TAMBAYA (202)❓
Assalamu'alaikum
malam barka da safiya
Tambayana
a kan sallah ne malam wai an ce dole kowani musulmi ya san malamin da ya koya mai
sallah?
Ni kuma wallahi bawan da ya koya mun na taso Na ga ana yi ne malam Dan Allah a koya mun 🙏🏼???
AMSA❗
In dai har
ya zama dole a dinga bawa gangar jiki abinci da ruwa don ta tayu to ya zama
dole mutum ya koyi yanda ake bautawa Allaah Azzawajallah don wannan Ibadar ita
ce abinci da abin shan Ruhin kowanne dan Adam kafiri da musulmi, wanda daman
babban dalilin da ya sa Allaah ya haliccemu shi ne don mu bauta masa
Kamar yanda
ya jaddada haka a cikin ayoyi da yawa daga Qur'ani:
( وَأَنِ اعْبُدُونِي ۚ
هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ )
يس (61) Yaseen
"Kuma
ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."
Kuma daman
duk wanda bai bautawa Allaah ba to kuwa zai bautawa son zuciyarsa, daganan wuta
tazamo makomar:
( وَقَالَ رَبُّكُمُ
ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ ۚ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي
سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ
)
غافر (60) Ghafir
Kuma
Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara
daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu."
Tunda dai
har bai halicci mutum da Aljan ba sai domin su bauta masa:
( وَمَا خَلَقْتُ
الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
)
الذاريات (56)
Adh-Dhaariyat
Kuma Ban
halitta aljannu da mutane ba sai dõmin su bauta Mini
Kenan ta
yaya zamu bauta masa❓
Ta yanda
ManzonSa ya koyar damu
Sai mu tuno
da hadisin dake cikin Sahihayn (Bukhari da Muslim riwayar Abu Hurairah
(Radiyallahu anhu) Wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Sallu
kama ra'ayat muni usalli", bi ma'ana: "Kuyi Sallah kamar yanda kuka
ga Ina yi"
Wannan fa
Umarni ne bawai shawara ba
Kenan cikin
biyu dole zamu fada daya:
Ko dai muna
Sallar mu ne irin yanda Annabin ya koyar da Sahabbansa ta hanyar karanta
littattafai irinsu: "SIFATU SAKATIN NABY MINAT TAKBIRI ILAT TASLIM
KA'ANNAKA TARAHA" (Siffar yanda Annabi ya koyar da Sallah tun daga Takbir
har zuwa Sallama Kamar kana kallon Sallar)
Ko Kuma na
biyu, mun ta so ne mun ga ana Sallar a al'adance muma muja ara muka yafa. Wanda
dole a nan za a Kura kurai kam
In dai har
wancan Sahabin zai maimaita Sallah sau 3 a Masjidin Nabawy Kuma Ma'aiki
Sallallahu alaihi wasallam ya ce masa ko ma ka sake Sallah domin kuwa baka da
sallah
To Ina Kuma
ga mu yan karshen Zamani Wanda tazararmu da wancan lokacin ta zarce shekaru
1,400❓
Ka ga kenan
akwai aiki jajawur a gabanmu
Akwai wani
Sahabin da baya yin Cikakkiyar Ruku'u da cikakkiyar Sujjada, haka Ma'aiki ya ce
wallahi da zai mutu yana hakan to da sai dai a tashe sa a cikin mutanen Zamanin
Jahiliyya
To ka ga
kenan dole kowa ya zamana yana da Malamin da ya yarda dashi wanda zai koya masa
Sallah irin ta Annabin tsira ba Sallah irin ta al'adah ba
Wannan
dalilin ne ya sa na rubuta littafin: "KURA KURAI 100 A CIKIN
SALLARMU" , idan kana bukatar lectures din sai ka shiga Telegram dinka
kayi searching "USMANNOOR ACADEMY", kana daga gida zaka gyara
sallarka ta waya ba tareda kaje wani wajen ba kuma FREE ne, babu Registration
Ka ga kamar
ni yanzu, zan iya kafa hujja da a qalla sama da Malamai guda 9 da na koyi
Sallah a wajensu
1) Shaikh
Muhammad Nasiriddin al-Albany (Rahimahullah)
2) Shaikh
Jafar Mahmud Adam (Rahimahullah)
3) Shaikh
Muhammad Auwal Albany Zariya (Rahimahullah)
4) Shaikh
Assim Alhakim (Malaminmu ne a yanzu haka yana koyar da mu Seerah a makarantar
ZAD ACADEMY dake Makkah)
5) Shaikh
Prof. Mansur Isah Yelwa Esq (Hafizahullah)
6) Shaikh
Aminu Daurawa (Hafizahullah)
7) Shaikh
Tijjani Guruntum (Hafizahullah)
8) Dr.
Abdallah Usman Gadon Kaya (Hafizahullah)
9) Shaikh
Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo (Hafizahullah)
Don Allaah
ku turawa wasu su ma su amfana
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.