Ticker

6/recent/ticker-posts

Sabani Tsakanin 'Yan Falsafa Da Masu Hankali A Kan Daukakar Allah

SAƁANI TSAKANIN 'YAN FALSAFA DA MASU HANKALI A KAN ƊAUKAKAR ALLAH

Shi ya sa magabata suka ce:

كل معطل مشبه

"Dukkan Mai kore Siffofin Allah to Mai kamanta Allah da wani abu ne".

Ma'ana kafin ya kore Siffofin Allah sai da ya kamanta Allah da mutum, sai ya ga bai kamata haka ya kasance ba, sa'annan sai ya kore Siffofin, sai kuma ya afka cikin kamanta Allah da babu, ko kuma da abun da ba zai yiwu ba.

Saboda haka wadannan 'Yan Falsafan da muke gani, kafin su kore daukakar Allah a saman halitta sai da suka kamanta Allah da mutum, saboda su abin da tunaninsu ya ba su shi ne; in an ce: Allah yana sama, kuma yana saukowa zuwa sama ta Duniya to ai saman Nigeria ba ita ce saman KSA ba. Haka in an ce yana saukowa a kowane dare to ai lokacin da 2/3 na dare ya yi a Nigeria to a America rana ce...

Haba Makaho Dan Falsafa!

In ka fadi haka, ai wannan kana misalta daukaka da sauka ne na mutane ba na Allah ba!

To wannan tunani ne na mai karamin kwakwalwa, mai kuncin tunani, maras basira, mai kwatanta daukakar Allah a sama da daukakar mutane a sama ko jirgi ko tsuntsu ko sauran ababen halitta. Haka kuma yana kwatanta saukowar Allah daga sama da ta mutane ko sauran halitta.

Ya Mai kwatanta Allah da halitta!

Ya Mai kwatanta Siffofin Allah da siffofin halitta!

Ya kamata ka san cewa; Allah ba shi da makamanci.

{لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ } [الشورى: 11]

Da zarar ka kamanta daukakarsa a sama da daukakar halitta, ka kwatanta saukowarsa daga sama da saukar halitta, to ka kama hanyar bata, ka wayi gari "Mushabbihi" (mai kamanta Allah da halitta), sai kuma ka afka cikin "Ta'atili" ka zama mai kore ma Allah abin da ya tabbatar ma kansa na Daukaka a kan dukkan halittu, da kore saukowarsa zuwa sama ta Duniya da ya tabbata ta harshen Manzonsa.

Su abin da wadannan jahilai masu wayo da kwazo marasa hankali suka manta shi ne; Ana iya sanin abu ne ta hanyoyi guda uku:

1- Imma saninsa ta hanyar hawas (gani ko ji...).

2- Ko ta hanyar sanin makamancinsa.

3- Ko ta hanyar ba da labari a kansa.

To Shi Allah Madaukaki babu wanda ya taba ganinsa, ko ya san shi ta hanyar hawas.

Kuma ba shi da makamanci, balle a ce an san shi da hankali ta hanyar sanin makamancinsa.

Don haka sai dai a san shi ta hanyar Labarin da ya bayar cikin Littafinsa ko ta harshen Manzonsa.

Saboda haka ashe hanya daya ce kawai ta sanin Allah da Siffofinsa da sanin inda yake, ta cikin Littafinsa da Hadisan Manzonsa, duk wanda ya karyata su ya kore siffofin Allah da suka zo a cikinsu, ko ya yi tawilinsu to ya zama "Mushabbihi", "Mu'attili", kuma "Muharrifi", wato mai kamanta Allah da wani abu, kuma mai kore wa Allah Siffofinsa na kamala da daukakarsa a saman dukkan halitta, kuma mai canza maganar Allah da karyata hakikaninta.

Don haka mu mun yarda Allah yana sama kamar yadda ya fada, ya daukaka a kan dukkan halittunsa, kuma ya yi "Istiwa'i" a kan Al'arshinsa:

{الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى } [طه: 5]

Kuma yana saukowa zuwa sama ta Duniya a kowane dare, kamar yadda Manzonsa ya fada, saboda ba ya magana ta son rai, duk abin da ya fada Wahayi ne daga Allah.

Amma ba mu san kamannin daukakar tasa da "Istiwa'in" nasa ba, saboda bai ba mu labari ba, balle mu san cewa; za a samu matsala saboda saman Nigeria ba ita ce saman KSA ba. Saman Argentina ba ita ce saman Australia ba.

Haka kuma ba mu san kamannin saukowar tasa ba, balle mu san za a samu matsala a saukarsa a cikin dare saboda lokacin da 2/3 na dare ya yi a Nigeria to a America rana ce. Idan kuma 2/3 na daren America ya yi to na Austria ya fita. Idan na Austria ya fita to na UK zai shiga!

Mu dai mun san Allah Mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Kuma daukakarsa a saman halitta ba irin daukakar abin halitta ba ne, haka saukowarsa zuwa sama ta Duniya ba irin sauka da abin halitta yake yi daga sama ba ne. Mu dai kawai mun yi imani ne da gaibi, ba ma kutsawa yin bincike a kan gaibin, kamar yadda Allah ya yabi Muminai inda ya ce:

{ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ } [البقرة: 3]

Sabanin 'Yan Falsafa masu inkarin gaibin, masu karyata Manzannin Allah, kamar yadda Imamul Gazzaliy bayan ya gama karance Falsafar sai ya siffanta su da cewa:

وحكاية حاصل علومهم، فإني رأيتهم أصنافاً، ورأيت علومهم أقساماً وهم - على كثرة أصنافهم - يلزمهم وصمة الكفر والإلحاد

المنقذ من الضلال (ص: 42)

"Labarin Ilimin nasu kwacokom dinsa, na same su ne mabanbanta masu sabani, kuma na ga Ilimin nasu a rarrabe yake cikin sabani, su kuma duk da yawan rarrabuwar tasu amma SIFFAR KAFIRCI DA ILHADI TANA MANNE DA SU".

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments