𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah. malam ina da tambaya, Muna dafa kaza da Tantabara da magani da rubutu muci saboda gyaran jikinmu, ita Tantabara muna rubuta yasin kafa 3 kasancewarta zuciyar Alqur'ani ne, mu haɗa da magani don samun soyayyar miji da kulawa ita kuma kaza Arrahman muke rubutawa kasancewarta Amaryar Alqur'ani ne, idan mun cinye sai mu binne kashin, bama sashi ashara to ya halatta ko ya saɓawa sunnah? Jazakumullahu bikhair.
Karin bayani
akan hakan Malam shine ba waɗannan surorin ne kaɗai ake rubutuwa ba, akan rubuta waɗansu surorin daban
sannan a buɗe minjaye a rubuta sunan mijin a haɗa da wani abun a
sha. Allah ya saka da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Gaskiya
ire-iren waɗannan abubuwan ba su halatta ba. Dalili kuwa shine :
- Shi
Alqur'ani an saukar dashi ne domin mu yi riko dashi mu samu shiriya da kuma
warakar chututtukanmu. Amma ba a saukar dashi don wasu Manufofi irin waɗannan naku ɗin ba.
- Koda
Maluman da suke ganin halaccin shan rubutu, Wannan ya keɓanci marasa lafiya
ne kaɗai.
- Bai
halatta arika chakuda Alqur'ani da wasu abubuwan Kulumboto ba.
- Hakanan
duk wani abu Kulumboto ko Surkulle da za a yi shi domin juyar da soyayya zuwa
Qiyayya, ko Qiyayya zuwa Soyayya to wannan Sihiri sunanshi. Kuma haramun ne.
Masu yin
irin waɗannan abubuwan ba
su da wata Hujjar yin haka daga Alqur'ani ko Sunnah ko ayyukan magabata na
kwarai.
Gyaran jiki
wannan ba laifi bane. Amma duk abin da mutum zai yi don juyar da zuciyar wani,
in dai ba addu'a bace to haramun ne.
Ya kamata
Mata masu yin irin wannan suji tsoron Allah. Domin daga haka ne ake zarcewa
zuwa ga bin bokaye da 'yan bori. (Allah shi kiyayemu ameeen).
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.