SHIN YA HALLATA MIJINA YA SADU DA NI A ƊAKIN KISHIYATA?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Malam ina da tambaya, mu biyu ne a gurin mijinmu, amma ba mu a tare kowa da garinsa, mukan yi wata uku ba mu haɗu ba sai dai idan za a yi sha'ani tukunna mukan haɗu da juna, to sai wata rana ni na tafi garin da kishiyar tawa take da watan azumi, kuma a lokacin mijin namu yana gurinta, to irin tana zuwa sallar Tahajjud da karfe dayan dare (1:am), to a ranar ma ta tafi sallar, kuma ta tafi ta bar mu a dakinta muna kwance mu biyu da ni da mijina, sai bayan ta tafi sallah sai shi mijina ya nemi ya sadu da ni a gadonta amma sai na ki yarda, na ce ai wannan cin amana ne, to don Allah malam kin amincewan da na yi ina da laifi a gurin Allah? Saboda na roke shi ya yafe min idan na yi ba daidai ba, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, Allah ne mafi sanin dai-dai, amma ni a fahimtata kin yarda da kika yi
bai dace ba, saboda kasancewar da yardarta ta tafi ta bar ku a ɗakin a kwance da ke
da mijin naku, saboda ba sharaɗi ba ne sai a ɗakinki sannan zai iya kusantarki da mu'amalar aure,
matuqar an sami kaiɗaituwar da ba wanda ya san abin da ke gudana a tsakanin
ma'aurata, saboda haka nake fahimtar qin amincewarki da shi a matsayin kuskure.
Duk da dai lamarin yana kunshe da shubhohi.
Ya tabbata a
littafan hadisi da littafan Tafsiri cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya
kusanci baiwarsa Mariyatul Qibɗiyya a ɗakin Nana Hafsa a lokacin da ta tafi ziyartar iyayenta,
sai Nana Hafsa da ta dawo ta same su a ɗakinta, ta dakata ba ta shiga ba, har sai da Mariya ta
fito sai ta shiga ɗakin, da ta shiga sai ta ce wa Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya Manzon Allah a ɗakin nawa, kuma a kan shimfiɗana? Sai Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam bai ji daɗin haka ba, a qarshe ya haramta wa kansa kusantar Mariya,
kuma ya ce kada ta faɗa wa Nana A'isha abin da ya faru, da kuma maganganun da
ya faɗa mata, sai Nana
Hafsa ta yi kuskure ta sirranta wa Nana A'isha abin da ya faru, da faruwar haka
sai Allah ya saukar da suratut Tahreem, wanda a cikinta aka gargaɗi Nana A'isha da
Nana Hafsa a kan wannan abu da ya faru, kuma aka goge haramcin da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi wa kansa ba zai sake kusantar kuyangarsa
Mariya ba...
Abin lura a
wannan qissar shi ne ba a zargi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da abin da ya
aikata na kusantar wancan baiwa tasa a ɗakin Nana Hafsa kuma a kan shimfiɗarta ba. Abin ma da
Allah ya ce shi ne: Don me yake haramta wa kansa abin da Allah ya halasta masa?
Duk da ba an ba da qofar yin hakan ba ne, amma wannan yana nuna cewa idan
lalura ta sa za a iya yin hakan, sai dai barin hakan shi ya fi alheri musamman
a irin zamantakewarmu na aure na wannan lokaci.
Domin samun
cikakken bayanin sai a duba Tafseeeruɗ Ɗabariy ko Tafseerul Qurɗabiy, ko Tafseerul
Qur'anil Azeem na Ibn Katseer a qarqashin surat Tahreem. Ko a duba Almu'ujamul
Ausaɗ na Aɗɗabarániy hadisi mai
lamba ta 2316, ko Sunanud Dáruquɗniy hadisi mai lamba ta 4013.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.