AQIDAR ASHA'IRAN FARKO TA BANBANTA DA TA 'YAN BAYA
'Yan Ash'ariyyan baya tun daga kan Imamul Haramaini Abul Ma'aliy Al-Juwainiy - wanda ya fara mayar da Mazhabar Ash'ariyya kusa da Mu'utazilanci - har zuwa yau, duk sun saba wa magabatansu, hatta babban Limamin Mazhabar wato Abul Hassan Al-Ash'ariy, ta yadda suka bar tafarkinsa na tabbatar ma Allah Siffofinsa da ya ba da labarinsu, kamar Siffofn Zatinsa, da kuma Siffofinsa na aiki, wadanda ba a saninsu ta hanyar hankali sai ta hanyar Nassi, duk da cewa; hankali yana tabbatar da yiwuwar tabbatuwarsu ga Allah.
Irin
wadannan Siffofi su ne kamar Sifar Fiska, Hanaye biyu. Wadannan Siffofi ne na
zati. A Siffofinsa na aiki kuwa, kamar Siffar "Istiwa'i", wato
daukakar Allah a kan Al-Arshi.
A tabbatar
da wannar Sifa ta Isti'wa'i, Abul Hassan Al-Ash'ariy ya ce:
"وأن الله تعالى استوى
على العرش على الوجه الذي قاله، وبالمعنى الذي أراده".
الإبانة عن أصول الديانة (ص: 21)
"Kuma
lallai Allah Madaukaki ya DAUKAKA A SAMAN AL-ARSHI, kamar yadda ya fada, kuma
bisa ma'anar da yake nufi".
Wannar ita
ce Aqidar Magabatan wannar Al'umma gaba daya, suna tabbatar da cewa; Allah yana
sama, ya daukaka a saman Al'arshi, shi kuma Al-Arshin yana saman dukkan halittu
gaba daya. Babu wata halitta sama da shi.
Kuma Abul
Hassan Al-Ash'ariy ya tabbatar da cewa; fassara "Istiwa'i" da
"Istaula", da cewa; Allah yana ko'ina, Aqida ce ta Mu'utazila da
Jahamiyya da Khawarijawa ba ta Ahlus Sunna ba ce, inda ya ce:
"وقد قال قائلون من
المعتزلة والجهمية والحرورية: إن معنى قول الله تعالى: (الرحمن على العرش استوى)
(طه: 5) أنه استولى وملك وقهر، وأن الله تعالى في كل مكان، وجحدوا أن يكون الله عز
وجل مستو على عرشه، كما قال أهل الحق، وذهبوا في الاستواء إلى القدرة".
الإبانة عن أصول الديانة (ص: 108)
"Mu'utazila
da Jahamiyya da Khawarijawa suka ce: Ma'anar fadin Allah: {Mai rahma ya daukaka
a saman Al-Arshi} shi ne "Istaula", wato ya mamaye Al-Aarshi, ya
mallake shi, ya yi galba a kansa, -wai kuma- Allah yana ko'ina, sai suka musa
kasancewar Allah ya daukaka a kan Al-Arshinsa kamar yadda Mabiya gaskiya suke
fadi, sai suka tafi a kan cewa; -wai- "Istiwa'i" shi ne iko".
To, tabbatar
da cewa; Allah yana sama, ya daukaka a saman Al-Arshi, wannar ita ce Aqidar
Asha'iran farko, kafin su Juwainiy su lalata Mazhabar, su shigar da tunanin
Mu'utazilanci a cikinta. Saboda da ma shi Juwainiy, an san shi da karanta
littatafan Mu'utazilawa, a nan ya tasirantu da su, har ya lalata Mazhabar
Ash'ariyya.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.