Ticker

6/recent/ticker-posts

Haramta Wakar Soyayya Tarihi Ne Ke Maimaita Kansa

HARAMTA WAƘAR SOYAYYA TARIHI NE KE MAIMAITA KANSA (1)

A cikin tarihin adabin Larabawa, ba a samu wata waƙa ta soyayya da aka haramta a hukumance ba. Duk da haka, akwai mawaƙa da suka fuskanci hukunci ko ladabtarwa saboda salon waƙoƙinsu ko abubuwan da suka furta a cikin waƙoƙinsu. Misali, Al-Ahwas Al-Ansari, wani shahararren mawaƙi daga Madina a zamanin Daular Umawiyya, ya fuskanci ladabtarwa saboda salon waƙoƙinsa.

Waƙoƙinsa na soyayya sun saba wa al'adun zamantakewa na lokacin, musamman ma yadda ya ambaci sunayen mata masu daraja a cikin waƙoƙinsa. Hakan ya sa aka kore shi daga Madina zuwa tsibirin Dahlak a cikin Tekun Bahar Maliya, inda ya zauna a cikin ƙunci har zuwa bayan rasuwar khalifa Umar bin Abdulaziz.

Haka kuma, Imru' al-Qays, wani shahararren mawaƙi daga zamanin Jahiliyya, ya fuskanci suka daga iyayensa da al'ummarsa saboda waƙoƙinsa na soyayya da suka bayyana sha'awa da kuma ambaton mata da sunayensu. Wannan ya sa mahaifinsa ya kore shi daga gida, duk da cewa daga baya ya karɓe shi bayan ya tuba.

Waƙar da aka fi ce-ce-ku-ce a kanta daga cikin waƙoƙin Imru al-Qais ita ce wadda ta ƙunshi baitin da ke bayyana ganawa da mace a cikin daji, da kuma abubuwan da suka faru a tsakaninsu cikin yanayi mai ban shaawa.

Malaman addini bayan zuwan Musulunci sun soki baitin saboda zafinsa, musamman wajen bayyana abin da ya faru tsakaninsa da wata mace a cikin dusar ƙanƙara da kuma yadda ya siffanta jikinta da motsinta.

Ga baitin da ake ce-ce-ku-ce a kai:

ويومَ دخلتُ الخِدرَ خدرَ عنيزةٍ

فقالت لك الويلاتُ إنك مرجلي

تَقول وقد مالَ الغَبيطُ بنا معًا

عقرتَ بعيري يا امرأَ القيسِ فانزلِ

فقلتُ لها سيري وأرخي زمامهُ

ولا تُبْعديني عن جَميلٍ مُرَحَّلِ

Dalilan da yasa baitin ya tayar da kura:

1. Ya bayyana ganawa da mace a rufaffen wuri (khidr = tantin mace).

2. Kwatanta yadda suka hau dabbobi tare da magana mai nuni da kusanci jiki.

3. Kalmomi masu nuni da nishaɗi da motsa sha’awa.

4. A mahangar addini daga baya, an soki baitin saboda yana nuna halin da ya saba da tsarkin mace, musamman budurwa daga dangin manya.

A zamanin jahiliyya babu tsarin shari’a da ke hana irin waƙar. Imru al-Qais ya kasance ɗan sarki kuma mashahurin mawaki. An fi girmama shi saboda fasaharsa, ba wai halayensa ba.

Amma bayan zuwan Musulunci, malamai da masana suka dinga sukar wannan baitin da makamantansa, suna ganin cewa ya kamata a kalle su da kula ko a hana yawan karantawa, saboda yana haifar da fitna da sha’awa.

Umar ibn Abi Rabi'ah shi ma daya ne daga cikin mawakan soyayya na Larabawa da waƙoƙinsa suke yawan haddasa ce-ce- ku-ce amma  ba a taɓa haramta su ta fuskar doka ko tsarin mulki ba, amma manya daga cikin baitocin ghazal dinsa sun sha suka sosai daga malaman addini da masu kula da ɗabi'a, musamman saboda salon soyayya da ya ke cike da ambaton mata manya a fili, da kuma maganganun da ke da nuni da sha'awa.

Ɗaya daga cikin baitocin da suka fi jawo ce-ce-ku-ce yana farawa da:

"Ku masu sa ido, ba za ku bar mu mu huta ba?"

Da kuma wakarsa mai suna"

"Ni mai bautar Layla ne, Allah kada Ya sa in ƙi ta."

Waɗannan waƙoƙin sun ja hankali saboda:

Ya ambaci sunayen mata kai tsaye (kamar Layla, Hind, ko Thuria).

Ya bayyana labaran soyayya yayin aikin Hajji wurin mai tsarki na Musulmi da ba a ambaton wasu maganganu na duniyanci a wajen.

Waƙoƙinsa sun yi nuni da ganawa a ɓoye da  rubuce-rubucen soyayya da kallon juna a ɓoye, waɗanda duk ana ɗaukar su da rashin ɗabi'a ko zunubi a tsarin addinin Musulunci.

Malaman addini irin su Al-Ghazali da wasu sun soki waƙoƙinsa saboda suna haifar da fitina (jaraba).

Bayyanar soyayya da sha’awa a cikin wurare masu tsarki ya yi matuƙar tayar da kura.

Ambaton sunayen mata a fili, musamman daga manyan iyalan Kurayshawa, an ɗauke shi  a matsayin abin kunya.

Amma duk da haka, waƙoƙin Umar ibn Abi Rabi'ah ba su fuskanci haramci daga doka ba, amma da dama daga cikin ghazal ɗinsa musamman waɗanda suka haɗa tsarkakan batutuwa da nuni da soyayya ko sha'awa sun fuskanci suka daga malamai da masu tsattsauran ra'ayi.

Da alƙalamin:
Dr. Abdulrahman Aliyu Katsina 

Amanata Hamisu Breaker

Post a Comment

0 Comments