Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Aikata Zina A Ramadan Saboda Tana Son Mallakar Kayan Da Za Ta Saka Da Sallah

TA AIKATA ZINA A RAMADAN SABODA TANA SON MALLAKAR KAYAN DA ZA TA SAKA DA SALLAH

TAMBAYA (255)

Assalamualaikum warahmatullahi wabara katuhu,malam ansha ruwa lafiya y ibadah

Dan Allah ina da tambaya malam

Miye hukuncin wadda ta yi Zina a watan azumi Kuma d rana, Sbd dubu hamsin Batada ko dankunne na sallah ta yi Neman taimako ko bashi Bata samuba,taje ta aikata

Wannan barnar watace tasani nama tambaya assalamualaikum👏

AMSA

Waalaikumus salam warahmatullahi wabarakatuhu

Innalillahi wainna ilaihirrajiun

Ita kam wannan wace irin mace ce mara tsoron Allaah haka

Da watan azumi ?

Aikata zina ko da ba a watan azumi ba haramun ne amman a watan azumin zunubbin nasa yana ninnunkuwa

Allaah Azzawajallah ya ce:

( وَالَّذِينَ لَا يَدْعُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ وَلَا يَقْتُلُونَ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَا يَزْنُونَ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ يَلْقَ أَثَامًا )

الفرقان (68) Al-Furqaan

Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,

( يُضَاعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَيَخْلُدْ فِيهِ مُهَانًا )

الفرقان (69) Al-Furqaan

A riɓanya masa azãba a Rãnar kiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce.

( إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا )

الفرقان (70) Al-Furqaan

Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai.

Abin da na sani shi ne Allaah Azzawajallah yana yafe kowanne irin laifi ga wanda ya ga dama in dai ba mutuwa mutum ya yi yana shirka ba. Allaah Azzawajallah ya ce:

( قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ )

الزمر (53) Az-Zumar

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."

An tambayi Committe Fataawa na Saudiyya akan mene ne hukuncin wanda ya yi zina a watan Ramadan ?

Suka ce:

"Zaiyi Taubatun Nasuha ne, ta hanyar yan ta bawa, idan ba shi da halin hakan sai ya yi azumin watanni biyu a jere, idan ba zai iya ba sai ya ciyar da miskinai 60 sannan kuma zai rama wannan azumin da ya karya (silar zinar) da kuma ya dade bai rama azumin ba zai bayarda kilogram 1 da rabi na alkama"

(Fatawa Al-Lajnah Ad-Da’imah, 9/255)

Yanzu don Allaah matakin lalacewar wasu matan har yakai ace saboda ba su da kayan sallah har sai sun bada kansu anyi zina dasu kuma a watan Ramadan ?

Wannan wanne irin jahilci ne da rashin sanin yakamata. Ko a zamanin jahiliyya mata gori sukewa mazinata ballantana kuma yanzu muna zamani ne da ilimi ya yi yawa sai dai idan ba ka son ka tashi ka nema

Allaah ya kiyaye mu daga aikata danasani

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments