Duk da cewa; tun farko Sufanci ya faro ne daga karkacewar masu son yin Zuhudu, a lokacin da suka cakuda shi da Bidi'o'i da Almarori, to saboda karkacewa daga Tafarkin Sunna da Shari'a a Zuhudu sai kuma karkacewar ta yi ta karuwa karuwa mai yawa kuma mai matukar muni, ta yadda sai da aka wayi gari ya cika da munanan Aqidu da Ilhadin 'Yan Falsafa da Kafircin Kiristoci.
Daga cikin
mummunan karkacewa da Sufanci ya yi, Kiristanci ya yi tasiri a cikinsa, saboda
cakuduwar Sufayen da Kiristoci masu bauta a Kasar Sham, inda suka fara sanya
tufafi irin nasu, da wasu kayayyakin sawa a jiki da masu bautan Kiristocin suke
amfani da su. Da "uzla" kauracewa wa mutane, da "khalwa",
da kin aure, da sauran abubuwa da Kiristoci suke yi na Ruhbananci da suka
kirkira.
Haka suka
dauki Aqidar "Hululi" (Allah yana shiga jikin halittu) daga
Kiristoci, kamar yadda Hallaj ya shigo da ita cikin Sufancin, da kuma Aqidar
"Ittihadi" (KOMAI ALLAH NE), kamar yadda Ibnu Arabiy da sauran
abokansa suka shigo da su.
Haka kuma
suka fara amfani da Kalmomin Kiristanci, kamar; "Lahuut",
"Nasuut", "Rahbuut" da sauransu.
Wani babban
Shehin Sufaye, Dr. Abul Wafa'i Al-Taftazaniy ya ce:
فنحن لا ننكر تأثر بعض الصوفية المتفلسفين بالمسيحية، على
نحو ما نجد عند الحلاج الذي استخدم في تصوفه اصطلاحات مسيحية كالكلمة واللاهوت
والناسوت وما إليها
مدخل إلى التصوف الإسلامي (ص: 29)
"Mu ba
ma inkarin tasirantuwar wasu Sufaye 'Yan Falsafa da Kiristanci, kamar yadda
muka samu a wajen Hallaj, wanda ya yi amfani da ma'anonin Kiristanci a cikin
Sufancinsa, kamar "Kalma" (Kiristoci suna cewa; kalmar Allah ce ta
shiga jikin Annabi Isa (AS)), "Lahuut", "Nasuut" da
makamantansu".
Kai hatta
Aqidar Trinity (Allah uku) ta Kiristoci an samu a cikin Sufanci, inda Ibnu
Arabiy ya ce:
تثلَّثَ محبوبي وقد كان واحداً * كما صير الأقنام بالذات
أقنما
Haka Sufanci
ya tasirantu da Falsafar Hindu da ta Farisanci, ta hanyar Saharawardiy, wanda
ya shigar da Falsafar gabashi cikin Sufancin. Inda suka shigar da abin da ya
shafi "Ruhanai", da "Tanasukh", da sauransu.
Babban
Shehin Sufaye, Mahmud Abul Faidh Al-Manufiy ya tabbatar da haka inda ya ce:
وأكثر الصوفية الأعاجم خلطوا بين الفلسفة الفارسية القديمة
أو الهندية وما قبسوه عن اليونانية والأفلاطونية الحديثة وبين تصوفهم الخاص، وقد
تأثر أمثال أولئك ببراهمة الهند والفرس في أزيائهم وطقوسهم، واعتنقوا من أفكارهم
جمهرة الأولياء وأعلام أهل التصوف
(1/ 266 - 267).
"Mafiya
yawan Sufaye Ajamawa sun cakuda tsohuwar Falsafar Farisa ko Falsafar Hindu, da
abin da suka tsakuro daga Falsafar Girka da sabuwar Falsafar Plato, sun cakuda
su da Sufancinsu. Kuma irin wadannan Sufaye sun tasirantu da Barahiman Hindu da
Farisawa a tufafinsu (na Sufanci) da aiyukan Ibadunsu, kuma suka rungumi
tunaninsu".
Haka
Falsafar Girka ta yi tasiri cikin Sufanci, ta hanyar sabuwar Falsafa Plato,
inda suka dauko Aqidar "Wahdatul Wujudi" (KOMAI ALLAH NE) da
nazariyyar "Faira" daga gare shi.
Babban
Shehin Sufaye, Dr. Abul Wafa'i Al-Taftazaniy ya ce:
ونحن لا ننكر الأثر اليوناني على التصوف الإسلامي، فقد وصلت
الفلسفة اليونانية عامة، والأفلاطونية المحدثة خاصة، إلى صوفية الإسلام عن طريق
الترجمة والنقل، أو الاختلاط مع رهبان النصارى في الرها وحران. وقد خضع المسلمون
لسلطان أرسطو، وإن كانوا قد عرفوا فلسفة أرسطو على أنها فلسفة إشراقية، لأن عبد
المسيح بن ناعمة الحمصي حينما ترجم الكتاب المعروف بـ (أثولوجيا أرسطو طاليس) قدمه
إلى المسلمين على أن لأرسطو على حين أنه مقتطفات من تاسوعات أفلوطين.
وليس من شك في أن فلسفة أفلوطين السكندري التي تعتبر أن
المعرفة مدركة بالمشاهدة في حال الغيبة عن النفس وعن العالم المحسوس، كان لها
أثرها في التصوف الإسلامي فيما نجده من كلام متفلسفي الصوفية عن المعرفة. وكذلك،
كان لنظرية أفلوطين السكندري في الفيض وترتيب الموجودات عن الواحد أو الأول، أثرها
على الصوفية المتفلسفين من أصحاب الوحدة كالسهروردي المقتول، ومحيي الدين بن عربي،
وابن الفارض، وعبد الخالق بن سبعين، وعبد الكريم الجيلي، ومن نحا نحوهم.
ونلاحظ بعد ذلك أن أولئك المتفلسفة من الصوفية نتيجة
اطلاعهم على الفلسفة اليونانية قد اصطنعوا كثيرا من مصطلحات هذه الفلسفة مثل:
الكلمة – العقل الأول - العقل الكلي – العلة والمعلول... إلخ
مدخل إلى التصوف الإسلامي (ص: 33 - 34)
"Mu ba
ma inkarin tasirin Falsafar Girka a cikin Sufancin Musulmai, saboda gamayyar
Falsafar Girka da sabuwar Falsafar Plato a kebance sun isa ga Sufancin Musulmai
ta hanyar tarjama da nakaltowa, ko kuma ta hanyar cakuduwa da masu bautan
Kiristoci a garin Şanlıurfa da Harran (garuruwa ne da a yanzu suke Kasar
Turkey...".
A takaice
sakon da muke so mu isar ga al'ummar Musulmi shi ne; Wannan Sufancin da muke
gani a yau, ba shi da alaka da Muslunci, saboda ga shi mun ga inda aka tattaro
shi. Munanan Aqidu ne aka harhado su daga Falsafar Girka da ta Hindu da ta
Farisa da kuma Addinin Kiristanci.
Saboda haka
muna kira ga mabiya Sufanci su yi bincike, don kar su mutu a kan wannan
mummunan tafarki da suke kai.
Allah ya yi
mana tsari da bata.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.