Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Bikin Saukar Al-Qur'ani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Wa Ramatullahi Allah ya gafarta malam barka da warhaka, Allah shi qara yi maka jagoranci ya kuma saka maka da mafificin alkhairinSa akan irin qoqarin da ka ke yi amin. malam don ALLAH ina son ataimaka a yi min Qarin haske akan matsayin bukin saukar al-qur'ni mai girma da kuma falalar yanka dabba yayin addu'ar saukar. na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu:-

Hakika Addinin mu na Islama, addini ne wanda komai nasa yake tafe cikin tsari da kuma dokokin Allah. Kuma Allah ya halasta mana mu nuna Murnar mu da kuma godiyar mu bisa dukkan wata ni'ima wacce yayi mana. Allah yana cewa;

وَاشْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ

"KU GODE MA NI'IMAR ALLAH IN HAR KUN KASANCE GARE SHI KUKE YIN BAUTA". (Suratun Nahli ayah ta 144).

Daga cikin irin waɗannan ni'imomin akwai, Aure, Haihuwa, tarewa a sabon gida, Samun lafiya daga wata jinya, Dawowa daga wata tafiya, Kammala Hadda ko kuma Saukar Alqur'ani, da sauransu. Kuma mutum zai iya yin wannan godiyar ta hanyar yin wata ibadah ta musamman kamar, salloli, Azumin tadawwu'i, Yanka dabba domin Allah, ko kuma kiran mutane ka ciyar da su domin Allah.

A cikin Tafseerin Suratul Kauthar, Ibnu Taymiyyah yana cewa, "Allah yayi ma ManzonSa babbar baiwa tunda ya ba shi alkausara. Shi ya sa ya umurce shi da yin godiya ta hanyar yin Mafificiyar ibadar da ake yi da jiki, wato sallah. Sannan da kuma Mafificiyar ibadar da za a yi da kuɗi. Ita ce YANKA domin Allah. Saboda irin wannan godiyar ne Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yanka Rakumma 63 a lokacin hajjin ban-kwana. (A duba Majmu'ul Fataawah juzu'i na 16, shafi na 532).

Ya halatta (Mustahabbi ne) mutum ya tara mutane ya ciyar da su, ko kuma yayi yanka ya sadakar da naman domin nuna murnar sa da godiyar sa ga Allah a bisa ni'imar Yaron sa ya haddace Alqur'ani, ko kuma ya sauke karatu.

Amma akan samu kuskuren fahimta daga wasu mutanen, zaka ga suna cewa wai idan ba a yima yaro wannan sadakar ba, wani mummunan abu zai same shi ko kuma zai haukace. Wannan ba gaskiya bane.

Hasali ma Qudurce hakan Shirka ne. Kuma in dai mutum ya kudurce haka toh bai halatta yayi yankan ba. Kuma idan yayi ma bai halatta a ci naman ba. Don Qarin haske a duba, ALMAUSU'ATUL FIQHIYYAH, juzu'i na 26 shafi na 180-181. FATAWAL LAJNAH ADDA'IMA juzu'i na 1 shafi na 114.

Sannan bai Halatta ace Baban ki bai da Halin yi miki Ƴanka, bai da Halin yi Siyo Shinkafa da sauran Abunda Za a yi Wannan hidimar da shi, a Saka Shi Dole-dole Sai ya Karɓo Bashi a ko ina ya zo ya Haɗa Karya da Gaskiya domin a yi Buƙin Saukar Al Qur'ani ba. Idan bai da shi, mahaifiyar ki ma ba ta da shi, Shikenan ba Dole bane wai sai kun karɓo bashi domin yin bukin Saukar Al Qur'ani ba. Idan an yi haka an koma wani Ɓangaren da Shari'a bai yarda da shi ba.

Sannan Wannan bukin a yi Shi domin Allah ya Halatta, amma in dai Za a yi shi wai domin ai ƴar Uwata ma ta yi ko ai Yaran su wane ma an yi musu, kema ki ce dole sai na yi kuma sai na yi Abun da ya fi nata wanda zai burge duk wanda ya zo gurin saukar, toh Gaskiya bai Halatta ba, an shigar da RIYA a Cikin sa da Hasada da kyamaci da son zuciya.

Kuma in dai Za a haɗa Mata da Maza sannan a Sanya Suturar da Sharia bai yarda da shi ba, duk Wannan bai Halatta ace an yi Saukar Alqur'ani ba. Saboda Haka idan mutum zai yi toh ya tabbatar cewa yayi shi abisa tsari kamar yadda bayani ya gabata a Sama bawai cewa na ga wasu sun yi kema ki ce sai kin yiwa Yaran ki, ko kema sai kin yi idan kin sauke ba Kuskure ne wannan.

Idan Mahaifin ki ko mahaifiyar ki ko ke kanki, duk kuna da Wadatar yi sai ku yi har da ƴankar a rabawa Jama'a Sadaka a kira Jama'a su ci su Sha a yi miki fatan Alkhairi, idan babu sai a Siya Shinkafa kawai ba tare da nama ko Yanka ba, a Dafa a raba kowa ya ci Shikenan, idan babu Wannan ma Shikenan sai a hakura ba sai an takura mahaifi ko mahaifiya ace dole a karɓo bashi ba an yi ba.

Sannan kuma a yi RIYA? Babu Haɗa Mata da Maza a gurin, Babu Sanya Suturar da Addinin ki bai yarda da shi ba, sannan za ki yi ne domin Allah bawai don wani yayi ko wasu an yi musu ba, sannan idan kina da hali ne za ki yi bawai ku karɓo bashi ki ce dole dole sai kin yi ba. idan hakane yadda na lissafa toh ya halatta, saɓanin Wannan toh gaskiya bai Halatta ba a hakura kawai ya fi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments