TA YAYA ZA KA GANE "QUR'ANIC FESTIVAL" BIDI'A NE KO A'A?
Yanke Hukunci wa aiki da Bidi'a yana da ka'idoji na musamma, wadanda Malamai masana suke amfani da su kafin su gano aiki kaza bidi'a ne, ko ba Bidi'a ba. Saboda rashin umurnin Annabi (saw) ga aiki, ko rashin aikatawarsa, ko rashin aikatawa a zamaninsa da zamanin Sahabbai ba shi ne kadai zai sa a yanke hukunci ga aiki da Bidi'a ba. Dole akwai ka'idoji, da matakai na ilimi da Malamai masana suke bi.
Shi ya sa za
ka sha mamaki matuka idan ka ga wadanda ba Malamai ba, amma kuma ka ji mutum
yana cewa: "Ni a fahimtata, "Qur'anic Festival" ba shi da
banbanci da Maulidi".
Kai za ka
dauka dalilai bisa ka'idojin Shari'a zai kawo, kawai sai ka bibiye shi sai ka
ga ya buge da surutai, da danganta abin ga siyasa.
A takaice,
ya kamata mu san cewa; ba ka isa ka yi inkari ko zargi ga abin da Shari'a ba ta
yi zargi a kansa ba, ko ta zargi mai yi ba.
Farko, idan
sabon abu ya bayyana, to ka tsaya ka duba ka gani, a wane bangare yake? A
bangaren tabbatattun abubuwa yake (الثوابت), ko kuma abubuwa ne masu canzawa (المتغيرات)?
Idan a
bangaren tabbatattun abubuwa yake (الثوابت), to Ijtihadi ba ya shiga cikinsa.
Idan kuma a
bangaren abubuwa ne masu canzawa yake (المتغيرات), to wannan bangaren ne kadai Ijtihadi zai
shiga cikinsa.
Imam Ibnul
Qayyim ya ce:
"الأحكام نوعان:
نوع لا يتغير عن حالة واحدة هو عليها، لا بحسب الأزمنة ولا
الأمكنة، ولا اجتهاد الأئمة، كوجوب الواجبات، وتحريم المحرمات، والحدود المقدرة
بالشرع على الجرائم ونحو ذلك. فهذا لا يتطرق إليه تغيير ولا اجتهاد يخالف ما وضع
له.
والنوع الثاني: ما يتغير بحسب اقتضاء المصلحة له زمانا
ومكانا وحالا، كمقادير التعزيرات وأجناسها وصفاتها، فإن الشارع ينوع فيها بحسب
المصلحة...".
إغاثة اللهفان (١/ ٥٧٠ - ٥٧١)
Sai ya nuna
cewa; akwai mas'alolin da hukuncinsu ba ya canzawa, kuma Ijtihadi ba ya shiga cikinsu.
Akwai kuma
mas'alolin da suke canzawa gwargwadon maslaha, saboda canjin zamani, ko wuri,
ko hali da yanayi. Wadannan su ne wadanda Maslaha take sa a samar da su.
Haka
al-Allama Ibnu Si'idiy ya ce:
"القاعدة الحادية
والعشرون: القرآن يجري في إرشاداته مع الزمان والأحوال في أحكامه الراجعة للعرف
والعوائد
...فما كان من المعروف
لا يتغير في الأحوال والأوقات، كالصلاة والزكاة والصوم والحج وغيرها من الشرائع
الراتبة، فإنه أمر به في كل وقت، والواجب على الآخرين نظير الواجب على الأولين من
هذه الأمة. وما كان من المنكر لا يتغير كذلك بتغير الأوقات، كالشرك والقتل بغير حق
والزنا وشرب الخمر ونحوها، ثبتت في كل زمان ومكان لا يتغير ولا يختلف حكمها.
وما كان يختلف باختلاف الأمكنة والأزمنة والأحوال هو المراد
هنا؛ فإن الله تعالى يردهم فيه إلى العرف والعادة والمصلحة المتعينة في ذلك الوقت...".
القواعد الحسان (ص: ٦٢)
Sai ya
bayyana cewa mas'alolin da suke iya canzawa Shari'a ta mai da su zuwa ga aiki
da maslaha da urfi da al'ada.
Shi ya sa
Malamai suke kirga "Usul Aqa'id", da Farillai, Wajibai, da Abubuwan
da aka haramta a jerin tabbatattun abubuwa (الثوابت).
Kuma suke
sanya abubuwan da Shari'a ta yi afuwa, da abubuwa na al'ada, da kuma hanyoyin
aikata wajibai a jerin abubuwa masu canzawa (المتغيرات).
Kasancewar
Shari'a ta zo ne da samar da maslaha da samar da duk wani abu mai amfani, da
kuma kawar da barna, shi ya sa ta halasta duk abin da akwai maslaha da amfani a
cikinsa, kuma ta yi hani a kan duk abin da babu maslaha babu amfani a cikinsa,
balle idan barna ce a cikinsa.
Maslahohi
nau'i uku ne:
1-
Maslahohin da suka zo a Shari'a (المصالح الشرعية).
2-
Maslahohin da Shari'a ta yi hani a kai (المصالح الملغاة).
3-
Maslahohin da Shari'a ta yi shiru a kansu (المصالح المرسلة).
To nau'i na
daya, Maslahohi ne na Shari'a, Shari'a ce ta zo da su.
Amma na uku
kuma Maslahohi ne wadanda Shari'a ta yi shiru a kansu, don haka ya halasta su
zama hanyoyin da ake aikata Wajibai da su. Su ne Maslahohin da Shari'a ta yi
shiru a kansu, kuma ta hana bincike a kansu. Annabi (saw) ya ce:
"إن الله فرض فرائض
فلا تضيعوها، وحد حدودا فلا تعتدوها، وحرم أشياء فلا تنتهكوها، وسكت عن أشياء رحمة
لكم غير نسيان، فلا تبحثوا عنها".
Ka ga sai ya
ce: Kuma Allah ya yi shiru a kan wasu abubuwa, don rahma gare ku, ba don ya
manta ba, to kada ku yi tone-tone a kansu.
Misali a kan
haka, Allah ya wajabta kyautata wa Iyaye, amma bai ce kaza za ka yi ba, kawai
za ka yi abin da yake kyautatawa ne a al'ada da urfi.
Haka Allah
ya wajabta yin da'awa da yada Muslunci, don manufar kare Addini, amma Shari'a
ba ta kayyade mana hanya daya ba. Don haka sai a yi amfani da hanyoyi da za su
samar da amfani da maslaha (المصالح المرسلة), kamar Wa'azin kasa, shirya Lakca, Daura,
Conference na Alkur'ani, ko Hadisi, ko Fiqhu da Usul, ko Siran Annabi (saw), ko
a kan Sahabbai, ko Seminer, d.s.
Don haka
duka wadannan hanyoyi ne da ba za a kira su Bidi'a ba, saboda Maslahohi ne da
Shari'a ta yi shiru a kansu, ba ta hana su ba (المصالح المرسلة). Kuma duka suna cikin hanyoyi na yada
Addini, don haka suna cikin manufar kare Addini (حفظ الدين).
Saboda haka
duka hanyoyin kira ga Muslunci da yada Addini, matukar ba su saba Shari'a ba to
ya halasta a yi amfani da su, saboda ba Bidi'a ba ne. A Shari'a ba a kiransu da
sunan bidi'a, sunansu (المصالح المرسلة).
Kuma suna daga cikin hujjojin Fiqhu.
Don haka a
irin wannan idan ka ji mutum yana tambayarka Aya ko Hadisi to ka tabbatar bai
san inda ilimin Shari'a ya dosa ba.
Sai wasu
masu kawo shubuha, wadanda su a iya karancin iliminsu ba su ga banbanci
tsakanin "Qur'anic Festival" da Maulidi ba!
Haba Malam!
Ka ji tsoron Allah ka rufe bakinka!
Ai shi
Maulidi ibada ce mai cin gashin kanta. Amma "Qur'anic Festival" kuma
iyakacinsa a ce hanya ce ta yada Buwayar Alkur'ani, don haka tana cikin hanyoyi
ne wadanda Shari'a ta yi shiru a kansu, wato yana cikin "المصالح المرسلة".
Shaikhul Islam ya yi bayanin banbancin da ke tsakaninsu inda ya ce:
"كل أمر يكون المقتضي
لفعله على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم موجودا لو كان مصلحة ولم يفعل يعلم
أنه ليس بمصلحة. وأما ما حدث المقتضي له بعد موته من غير معصية الخلق فقد يكون
مصلحة".
اقتضاء الصراط المستقيم (٢/ ٥٩٨)
Ma'ana; duk
abin da aka kirkira, alhali abin da zai sa a kirkire shi akwai shi a zamanin
Annabi (saw) amma kuma bai aikata shi ba to Bidi'a ne ba Maslaha ba. Kamar
Maulidi, da a ce abu mai kyau ne da an yi shi a zamanin Annabi (saw), amma da
yake ba mai kyau ba ne bai yi ba, Azumi yake yi a duk ranar Litinin.
Amma shi
kuma Conference fa, don nuna buwayar Alkur'ani, babu bukatarsa a zamanin Annabi
(saw) sai a wannan zamani, don haka yinsa "Maslaha ce Mursala", babu
laifi a yi amfani da ita. Kuma za ta iya zama wajibi, ko mustahabbi ko mubahun.
A takaice,
babu mai hada "Qur'anic Festival" da Maulidi sai wanda bai san yadda
ake gane Sunna daga Bidi'a ba.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.