Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wankan Juma'a Yana Kan Mai Zuwa Juma'a Ne Ko Har Da Wanda Yake Gida?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam Shin Wankan Juma'a Yanakan Mai Zuwa Juma'a Ne Ko Har da Wanda Yake Gida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh

Wankan juma'a mustahabbine ba wajibi bane abisa maganar jamhur ɗin malamai. Wasu suntafi akan wajabcinsa.

Wankan juma'a Sunnah ne akan wanda zaije Sallar juma'a mace ne ko namiji, duk da cewa maza aka nemi suhalarceta a cikin faɗin Allah maɗaukakin Sarki:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga Sallah a rãnar Jumu´a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alheri a gare ku idan kun kasance kunã sani.

Saidai idan mace ma zata juma'ar an shar'nta mata wanka saboda juma'ar dakuma ladabtuwa da ladabin juma'a ɗin.

Hakika ibnu hibban yayi babi a cikin Sahihin littafinsa ya ce ( Babinda zai magana akan mustahabbancin wankan juma'a ga mata idan sunasan halartar juma'ar)

Sanna yakoro hadisin Usman Bin waqid Umry daka nafi'u daka Ibnu Umar ya ce: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Wanda zashi sallar juma'a cikin maza ko mata to yayi wanka)

Hadisin Bukhari da muslm sun ruwaitoshi banda karin ( Cikin maza da mata) wannan karin Ibnu kuzaima da ibnu hibban da baihaqi a cikin sunan sun ruwaitota, Malamai sun yi Saɓāni akan ingancinta.

Nawawi Allah yajikansa darahama yaingantata a cikin maj-mu'u ( 4/405) da ibnu mulqim a cikin Badarul Muneer ( 4/649)

Alhafiz ibnu hajar Allah yajikansa da rahama a cikin fat-hul bari ( 2/358) ya ce: Maruwaita hadisin amintattune, saidai bazzar ya ce: Ina tsoran kada yakasance Usman bin waqid wahami yayi.

Abunda Ibnu bazzar yaji tsoro na wahamin usmanu bin waqid abu daudama yatafi akansa Allah yajikansa da rahama.

Abu Ubaidal Ujuri ya ce: Natambayi Abu Dauda akan usman bin waqid ya ce: Za'ifine,

Sai na ce da Abu dauda Abbas bin Muhammad yaruwaito daka yahya bin Ma'een cewa amintaccene shi? ya ce: Za'ifine yaruwaici hadisi Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce ( Wanda zashi sallar juma'a cikin maza ko mata yayi wanka) Bamusan wani daya fadi hakan ba sai shi Tahzeebul kamaal ( 19/505)

Shaik Albani ya raunana wannan hanyar yakuma nuna fandararriya ce duba sil-sila za'ifah ( 8/430)

Daka cikin Abunda yake karfafa cewa mata zasuyi wankan juma'a inzasuje sallar shine abunda ibnu Abu shaiba ya ruwaito a cikin Musannaf dinsa daka Ubaidata bintu na'il ta ce: Naji ibnu Umar da ibnata sa'ad bin Abu waqqas suna cewa: ( wacce zataje masallaci a cikinku ta yi wanka) dawuus yaruwaito irin wannan hadisin, daka shaqeeq yakasance yana Umartar iyalinsa maza da mata suyi wankan ranar juma'a duba Al-Musannaf ( 2/9)

Wankan juma'a ma'narsa shine tsafta da gusar dawari mara daɗi daka jikin mutum saboda haka aka umarci mace idan zataje ta yi wanka.

Imamun Nawawi Rahimahullahu ya ce: Wankan juma'a bawaji bane wajinbinda idan kabarshi ka yi saɓo sunnah ne ga maza da mata, duba Al-maj-mu'u ( 4/405)

Dan haka wankan juma'a bayakan wanda yake gida saiga wanda zashi sallar juma'a, Sunnah ne ahakkin mace dana miji.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments