Mijina Ɗan Caca Ne (Bet9ja)
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Dan Allah mijina yana yin bet9ja wato chacha, ko za aban shawara?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
wa alaikumussalam... Bet9ja wata caca ce Wadda
Yahudawa suka kirkira Don cin dukiyar al'umma ta hanyar barna. Ana yin Wannan
wasa ta hanyar Kowa ya zuba kuɗi ya tura
sa'annan ya canki sa'a ga Dukkan kungiyar kwallon kafan da yake ganin za ta yi
nasara a Wannan wasa. Saboda Haka Bet9ja ya ɗauki Hukuncin "CACA"
Yahudawa sun yi alkawarin cewa ba su Taɓa yarda da musulmi ba har Sai ya bi aqeedar su Kamar
yadda Nassi ya nuna a Cikin Suratul Baqara... Kuma shaiɗan ya jefa mummunar aqeeda ta waɗannan Yahudawa a Cikin zukatan wasu masu raunin Imani
Daga Cikin musulmai.
ALLAH ya Haramta caca da shan giya da bautan
gumaka da Neman sa'a ta jahiliyya a Cikin Aya guda. Allah ya ce:
ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺍﻟْﺨَﻤْﺮُ ﻭَﺍﻟْﻤَﻴْﺴِﺮُ
ﻭَﺍﻟْﺄَﻧﺼَﺎﺏُ ﻭَﺍﻟْﺄَﺯْﻟَﺎﻡُ ﺭِﺟْﺲٌ ﻣِّﻦْ ﻋَﻤَﻞِ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥِ ﻓَﺎﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﻩُ ﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ
ﺗُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
Ya ku waɗanda suka yi ĩmani!
Abin sani kawai, giya da caca da bautan gumaka da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku
nĩsance shi, wa la'alla ku Rabauta a gobe Alqiyama. (Suratul Maaida Aya ta 90)
ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥُ ﺃَﻥ ﻳُﻮﻗِﻊَ ﺑَﻴْﻨَﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌَﺪَﺍﻭَﺓَ
ﻭَﺍﻟْﺒَﻐْﻀَﺎﺀَ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺨَﻤْﺮِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻴْﺴِﺮِ ﻭَﻳَﺼُﺪَّﻛُﻢْ ﻋَﻦ ﺫِﻛْﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻋَﻦِ
ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ۖ ﻓَﻬَﻞْ ﺃَﻧﺘُﻢ ﻣُّﻨﺘَﻬُﻮﻥ
Abin sani kawaĩ Shaiɗan yana nufin ya aukar da adawa da ƙeta a tsakaninku, a cikin
giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga
sallah. To, shin, kun Yarda cewa Zaku daina? (Suratul Maaida Aya ta 91)
Kafin wannan Ayan ta sauka, Yawanci sahabbai ba su
daina shan giya ba, Amma da Allah ya saukar da wannan Ayan sayyidina Umar (R.A)
ya ce: Mun daina! Mun daina!! Mun daina!!
Kuma faɗin Ayan na Kara
nuna muna cewa: Lallai giya da caca Babu abunda suke haifarwa a Cikin mutane
face kiyayya da gaba. Saboda Dukkan Wanda ya zuba kuɗin sa kuma bai ci ba Toh lallai akwai wani Kunci tattare
dashi. Lallai caca Tana Hana mutum ambaton Allah da Sallah. Saboda a Cikin caca
akwai zaman banza Wanda Babu alkhairi a tattare dashi, shaiɗan yana Gurata ma mutum ya zauna Kada ya damu da duk wani
ibada.
Caca Tana haifar da masifa da zaman banza a Cikin
Al'umma ta yanda mutum yana zaune kawai yaji kuɗi sun shigo masa ba tare da yayi aikin komai ba. hakan
zai iya haifarwa masa da yin sata ko fashi da makami.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance
Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.