Ticker

6/recent/ticker-posts

Abokansa Sun Yaudare Shi Ya Aikata Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. Ni Magidanci ne ina da aure. To tun kwanakin baya matata ta yi tafiya ba ta dawo ba. To akwai wasu abokaina da suke harkar neman mata, rannan sai suka kawo 'yan matansu nan gidana, Nima ina gidan alokacin ashe sun kawosu ne da niyyar za su aikata lalata dasu. Naso in hanasu amma ina tsoron za su ga kamar na yi musu gadara tunda gidana suka zo. Na zauna cikinsu muna zance har shaiɗan ya rinjayeni har na yi zina da wata daga cikin matan nan da suka kawo. To tun daga ranar kullum sai na yi kuka saboda bakin ciki da tunane-tunane. Na kasa samun kwanciyar hankali domin tunda nake ban taɓa aikata wannan mummunan aikin ba sai ranar nan. Na rasa yadda zan yi. Shin Malam kana ganin Allah zai gafarta mun, ko kuwa sai na sanar da matata idan ta dawo, tunda kamar naci amanarta ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Hakika ka tafka babban kuskure. Domin zina tana cikin Kaba'irori wato zunubai mafiya girman laifi awajen Allah. Awani hadisi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa ya yi "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girman laifi kamar maniyyin da namiji ya sanyashi acikin mahaifar matar da ba ta halatta gareshi ba".

Sannan bayan haka ka cire kanka daga cikin sahun muminai ta dalilin wannan mummunan aikin. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "mazinaci ba zaiyi zina alokacin da yake zina alhali yana mumini ba". Wato ana cire wa mutum rigar imani ne alokacin da yake aikata zina ko sata ko shan giya. Ba za a dawo da ita gareshi ba, har sai bayan ya tuba.

Tunda kayi nadama kuma kana da niyyar tuba, to ga hanyoyin tuban kamar haka:

1. Yin nadama bisa abin da ka aikata.

2. Ɗaukar niyyar har abada ba zaka sake aikata wannan zunubin ba. Yanke alaqah tare da nisantar duk wani dalilin da zai kaika zuwa ga sake aikata wannan laifin.

3. Dena aikata laifin nan take ba tare da jinkiri ba.

Sannan yana daga cikin cikar tubanka ka yanke alaqah da waɗannan miyagun abokan naka domin akwai alamar watakil su sun riga sun saba da wannan mummunan aikin. Ci gaba da hulda dasu zai iya sake jefaka cikin rudanin nan nasu. Kada su sake yaudararka.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya fadi muhimmancin abokai nagari da kuma illar haɗa abota da mutanen banza, a inda ya ce : "kada kayi abota sai da mumini, kuma kada wani yaci abincinka sai mai tsoron allah". (Abu Dawud, Tirmidhiy da Ahmad ne suka riwaitoshi).

Malamai suka ce wannan hadisin yana Kaɗaitar da mutum musulmi ne akan cewa lallai ya kasance tare da mutanen kirki kuma ya guji abokantaka da mutanen banza misali kamar kafirai, munafukai, ko masu aikata miyagun laifuka irin su zina, shaye-shaye da sauransu. Domin kuwa abota takan chanza wa mutum tarbiyyarsa da halayyarsa.

Acikin wani ingantaccen hadisi kuma wanda Imam Abu Dawud da Tirmidhiy suka riwaito ta hanyar Sayyiduna Abu Hurairah, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa ya yi : "mutum yana kan addinin abokinsa ne. don haka kowanne daga cikinku ya rika lura da irin mutumin da zai yi abota dashi".

Ma'anar wannan hadisin ita ce: wato lallai ne ka rika zabar irin mutanen da zaka Qulla abota dasu domin tarayya irin wannan takan yi tasiri wajen lalacewa ko kyautatuwar tarbiyyar mutum da rikon addininsa. Kamar dai yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya fada acikin wani shahararren hadisi "mutum yana tare da wanda yake qauna"

Don haka nake baka shawarar cewa ka chanza wasu abokai na kirki waɗanda tarayyarka dasu za ta amfaneka awajen Allah, banda irin waɗannan abokan banza waɗanda sai kayi nadamar saninsu aranar Alqiyamah.

Kaci gaba da tuba da kula da ayyukanka na farilla da kyautatawa mahaifanka da makusantanka da masu Qaramin karfi. Idan Allah ya so zai karɓi tubanka ya yafe ma zunubanka. Amma ba sai ka gaya wa matarka abin da ya faru ba, domin kuwa wannan ba ya cikin sharudan tuba, kuma zai iya zama dalilin lalacewar alakarka da iyalinka ko zubewar mutuncinka awajenta.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments