Bisa "Istiqra'i" da bin diddigi ga Nassoshin Shari'a Malamai sun tabbatar da cewa; hukunce - hukuncen Shari'a sun ginu ne a kan hikimomi da maslahohi, wadanda don samar da su aka shar'anta hukunce - hukuncen. Kuma Malamai suna iya gano maslahohin, sai dai a babin Ibada, ita kam ba dole a san maslahar ba.
Wannan ya sa
a kan iya yin Qiyasi, a dauki abin da babu Nassi da ya yi bayanin hukuncinsa, a
riskar da shi ga abin da Nassi ya zo ya yi bayanin hukuncinsa, saboda sun
daidaita a hikima da maslahar shar'antawa. Jumhurin Malaman Muslunci sun yarda
da Qiyasi a matsayin dalili na Shari'a, amma sai 'yan Zahiriyya suka baude,
suka yi watsi da Qiyasi, saboda su kawai suna takaita ne a kan zahirin Nassi,
ba tare da nazarin ma'anarsa don gano hikima da maslahar hukuncin da ke cikinsa
ba.
Hakan nan
suka yi watsi da Maslahohi da hikimomin Shari'a wajen shar'anta hukunci, shi ya
sa suka saba a game da dalili daga cikin dalilan Shari'a mai suna
"al-Masalihu al-Mursalah" (المصالح المرسلة), wato maslahohin da Shari'a ba ta lura da
su ba, kuma ba ta yi watsi da su ba, wato ta yi shiru a kansu, amma kuma sun
dace da manufa daga cikin manufofin Shari'a.
Wannan ne ya
kai su ga rashin banbance Ibada da Al'ada, suka zama suna mu'amalantar Al'ada
irin mu'amalar Ibada. Alhali ba babi daya suke ba, ita Al'ada da mu'amala ana
iya sanin hikima da maslahar Shari'a a cikinsu, sabanin Ibada. Wannan ya sa
suke bidi'ntar da abubuwa na Al'ada da Mu'amala. Alhali wannan babban kuskure
ne, don babin Al'ada da Mu'amala daban yake da babin Ibada.
Ibada ce
bidi'a take shiga cikinta. Amma Al'ada da Mu'amala bidi'a ba ta shiga ciki, sai
dai idan an kayyade abin da Shari'a ta sake shi, ko aka sake abin da Shari'a ta
kayyade, ko aka gindaya ma wani abu sharadin da Shari'a ba ta shardanta ba, ko
aka mayar da Al'adar ta zama Ibada tsantsa.
To a wannan
zamani da Salafiyya ta shigo Nigeria, sai wasu suka fahimce ta a matsayin
Mazhabar Zahiriyya, wacce ba ta lura da Maslaha da hikimomi da manufofin
Shari'a, sai suka rinka bidi'antar da abubuwa na Al'ada da Mu'amala, alhali su
ba muhallin Bidi'a ba ne. Sai aka wayi gari duk abin da mutum zai aikata sai a
tambaye shi, ya kawo Aya ko Hadisi, kafin a yarda ya aikata. Idan kuma babu to
sai a ce; wannan abin ya zama bidi'a.
Haka suka
kasa gane wajabcin lura da maslaha da nesantar barna wajen umurni da kyakkyawa
da inkarin munkari. Sai suka zama masu bidi'antar da masu "Ta'awuni"
da taimakekeniya da 'yan bidi'a a kan aiyukan alheri, matukar akwai maslaha
mafi rinjaye a cikin hakan. Wannan za mu fadada a kansa, a rubutu na gaba insha
Allahu.
Alhali
Bidi'a ba ta shiga cikin Al'adu da Mu'amaloli, in dai ba a mayar da ita Ibadar
ba, ko aka ketare Shari'a.
Haka kuma
"al-Masalihul Mursala" ba bidi'a ba ne. Shaikh al-Shanqity ya ce:
"فالحاصل أن الصحابة -
رضي الله عنهم - كانوا يتعلقون بالمصالح المرسلة التي لم يدل دليل على إلغائها،
ولم تعارضها مفسدة راجحة، أو مساوية. وأن جميع المذاهب يتعلق أهلها بالمصالح
المرسلة، وإن زعموا التباعد منها.
ومن تتبع وقائع الصحابة وفروع المذاهب علم صحة ذلك...
واعلم أن العمل بالمصالح المرسلة المذكور ليس تشريعا جديدا
خاليا عن دليل أصلا، بل من يعمل بها من العلماء كمالك وغيره يستند في ذلك إلى أمور:
منها: عمل الصحابة - رضي الله عنهم - بها من غير أن ينكر
منهم أحد، وهم خير أسوة.
ومنها: أنه قد علم من استقراء الشرع الكريم محافظته على
المصالح وعدم إهدارها، ولا سيما إن كانت المصلحة متمحضة، لم تستلزم مفسدة، ولم
تعارض مصلحة راجحة، ولم تصادم نصا من الوحي".
المصالح المرسلة (ضمن المحاضرات للشنقيطي) (ص: ٤٥ - ٤٦)
Sai ya
tabbatar da cewa; amfani da "al-Masalihul Mursala" ba bidi'a ba ne,
ya kuma kawo hujjoji a kansa, wato "Istqra'in" nassoshin Shari'a, da
kuma aiyukan Sahabbai.
"Al-Masalihul
Mursala" suna da sharuda kamar haka:
1) Kar ta
saba Nassin Alkur'ani ko Sunna ko Ijma'i.
2) Kada ta
saba Qiyasi.
3) Kada ta
sa a rasa maslahar da ta fi muhimmanci ko wacce take dadai da ita.
4) Dole ya
zama babu sababin yinta a zamanin Annabi (saw).
5) Dole ne
Maslahar ta zama cikin abu ne da za a iya sanin hikimarsa da manufarsa.
"Al-Masalihul
Mursala" duk da cewa sun hadu da bidi'a a wajen kasancewar kowannensu
sabon abu ne kirkirarre, amma sai dai sun rabu a abubuwa kamar haka:
1- Ita
Bidi'a a Ibada ake samunta, ita kuma "Maslaha Mursala" ana samunta ne
a al'ada da mu'amaloli.
2- Ita
Bidi'a dole a samu ta saba wa Nassi Sarihi ko Zahiri, ko Manduqi ko Mafhumi, ko
a Ummi ko khususi, sabanin "Maslaha Mursala", ba ta saba wa kowane
Nassi.
3- Ita Maslaha
tana kasancewa ne wajen janyo amfani ko kawar da barna, shi ya sa take
kasancewa a hanyoyi (Wasa'il) na wasu aiyukan Ibada, wadanda suka dace da
manyan manufofin Shari'a, da gamammun ka'idojinta, sabanin Bidi'a wacce mai ita
yake zaton tana da amfani, alhali cutar da shi take yi a Addininsa. Kuma dole a
samu ta saba manufofin Shari'a.
Don haka
dole mutane suna bukatar kirkirar sababbin abubuwa da suke ganin akwai maslaha
da amfani a cikinsu, don haka idan a al'ada da mu'amala ne, da kuma hanyoyin
Ibada (Wasa'il) to babu laifi. Ga yadda ka'idar take, Shaikhul Islami ya yi
bayani kamar haka:
"إن الناس لا يحدثون
شيئا إلا لأنهم يرونه مصلحة، إذ لو اعتقدوه مفسدة لم يحدثوه، فإنه لا يدعو إليه
عقل ولا دين. فما رآه الناس مصلحة نظر في السبب المحوج إليه، فإن كان السبب المحوج
إليه أمرا حدث بعد النبي صلى الله عليه وسلم من غير تفريط منا، فهنا قد يكون إحداث
ما تدعو الحاجة إليه، وكذلك إن كان المقتضي لفعله قائما على عهد رسول الله - صلى
الله عليه وسلم -، لكن تركه النبي - صلى الله عليه وسلم - لعارض زال بموته.
وأما ما لم يحدث سببا يحوج إليه، أو كان السبب المحوج إليه
بعض ذنوب العباد، فهنا لا يجوز الإحداث".
اقتضاء الصراط المستقيم (٢/ ٥٩٨).
Sai ya
bayyana cewa; duk abin da mutane suke ganin akwai Maslaha a cikinsa, to sai a
duba sababin bukatuwa gare shi, idan akwai sababin a zamanin Annabi {saw}, kuma
babu abin da ya hana shi yi, to a nan ba za a kirkiri abin ba. Saboda babu
Maslaha a cikinsa, kamar Maulidi.
Amma idan
babu sababin bukatuwa gare shi a zamanin Annabi (saw), ko akwai, amma wani abu
ya hana shi yin aiki da shi, amma bayan rasuwarsa sai abin da ya hana shin ya
kauce, to ya halasta a yi amfani da shi, kuma ba bidi'a ba ne, Maslaha ne.
Abin nufi
shi ne ka dauki wadannan sharuda na "al-Masalihul Mursala" da
banbance - banbance tsakaninta da Bidi'a ka dora su a kan Qur'anic Convention,
Makon Sahabbai da sauransu, don ka fahimci kuskuren masu bidi'antar da tarukan
biyu da makamantansu.
A takaice
wannan abin da muke gani daga masu ikirarin bin Salafiyya, na bidi'antar da
"Makon Sahabbai", "Qur'anic Convention", "Taron daurin
aure", "Musabakar Alkur'ani" da sauransu, duka wannan ba
Salafiyya ba ne, Zahiriyyanci ne. Zahiriyyanci kuwa Mazhabi ne da ya saba
Mazhabar A'imman Salafiyya, irin su Imamu Malik, Shafi'iy, Ahmad. Kai, aiki da
"al-Masalihul Mursala" Mazhaba ce ta Sahabbai, da shi aka tattara
Alkur'ani, da shi Sayyidina Usman (ra) ya kona "Masahif", ya tattara
mutane a kan Mushafi guda daya. Da shi Tabi'ai suka dawwana ilmomin Shari'a, da
ka'idojin Larabci. Karanta al-Li'itisam na al-Shadibiy, ko "al-Masalihul
Mursalah" na al-Shanqidiy, ko wasunsu don ganin Misalai a kan haka.
Daga cikin
kuskuren masu ikrarin Salafiyya alhali Mazhabar Zahiriyya suke bi, akwai watsi
da ilimin Fiqhun Mazhabobi. Suka ce ba ruwansu da Mazhaba, ba ruwansu da
karatun littatafan Fiqhu, su dai sai Hadisi zalla. Suka wayi gari ba su san
"Usul Fiqh" ba, ba su san Fiqhu ba, ba su damu da shi ba. Alhali
wannan kuskure ne mai girma, shi ya sa idan suka yi Fatawa, ko suka yanke
hukunci, sai ka ga ya saba tafarkin Malamai.
Kuma saboda
mu abin da muka gani shi ne jagororin Salafiyya a wannan zamani duka Malaman
Fiqhu ne, kuma suna bin Mazhaba. Irin su Shaikh Ibnu Ibrahim Alu-Shaikh, Shaikh
Ibnu Si'idiy, Shaikh Ibnu Baaz, Shaikh Ibnu Uthaimeen da ire-irensu, da
almajiransu.
Abin nufi
shi ne; yanke hukuncin Bidi'a a kan taruka na Al'ada, ko abubuwa na Maslahohi
"Mursala" ba Salafiyyanci ba ne, Zahiriyyanci ne.
Saboda haka,
asali Salafiyya ita ce riko da Akidar Salaf, Ahlus Sunnati wal Jama'a, ba bin
Zahiriyya ba. Shi ya sa a Fiqhu Malik ya saba wa Abu Hanifa, Shafi'iy ya saba
wa Malik, Ahmad ya saba wa Shafi'iy, amma duka Akidarsu iri daya ce, sun yi
ittifaqi a kan Akidar Salaf. Kai, su ne ma jagororin Salafiyyar.
Saboda haka
Salafiyya daban, guluwwi a bidi'antarwa daban.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.