𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Sallar nafila ta walha da ake yi, malam an ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam bai yi sallar walha ba, kuma ya matsayin sallar walha yake a cikin sauran nafilolin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Sallar Walha
sunna ce Mustahabbiya, kuma akwai hadisai ingantattu da dama da suka tabbatar
da ingancin Sallar Walha daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam daga ciki
sun haɗa da:
1. Hadisin
da Abu Zarri Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce akan kowace gaɓa ta ɗayan cikinku sadaka na iya kasancewa kowane TASBIHI
sadaka ce kowane TAHMIDI sadaka ce kowace HAILALA sadaka ce kowace KABBARA
sadaka ce yin UMURNI DA ALHAIRI sadaka ce HANI GA ABIN-QI sadaka ce yana isarwa
ga sadaka yin raka'o'i biyu na Walha Muslim 720.
2. Abu
Buraidata Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa Lallai Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce ajikin mutum akwai gaɓoɓi guda ɗari uku da sittin
(360) yana iya yin sadaka da kowace gaɓa daga cikinsu sai Sahabbai suka ce Wanda kuma ya gaza fa
ya Manzon Allah? Sallallahu Alaihi Wasallam Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce To ya rufe majinar da ya gani a masallaci ko ya kawar da abu mai
cutarwa a kan hanya idan bai sami iko ba sai ya yi raka'o'i biyu na Walha sun
isar masa. Abu Dáwud 5242.
A dunqule
wannan na nufin duk wata gaɓa daga cikin gaɓoɓun jikin mutum zai iya yin aikin sadaka da ita haka nan
ambaton zikirori irin su SUBHÁNALLAH, ALHAMDULILLAH, ALLAHU AKBÁR da
makamantansu duk sadaka ce haka nan kuma yin raka'o'i biyu na Walha duk suna
matsayin sadaka ce kamar waɗancan sadakoki.
waɗannan dalilai da ke
sama sai ya zama ashe Sallar Walha tabbatacciya ce daga Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam Cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam bai yi ba kuskure ne da
rashin sani, saboda waɗannan ba su ne kaɗai ma hadisai ingantattu da suka yi magana a kan Sallar
Walha ba.
Mafi
qarancin raka'o'in Sallar Walha raka'a biyu ne, mafi yawa kuma raka'a takwas
kamar yadda hadisi ya tabbatar duk bayan raka'a biyu a yi sallama.
Lokacin
sallar walha yana farawa daga sanda rana ta fara zafi kamar yadda hadisin
Muslim mai lamba 748 ya tabbatar da hakan har zuwa dab da karkatar rana daga
tsakiyar sama.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.