Ticker

6/recent/ticker-posts

Qur’anic Convention: Haduwa Da ‘Yan Bidi’a

QUR’ANIC CONVENTION: HAƊUWA DA ‘YAN BIDI’A

Lallai abu ne sananne cewa; yana daga cikin Manhajin Salaf, Ahlus Sunnati wal Jama’a kaurace wa ‘yan Bidi’a. An ruwaito hakan daga gare su, kamar yadda muka gabatar a rubutunmu mai taken: “Me ya sa Izala ta ware Masallatai?”. A ciki mun kawo maganganun Salaf, wadanda suke nuni ga Manhajinsu na kyamar ‘yan Bidi’a, da kaurace musu.

To kasancewar ‘yan Bidi’a Sufaye suna cikin bangarorin wannan taro, na “Qur’anic Convention”, kamar yadda Izala take ciki, wannan ya sa wasu masu sukar taron suna kafa wa Izala kusa da cewa; cakuduwa da ‘yan Bidi’a ya saba Manhajin Izala, don daga cikin Manhajin Ahlus Sunna akwai kyamar ‘yan Bidi’a, da kaurace musu.

To amma sai dai Malamai sun yi kokarin fahimtar hikimar wannan kauracewa da aka ruwaito daga Salaf, inda suka samu cewa; Salaf suna kaurace wa ‘yan Bidi’a ne saboda abubuwa biyu:

1- Don horo da ladabtarwa ga ‘yan Bidi’ar, don su tuba, su gyara, su dawo tafarkin Sunna, su hadu tare da Jama’a.

2- Don kada mutum ya tasirantu da su, don idan ya cudanya da su, to za su jefa masa shubuhohin Bidi’o’insu.

To idan an lura za a ga wadannan manufofi biyu duka suna komawa ne ga Maslahar kare Addini. Saboda haka Malamai sun fitar da wadannan manufofi ne don amfani da su wajen gano hukuncin kauracewar. Don haka sai a ce: idan za a samu wannar Maslaha to za a kaurace musu. Idan kuma ba za a samu Maslahar ba, ko idan an kaurace musu barna za a samu, to bai halasta a kaurace musu ba. Shi ya sa Ibnu Abdilbarr yana magana a kan Hadisin kaurace wa Ka’ab bn Malik (ra) sai ya ce:

"وفي حديث كعب هذا دليل على أنه جائز أن يهجر المرء أخاه إذا بدت له منه بدعة أو فاحشة، يرجو أن يكون هجرانه تأديبا له وزجرا عنها...

ولا هجرة إلا لمن ترجو تأديبه بها، أو تخاف من شره في بدعة أو غيرها".

التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (6/ 118 - 119)

“A cikin wannan Hadisi na Ka’ab akwai dalili a kan cewa; ya halasta mutum ya kaurace wa dan’uwansa, idan Bidi’a ko alfasha ta bayyana daga gare shi, zai kaurace masa da fatan hakan ya zama masa ladabtarwa da tsawatarwa a kanta…

Amma ba a kauracewa sai ga wanda kake fatan zai ladabtu da kauracewan, ko kake tsoron sharrinsa a Bidi’ar tasa (na shubuhohi), ko wanin hakan”.

To ka ga wannan bayani sai ya nuna cewa; idan kauracewan ba zai amfani dan Bidi’ar ya ladabtar da shi ba, kuma ba ka tsoron sharrin shubuhohinsa, to babu bukatar kauracewar ma.

Wannan ne ma ya sa Malamai suke banbance ‘yan Bidi’ar, tsakanin mai bayyana bidi’ar tasa, mai kira gare ta, wanda yake yada shubuhohi da ake tsoron idan an cudanya da shi zai cutar da mutane da shubuhohin nasa, da kuma mai boye bidi’ar tasa, wanda ba shi da wani hatsari ko barazana ga mutane.

To shi wanda bai zama barazana ba, idan ba zai ladabtu ba, to babu wata Maslaha wajen kaurace masa.

Amma na farkon, mai yada shubuhohi shi dole gama-garin mutane su kiyayi cudanya da shi. Ga tafsili daga Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya kamar haka:

"رأى المسلمون أن يهجروا من ظهرت عليه علامات الزيغ، من المظهرين للبدع الداعين إليها، والمظهرين للكبائر. فأما من كان مستترا بمعصية، أو مسرا لبدعة غير مكفرة، فإن هذا لا يهجر، وإنما يهجر الداعي إلى البدعة؛ إذ الهجر نوع من العقوبة، وإنما يعاقب من أظهر المعصية قولا أو عملا. وأما من أظهر لنا خيرا فإنا نقبل علانيته ونكل سريرته إلى الله تعالى".

مجموع الفتاوى (24/ 175)

“Musulmai suna ganin za a kaurace wa duk wanda alamomin karkacewa suka bayyana daga gare shi, cikin masu bayyana Bidi’a, masu kira gare ta, da masu bayyana kaba’ira. Amma wanda ya kasance mai boye sabo, ko mai boye Bidi’a, ba ta kafirci ba, to lallai wannan ba za a kaurace masa ba, lallai kawai ana kaurace wa mai kira ga Bidi’a ne, don kauracewan nau’i ne na horo. To horo kuma ana yinsa ne ga wanda ya bayyana sabo kadai, sawa’un na magana ne, ko aiki.

Amma duk wanda ya bayyana mana alheri, to lallai za mu karbi zahirinsa ne, mu bar badininsa ga Allah Madaukaki”.

Saboda haka, kaurace wa ‘yan Bidi’a ba a sake haka yake ba, a’a, nazartarsa ake yi, a lura da abin a zai haifar da Maslaha. Shi ya sa a wani wajen ya ce:

"الهجر يختلف باختلاف الهاجرين في قوتهم وضعفهم، وقلتهم وكثرتهم، فإن المقصود به زجر المهجور وتأديبه، ورجوع العامة عن مثل حاله. فإن كانت المصلحة في ذلك راجحة؛ بحيث يفضي هجره إلى ضعف الشر وخفيته، كان مشروعا. وإن كان لا المهجور ولا غيره يرتدع بذلك، بل يزيد الشر، والهاجر ضعيف؛ بحيث يكون مفسدة ذلك راجحة على مصلحته، لم يشرع الهجر، بل يكون التأليف لبعض الناس أنفع من الهجر. والهجر لبعض الناس أنفع من التأليف، ولهذا كان النبي صلى الله عليه وسلم يتألف قوما، ويهجر آخرين...

كل ذلك بحسب الأحوال والمصالح".

مجموع الفتاوى (28/ 206)

A nan sai ya bayyana cewa; “Su Ahlus Sunna masu kauracewan, ta yiwu su zama masu yawa, masu karfi, to sai kauracewan nasu ya samar da Maslaha.

Ta yiwu kuma su kasance ‘yan kadan, masu rauni, wanda ba lallai ba ne kauracewan nasu ya samar da Maslaha. Saboda manufar ita ce tsawatar ma wadanda za a kaurace musun, a ladabtar da su, wato ‘yan Bidi’ar.

Don haka idan an kaurace musu, za a samu Maslaha mai rinjaye, ta yadda za a raunana sharrinsu, a hana su bayyana Bidi’ar, to an shar’anta kauracewar.

Amma idan kuma kauracewar ba za ta tsawatar wa ‘yan Bidi’ar ba, kai, ta yiwu ma abin nasu ya karu, a samu mafsada mafi girma, to a nan bai halasta a kaurace musu ba, janyo su a jiki ya kamata a yi. Saboda wasu mutanen janyo su a jiki shi ne yake amfanar da su, ba kaurace musu ba. Shi ya sa Annabi (saw) yake kaurace ma wasu mutane, wasu kuma ya janyo su a jiki, ya mu’amalance su da kyautatawa, sai su gyaru..

Don haka komai ana yinsa ne gwargwadon yanayi, kuma gwargwadon yadda za a samu Maslaha”.

Saboda haka, a kaurace wa ‘yan Bidi’a dole a lura da samar da Maslaha, a lura da hali da yanayi da karfin da ake da shi.

Ma’ana; ba a kowane lokaci ne kauracewan yake zama dadai ba. Saboda akwai lokacin da rashin kauracewar shi ne ya fi Maslaha, ya fi amfani a kan kauracewar, da sauran yanayi daban-daban na halin rayuwa.

Saboda haka, da wannan za ka fahimci kuskuren wadanda suke ikirarin kuskurantar da taron “Qur’anic Convention” din, don kawai akwai haduwa da ‘yan Bidi’a Sufaye. Alhali haduwa da su din yana da halaye daban – daban, ba hali ne guda daya ba.

Kuma bayan haka, asali Allah ya umurce mu da taimakekeniya da dukkan Musulmi a kan aiyukan alheri, ya hana mu taimakekeniya a kan aiyukan sabo da zalunci. Allah ya ce:

{وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ} [المائدة: 2]

Saboda haka haduwa da dukkan Musulmai a kan aikin alheri abu ne mai kyau a Shari’a.

Kuma wani abu da mutanenmu suka kasa fahimta shi ne; duk wata mu’amala ta Gomnatin Nigeria, kuskure ne a ce Musulmai za su kaurace. Kuma idan aka ce: Musulmai, ba magana ake yi ta ‘yan Izala kadai ba, dole har da ‘yan Bidi’a. Wannan ya sa suke haduwa a Ma’aikatar Shari’ar Muslunci, suke aiki tare. Haka a Hukumar jin dadin Alhazai, da hidimar aikin Hajji. Haka a Kwamitin Musabakar Alkur’ani. Haka idan Gomnati ta neme su a wani lamari na zaman lafiya, da duk wani lamari da ya shafi Addini da malumta da maslahar al’umma. Kar ka yi zaton Gomnati za ta kira wani bangare ne, ban da wani bangaren.

Saboda haka ka’ida ita ce:

1- Wajibi ne ku zama masu aikin umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Idan kana tare da Dan Bidi’a to idan ya bayyana Bidi’ar ka zama mai yi masa inkari a kan Bidi’ar tasa.

2- Na biyu kuma ka zama mai Nasiha wa al’umma, kana tsoratar da mutane game da Bidi’a da ‘yan Bidi’ar, mutane su kiyaye su, a nuna musu cewa; ba a karbar maganarsu a Addini, saboda karkacewarsu a cikinsa.

3- Wajibi ne ka nisanci MUDAHANA, wato hadin baki da su a kan Bidi’o’insu, da shiru a kansu, da kin yi musu inkari.

Saboda haka, maganar cakuduwa da ‘yan Bidi’a ba hujja ba ce ta sukar taron “Qur’anic Convention”.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments