Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Kunna Karatun Alqur'ani Ta Sa Earpiece Tana Bin Karatun A Cikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Wata ce naga zatayi sallar tarawih sai ta kunna karatun Qur'ani tasa earpiece, wai sai ta rinka bin karatun sabida ta tsawaita sallar. shin yin hakan ba laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Qwarai kuwa akwai laifi domin kuwa hakan da ta yi bidi'a tayi, babu wanda yasata yin hakan.

Alqur'ani yakamata ta ɗauka ta riqe tana kallo tana karantawa, inkuma bata iya karatunba, saita samu wata sura wacce ta haddace koda qulhuwallahu ne, sai takama qulhuwallahu tayita maimaitawa, kai koda aya ɗaya rak ta haddace to ya halasta kiyita maimaita wannan ayar harki gama tsayuwar kamar ILAHINNAS misali wannan ayar ace ita kawai ta iya acikin alqur'ani toh babu laifi tayita maimaitata har tagama tsayuwan darenda zatayi, domin hadisi ya tabbata manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yi tsayuwar dare guda babu ayarda yake karantawa face wani yankin wata aya can suratul ma'ida:

إِن تُعَذِّبْهُمْ فَإِنَّهُمْ عِبَادُكَ وَإِن تَغْفِرْ لَهُمْ فَإِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ

''Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bayinKa ne, kuma idan Ka gafarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima.'' (suratul Mâ'ida Aya ta 118)

Wannan yankin ayar ita ce yayita maimaitawa har yagama tsayuwar dare, kuma kasan dai tsayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ba irin taka bace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments