
from 14th Century to date’. February 25th to 28th.
Muhammad, I.A. (2022). Mene ne Ilimin Ƙirar Kalma? Maƙalar
da aka gabatar a Tsangayar Fasaha da Nazarin Ilimin Addinin Musulunci, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
New York: Oxford University Press.
Sani,
M.A.Z. (2002). Alfiyyar Mu’azu Sani 1: Tsarin Sauti Da Tasarifin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Scalise, S. (1984). Generative
Morphology. Foris Publication: Dorddrecht-Holland.
Skinner, N. (1977). Hausa
Grammar: For Secondary Schools and Colleges. Zaria: Northern Nigeria
Publishing Company.
Spencer, A. (2006). Morphological Universals. In Linguistic Universals. (Edts) Mairal,
Ricardo and Gil, Juana. pp101-129.
Spencer, A.& Luis, A.R. (2012). Clitics: An Introduction. Cambridge: Cambridge University Press.
Yu,
A.C. (2003). Morphology And Phonology of Infixation. Doctoral
Dissertation, University of Califonia,
Berkeley.
Yu, A.C. (2007). A Natural History of Infixation. Newyork: Oxford University Press.
[1]
Ina godiya ƙwarai ga Dr. Aliyu
Malami wanda ya ƙara
mini haske a kan ma’anar kalma a Larabci.
[2] Mutum
‘Person’, muhalli kuwa ‘location’.
[3] Akwai
bayanai daban-daban a kan wannan kason da aka yi kalmomin harsunan duniya. Ƙalubalen da ake fuskanta
wajen wannan kashe-kashen, shi ne akan sami harshe ɗaya,
yana nuna halayya daban-daban, sai a kasa gane inda za a sanya a harshe.
[4] Alama
ce da ake amfani da ita, wajen nuna iyakar ƙwayar kalma.
[5] Kamar
yadda ya zo a Yu (2003, 2007)
[6] An kira shi ne da ‘kama-ɗafi’, yakan zo ne da
siffa biyu, yakan zo da siifar ɗafi ‘-r’, ko cikakkiyar
kalmar ‘ta’. Domin ana iya cewa ko daidataawarsu ce ko kuma, daidaitaawa tasu
ce
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.