Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Taron Daurin Aure Bidi’a ne?

SHIN TARON ƊAURIN AURE BIDI'A NE?

Akwai mutane masu yawa, suna dangantuwa ga Sunna, cikin dalibai, har ma da Malamai, amma ba su fahimci hakikanin bidi'a ba. Wannan ya sa suke faɗa wa cikin kuskure, ta hanyar bidi'antar da abubuwan da ba bidi'a ba ne, har su zafafa inkari a kansu, har hakan ya kai su ga zargin masu aikatawa, da bidi'antar da su.

Abu ne sananne cewa; tun lokacin da ilimomin Sharia suka nuna, Malaman Shari'a sun kasa Shari'a zuwa gida uku:

1- Bangaren Akida: Shi ne bangaren kudurce rukunnan Imani, da gaskata labaran da Allah da Manzonsa suka ba mu, da kudurce su. Bidi'a a Akida ya fi muni, saboda Akida babin gaskatawa ne da ikirari da kudurcewa, saba hakan kuwa karyata Allah da Manzonsa ne. Saboda Akida babin labari ne game da Allah da Siffofinsa da sauran rukunnan Imani, da sauran mas'alolin da ake riskar da su.

2- Bangaren Ibada: Asali a wannan babi ba a yin wata Ibada sai da dalilin shar'anci daga dalilan Shari'a. To bidi'a a wannan babin yana bangaren bin sha'awar zuciya ne, da son bautar Allah, da neman lada.

Duk da cewa lamarin wannan bai kai na farko ba, to amma shi ma yana da hatsari, don Allah ba ya karban ibada ta bidi'a. Kuma mai yi yana cikin zargi. Misalinsu shi ne irin su bidi'ar Maulidi, da sauran bidi'o'i a bangaren Salloli da zikirori, kamar yadda lamarin yake a wajen Sufaye da 'Yan Shi'a.

3- Bangaren Mu'amala: kamar bangaren Aure da kasuwanci da sauransu. To asali a wannan babi shi ne halasci. Wato a aure komai halas ne, sai dai abin da ya saba Shari'a. Saboda haka mutum ba zai yi abun da bai saba Shari'a a aurensa ba, kai kuma ka zo kana cewa ya yi bidi'a.

Yaushe ake samun bidi'a a babin Mu'amala?

Ana samun bidi'a a Mu'amala ne idan mutum ya shardanta wani sharadi a cikin wani abu na mu'amala, alhali Allah da Manzonsa ba su shardanta shi ba. Kamar mutum ya shardanta wani sharadi a aure, ba tare da hujja daga Shari'a ba.

Don haka kuskure ne ka ji mutum yana sukar taron daurin aure, yana cewa; bidi'a ne. Da zaran ka ji wannan to ka sani bai fahimci me ake nufi da bidi'a ba.

Saboda haka idan ka ga mutum yana sukar Malamai a kan sun halarci taron daurin aure, to ka sani ba magana ta ilimi yake yi ba.

[8:57 pm, 21/01/2025] Umar Aliyu Misau: Ta yaya Wanda ya Haramta Taron Daurin Aure zai zama Dan Bidi'a?

Abu ne sananne cewa; magana a kan Addini da Sunna da Bidi'a dole sai da ilimi. Kafin ka ce kaza bidi'a ne sai ka san hakikanin bidi'a. Haka Sunna ma.

Kafin ka yi magana a kan hukuncin ayyukan bayi dole sai ka san asalinsu a Shari'a, wato mas'alar da ake kira da: (الأصل في أفعال المكلفين).

A takaice, aiyukan bayi kashi biyu ne; na Ibada, da na Al'ada da Mu'amala.

To, asali a aiyukan ibada shi ne haramun ne bawa ya aikata wani aiki da nufin Ibada har sai an samu dalili na Shari'a da ya ce ya aikata.

Amma idan aiyuka ne na Al'ada da Mu'amala, to wadannan asalinsu halas ne, ya halasta mutum ya aikata.

Don haka idan mutum ya aikata ba za a yi masa inkari ba, kuma ba za a nemi ya kawo dalili ba, matukar Shari'a ba ta haramta wannan aikin ba.

Don haka wanda ya yi inkari ga wanda ya aikata wani abu na Al'ada ko Mu'amala shi za a nemi ya kawo dalilin hani da haramci.

Wannar ka'ida tun tuni Malaman "Akida" da na "Usulul Fiqhi" suka tattauna ta, kuma Malamai masu Tahqiqi suka tabbatar da ita. Irin su Shaikhul Islam, Ibnul Qayyim, da Al-Shadibiy.

Haka daga cikin Malamanmu na zamani, Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ce:

والأصل في الأشياء حل وامنع * عبادة إلا بإذن الشارع

Ma'ana: Asali a ABUBUWA shi ne halasci.

A sharhi sai ya yi bayanin "الأشياء", ya nuna cewa ya shafi komai, aiyuka, da mu'amaloli, da al'adu da dukkan abubuwa masu amfani.

شرح منظومة أصول الفقه وقواعده (ص: ١١٢)

A bayanin Mu'amala sai ya nuna cewa dukkan mu'amaloli da ake kulla su sun shiga ciki, kamar kasuwanci, aure da sauransu. Saboda Allah ya ce:

﴿وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلۡبَیۡعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰا۟ۚ﴾ [البقرة ٢٧٥]

{Allah ya halasta kasuwanci, kuma ya haramta riba}.

Kuma ya yi umurni da cika mu'amaloli da aka kulla su, inda ya ce:

﴿یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ أَوۡفُوا۟ بِٱلۡعُقُودِۚ﴾ [المائدة ١]

{Ya ku wadanda suka yi imani, ku cika mu'amalolin da kuka kulla su}.

Sai Shaikh Ibnu Uthaimeen din ya ce:

"فأمر الله بالوفاء بالعقود على أي وجه عقدت، وبأي معاملة كانت، ما لم يثبت تحريمها".

"Sai Allah ya yi umurni da cika duk mu'amala da aka kulla, ta duk fiskar da aka kulla, kuma ta kowace irin mu'amala ce, matukar haramcinta bai tabbata a Shari'a ba".

شرح منظومة أصول الفقه وقواعده (ص: ١١٦)

Sai wannan ya nuna cewa; Aure yana cikin mu'amaloli da ake kulla su.

Haka a bayanin Al'adu ma sai ya bayyana cewa; duk abin da mutane suke aikatawa a bisa al'ada, to ba abin a yi musu inkari ba ne, matukar Shari'a ba ta yi hani a kai ba.

شرح منظومة أصول الفقه وقواعده (ص: ١١٧)

Bisa wannan bayani, idan mun lura za mu ga cewa; taron daurin aure da mutane suke yi al'ada ce da suka saba yi, har gari da gari ake halarta, har ya zama babbar hanyar sada zumunci, da faranta wa masu auren zuciya da dad'ad'a musu rai.

Haka Malaminsa Shaikh al-Sa'adiy ya ce:

"الأصل في عاداتنا الإباحة * حتى يجيء صارف الإباحة"

منظومة القواعد الفقهية وشرحها.

A wani wajen kuma ya ce:

"القاعدة السادسة:

الأصل في العبادات الحظر، فلا يشرع منها إلا ما شرعه الله ورسوله. والأصل في العادات الإباحة، فلا يحرم منها إلا ما حرمه الله ورسوله

...وأما العادات كلها من المآكل والمشارب والملابس كلها، والأعمال والصنائع والمعاملات والعادات كلها، فالأصل فيها الإباحة والإطلاق، فمن حرم شيئا منها لم يحرمه الله ورسوله فهو مبتدع...

وهذان الأصلان نفعهما كبير، وبهما تعرف البدع في العبادات والعادات، فكل من أمر بشيء لم يأمر به الشارع فهو مبتدع، وكل من حرم شيئا لم يحرمه الشارع من العادات فهو مبتدع".

القواعد والأصول الجامعة (ص: ٢٢ - ٢٣)

"Ka'ida ta Shida:

Asali a Ibada shi ne hani, ba a shar'anta wani abu na Ibada sai abin da Allah da Manzonsa suka shar'anta.

Asali a al'adu shi ne halasci, ba a haramta komai na al'ada sai abin da Allah da Manzonsa suka haramta.

...Amma al'adu gaba dayansu, na abinci da abinsha da kayan sawa kowannensu, da aiyuka da sana'o'i da mu'amaloli da al'adu kowannensu, asali a cikinsu shi ne halasci, kuma a sake suke ba kaidi. Duk wanda ya haramta wani abu daga cikinsu, alhali Allah da Manzonsa ba su haramta ba, TO SHI DAN BIDI'A NE...

Wadannan asali guda biyu amfaninsu yana da girma, da su ake sanin bidi'o'i a babin Ibadu da Al'adu.

Don haka duk wanda ya yi umurni da wani abu a matsayin Ibada, alhali Allah da Manzonsa ba su yi umurni da shi ba, TO SHI DAN BIDI'A NE.

Haka duk wanda ya haramta wani abu daga cikin al'adu, alhali Allah da Manzonsa ba su haramta ba, TO SHI DAN BIDI'A NE".

Saboda haka aure mu'amala ne, saboda yana babin "العقود". Kuma taruwan mutane don yin shaida a wajen daurin aure al'ada ne, abu ne da mutane suka saba yi, suke maimaita shi, har ya zama abu zaunanne a cikinsu, don haka halas ne.

Saboda haka, duk wanda ya haramta taron daurin aure, ya kira shi da sunan bidi'a to shi ne dan bidi'ar, bisa bayanin da Al-Allama Ibnu Si'idiy (r) ya yi.

﴿وَلَا تَقُولُوا۟ لِمَا تَصِفُ أَلۡسِنَتُكُمُ ٱلۡكَذِبَ هَـٰذَا حَلَـٰلࣱ وَهَـٰذَا حَرَامࣱ لِّتَفۡتَرُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۚ إِنَّ ٱلَّذِینَ یَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا یُفۡلِحُونَ ۝١١٦ مَتَـٰعࣱ قَلِیلࣱ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِیمࣱ ۝١١٧﴾ [النحل ١١٦-١١٧]

[8:58 pm, 21/01/2025] Umar Aliyu Misau: TARON DAURIN AURE BIDI’A NE SABODA ANNABI BAI YI BA

Daga cikin kuskuren da yake kaiwa ga rashin fahimtar hakikanin Bidi’a, akwai zaton da wasu suke yi cewa; BIDI’A ITA CE: DUK ABIN DA ANNABI (SAW) BAI YI BA, KO BA A YI A ZAMANINSA BA. Kamar yadda Sunna ita ce: duk abin da Annabi (saw) ya ce a yi, ko ya yi, ko aka yi ya tabbatar.

To alal hakika wannar fahimta ga ma’anar Bidi’a kuskure ce, wanda ya kai ga bidi’antar da abubuwan da alal hakika ba bidi’a ba ne. Saboda aiyukan bayi nau’i biyu ne; Ibada, da kuma Al’ada da Mu’amala.

Don haka abu na Ibada wanda Annabi (saw) bai yi ba yinsa Bidi’a ne. Abin da kuma bai yi ba, na Al’ada da Mu’amala yinsa ba bidi’a ba ne, yinsa HALAS ne. In ka ga dama ka yi, ko kuma ka bari. Shaikhul Islam ya ce:

"إن تصرفات العباد من الأقوال والأفعال نوعان:

عبادات يصلح بها دينهم.

وعادات يحتاجون إليها في دنياهم.

فباستقراء أصول الشريعة نعلم أن العبادات التي أوجبها الله أو أحبها لا يثبت الأمر بها إلا بالشرع.

وأما العادات فهي ما اعتاده الناس في دنياهم مما يحتاجون إليه، والأصل فيه عدم الحظر، فلا يحظر منه إلا ما حظره الله سبحانه وتعالى.

وذلك لأن الأمر والنهي هما شرع الله، والعبادة لا بد أن تكون مأمورا بها، فما لم يثبت أنه مأمور به كيف يحكم عليه بأنه عبادة؟

وما لم يثبت من العادات أنه منهي عنه كيف يحكم على أنه محظور؟

ولهذا كان أحمد وغيره من فقهاء أهل الحديث يقولون: إن الأصل في العبادات التوقيف، فلا يشرع منها إلا ما شرعه الله تعالى، وإلا دخلنا في معنى قوله: {أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ} [الشورى: 21].

والعادات الأصل فيها العفو، فلا يحظر منها إلا ما حرمه، وإلا دخلنا في معنى قوله: {قُلْ أَرَأَيْتُمْ مَا أَنْزَلَ اللَّهُ لَكُمْ مِنْ رِزْقٍ فَجَعَلْتُمْ مِنْهُ حَرَامًا وَحَلَالًا قُلْ آللَّهُ أَذِنَ لَكُمْ أَمْ عَلَى اللَّهِ تَفْتَرُونَ} [يونس: 59]".

مجموع الفتاوى (29/ 16 - 17)

Ma’ana; Aiyukan bayi nau’i biyu ne; “Ibada” da “Al-ada”. Abin da yake asali a Ibada shi ne; ba a yin Ibada sai dole ta tabbata da dalili na Shari’a. Ita kuma “Al’ada” - wato abubuwan da mutane suka saba yi, wadanda suke bukata a rayuwarsu - ba a hana yinta sai idan Shari’a ce ta hana a yi.

Idan muka kirkiri “Ibada” wacce babu ita a dalilan Shari’a, to mun zama kamar Mushrikan da suke shar’anta Addinin da Allah bai yi izni da yinsa ba.

Idan kuma muka haramta “Al’ada” wacce Allah bai haramta ba, to mun zama kamar Mushrikan da suke haramta arzikin da Allah ya saukar, alhali ba Allah ne ya musu izni ba, kawai karya suke yi wa Allah.

Saboda haka wannan shi ne asali, duk abin da Annabi (saw) ya bari bai yi ba, sai a tsaya a duba, idan a babin Ibada yake to sai mu ce yinsa Bidi’a ne. Idan kuma a babin Mu’amala da Al’ada yake to sai mu ce yinsa HALAS ne, babu laifi a aikata.

Akwai abin da za ka ji mutane suna cewa: “Ai Aure Ibada ne”, don haka a cikinsa dole a bar duk abin da Annabi (saw) bai yi ba!

Sai ka ga suna kafa hujjoji ta wata hanya ba irin hanyar masu ilimi ba.

To Malamai da suka san Shari’a sun saka Aure ne a babin Mu’amala, ba babin Ibada ba. Ka koma ka duba dukkan littatafan Hadisi, da Littatafan Fiqhu, za ka ga cewa; Aure yana bangaren Mu’amala ne. Shi ya sa Ibnu Taimiyya ya ce:

"وأما العقود من المعاملات المالية والنكاحية وغيرها فنذكر فيها قواعد جامعة عظيمة المنفعة؛ فإن القول فيها كالقول في العبادات".

مجموع الفتاوى (29/ 5)

“Amma mu’amalolin da ake kullawa na mu’amalolin dukiya da na AURATAYYA da ma wasunsu, za mu ambaci ka’idoji gamammu masu girman amfani, saboda magana a kansu kamar magana ce a kan Ibadu”.

Ka ga sai ya sanya harkokin dukiya, wato kasuwanci, da na AURE duka a babin MU’AMALA, saboda a cikin “العقود” suke, wato mu’amaloli ne da bayi suke kulla su a tsakaninsu.

Kuma sun zama cikin “Al’ada” ne saboda abubuwa ne da mutane suke bukatar amfani da su a rayuwarsu, kuma sun saba yinsu, kai, kasuwanci da aure tun kafin zuwan Muslunci mutane suke amfani da su. Don haka Aure “Al’ada” ce ta ba ni Adam.

Don ka san cewa; Aure da kasuwanci a babin “Al’ada” da Mu’amala suke shi ya sa aka halasta maka yin kasuwanci da kafirai, aka halasta maka Auren mata “Ahlul Kitabi”. Da a ce Aure a babin Ibada yake da ba a halasta maka Auren mata “Ahlul Kitabi” ba, don Ibada da Musulmai kadai ake yi.

Saboda haka Bidi’a ita ce: mutum ya kirkiri sabon aiki ko magana, ko sabuwar Akida, da nufin Ibada da neman kusaci ga Allah, ya shigar da shi cikin Addini.

Don haka duk abin da ba a bangaren Ibada yake ba, to kirkirarsa ba zai zama Bidi’a ba.

Wannan shi ne ma’anar Bidi’a a wajen Malamai, irin su Imamu Malik, Ibnu Taimiyya, al-Shadibiy da sauransu, wadanda suke takaita Bidi’a a kan Bidi’a ta Shari’a kadai, wacce aka yi zargi a kanta.

Amma duk mai daukar cewa: Bidi’a ita ce: duk abin da Annabi (saw) bai yi ba, ko duk abin da babu shi a zamaninsa, to wannan fahimta ce ta wasu Malamai, musamman Izz bn Abdissalam. To amma su wadannan suna bayanin Bidi’ar ce a ma’anarta ta “Lugha”. Wannan ya sa suke kasa Bidi’ar zuwa hukunce-hukuncen Shari’a guda biyar: Wajibi, Mustahabbi, Haramun, Makruhi, Mubahi. Izz bn Abdissalam ya ce:

"البدعة فعل ما لم يعهد في عصر رسول الله - صلى الله عليه وسلم -. وهي منقسمة إلى: بدعة واجبة، وبدعة محرمة، وبدعة مندوبة، وبدعة مكروهة، وبدعة مباحة".

قواعد الأحكام في مصالح الأنام (2/ 204)

“Bidi’a ce ita ce aikata abin da ba a san shi a zamanin Manzon Allah (saw) ba.

Kuma ta kasu zuwa: Bidi’a Wajiba, Bidi’a ta Haramun, Bidi’a Mustahabbiya, Bidi’a Makruhiya, Bidi’a ta Mubahun”.

To ka ga duk mai cewa: Bidi’a ita ce: “Duk abin da Annabi (saw) bai yi ba”, don haka TARON DAURIN AURE BIDI’A NE,

Sai mu ce masa: Su masu wannar fassara suna kasa bidi’ar kashi biyar, don haka TARON DAURIN AURE a wane kaso yake?

Bidi’a ce Wajiba, ko ta haramun, ko mustahabbiya, ko makruhiya, ko ta mubahun?

Ka ga bisa wannan, ashe ba kowace bidi’a ce take ba ta ba kenan!

Ba na jin masu cewa: TARON DAURIN AURE BIDI’A ne za su yarda cewa; akwai bidi’o’i na wajibi, wadanda dole sai an aikata su, wasu kuma mustahabbi ne a aikata su, wasu mubahun. Kuma ba sa ganin cewa; ba kowace bidi’a ce take ba ta ba.

Saboda haka, da wannan za mu fahimci cewa; don Annabi (saw) bai yi TARON DAURIN AURE, KO TARON SUNA BA, kuma ba a yi a zamaninsa ba, shi kenan sun zama Bidi’a. A’a, ba za su zama Bidi’a ba, saboda ba a babin Ibada suke ba, a babin Al’ada da Mu’amala suke, don haka yinsu HALAS ne, in ka ga dama ka aikata, in kuma ba ka ga dama ba kar ka aikata.

Da wannan nake yi mana Nasiha, mu kiyayi haramta abin da Allah bai haramta ba, ko bidi’antar da abin da yake a babin Mu’amala yake. Duk wanda zai bidi’antar da abin da a babin Mu’amala yake, ko ya haramta shi alhali Allah bai haramta ba, to shi DAN BIDI’A ne, kamar yadda mai kirkirar Ibada a cikin Addini yake DAN BIDI’A. Saboda wadannan abubuwa biyun su ne tushen bata. Shaikhul Islami ya ce:

"وأصل الضلال في أهل الأرض إنما نشأ من هذين:

إما اتخاذ دين لم يشرعه الله.

أو تحريم ما لم يحرمه.

ولهذا كان الأصل الذي بنى عليه أحمد وغيره مذاهبهم: أن الأعمال "عبادات وعادات"؛ فالأصل في العبادات لا يشرع منها إلا ما شرعه الله. والأصل في العادات لا يحظر منها إلا ما حظره الله".

اقتضاء الصراط المستقيم (2/ 86)، مجموع الفتاوى (4/ 196)

Ma’ana; sababin batan mutane shi ne wadannan abubuwa biyu:

1- Kirkirar Ibada wacce Allah bai shar’anta ba a Addini.

2- Haramta abu na al’ada, alhali Allah bai haramta ba.

[11:07 pm, 24/01/2025] Umar Aliyu Misau: Riga Malam Masallaci...

Babban abin mamaki a wannan zamani shi ne garaje ya yi yawa a mas'aloli da suke da alaka da Addini. Da zaran abu sabo ya bayyana, a maimakon gama garin mutane da dalibai su garzaya zuwa ga Malamai don neman Fatawa a kan wannan sabon lamari, a'a, sai dai kowa ya fara bude baki yana bayyana ra'ayinsa. Ya goyi baya, ko ya haramta, ya bidi'antar da abin. Duk da hatsarin hakan.

Sai ya zama tun kafin Malami ya yi magana, jahilai sun gama yanke hukunci. Don haka duk abin da Malami zai fada to zai sha suka, daga jahilan da suka saba masa.

Misali a kan haka, shi ne "Qur'anic Festival" da yanzu ake ta magana a kansa. Bai kamata a yi gaggawan yanke hukunci ba, ko da kuwa Malami ne, tun kafin a fahimci hakikanin abin.

Kowace sabuwar mas'ala idan ta fito, dole sai an bi matakai na ilimi kafin a isa ga yi mata hukunci. Kai, wata mas'alar sai an yi mata "Ijtihadin Jama'a".

Saboda haka ya wajaba mutane su kiyayi kansu. Magana a kan Addini, na yanke hukunci a kan abu cewa Halal ne ko Haram, Sunna ne ko Bidi'a bakin rijiya ne. Ba aikin dalibai ba ne balle gama garin mutane. Kai, ba aikin Malamai masu wa'azi ba ne. A'a, aiki ne na Malamai Mujtahidai, wadanda sun kai su kalli mas'ala, su yi nazari cikin dalilan Shari'a da ka'idojinta don samar mata da hukunci. Wannan matsayi kuwa matsayi ne wanda duk dalibin ilimi ya san ya fi karfin Malami mai wa'azi, balle dalibin da bai gama fahimtar "Ulumul Ala" ba.

Ala ayyi halin, wajibi ne kowa ya tsaya a matsayinsa.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments